KI ZABE NI By Bala Anas Babinlata
EXT. harabar gida a cikin unguwa - aFTERNOON
Mata/yara
Mace na shigar da yara 'yan kasa da shekara biyar daki cikin
sauri tana boye su.
YAN POLIO MATA
Suna shigowa gidan.
Salamu alaikum, ga masu digon baki na polio.
Mace 1
Ta fito daga daki
Yaran ba sa nan, an kai su wajen kakarsu.
Yaro
Ya dan daga labule ya leko, suka hada ido da 'yan polio.
Yan POLIO MATA
Su dubi yaron dake leke ta kafar labule sannan suka dubi juna
cikin rashin fahimta, sannan suka dubi matar.
To, sai an jiman ku.
INT. zauren gida 2 - aFTERNOON
Yar POLIO
Wannan aiki da wulakanci yake, ni fa wallahi na
soma gajiya.
EXT. gidan biki kofar gida - eVENING
Masu kalangu na ta cashewa yayin da mata 'yan biki ke ta liki
wasu na rawa. Da dama daga cikin su sun yi shigar anko.
Dakta husna
(35) Cikin kwalliyar biki tana rike da hannun Hafsa suna ta raha
yayin da suke kallon 'yan rawar.
Hafsa
(10) Ta yi wa Husna rada yayin da Husna ta gyada kai alamar
amince wa sannan ta shiga cikin 'yan rawa suna rawa ana ta yi mata dariya.
DAKTA HUSNA
Wayar dake rike a hannunta ta yi zuruftu wanda ya ja hankalinta
ta duba. sunan Baban Hafsa ya bayyana a kan
gilashin wayar. Maimakon ta amsa sai ta kyabe baki gami da tