Thursday, May 3, 2012


FADE IN:
EXT. eSTABLISHMENT SHOT kauyen badole - nIGHT
Babu haske ko ina, sai tsalli-tsalli. Garin yayi tsit alamar dare yayi nisa, ba a jin motsin komai sai na kukan gyare da sauran kwari.
DISSOLVE TO:
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - nIGHT
Wajen cikin hasken farin wata. Kayan aikin gida a killace.
AMINU
Mai shekaru (30-32) yana kwance kan wata tabarma yana bacci.
Garba mai Angara mafarauci (50-55) mahaifin Aminu, akwance yana bacci, yana motsawa akai-akai alamun yana mafarki.
MATCH CUT TO:
EXT. cIKIN DAJI - eVENING
Wani maciji na gudu yana neman tsira.
GARBA/aminu
Suna biye da shi. Garba ne a gaba, Aminu na biye.
Macijin ya bace. Suka tsaya suna neman inda ya bi. Garba yayi shiru kamar yana shinshina wani abu.
GARBA
Aminu.
AMINU
Na'am, Baba.
Idanun Garba na kallon wata tarin kasa da ke daga dan nesa da inda suka a tsaye.
GARBA
Maza daukomin Angara ta, a inda muka zauna.
Aminu ya juya a guje ya tafi. Garba ya jira, har sai da ya daina jin motsin Aminu, sannan ba tare da ya dauke idanunsa daga kan tarin kasar ba, ya cire Dagar da ke dantsensa, ya ajiye a kasa sannan ya fito da wani kullin magani, ya rintse idanuwansa kafin ya bada akan Dagar. Wani irin hayaki ya tashi a wajen.
Garba ya bude idanuwansa, sai ya hangi Macijin na gudu zuwa wajen buya. Garba ya bi macijin, yana isa wajen sai ya ga ramin da mcijin ya shiga, ya tsaya a bakin ramin yana kallo.
Sannan ya zaro wata sharbebiyar kuka daga kundukukinsa ya kafta a cikin ramin. Jini ya fallatsa a gefen wuyan Garba.
Nan da nan dajin ya cika da wata irin kara da hargowa.
BACK TO:
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - nIGHT
GARBA
Yayi zumbur ya tashi zaune, duk jikinsa ya jike da gumi.
Yayi shiru yana mamaki, sannan ya juya ya kalli Aminu wanda yake ta sharar baccinsa ba tare da yasan halin da Garba ke ciki ba. Garba har yanzu yayi shiru yana mamakin abin da ya gani a mafarki. Daga bayan fage, aka fara kiran salla.
FADE TO:
EXT. garin badole (dandaLI) - MORNING
Matsakaicin gari a karkara. Kai da kawon mutane kowa na harkokinsa. Masu kayan saye da sayarwa kowa ya kasa nasa.
Gindin bishiya a kishingide, Garba Mai angara ne, sanye da riga 'yar shara, yana hutawa. Wata yarinya mai tallar Dinkin tazo zata wuce Garba ya kira ta, ta zo ta durkusa ta sauke.
GARBA
Bani na hamsin.
Yarinya i
He dai na murtala uku.
GARBA
Cikin sakin fuska
Dalili?
YARINYA I
Kahin ahirin ahirin ne.
Garba yana fara'a
GARBA
To ki sayarmin uku hamsin din mana.
Yarinya ta girgiza kanta.
YARINYA I
A gida za'a yimin fada.
Garba ya karkace ya dauko kudin ya mika mata
GARBA
Ga naira sittin Ba zan so a yi miki fada a gida ba.
Yarinya ta nuna jin dadinta ta saka a cikin leda ta baiwa Garba wanda ke kallonta cikin sakin fuska yana mai mamakin wayon yarinyar. Sannan ta dauki kayanta ta yi gaba.
Garba Ya bita da kallo, murmushin fuskarsa ya gushe saboda Hango dan sa Aminu (32-35) ya nufo wajensa cikin yanayi na tashin hankali.
Garba yayi maza ya tashi zaune tun kafin Aminu ya karaso wajensa.
GARBA (CONT'D)
Lafiya, Aminu?
AMINU
Rashin lafiyar Mairo ne ya tashi Abba.
Nan da nan suka mike tare, Aminu na karbar ledar Dinkin din kafin su nufi hanyar zuwa gida da Aminu cikin gaggawa.
Wani matashi ya kira yarinyar mai Dinkin yana saya.
YARINYA I
Ahirin ahirin.
Matashi
Kin sayar biyu talatin?
Ta yi jim tana juya dinkin din.
YARINYA I
Talatin da biyar.
MATASHI
Ya juya kamar zai tafi
Ke ina da bin yi. In kin sayar haka, na biya.
Ya fara tafiya, yarinyar tayi maza ta kira shi.
YARINYA I
Kawo kudin.
Tana kokarin sanya masa a leda.
INT. gIDAN GARBA (cikin daki) - mORNING
Dakin cikin matsakaicin haske, wani kwanon sha a rufe dauke da ruwan jikon magani a ciki. Wani hayaki na turara dakin mai dauke da kaya ko shirgi irin na dattijuwar mace.
Laraba, mahaifiyar Aminu, na rungume da Mairo, (22-24) wadda gumi ke bin fuskarta tana numfarfashi da yin yunkuri a lokaci guda. Wata irin dafara na fitowa daga bakinta.
Garba na gaba Aminu na biye da shi, suka shigo dakin a sukwane cikin yanayi na tashin hankali. Garba ya durkusa gaban mara lafiyar.
GARBA
Ya fara addu'a yana tofawa Mairo a fuska, da sauran jikinta.
Aminu
Yana tsaye cikin yanayi na karin damuwa tare da tausayawa Mairo na halin da ke ta ciki.
LaRABA
Mikomin kwanon shan nan na bata jikon maganin da ke ciki.
Aminu ya dauko ya mika mata, ta karba tana baiwa Mairo wadda jikinta ya fara sauki har ya zuwa lokacin da ta fara bacci. 
GARBA
Ki rinka yawaita karanta mata ayoyin al'kur'ani, a duk lokaci da kika ga alamun ciwon zai tashi.
Garba yayi jim yana kallonta kafin ya mike tsaye cikin sanyin jiki suka nufi kofa tare da Aminu.
EXT. gIDAN garba (TSAKAR GIDA) - mORNING
Kayan farauta a ma'ajiyarsu da sauran kayan aikin gida barbaje ko ina.
Garba ya fara fitowa daga dakin, Aminu na biye da shi.
GARBA
Aminu.
AMINU
Na'am, Abba.
Garba ya dan yi jim kamar yana tunani kafin yayi ajiyar zuciya ya kalli Aminu.
GARBA
Ka kula da rashin lafiyar yarinyar nan. Bacin rai ko akasin haka kan iya tayar da ciwon.
Aminu yayi shiru alamar girmama maganar. Laraba ta fito ta nufi wajen Randar ruwa zata diba. Garba ya juya ya kalle ta.
GARBA (CONT'D)
Yaya kika fito?
LARABA
Bacci ya dauke ta.
FADE TO BLACK.
Opening Credit on Blank Screen
EXT. establishment shot kauyen cima - eVENING
Rana ta yi ja, tana daf da faduwa. Haskenta na haska kusan ko ina na kauyen Cima mai 'yan gidaje tsalli-tsalli.
DISSOLVE TO:
EXT. gidan su unaiza (tsakar gida) - eVENING
Gida ne matsakaici mai dakuna dabam dabam. Kayan aikin gida kowanne a mazauninsa. Wata tsohuwar kwatanniya daga gefe an rufe bakinta da wani tsohon faifai.
Nishin wata yarinya na fitowa ta daya daga cikin dakunan da ke gidan.
Int. GiDAN SU UNAIZA (cikin daki) - eVENING
Matsakaicin daki ne na babbar mace. Mahaifin su Unaiza da mahaifyarta suna rike da karamar kanwar Unaiza, Gazah, wadda ke cikin wata irin rashin lafiya tana numfarfashi da yin yunkuri a lokaci guda. Ta hada gumi kamar an zuba mata ruwa.
Lambai
(Cikin yarensu)
Bata iska, Tumano!
Ya kalli matarsa da ke tsaye kusa da kan yarinyar.
Tumano
Fuskarta dauke da damuwa
(Cikin yarensu)
Ban ce ta fita ba, Yanzu gata cikin larura.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (TSAKAR GIDA) - eVENING
Unaiza
Mai shekaru (22-24) ta shigo dauke da kayan itace ta jefar. Hankalinta ya kai ga jin nishin da 'yar uwarta ta ke yi.
INT. gIDAN SU UNAIZA (CIKIN DAKI) - eVENING
Unaiza ta fado cikin yanayin damuwa, ta kalli mahaifyarta.
TUMANO
Unaiza, kinga jikinta ko?
Unaiza
Mama yaya aka yi haka?
Tumano ta fara jujjuya hannu cikin yanayin gazawa. Lambai yana rike da yarinyar da ya yi mata wani surkulle ya kalli Unaiza fuskarsa dauke da damuwa.
LAmBAi
Unaiza.
UNAIZA
Baba.
Ta gurfana a gabansa shi da yarinyar tana kallonta.
LAMBAI
Zan fada miki wasu magunguna ki koma dawa, maza ki debomin su na hada mata sinadarin ciwon.
UNAIZA
Ina jinka, Baba.
Tana yiwa yarinyar abubuwan al'ada cikin yanayin karin damuwa har Tumano ta matso kusa da su ta tsaya. Lambai na ci gaba da abin da ya ke yi.
TUMANO
Har ta je ta dawo? Yamma fa ta yi.
LAMBAI
Har ta je ta komo.
Ya kalli Unaiza
Bishiyoyin da na nuna miki da saiwar itaciyar nan (ya kwantata mata wajen) su zaki je ki kawomin.
Unaiza ta mike da gurfanar da tayi.
UNAIZA
To Abba.
EXT. cikin daji - eVENING
Garba Mai angara na gaba sanye da kayan farauta. Aminu na biye dashi rike da wasu kayan farautar.
Garba ya hangi wata dabba, yayi kamar bai ganta ba.
Aminu ya hange ta shima ya fara fakonta. Har zai kai mata harbi, Garba ya kabe makamin Aminu.
Garba
Ba kowane abu ne dabba ba.
Aminu yayi shiru yana kallon mahaifinsa cikin mamakin jin abin da ya ce masa. Garba ya juya yayi gaba.
Aminu ya kalli inda dabbar take sai ya ga babu komai.
EXT. cikin DAJI (wajen bishiyoyi) - eVENING
Unaiza a jikin wata bishiya tana tsinkar irin ganyayen da babanta ya fada mata cikin gaggawa daga wata bishiyar zuwa wata.
Ta bar nan zuwa wanu sashin, inda ta tsaya tana kokarin tuna daidai wajen da ta ke nema. Tayi jim cikin yanayi na zakuwa, kafin ta dauko wani kulli ta bada a wajen, wani hayaki ya tashi sama.
UNAIZA
Ta yi dan karamin murmushi, hayakin na ci gaba da karuwa.
EXT. cIKIN DAJI - eVENING
Aminu yayi hasashen hayakin, yayi sassarfa, kana ya juya ya kalli wajen bangaren da hayakin ke tashi ya nufi wajen. Garba ya juyo gareshi.
GARBA
Aminu!
Aminu ya saurara ya waigo
Aminu
Hayaki, Abba.
Gaba dayansu suka nufi wajen da hayakin ya ke tashi da sauri.
EXT. cIKIN DAJI (WAJEN BISHIYOYI) - eVENING
Unaiza a tsugune daidai wajen da hayakin ya ke tashi. Wata saiwa ta fito. Ta yi wani karatu a boye tana mai hura hannunta sannan ta yi maza ta ciri saiwar.
Jin alamar motsin takun sawun mutane, yasa ta tayi maza ta buda wani gari. Nan da nan ta bace.
Garba da Aminu suka karaso wajen suna waige/duba wajen.
AMINU
Kamar na ga mutum anan?
GARBA
Mece ce, ta kuma bar wajen.
AMINU
Ta bata.
Garba yayi jim yana kallon Aminu cikin mamakin jin abin da ya fada. motsi ko jin kukan wata dabbar yasa suka nufi wajen da suka ji gaba daya.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (TSAKAR GIDA) - eVENING
TUMANO
Ta dauko kokon ta zo ta bude kwatanniyar ta kifa shi a ciki, sannan ta kanfato ruwan, ta je ta zubar da kadan a gindin bandaki sannan ta nufi cikin dakin.
INT. gIDAN SU UNAIZA (CIKIN DAKI) - eVENING
Gazah ta gama galabaita. Har yanzu Lambai na kokarin shawo kan ciwon. Tumano ta shigo da kokon.
TUMANO
Gashi.
Lambai ya mika hannu ta bashi, ya ajiye a kusa da yarinyar. Babu dadewa Unaiza ta shigo dauke da abubuwan da ta debo.
TUMANO (CONT'D)
Kin dawo?
UNAIZA
Na dawo.
Lambai ya karba kafin ya kalleta cikin shakku.
LAMBAI
Ba su tarar da ke ba?
UNAIZA
Kafin su iso, na kaucewa ganinsu.
Ya nuna alamar gamsuwa ya karba ya hada guri guda, sannan ya fara tsomawa a cikin ruwan kokon da Tumano ta ajiye masa, yana yarfawa Gazah wadda nan da nan ta fara atishawa.
Murmushi ya bayyana a fuskokin Unaiza da Tumano daidai lokacin da Gazah ta tashi zaune.
TUMANO
Gazah, sannu.
Gazah
Ta dan motsa a hankali
Yauwa.
EXT. gidan garba (tsakar gida) - eVENING
Tunkuyar sanwa akan wuta, wasu butocin alwala guda biyu a kusa da inda randar ruwa take.
Laraba tana girki. Mairo daga gefe akan shimfida tana tankade garin tuwo, ta gama ta dauko ta zo ta kawowa Laraba.
Mairo
Umma, gashi.
Laraba
To, sannunki, Mairo.
Ta karba ta zata yi rude, Mairo kuma ta nufi wajen da sauran kayayyaki suke dan kintsa su. Garba da Aminu suka yi sallama, suka shigo. Aminu rataye da jaka mai dauke da abin da suka samo a daji. Mairo ta tashi da sauri ta karbi jakar.
Mairo
Abba, Yaya Aminu, sannunku da zuwa.
Laraba ta yi musu sannu da zuwa tana mai ci gaba da abin da ta ke yi. Suka amsa mata. Garba ya kalli Mairo cikin fara'a.
GARBA
Wato yau da yake yayanki ne, ke dauke da jakar, sai baki barshi da ita ba. Amma a jiya, sai da na tamabaye ki tukuna kika fito daga daki.
Mairo
Abba ai lokacin ina sallar magariba ka shigo da yake kai kadai ka je. Yau kuwa da kuka tafi tare da Yaya, gashi kun dawo da wuri.
GARBA
Amma kuwa ai yau dawa ba ta yi nama ba, da yake shi ya jagoranci farautar.Idan Allah Ya kai mu gobe, har da ke za mu tafi, ke kuma na ga na ki kokarin.
Suka yi dariya kafin Garba ya nufi wajen bandaki, Aminu kuma ya je ya ajiye sauran kayan da suke kafadarsa. Mairo na biye da shi kusa da kusa.
Mairo
Yaya, yau tare na ke son muje dandali.
AMINU
Me yasa, Mairo?
Cikin fara'a yana kallonta
Mairo
Fuskarta cikin wani irin murmsuhi
Kowace yarinya zata je da saurayinta. Ni kuma bani da saurayi.
AMINU
Yana ci gaba da abin da ya ke yi
Ke ce ai. Kin ki ki baiwa Jabbi dan gidan Baffa Bello kai. Kuma ya dade yana nuna miki yana son ki.
Mairo ta dan sauya fuska tana kallonsa
Mairo
Ni mutunci ne tsakaninmu.
AMINU
Yayi 'yar dariya yana mai nufar wajen da buta take.
Ai daman mutunci shine ginshikin kowace amintacciyar soyayya mai dorewa.
Kafin ya dauki butar, Mairo ta riga shi ta fara zuba masa ruwan yin alwala.
Mairo
Don Allah Yaya Aminu ka bar wannan zancen.
Ta gama zubawa ta mika masa
Kuma koda ma ina da shi kai nake so muje tare, don in ba kafi kowa a waje na ba, to kuwa babu wanda zai zarta ka a cikin zuciya ta.
Aminu ya yi jim cikin nuna mamakin abin da ta fada, yayin da sautin kiran salla ya fara ratsowa cikin gidan, daidai fitowar Garba daga bandaki.
Mairo (CONT'D)
Ta tsare shi da ido
Zamu je ko kuwa a'a?
EXT. garin badole (dandali) - nIGHT
Amon kidan na tashi. Masu kayan ciye-ciye, da sauran kayan sayarwa ko ina.
Aminu tare da sauran mutane sun  yi da'ira suna kallon kalangun da ake yi, yan mata na rawa. A tsakiyar fage tare da sauran 'yan mata, Mairo ce tana rera wata waka mai dadi.
Jabbi ya nufo wajen ya hangi Aminu yayi wajensa.
Mairo
Tana ci gaba da waka cikin fara'a tana mai nuni zuwa wajen bangaren da Aminu ya ke a tsaye.
Jabbi ya taba Aminu yayi masa sallama, Aminu ya juyo suka gaisa daidai lokacin da Mairo ke bukatar Aminu ya kallo wajenta.
Aminu suka gaisa cikin raha.
AMINU
Ai nasan sai kazo, ko dan saboda Mairo.
Suka yi dariya suka tafa cikin raha.
Jabbi
Yana murmushi
Naje gida ne, aka ce kun taho nan shi yasa na biyo ku.
AMINU
To zan fada mata na ce ba dan ita ka zo ba.
JABBI
Ka rufa min asiri, sai ta yi fushi.
Suka sake yin dariya cikin raha.
AMINU
In dai ba ka son na fada to ka shiga ka yi liki.
JABBI
Sai dai muje tare.
AMINU
Ai ni yayanta ne.
JABBI
To nima zan fada mata cewa yayanta yace ba ta cancanci ayi mata liki ba.
AMINU
A'a, to mu shiga.
Suna dariya suka shiga cikin fage tare suna yiwa Mairo liki.
Mutane aka rude da shewa da Guda. Fuskar Mairo cikin nuna jin dadin abin da suka yi mata.
Aminu da Jabbi suka fita daga fage, Mairo ta bisu cikin nuna jin dadinta, suka nufi hanyar gida, yayin da kidan ke ci gaba.
EXT. gIDAN GARBA (kofar gida) - nIGHT
Daga nesa a bayan fage, amon kidan na ratsowa. Suka iso kofar gidan tare. Za su shiga Jabbi ya dakata, su ma suka saurara.
Mairo
Ba za ka shiga ba?
JABBI
Sai da na zo nan kafin na tarar da ku a dandali.
Aminu ya saci kallon Mairo yana yi mata dariya ta dan daure fuska.
AMINU
Ni zan shiga ciki. In zaka wuce sai ka yimin magana na zo na raka ka.
JABBI
Ai ba dadewa zan yi ba. Nazo ne mu gaisa.
AMINU
Cikin raha yana nuna Jabbi
Fadi gaskiyarka na daure.
JABBI
A sake ni, Aminu.
AMINU
An sake ka.
Suka kwashe da dariya gaba dayansu, Aminu ya juya ya shiga ciki. Mairo ta dada nutsuwa ita da Jabbi suka ci gaba da hira.
JAbBI
Ranar juma'a kika ce za ki zo shiru. Har Janne na cewa zata zo.
Mairo ta dan yi murmushi cikin kawaici.
Mairo
Ai gobe za mu zo tare da su Abba. Daga nan zan biyo ta wajen.
JABBI
Kice gobe Janne na da bakuwa.
Mairo
Cikin raha ta kalle shi
Au kana nufin ban da kai?
JABBI
Ni, na isa?
Suka yi 'yar dariya gaba dayansu.
EXT. kauYEN badole (bayan gari) - mORNING
Wasu mata dauke da kunshin kayan su, na shiga garin.
GARBA/aminu/Mairo
Sun fito daga cikin garin, sun nufi cikin dajin.
EXT. gidan baffa bello (tsakar gida) - mORNING
Janne (26-28) tana hada kayan koran tallar Nono waje daya. Mahaifiyarta, Inna wuro, ta fito daga daki ta tsaya tana mamakin ganin abin da ta yi. Ta debi koran ta je ta ajiye. Inna wuro ta bita da kallo
INNA WURO
(Cikin fillanci) Janne yau ba za kije kasuwa ba ne?
JANNE
(Cikin fillanci) Mairo na zuwa yau.
INNA WURO
(Cikin fillanci) Allah Yasa. Don haka rannan kika ki zuwa kasuwa kina jiranta, amma ba ta zo ba.
Janne ta koma yin wani abin.
JANNE
(Cikin fillanci) Mai yiwuwa tare da Aminu za su zo.
Inna wuro ta yi jim kafin ta nufi wajen kayan abinci.
Inna wuro
(Cikin fillanci) Sai kiyi maza saboda akwai sakon da za ki je ki kaiwa Baffanku.
Janne ta yi jim, Inn wuro ta nufi wajen wasu kaya da ke zube
 janne, Jabbi fa?
Janne
(Cikin fillanci) Ya bi Baffa kiwo.
EXT. bakin hanya - mORNING
Garken shanu na tahowa zuwa bakin hanya.
JABBI/bello
Jabbi da Bello mahaifinsa suna tafiya da garken shanun na tsallaka babbar hanyar mai karancin abubuwan hawa zuwa cikin dajin.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (TSAKAR GIDA) - mORNING
Gazah a zaune kusa da Tumano wadda ke ninke kayan wanki da ke kan igiya a shanye. Unaiza ta fito daga dakin babarta, ta nufi hanyar fita.
TUMANO
(cikin yarensu) Ina zaki?
LAMBAI
(cikin yarensu) Ragowar sauyoyin zan je na debo.
TUMANO
(cikin yarensu) Kada ki dade.
UNAIZA
(cikin yarensu) To, Mama.
Gazah
(cikin yarensu) Anti a dawo lafiya.
Unaiza ta juyo ta amsa mata kafin ta fice daga gidan.
EXT. cIKIN DAJI (wajen hutawa) - mORNING
Garba na gaba ya dan baiwa Aminu da Mairo tazara suna biye da shi sun nufi wani fili, inda suka saba zama su huta, idan sun zo yin farauta.
Mairo
Ji na ke kamar na fasa zuwa gidan su Jabbin nan.
Ta kalli Aminu, wanda yayi kamar bai ji abin da ta fada ba.
Mairo (CONT'D)
Ka yi shiru ba kace komai ba.
AMINU
Mafi darajar mutane, shine wanda yayi alkawari ya cika.
Mairo ta sake kallonsa suna ci gaba da tafiya.
Ba zan goyi bayan ki ki zuwa ba, ko dan alkawarin da kika dauka. Sannan na tabbata Janne sai ta dakatar da komai saboda tabbacin zuwan ki a wannan makon, ba kamar wancan satin da kika ce za ki je, amma daga baya kika fasa.
Garba ya isa wajen da suke zama don hutawa.
Mairo
Cikin yanayin shagwaba
Ba kai ne ranar ka yi tafiyarka, ka barni ba.
Suka tsaya tare. Aminu cikin nuna nufin abin da zai fada.
AMINU
Lallai ne komai sai da ni za ki yi? Ai dole wata rana za mu rabu.
Mairo ta cika da mamakin abin da ya fara fada mata.
Mairo
Rabuwa fa ka ce, Yaya Aminu?
AMINU
I mana. Ko ba mutuwa, ai watan wata rana za ki aure.
Mairo ta yi maza ta kalle shi cikin nuna jin zafin maganar. Har zata yi masa magana sai Garba ya kira su.
GARBA
Tsayawar me kuka yi? Ku karaso mana.
Suka karasa wajensa. Aminu ya fara zube kayan da ke tare da shi, kafin ya karbi buhu/jakar da ke hannun Mairo ya ajiye suka zauna kusa da mahaifinsu. Garba ya lura da 'yar damuwar da ke tare da Mairo.
GARBA (CONT'D)
Mairo menene?
Mairo
Ba komai, Abba.
Garba yayi jim sannan ya kalli Aminu cikin daurewar fuska.
GARBA
Me ka yi mata?
AMINU
Ya kalli Mairo sannan Garba.
Me kuwa na yi mata? Babu komai.
Garba ya yi jim sannan ya mike ya dan yi gaba daga inda suke kusa da wata bishiya sannan ya tsaya.
GARBA
Aminu zo ka debamin sassaken itaciyar nan.
Aminu ya tashi da sauri da daya daga cikin kayan farautar, ya riski uban. Kafin ya fara yin abin da ya ce yayi masa.
GARBA (CONT'D)
Na sha gayamaka Aminu, ka rinka kiyaye damuwar yarinyar nan saboda larurarta, amma sai naga kamar ba ka damu ba.
Aminu cikin rashin fahimta.
AMINU
Wace yarinya fa, Abba?
Garba ya waigo ya dube shi suka hada ido sannan ya dafa shi.
GARBA
Mairo mana. Mairo kanwarka.
Aminu ya nuna alamar ya fahimta sannan suka juya ba tare da ya sassaki itaciyar ba, har suka isa inda Mairo ta ke a zaune.
GARBA (CONT'D)
Ka bari zan duba wata bishiyar da ta dace da kaina.
Suka tsaya kusa da Mairo
Yanzu ka je ka takawa Mairo ta tafi gidan su Jannen kada a barta jira. Amma fa kada ka yi nisa don mai yiwuwa kaga Mallam Bello yanzun nan.
Mairo ta mike tana gyara jikinta
Mairo
Bari muje.
GARBA
To Mairo, ki gaishe su.
Garba ya gyara waje ya zauna. Mairo da Aminu suka nufi wajen hanyar garin Cima.
EXT. cikIN DAJI - dAY
Garken shanun na yawatawa a wajen. Jabbi na kula da su.
Baffa Bello
Ka lura da dabbobi nan. Zuwa jimawa ku waiwayi gida.
JABBI
To Baffa.
Ya amsa cikin ladabi kafin shi kuma ya juya ya tafi.
EXT. cIKIN DAJI - dAY
Aminu da Mairo suna tafiya suna hira.
AMINU
Na so ace tare za mu je.
Mairo
Saboda Abba tun da yana jiranka. Ka koma daga nan, zan karasa.
Suka yi sallama ta yi gaba shi kuma ya juya.
EXT. cIKIN DAJI (WAJEN HUTAWA) - dAY
Baffa Bello ya iso wajen daidai lokacin da Garba ke shirin tashi. Suka hadu suka gaisa cikin fara'a suna masu komawa su zauna.
GARBA
Har na fara tunanin ko ba za ka sami bullowa ba.
BAFFA BELLO
Haba. Ai ko dan muka karasa shawarar da muka fara tattaunawa, akan Aminu da Janne, lallai ne na zo na same ka.
Garba yana fara'a ya dauko goro ya bantara ya baiwa Baffa Bello ya karba.
GARBA
Ai na yi zaton ko tare za ku taho da Janne.
BAFFA BELLO
Babu dadewa zaka ganta. Tunda na sa ta biyo ni da damammen Dawo.
EXT. cIKIN DAJI - dAY
Mairo tana tafiya ta iso wajen bishiyar da Unaiza ta ciri dan itaciyar. Hankalin Mairo ya kai kan ragowar dan itaciyar da Unaiza ta bari jiya. Har Mairo ta kai hannu zata cira, Unaiza ta dakatar da ita.
UNAIZA
Ahir!
Mairo ta saurara ta juyo suna fuskantar juna da Unaiza, wadda ke karasowa wajenta. Mairo ta yi mata wani irin kallo ta watsar, cikin yin tsaki sannan ta juya ta sake kai hannu.
UNAIZA (CONT'D)
Hakuri. Taimaka. Ina da bukatarsa.
Mairo ta sake juyowa ta kalleta shekeke.
Mairo
Bukata?(yar dariya) to nima ina da bukata da shi.
Cikin fushi da nuna kadara, ta cisge dan itaciyar ta rike.
Unaiza ta yi shiru tana kallonta cikin yanayi jin takaici.
UNAIZA
Kaico da bin umarnin zuciya don nuna gadara da isa wadda kan iya zama cuta ga mai bukatar warakar larurar waninsa.
Mairo ta kalli dan itaciyar a hannunta ta sake kallon Unaiza wadda ta juya da nufin barin wajen cikin yanayi na gazawa.
Mairo
Ai nasan dole ki tafi tunda kin gayamin bakar magana, saboda na tsinki dan bishiyar da kika dasa, kika raina da kanki.
Yanayin fuskar Unaiza ya sauya, ta juyo, suka sake fuskantar juna da Mairo.
Daga nesa Janne ce ke wucewa, murmushi ya bayyana a fuskarta saboda gane Mairo da tayi, ta nufo wajensu.
UNAIZA
Abin har ya kai haka, saboda na fadi bukata ta da shi?
Mairo
I, na fada.
Ta yar da dan itaciyar a kasa, ta sa kafa ta mutsikke.
In kin ji haushi, naji saukar mari.
Tana rufe baki tana tsinke ta da mari. Mairo ta rike kunci.
Mairo (CONT'D)
Kai, kai, kai! Kika mareni?
UNAIZA
Sakamakon mai izgili da wulakanci kenan.
Mairo cikin karin fusata ta yi kan Unaiza zata rumbace ta/ko ta mare ta, Unaiza ta kauce mata. Har Mairo ta sake wani kokarin, sai Janne ta dakatar da ita.
JANNE
Mairo menene haka?
Mairo ta ji maganar kamar daga sama abin da yasa ta saurara.
Janne ta karaso wajen su cikin mamakin abin da ta gani.
Mairo ta sake juyawa a fusace zata yi kan Unaiza.
Mairo
Ai kuwa ba zan yarda ba sai na rama.
UNAIZA
Ki kuskura hannunki ya taba jiki na, ki gane kuskurenki a rayuwa.
JANNE
Mairo kada kiyi!
Mairo ta tsaya suna kallon kallo da Unaiza.
Janne ta iso wajensu ta kalli Unaiza cikin yanayi na karaya.
JANNE (CONT'D)
Baiwar Allah kiyi hakuri, yar uwa ta ce.
Unaiza ta yi ajiyar zuciya idanunta suka cika da kwalla.
UNAIZA
Da tasan daga inda na taho, da dalilin da yasa, da ba ta tsinka ba, balle har ta saka kafa ta mutsikke.
Sannan ta juya ta bar wajen tana mai matse idanuwanta.
JANNE
Haba Mairo, ba kowane abu a ke gani a daji a tsinka ba.
EXT. cIKIN DAJI (WAJEN HUTAWA) - dAY
Garba da Baffa Bello na ci gaba da tattaunawa, sai suka hangi Mairo da Janne suna karasowa wajensu tare.
BAFFA BELLO
Allah Ya bamu damar cika wannan burin namu.
GARBA
Amin dan Sarkin da yayi ruwa da iska.
Cikin fara'a yana kallon wajen yaran
Ga jannen nan zuwa.
Janne da Mairo suka iso gare su cikin ladabi Janne ta gaisar da Garba kafin Mairo ta gaisar da Baffa Bello. Mamakin ganin su da Mairo tare.
Mairo
A hanya muka gamu shine muka dawo.
BAFFA BELLO
(cikin fillanci) Tare zaku koma?
JANNE
(cikin fillanci) Tace kwana za ta yi.
Garba ya kalli Mairo yana murmushi.
GARBA
Ai gwara ki kwanan zai fi. Don babu mamaki wata rana ki koma gidan da zama.
Suka yi dariya Mairo kamar ranta bai so ba.
JANNE
Janne cikin kawaici ta kalli Garba
Baffa ashe ka fara jin fillanci?
BAFFA BELLO
Kaji sakarai. Tun kafin a haife ki muke tare yaya ba zai ji fillanci ba.
Suka kwashe da dariya, Janne ta rufe fuska cikin jin kunya.
EXT. cIKIN DAJI - dAY
Aminu na tafiya, wani kwaro ya bi jikinsa. Ya tsaya ya duba. Nan da nan wajen ya fara kumbura, abin da yasa yayi maza ya zauna, daidai lokacin da Unaiza ke karasowa wajen wadda ta ga kwaron na tafiya, abin da yasa ta yi zargin abin da ya faru.
UNAIZA
Shi ya kware ka?
Aminu ya daga kai suka hada ido da ita ya amsa mata da ka yana kokarin sosa wajen.
UNAIZA (CONT'D)
Kar ka sosa.
Ya dakata cikin mamaki yana binta da kallo, tana mai tsugunawa a kusa dashi tana kallon wajen da ciwon yake.
UNAIZA (CONT'D)
Hannu kan iya zama guba. Kumburi na iya zama miki, har ya rinka zubar da mugunya, karshe ya kai ga nakasar jiki ta har abada.
Ta mike tsaye ta duba ta je ta tsinko wasu ganyayyaki ta dawo ta mutsikka ta matsa masa ruwan akai. Nan da nan ciwon yayi kumfa kana ya koma, nan ta ke wajen ya kone yayi baki. 
AMINU
Ya kara cika da mamaki yana kallonta
Me kenan?
Ta yi jim tana kallonsa ta dan yi murmushi kana ta sake mikewa ta tsinko wani ganyen ta murza a hannunta ta shafa wajen. Nan da nan tabon ya bace. Abin da ya karawa Aminu mamaki.
AMINU (CONT'D)
Baiwar Allah wacece ke?
Ta yi 'yar dariya ta sake mikewa tsaye tana kallonsa
UNAIZA
Sunana Unaiza.
Ta juya zata tafi. Aminu ya mike ya bita suna tafiya tare.
AMINU
Daga ina kike?
EXT. kAUYEN CIMA (DANDALI) - dAY
Dandalin babu mutane sosai, Aminu da Unaiza suka iso wajen. Unaiza ta tsaya shi ma ya tsaya.
UNAIZA
Mu rabu anan.
AMINU
Ki kaini gidanku mana.
UNAIZA
Tana mai girgiza kanta cikin murmushi
Ba yanzu ba.
Ta juya kamar zata tafi, ya sake binta.
AMINU
Ki kwatantamin.
Unaiza ta yi kamar bata ji shi ba tana murmushi ta kara sauri inda ta bashi tazara har ta kai shiga wani lungu. Aminu ya shiga, amma sai bai ganta ba. Yayi jim yana dube duben inda ta yi sannan ya juya ya koma inda ya fito.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (TSAKAR GIDA) - dAY
Unaiza ta shigo daidai fitowar Tumano daga bandaki.
TUMANO
Kin yi jinkiri Unaiza.
UNAIZA
Na isa, na tarar an cire.
Lambai ya shigo a fusace ya nufo wajen su.
LAMBAI
Kin fadi son rai.
Unaiza ta juya da sauri cikin fargaba
LAMBAI (CONT'D)
Kin bi son zuciya. Wanene ke biye a bayanki?
Ta yi maza ta rakube jikin mahaifiyarta ganin yanda ya fusata.
TUMANO
Hakuri dai.
LAMBAI
Kaico! Nace kaico.
Yana girgiza kansa cikin nuna bacin ransa.
Daga yau kada naji kada na gani, ke da shi tare, Gargadi na gareki.
Sannan ya wuce cikin daki cikin tsanantar damuwa.
TUMANO
Cikin yanayin gazawa
Kiyayi damuwar Babanki.
Unaiza tayi shiru cikin yanayi na karin damuwa.
DISSOLVE TO:
INT. gIDAN GARBA (DAkin aminu) - nIGHT
Dakin yayi tsit cikin karamin haske sai kukan gyare da sauran kwari alamar dare yayi nisa.
AMINU
A kwance yayi kasake cikin yanayi na tunanin abin da ya faru tsakaninsu da Unaiza. Yayi jim kamar yana sauraren wani abu, sannan ya tashi zaune ya duba jikin kafarsa daidai wajen ciwon.
DISSOLVE TO:
Wakar dajin so
Dukkaninsu suna rerawa bisa yanda tsarin baitikan wakar suke.
BACK TO:
INT. gIDAN GARBA (DAKIN AMINU) - nIGHT
Yayi shiru na wani lokaci kafin ya sake komawa ya kwanta, yana mai juyar da fuskarsa zuwa daya bangaren.
CUT TO:
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - nIGHT
Wajen yayi tsit babu haske sosai.
GARBA
A kwance kan shimfida yana bacci. Motsin tafiyar maciji na kusanto wajen da Garba ya ke kwance.
CUT TO:
INT. gIDAN GARBA (DAKIn aminu) - nIGHT
Dakin cikin matsakaicin haske.
AMINU
Yana juye juye alamun yana mummunan mafarki. Sautin kwalla karar Garba daga waje. Aminu bai motsa ba.
BACK TO:
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - nIGHT
GARBA
Gumi na bin fuskarsa, idanunsa a kakkafe, dafara na fitowa daga bakinsa, yana kakari kamar wani abu ya shake shi.
BACK TO:
INT. gIDAN GARBA (DAKIn aminu) - nIGHT
AMINU
Ya farka a firgice, ya hada gumi sharkaf. Yayi shiru cikin yanayi na mamaki. Sautin kakarin Garba na shigowa dakin.
Aminu yayi jim cikin saurare, yayin da nishin yana raguwa. Aminu ya mike cikin gaggawa ya fita.
BACK TO:
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - nIGHT
GARBA
A kwance idanunsa a kakkafe, dafara na fitowa daga bakinsa, gumi ya jika fuskarsa.
Aminu ya fito daga dakin a gigice. Ganin halin da Garba yake ciki, yasa Aminu karin tashin hankali ya zube a gabansa.
Aminu
Abba.
Ya fara taba shi yana girgiza shi.
Abba, Abba. Nine!
Aminu fuskarsa cikin yanayi na karin tashin hankali saboda alamar saran miciji a wuyansa fahimtar Garba ya rasu.
Yayi tsai yana duban mahaifinsa. Alamun motsi, yasa Aminu ya juya ya kalli wajen da motsin ya ke.
Karshen jelar macijin ya gani tana karasa fita ta rariya.
FADE TO:
EXT. gIDAN GARBA (KOFAR GIDA) - mORNING
Taron jama'a 'yan zaman makoki cikin yanayin alhini.
baffa bello/mallam modibbo
A zaune tare da 'yan uwan mamacin ana yi musu ta'aziyya.
AMINU/jabbi
Aminu cikin hawaye, yayin da Jabbi ke lallashinsa.
INT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - mORNING
Wasu mata sun shigo yin ta'aziyya.
LaRABA/INNA WURO
Suna karbar gaisuwa cikin alhini da jimamin rashi.
Mairo/janne
Suna daga gefe, yayin da Mairo ke cikin matsanancin kuka.
INNA WURO
Mairo, ki zama mai yi masa addu'a don nema masa rahma.
FADE TO:
EXT. gIDAN GARBA (KOFAR GIDA) - dAY
AMINU/JABBI
Suna kwashe tabarmin da ke wajen. Daga nesa da su kadan, Baffa Bello ne tare da Mallam Modibbo suke tattaunawa akan komawar iyalan Garba gidan Baffa.
BAFFA BELLO
Da wata shawara na yi, na ce ko Laraba tare da yaran su koma waje na saboda saukaka wasu abubuwa na halin yau da gobe?
MALLAM MODIBBO
E, to wannan ma abu ne mai kyau. Amma sai na ke ganin, me zai hana mu bar su su ci gaba da zama anan, don shi yaron ya fara sabawa da jagoranci tun kafin lokacin da nauyi zai hau kansa gaba daya.
BAFFA BELLO
Ya dan yi jim cikin yanayi na gamsuwa da maganar
Wannan ma hanzari ne. Amma duk da haka ya dace a kira shi a yi masa nasiha tun daga yanzu. Don shi yaro man kaza ne.
MALLAM MODIBBO
Gaskiya ne, Baffa. Bari kira shi.
Ya juya wajen da su Aminu suke.
Aminu shiga ciki ka kirawo Mairo kuzo tare.
AMINU
To Abba.
Ya bar Jabbi da sauran aikin ya shiga cikin gida.
BAFFA BELLO
Cikin yanayin alhini
Alla ka jikan Garba.
MALLAM MODIBBO
Amin, Baffa.
Aminu da Mairo suka fito daga cikin gida suka nufo wajensu.
BAFFA BELLO
(cikin fillanci ya kira Jabbi)
Shima ya biyo su suka zo suka durkusa kusan lokaci guda.
MALLAM MODIBBO
To Aminu da kai da Mairo dukkaninku babu mai karancin shekarun da za'a ce bai san menene rayuwa ba da kuma kalu balen da ke cikinta.
Kowannensu ya nutsu yana sauraron jawabinsa.
MALLAM MODIBBO (CONT'D)
Don haka, ko menene ya faru ga musulmi mumini, sai ya dauke shi jarrabawa ce daga Sarkin da ya halicce shi.
BAFFA BELLO
Wannan hakkun.
Cikin karfafa maganar Modibbo.
MALLAM MODIBBO
Saboda haka, kai Aminu ya zama wajibi gareka da ka kula da dukkan wasu dawainiyar mahaifiyarka da kuma ta wannan yarinya, musamman na abubuwan da mahaifinka ya nusar da kai tun kafin ya koma ga Allah.
BAFFA BELLO
Gaskiya ne, Modibbo. Mu kuma za mu ci gaba da bibiyar ka don lura da abubuwan da zasu rinka gudana.
MALLAM MODIBBO
Don haka, ni dai, babu abin da zan ce da Baffa Bello, illa Ubangiji Allah Ya bashi ikon daukar nauyinku, Ya kuma saka masa da alheri. Domin tun kafin rasuwar mahaifinku, duk wanda ya sanshi, tare suke tun suna kanana.
BAFFA BELLO
Ya sunkuyar da kansa cikin yanayin alhini kamar zai yi kuka.
MALLAM MODIBBO
Da Baffa da Yaya Garba, daya ne a wajenku. In kun saba masa, kamar kun sabawa mahaifin ku ne. Saboda da haka, ina yi muku nasiha da ku ci gaba da bin tafarkin da mahaifinku ya gadar da ku a kansa.
Yayi jim yana kallon Aminu
Ka kula da ita, Aminu. Mace ce tana da rauni. Ka kuma tuna da wasiccin mahaifinka a kanta.
BAFFA BELLO
Kai ma Jabbi da kai da 'yar uwarka ya dace ku rinka zagayo su akai akai saboda dauke musu kewa.
MALLAM MODIBBO
Suma din ya dace suka karfafa zuwa wajen na ka. Don dorewar zumuncin da ke tsakani.
BAFFA BELLO
Wannan ma shawara ce ta kwarai.
MALLAM MODIBBO
Ya saurara yana kallon Aminu da Mairo kamar zai yi kuka.
Allah Ya jikan Yaya.
Suka amsa gaba daya. Mallam Modibbo Ya fara shashshekar kuka.
Allah Ya gafartawa Yaya.
Baffa Bello ya ci gaba da lallashinsa tare da baiwa juna hakurin rashin Garba da suka yi.
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - mORNING
Aminu cikin shirin fita zuwa farauta. Laraba na tattara wasu kayayyakin gida cikin lullubi. Mairo a zaune ta yi jugum har yanzu tana cikin alhinin mutuwar babansu. Aminu ya matsa kusa da ita yayi jim yana kallonta cikin tausayawa sannan ya durkusa gabanta.
AMINU
Mairo kiyi hakuri. Mutuwa sako ce wadda zata zaikewa kowa.
LARABA
Tana wucewa da wasu kayan zuwa wajen da zata ajiye.
Ki samawa kanki sa'ida Mairo, dan zuciyar dan uwanki ta karfafa.
MAIRO
Ta juya ta kalli Laraba cikin tausayawa kanta.
Umma na gode.
EXT. cIKIN DAJI (WAJEN HUTAWA) - dAY
Aminu da Jabbi suka isao wajen kusan lokaic guda. Jabbi ya fito kiwo, shi kuma Aminu ya fito daga farauta.
AMINU/JABBI
Suka zauna suna tattaunawa cikin yanayi na nishadi.
EXT. gidan baffa bello (TSAKAR GIDA) - mORNING
Inna wuro na kwance dabbobi zuwa waje.
Sun hadu gaba dayansu suna karin kumallo cikin nishadi.
AMINU/JABBI
A waje guda suna cin abinci tare.
JANNE/Mairo
Daga daya bagaren suma da nasu abincin, suna yi suna tsokanar su Jabbi. Aminu ya mike zai je ya wanke hannu, Janne ta tashi ta je ta zuba masa ruwa. Mairo ta bita da wani irin kallo.
BAFFA BELLO
Ya fito daga bandaki da buta ya ajiye.
INNA WURO
Ta bar abin da ta ke yi, taje ta dauko masa Sanda da Jallonsa ta kawo masa ta risna ta bashi.
Yaran suka taso suka zo suka yi masa a dawo lafiya kafin su koma wajen da suke.
Baffa ya fiddo kudi ya baiwa, Inna wuro, cikin ladabi da girmamawa tasa hannu biyu ta karba. Sannan ya rataya Sanda da Jallon, ta dan taka masa kafin su yi sallama ya fita.
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (kofAR GIDA) - aFTERNOON
Wasu yara suna wucewa, daya na rike da rigar suna gara gare-gare. Aminu da ke zaune yana hutawa ya bi su da kallo yana yi musu dariya.
Janne
Ta fito da kwaryar fura, cikin fara'a ta mika masa.
AMINU
Ya karba, yana murmushi cikin tsokana, yana nuna mata furar bata damu ba.
Janne ta karba ta tsugunna ta na sake damawa suna yi suna hira tare.
Mairo
Ta ci ado cikin sakin fuska, ta fito da niyyar zuwa wajen Aminu, sai ta rakube daga gefe, ganinsu da hangen abin da yake faruwa tsakaninsu. Sannan ta juya cikin gida a guje.
Janne ta gama ta mikawa Aminu ya karba daidai dawowar Baffa wanda ya kalle su cikin kawaici da nuna jin dadi. Suka yi masa sannu da zuwa.
BAFFA BELLO
Ya wuce cikin gida yana fara'a.
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (TSAKAR GIDA) - aFTERNOON
Mairo a zaune ta takure cikin damuwa tana kallon hanyar waje. Shigowar Baffa Bello, yasa ta yi maza ta goge hawayen da ke neman zubowa daga fuskarta. Baffa ya ankara da halin da ta ke ciki.
BAFFA BELLO
Mairo lafiya?
Tayi maza ta share hawyen kafin ta mike da sauri tana murmushin karfin hali.
Mairo
Babu komai, Baffa. Sannu da zuwa.
Tana kokarin karbar jallon ruwansa.
BAFFA BELLO
Ba kuka kike yi ba, Mairo?
Ta girgiza kanta tana yi masa murmushi don boye damuwar da ta ke ciki, ta nufi wajen da zata ajiye.
Mairo
Na tuna da Abba ne.
Yayi shiru, kafin ya juya ya kalli wajen kofar gida sannan ya sake kallonta daidai fitowar Inna wuro daga daki cikin alamun ta tashi daga bacci.
INNA WURO
(cikin fillanci ta yi masa sannu da zuwa).
EXT. gidan baffa bello (bayan gida) - mORNING
Janne da Mairo dauke da tuluna, zasu je debo ruwa, suna tafe suna hira, fuskar Mairo babu walwala.
JANNE
Ni kuwa ban faya son na ganki cikin damuwa ba. Ko wani abu aka yi miki?
Mairo
Ko kadan Janne. Damuwa ta, rashin ganin Aminu a koda yaushe.
Janne ta dan saci kallonta suna ci gaba da tafiya.
JANNE
Ni kaina wani lokaci sai na ji duk duniya shi kadai na ke son na gani.
Mairo ta yi maza ta kalle ta cikin yanayi na zargi
Mairo
Me yasa?
Suka isa wajen ruwan, Janne ta dan yi murmushi.
JANNE
Dabi'unsa da halayensa. Dole ne zuciya ta aminta da shi kamar yadda amincin sunansa yake.
Tana danna tulun a ruwa tana diba                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                             
Haka nan Aminu na daga cikin irin mutanen da kowace mace mai bukatar kyakykyawar rayuwa, zata yi fatan kasancewa da shi.
Mairo ta yi kasake tana kallonta
Mairo
Wadannan alamomin da ke nuna kina son sa ne.
Janne ta yi 'yar dariya ta dora tulunta, kafin Mairo itama.
JANNE
Koda yaushe zuciya na kaunar wanda ya ke kyautata mata.
Suka nufi hanyar gida, fuskar Mairo cikin damuwa.
EXT. gIDAN garba (KOFAR GIDA) - mORNING
Aminu ya fito suka yi kacibus da Baffa bello yana zuwa zaune kan wata karauni ya bude littafi yana karatu.
Aminu ya fito zai tafi farauta, suka yi da Baffa Bello yana zuwa gidan. Aminu ya durkusa ya gaishe da Baffa, har ya mike Baffa ya dawo da shi.
BAFFA BELLO
Daman wata magana nake son na tambaye ka ko kun taba yin ta da Abbanka kafin ya rasu?
Ya dada nutsuwa cikin ladabi
AMINU
Wacce magana fa, Baffa?
BAFFA BELLO
Maganar hada ka aure da Janne.
Yayi maza ya kalli Baffa cikin matukar mamakin abinda yace.
AMINU
Bamu taba yi ba, sai dai tun da ka fada Baffa, ai akwai maganar kenan.
Baffa ya girgiza kansa yana murmushi
BAFFA BELLO
Ba za'a yi haka ba Aminu. Ko wane aure da ka gani, yana bukatar soyayya da amincewar ma'aurantan, domin samun ingatccen zaman aure mai dorewa.
Aminu ya sunkuyar da kansa yana sauraronsa
Daman na tambaye ka don naji ko kana da masaniyar hakan. Tun da a 'yan kwanakin nan, ina lura da abubuwan da suke faruwa tsakaninku.
AMINU
Ya jinjina kansa
Haka ne Baffa.
BAFFA BELLO
Kaga tashi kaje. Allah Ya bada sa'a. Wani lokaci ma tattauna akan yiwuwa ko rahsin yiwuwar al'marin.
Aminu ya mike ya nufi inda za shi daidai lokacin da wani mai jaki ke wucewa dauke da taki zai kai gona.
EXT. cIKIN DAJI (wajen kiwo) - dAY
Shanun na kiwo, Jabbi da Aminu suna tare zaune a gefe.
JABBI
Ya tashi yana shan kan shanun, ya bar Aminu a zaune.
Daga nesa Unaiza ta zo zata wuce, ta hangi Aminu. Har ta wuce, sai ta lura bai ganta ba, ta dawo ta tsaya a gabansa sannan ya ankara da ita.
AMINU
Sannunki.
UNAIZA
Cikin fara'a
Sannun ka kaima. Fushi kayi ka daina zuwa nan?
AMINU
Mahaifina ne ya rasu.
Yanayin fuskarta ya sauya zuwa tausayi.
UNAIZA
Wayyo ka yi rashi. Halinsa na gari ya bishi.
Aminu yayi mata wani irin kallo ya kawar da kai. Jabbi ya dawo wajen da suke.
Unaiza (CONT'D)
Ka sami gibi babba a rayuwa. Kabi halin mahaifinka domin rayuwarka ta kyautata.
AMINU
Itace Unaizar da nake baka labari, Jabbi.
Jabbi yayi mata murmushi yana mai dogara sandarsa ta kiwo.
JABBI
Sannu Une. Ba mu ganki wajen makoki ba.
UNAIZA
Ta dan bata rai tana kallon Jabbi
Abokinka, bai bani muhimmanci ba. Ya kangarar da ni a zuciyarsa.
Aminu yayi shiru yana kallonta.
JABBI
Yana fara'a
To yanzu ya tabbatar da ke a cikin rayuwarsa. Kuma da magariba muna nan tafe za mu zo tadi.
Suka yi dariya
AMINU
Zamu zo gobe.
Unaiza ta yi jim kamar tana tuna gargadin mahaifinta.
JABBI
Ko muna da abokin hamayya ne?
AMINU
Kaima ka fada, Jabbi. Duk lokacin da nace zan je wajenta ba ta yarda.
UNAIZA
Kasan halin manya.
Ta dan yi jim sannan ta yi murmushi
Yaushe zaku zo? Ni zan san mafita.
JABBI
Indai da matsala ki fada mana.
UNAIZA
Matsala akwai. Amma babu wanda zai santa.
Aminu da Jabbi suka yi musayar kallo.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (kofAR GIDA) - eVENING
Aminu/JABBI
A kofar gida a tsaye sun zo wajen Unaiza zance suna jiran fitowarta. Gazah ta fito tazo ta gaishe su.
GAZAH
(cikin yarensu) Sannunku. Tace tana zuwa.
AMINU
Yayi mata murmushi alamar ya fahimci me take fada
Ki gaishe da Baba.
Jabbi ya bita da kallo cikin rashin fahimtar abin da ta fada.
JABBI
Kace daman kana jin yarensu?
AMINU
Yau da gobe taki wasa.
Unaiza ta fito ta yi ado ta zo ta riske su cikin ladabi ta gaishe su.
UNAIZA
Daga yau za mu sauya wajen tsayuwa.
JABBI
Zai dai fi kam.
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (bayan GIDA) - eVENING
Aminu ne a zaune cikin yanayin damuwa. Mairo ta zo ta riske shi. Ya daga kai ya kalle ta suka hada ido tayi masa murmushi.
Mairo
Na duba cikin gida banganka ba.
Aminu ya kawar da kansa cikin damuwa
AMINU
Wata magana ce take neman damamin lissafi shi yasa nazo nan na zauna.
Mairo ta zauna a kusa da shi tana mai kallonsa
Mairo
Wace maganar ce?
Ya dan yi shiru kamar yana tunani.
Mairo (CONT'D)
Yaya Aminu ka fadamin mana.
Ya dan sake yin jim sannan ya juya ya kalle ta.
AMINU
Baffa ne dazu ya ke fadamin cewa wai sun taba maganar da Baba cewa za'a hada ni aure da Janne.
Nan da nan yanayin fuskar Mairo ya sauya.
Mairo
Janne? Wata irin Janne kuma babu dadin ji?
Ta kawar da kanta kamar ranta bai so ba
Ko da yake ban sani ba ko daman kana sonta ne shi yasa, su Abban suka yanke shawarar hada ka aure da bazawara.
AMINU
Haba Mairo yaya za ki cemin haka? Kin taba jin na ce miki ina sonta ko kafin mu dawo gidansu, kin taba ganin na zo wajen ta zance?
Mairo
Har yanzu bata kalle shi ba
A to na sani. Tun da duk maza sunansu daya ne.
AMINU
Ni dai yanzu duk ba wannan na nema ba. Shawararki na ke so na ji a matsayinki na 'yar uwata. Me kika gani?
Mairo
To ni dai a matsayi na na yar uwarka, ba zan so ka auri wadda ba ka ra'ayi ba, musamman ma wadda mijinta ya rasu sakamakon rashin lafiyar da ba a santa ba.
Aminu yadada kallonta cikin karin mamakin jin abinda ta ce.
Mairo (CONT'D)
Cikin yanayin gazawa
Amma duk haka nasan shan koko daukar rai ne. In kaga kana sonta shikenan.
AMINU
...Haba Mairo, ai duk abin da kika nuna ba kya so, to zan hakura da shi ko menene.
Mairo ta juyo ta kalle shi tana murmushi.
EXT. kAUYEN CIMA (wajen zance) - eVENING
AMINU/JABBI
Sun zo zance wajen Unaiza.
Unaiza
Tana zolayarsu cikin yanayi na raha, suna tadi, har ya zuwa lokacin da suka yi niyyar tafiya, Unaiza ta raka su.
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (TSAKAR GIDA) - nIGHT
Janne na tattara kaya, Mairo ta fito daga cikin daki tana yafa mayafi fuskarta babu walwala. Janne ta mike cikin mamaki.
JANNE
Mairo ina zaki?
Mairo
Ba tare da ta juyo ba
Aminu zan je nema.
Janne cikin karin mamaki
JANNE
Unguwa fa suka je shi da Jabbi.
Mairo ba ta saurare ta ba ta fice daga gidan cikin damuwa.
EXT. cikin garin kuki (DANDALI) - eVENING
Wajen cike da mutane kowa yana harkokinsa. Aminu da Jabbi suka iso kusa da wajen suka nemi wani waje suka kebe suna sallama. Har Unaiza ta juya zata tafi, sai ta ji magana kamar daga sama.
Mairo
Aminu! Daman wajen wannan abar kake zuwa?
Unaiza ta juya a fusace saboda jin muryar Mairo.
Daga nesa Mairo ce ta ke tahowa tana mai hangen abin da ke faruwa tsakaninsu. Yanayin fuskarta ya fara sauyawa tun kafin ta karaso ta riski su Aminu da Jabbi. Ganinta yasa suka kalli juna cikin mamaki, yayin da Unaiza take yi mata wani irin kallo alamun ta fahimci wani abu a tare da Mairo.
AMINU/JABBI
(Cikin hadin baki suka tambayeta inda zata je)
Ta yi kamar ba ta ji me suka fada ba.
Mairo
Ka yi shiru kana kallo na.
Aminu da Jabbi suka yi musayar kallo.
AMINU
Cikin mamaki ya kalle ta
Me kike so nace miki, Mairo?
Ya juya ya kalli Jabbi
Unaiza
Cikin kishi da damuwa
Kai kasan abin da ka ce mata. Daman kasan da ita , shine ka ke zuwa wajena don yaudara?
Mairo
Fuskarta ta sauya tana kallon Unaiza
Munafuka, algunguma.
Har Unaiza zata martana mata, sai ta ga yanayin fuskarta ya fara sauyawa alamar rashin lafiyarta zai tashi. Aminu da Jabbi suka yi musayar kallo cikin karin tashin hankali.
JABBI
Mairo, lafiya?
AMINU
Mairo menene haka? Ba ki da hankali ne?
Mairo
Ta juya ga Aminu tana numfarfashi
Ka fadi haka mana. Tun da Janne ta baka a cikin fura ka sha.
Aminu ya fusata yayi kanta kamar zai daketa. Unaiza ta daka masa tsawa.
UNAIZA
Ahir din ka!
Jabbi yayi maza ya tare shi.
JABBI
Haba Aminu. Macece fa, kuma 'yar uwarka. Kasan dole ta yi kishinka.
Kafin su ankara Mairo ta zube kasa tana wani irin nishi idanunta a kakkafe rashin lafiyarta ta shi.
Fuskokin Aminu da Jabbi kowannensu cikin tashin hankali.
Unaiza ta yi maza ta rike ta tana kallonta saboda ganin ciwon irin na Gazah, sannna Unaiza ta kinkimi Mairo ta mike da ita.
UNAIZA
Mu je gida.
Suka nufi hanyar gida da ita.
EXT. gIDAN garba (TSAKAR GIDA) - eVENING
LARABA
A gindin randa a tsaye tana zuba ruwa a kan sauyoyin da ke cikin kokon da ta ke rike da shi.
Mairo
Tana kwance kan shimfida, idanuwanta a rufe tana numfashi, alamar ta galabaita. Sannan ta bude idanuwanta ta kalli Unaiza wadda ke durkushe kusa da ita tana yi mata fifita.
UNAIZA
Sannu.
Mairo ta amsa mata da ka, ruwan hawaye ya biyo kuncinta.
Inna wuro/JANNE
Suka shigo kusa lokaci guda, Baffa Bello yana biye da su rataye da jllonsa fuskarsa cikin yanayin damuwa. Suka yi mata sannu kafin su koma gefe suna tattaunwa.
Daga gefe guda Baffa ne da Aminu a tsaye cikin jimamin abin da ya faru. Jabbi ya shigo da wasu saiwowi ya nunawa Baffa.
JABBI
(cikin fillanci) Gashi, Baffa.
BAFFA BELLO
(cikin fillanci) Mikawa Inna wuro. Ku bata yanzu ta sha.
Jabbi ya nufi wajen Inna wuro, daidai lokacin da Unaiza t amike zata tafi. Inna wuro ta karba ta zuba a cikin kokon da ke wajenta, ta kalli Unaiza.
LARABA
Har zaki tafi, ba zaki bari kici abinci ba?
UNAIZA
Saboda manya.
Sannan suka yi sallama, Janne ta rakata zuwa kofar gida.
INNA WURO
Sai  kuma muka jikinta ya sake tashi.
Laraba tana baiwa Mairo maganin da Inna wuro ta hada.
LARABA
Kin ganshi nan kullum sai ya jawo abin da zia tashi ciwon yarinyar nan, har yanzu ya ki yakiyaye abin da mahafinsa ya gargade shi akai.
Aminu yayi jim alamar ya ji maganr da Laraba ta fada.
AMINU
Umma, magana kike yi?
LARABA
Ta kalle shi fuskarta a daure tana mai kwantar da Mairo
Aminu ya kamata kika yi duk wani abu da zai saka yarinyar nan cikin damuwa. Ka fa san yanda larurarta ta ke.
AMINU
Ban fa yi mata komai ba, Umma.
INNA WURO
Tana kallon Aminu
Ka yi mata mana. Dan me rai zai rinka baci ba'a yi masa komai ba?
Aminu yayi maza ya kalli Baffa cikin nuna rashin fahimtarsa. Laraba ta mike zata shiga daki ba tare da ta saurare shi ba.
Aminu ya juya zai fita, suka hadu da Janne.
JANNE
Baffa na kiranka.
Aminu ya nufi kofar gida. Janne ta isa wajen su Mairo.
EXT. gIDAN garba (KOFAR GIDA) - eVENING
Baffa na tsaye, fuskarsa cikin damuwa, Aminu ya zo ya same shi, fuskarsa cikin rashin walwala.
AMINU
Baffa gani.
BAFFA BELLO
Aminu ya kamata ka kiyaye dukkan abubuwan da mahaifinka ya gargade ka game da yarinyar nan.
AMINU
Cikin kokarin kare kansa
Yanzu shi kenan dan tana yar uwata, babu ni ba yin magana da kowa sai wanda ranta ya amince.
BAFFA BELLO
Macece, dole ta yi kishinka, saboda itama zuciya ce da ita kamar irin ta Unaiza, da kuma Janne.
DISSOLVE TO:
EXT. cIKIN DAJI (WAJEN HUTAWA) - dAY
Zamu fara da ganin farkon lokacin da su Janne da Mairo suka zo sukasame su lokacin da suka kawo fura har ya zuwa lokaicn da Janne ta rufe fuska.
Suka kwashe da dariya, Janne ta rufe fuska cikin jin kunya. Janne da Mairo sun nufi hanyar gida, yayin da Garba da Baffa ke ci gaba da tattaunawa.
Muryar baffa bello
Bayan tafiyarsu, sai muka ci gaba da tattauna maganar hada auren ku da Janne inda daga baya na nunawa mahaifinka cewa ni nafi goyon bayan hada ku aure da Mairo, kasancewar ita marainiya 'yar babban aminin mahaifinku, wanda saboda shi ya sanya maka sunansa.
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - dAY
Laraba/INNA WURO
A gefe guda, cikin yanayi na alhini.
Aminu II
Mai shekaru (4-6) yana kusa da su yana wasa da wata 'yar karamar Gwafa.
Malam aminu
Rike da jinjinniyar a hannunsa yana kallonta cikin yanayi na alhini.
GARBA/BAFFA BELLO
Suna kusa da shi suna lallashinsa tare da bashi hakurin rasuwar matarsa. Garba ya karbi jinjinniyar ya mikawa Laraba wadda ta sa hannun biyu ta karba tana mai kallon jinjinniyar cikin tausayawa.
Muryar baffa bello
Kuma bayan rasuwar mahaifiyar Mairon lokacin da bata wuce shekara ba, aka dawo da ita wajen mahaifiyarka don ta ci gaba da rainonta.
EXT. gIDAN GARBA (KOFAR GIDA) - dAY
GARBA/BAFFA BELLO
Suna tsaye, Baffa cikin sauraron abin da Garba ya ke fada
MURYAR BAFFA BELLO
Shi kuma ya nuna min hakan ba kuskure ba ne. Sai dai shi bisa ra'ayinsa da kuma abubuwan da ya ke gani kamar Jabbi yana son Mairo shi yasa shi a wajensa zai fi son a hada kai da Janne shi kuma Jabbi a bari a ga abin da zai kasance tsakaninsu da Mairo.
BACK TO:
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (KOFAR GIDA) - eVENING
Baffa yayi shiru yana kallon Aminu cikin yanayi na tausayawa.
AMINU
To Baffa bansan wannan ba.
BAFFA BELLO
Yaya kuwa za'a yi ka sani, tunda iyayenka basu nuna mata bambanci da kai ba. Mahaifiyarta ta rasu, sai aka dauke ta, a lokacin ba ta cika shekara guda ba, wanda ni da shi muka yi zargin shine dalilin rashin lafiyar nan tata.
Jabbi ya fito da sauri ya riske su.
JABBI
Jikin Mairo ya sake dawowa.
Suka juya cikin gaba dayansu.
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (TSAKAR GIDA) - eVENING
Mairo
A inda take ciwon ta ya tshi gumi na bin fuskarta kamar an zuba mata ruwa.
JANNE/inna wuro
Suna rike da ita cikin yanayi na tausaya mata.
Jabbi da Aminu da Baffa suka karaso wajen. Baffa ys gurfana yana yi mata tofin addu'oi. Karin tashin hankali da dimauta a fuskar Aminu. Aka ci gaba da yi mata addu'o'i har ta fara bacci.
BAFFA BELLO
Ya saurara da tofin yana kalonta
Allah Ya kawo hanyar rabaki da wannan larura.
Suka amsa gaba dayansu.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (TSAKAR GIDA) - mORNING
UNAIZA
A zaune ita kadai ta hada da gwuiwa kamar tana tunani.
TUMANO
Ta saurara da abin da ta ke yi
Ki yi tunani a hankali don ki kubuta daga sharrin da yawaitarsa ke haifarwa.
Unaiza ta yi ajiyar zuciya kafin ta mike ta nufi inda wasu kullin magunguna suke ta dauka ta yi shiru tana dubawa, sannan ta juya ta fita da sauri fuskarta cikin yanayin damuwa.
LAMBAI
Ya fito daga cikin daki
(cikin yare) Ina ta tafi?
TUMANO
(cikin yare) Ba ta fadamin ba.
Fuskarta cikin yanayi na fargabar abin da zai biyo baya.
Lambai ya shuri takalmansa ya bi bayan Unaiza.
EXT. kAUYEN KUKI (CIKIN GARI) - mORNING
Aminu da Jabbi sun fito cikin gari, kowannensu akwai rashin walwala a tare da shi. Unaiza ta shigo cikin garin, ta hangi su Jabbi ta nufo wajen su.
UNAIZA
Jabbi!
Suka juya gaba dayansu kusan lokaci guda, kafin ta karaso wajen da suke. Bayan sun gaisa ta kalli Aminu.
UNAIZA (CONT'D)
Yaya mai jiki?
AMINU
Mai jiki da sauki.
Unaiza ta dauko wasu magunguna ta mikawa Jabbi.
UNAIZA
Ka kai mata wannan.
(Ta fada masa yanda za'a yi amfani da shi).
AMINU
Me zai hana muje gidan gaba daya?
Unaiza ta girgiza kanta tana murmushi.
UNAIZA
Ba a yanzu ba.
JABBI
Dalili?
LAMBAI
Une!
Dukkaninsu suka juya, yayin da fuskar Unaiza ta cika da firgici tun kafin ta juya saboda gane muryar mahaifinta.
Ya nufo wajen su cikin fusata inda kafin ya karaso Unaiza ta runtuma a guje ta yi hanyar gida, Lambai ya juya ya bita cikin karin fusata.
Aminu yayi kamar zai bisu, Jabbi ya rike hannunsa.
JABBI
Kada ka soma. Babanta ne.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (TSAKAR GIDA) - mORNING
Tumano na dab da shiga daki, Unaiza ta fado cikin gidan, abin da yasa Tumano ta tsaya cikin mamakin abin da ya koro Unaiza.
TUMANO
(cikin yare) Lafiya?
UNAIZA
(cikin yare) Baba ne.
Lambai ya shigo yana fada cikin yare ya nufo wajen su. Unaiza ta rakube jikin Tumano. Yayi kanta kamar zai jawo ta. Tumano ta dakatar da shi.
TUMANO
(cikin yare) Haba mai gida. Menene laifinta?
LAMBAI
(cikin yare) Gargadin da na yi mata ta karya.
Ya sake kaiwa Unaiza wawura, Tumano ta sake tare shi. Unaiza ta yi maza fada cikin daki.
TUMANO
Haba shugaba. Rayuwa mataki mataki ce. Shekaru suke jan ragamar rayuwa zuwa kowane mataki. Unaiza ta yi munzali, dole a zo wajenta.
Lambai ya tsaya yana yi mata wani irin kallo.
I/e. Cikin daji (wajen waka) - night
Dukksninsu sun hadu suna rerawa bisa yanda batinkan ta ya ke.
EXT. kAUYEN KUKI (RUGAR SU JABBI) - dAY
Janne da Mairo suna yawatawa, har yanzu akwai alamu na rashin karfi a tare da Mairo.
MAIRO
Cikin sasaukar murya
Janne, ki yafe ni na so na yi shishshigi a cikin al'amarin da bai kamata na fiya zakewa a kansa ba.
JANNE
Ba haka ba ne, Mairo. Ni kaina ina goyon bayan kasancewar ki tare da dan uwanki domin ya zama sahibin zaman rayuwarki na har abada.
MAIRO
Janne na rigaya na yi kuskure tun farko.
JANNE
Ta juyo ta kalle ta
Kamar yaya, Mairo?
MAIRO
Saboda ban fayyace al'amari na ga Aminu ba. Don haka, ni ban zarge shi ba, saboda a kullum yana zaune da nine a matsayin 'yar uwarsa wadda suke uwa daya uba daya.
JANNE
Ta dan yi shiru tana jinjina maganar Mairo
Gaskiya ne. Amma duk da haka ni ina ganin har yanzu kina da dama ta ci gaba da soyayya da shi.
MAIRO
Ba zai yiwu ba, Janne. Kada ki manta, tun kafin rasuwar Abba sun rigaya sun yi da Baffa za'a hada ku aure da Aminu.
JANNE
Za'a iya sauyawa.
Mairo ta kalli Janne cikin mamakin jin abin da ta fada.
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - dAY
Laraba da Inna wuro suna zaune kayan shirye shiryen aure a gaban su.
INNA WURO
Ai gwara da aka yi haka.
Laraba tan duba wasu kayan cikin fara'a da nuna jin daji.
LARABA
Allah dai yayi da ita za'a yi.
INNA WURO
Haka hukuncin Allah ya ke.
LARABA
Allah dai Yasa a yi damu.
INNA WURO
Amin.
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (BAYAN GIDA) - dAY
Aminu a zaune, shi kadai cikin yanayi na tunani. Mairo ta taho wajensa har yanzu akwai alamu na rashin karfin jiki a tare da ita. Ta dan yi jim kafin ta karaso gare shi.
MAIRO
Salamu alaikum.
Aminu ya daga kai ya kalle ta cikin murmushina karfin hali.
AMINU
Wa alaikis salam.
Yana kallonta cikin dan karamin murmushi.
Zauna mana.
MAIRO
Ta zauna a kusa da shi
Yaya Aminu ka mayar da nan dai wajen dauke maka kewa a duk lokacin da kake cikin damuwa.
AMINU
Wani lokaci ne, sai nazo nan na ke dan ji saukin wasu abubuwan.
Ta jinjina kanta
MAIRO
Haka ne Yaya Aminu. Nima yanzu na zo ne domin na nemi wata alfarma a wajenka.
AMINU
Yayi jim yana kallonta
Alfarma, Mairo? Wace irin alfarma?
MAIRO
Yaya aminu nasan abubuwa da yawa sun faru tsakaninmu tun daga lokacin da nake matsayin 'yar uwarka ta jini har ya zuwa yanzu da komai ya koma matsayinsa na gaskiya. Saboda haka na ke rokon alfarmar afuwarka na abubuwan da na nemi na haifar tsakaninka da Unaiza da kuma Janne. Sannan ina rokon alfarmar ci gaba da rike ni a matsayin 'yar uwa.
AMINU
Mai ya kawo wadannan maganganun?
MAIRO
Fahimtar gaskiya, da kuma gane cewa mafi ingancin aure shine wanda a gina shi akan tsari mai kyau da kuma soyayya ta gaskiya, kamar irin soyayyar ka da Unaiza ko kuma nace soyayyar kai da Janne.
Yayi shiru yana kallonta ba tare da yace mata komai ba.
EXT. kAUYEN KUKI (RUGAR SU JABBI) - eVENING
Aminu da Jabbi suna zaune akwai damuwa a tare da Aminu.
JABBI
Ina son ka dauki komai da sauki. Duk wanda zai san abubuwan da ke faruwa zai fi yarda da aurenka da Mairo.
Aminu har yanzu bai ce da shi komai ba. Akwai yanayi na tunani a tare da shi.
JABBI (CONT'D)
Idan kuma kana ganin hukuncin da Baffa ya yanke akan tabbatar da auren ka da Mairo bai yi adalci ba, ni zan yi maka alkawarin dakatar da komai.
AMINU
Yayi maza ya kalli Jabbi
Wace irin magana ce wannan Jabbi? Kana son ka nunamin cewa Baffa kai kadai ya haifeka ko me kake nufi?
JABBI
Ba haka bane, Aminu. Na yarda komai rayuwa komai kaddara ne.
AMINU
Nima haka.
EXT. kAUYEN KUKI (RUGAR SU JABBI) - dAY
Mairo tana share hawayen da ke fuskarta. Janne ta yi shiru cikin yanayi na karaya.
MAIRO
Yaya kike jin aure tsakani na da Aminu?
Janne ta yi ajiyar zuciya, kafin su sake ci gaba da tafiya.
Janne
Haka rayuwa ta ke. Kowannen mu sai ya bi tafarkin da aka kaddara masa.
Suka fara yin nisa da wajen yayin da rana ke karasa sauka alamar zata fadi.
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (TSAKAR GIDA) - dAY
Baffa Bello na shirin fita, Inna wuro tana kintsa kaya.
INNA WURO
Cikin fillanci) Na ce ko Modibbo yasan da maganar auren nan?
BAFFA BELLO
(cikin fillanci) in sha Allahu gobe ma za ki ganshi.
Yasaba jallonsa ya fita.
EXT. gIDAN GARBA (tsakaR GIDA) - dAY
Dukkaninsu sun hadu, mazan a waje daya tare da Mallam Modibbo a gefe guda kowannensu yayi jungum-jungum.
mallam modibbo
Wannan ai lamari ne da ba zai taba yiwu ba.
Kowannensu yayi shiru ba tare da yace komai ba.
BAFFA BELLO
Ya kalli Modibbo cikin mamaki
Yo Modibbo menene rashin yiwuwarsa? Don sun tashi gida daya, an kuma reno su tare, menene aibunsa?
MALLAM MODIBBO
Ai ko da akwai.
Ya nuna Laraba cikin nufin abin da zai fada
Laraba kuma tafi kowa sanin dalilin da zai hana yin wannan auren.
Mairo ta kalle shi a rude kafin sauran da ke mamakin maganar Modibbo, musamman Laraba wadda ke kallon Modibbo a kurace.
LARABA
Modibbo me ye laifi na?
MALLAM MODIBBO
Sau nawa ina shigowa gidan nan ina tarar da ke kina shayar da ita nono? Kuma a matsayin musulmi Allah S.W.T. Ya lissafa wadanda haramcin aure ya tabbata a tsakninsu.
Ya nuna Aminu da Mairo cikin tabbatar da maganarsa
Ku biyun nan kun fado cikin waccan aya da ta ke cewa Wa akhwatakum minar rarda'ah" Da yar uwarku a wajen shayarwa ma'ana wadda aka shayar da ku tare.
DISSOLVE TO:
EXT. gIDAN BAFFA BELLO (TSAKAR GIDA) - dAY
Laraba na zuane da jinjinniyar a hannunta tana jijjigata ta yi bacci. Inna wuro ta fito daga daki dauke da kwaryar nono ta zo ta zauna kusa da Laraba.
INNA WURO
Tun da kika ce ba zaki sha ba to, ga nono nan sai ki tafi dashi.
LARABA
An gode.
Inna wuro ta nuna babu komai
Ni kuwa Inna wuro wani abu na keso na shawarce ki. Yarinyar nan gani nake kamar bai kamata a dauke ta da wuri haka ba, ko kuwa me kika gani?
INNA WURO
Ni kaina Laraba, tun ranar da aka kawo ta na so na yi maganar. To amma sai Baffa da muka yi maganar da shi naga kamar bai goyi baya ba shi yasa nima sai banyi miki maganar ba.
LARABA
To nima da na yiwa Baban Aminu magana yace min ai tun da ga madara ana bata babu abin da zai same ta.
Inna wuro ta gyara zama tana kallon Laraba
INNA WURO
Kinga kawai ki ci gaba da shayar da ita koda na karin wata shidda ne nan gaba tun da ba lallai ne ya sani ba. Kuma daman gashi duka duka yau mako nawa da barin cikin da kika yi?
LARABA
Kin ga kuma haka za'a yi.
BACK TO:
EXT. gIDAN GARBA (TSAKAR GIDA) - daY
Laraba ta sunkuyar da kanta cikin yanayi na nadamar abin da ya faru, yayin da kowa yayi shiru, musamman Mairo wadda hawaye suka kwaranyo mata kafin ta daga kai ta kalli Aminu wanda shi ma ya sunkuyar da kansa.
MATCH CUT TO:
EXT. gIDAN SU UNAIZA (KOFAR GIDA) - eVENING
Baffa Bello a tsaye laamun ya dade yana jira. Zuwa wani lokaci Tumano ta leko.
TUMANO
Ganinsa ya bayyanr da mamaki a fuskarta, ta juya ba tare da ta yi masa magana ba.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (TSAKAR GIDA) - eVENING
Tana dawowa ciki, Lambai zai fita zuwa waje.
LAMBAI
Waye?
TUMANO
Fuskarta cikin damuwa
Bello ne.
Lambai yayi jim ya juyo ya bita da kallo ta nufi daki.
LaMBAI
Wane Bello?
TUMANO
In ka isa ka gane.
Ya sake yin jim kafin ya juya ya nufi kofar gidan.
EXT. gIDAN SU UNAIZA (KOFAR GIDA) - eVENING
Jin motsin tahowar Lambai, Baffa ya juya inda suka yi ido biyu.
LAMBAI
Me ya kawo ka gida na? Abin da kuka yimin kai da abokinka, lokacin budurcin Tumano, shine yanzu kazo, dan dansa ya sake maimaitawa.
BAFFA BELLO
Cikin sassaukar murya
Haba Lambai, mafi cin ribar rayuwa shine wanda ya yafe kuskuren da aka yi masa.
Yayi shiru yana kallonsa
Kuma ai ko da kuka yi kasayyar neman auren Tumano da Marigayi Garba, ba gashi kai ne dai ka aure ta ba.
Lambai ya kawar da kai kamar ransa bai so ba.
BAFFA BELLO (CONT'D)
Lambai ka dauki komai na rayuwa kaddara ne. Haduwar Aminu da unaiza ba kai ne ko Garba ko kuma ni na hada ba. Wata haduwa ce ta kaddara.
Lambai yayi shiru yan mai sunkuyar da kansa cikin nadama.
Don haka ina fatan wannan ya zama wani sabon tushe na kulluwar zumunci mai dorewa tsakaninka da iyalin Garba Mai Angara.
LAMBAI
Yayi ajiyar zuciya ya kalli Baffa Bello cikin murmushi kafin ya mika masa hannu suka gaisa.
EXT. cIKIN DAJI (bakin kogi) - eVENING
Iska na kada ruwan wanda ke kwarara daga wani sashi zuwa wani. Akan ruwan inuwar Unaiza ce da Aminu wadanda suke zaune sun sa ruwan a gaba cikin yanayi na dauke kewa.
UNAIZA
Cikin sasaukar murya
Hakika kaddarar rayuwarmu, ita ta gadar da mu zuwa ga abubuwan da muke ciki. Kuma zan iya yarda da dukkan abin da zuciya tayi tunaninsa a karo na biyu.
Aminu yayi jim yana kallonta cikin fahimtar abin da ta fada.
AMINU
Ni kaina a yanzu na gane cewa, a koda yaushe amincin zuciya, shine ta kasance da wanda ta ke kauna. Don Haka ina fatan abin da ya faru tsakaninmu, ya zama matakin farko na tubalin da zamu gina rayuwar mu zuwa gaba.
Unaiza ta kalle shi suka yiwa juna murmushi.
UNAIZA
Godiya ga wanda ya riki abar kauna aminiya ta hakika.
Yana kallonta cikin murmushi
AMINU
Godiya ga wadda ta aminta da kaunar wanda ya ke sonta.
Suka yiwa juna wani lallausan murmushi.
FADE TO BLACK.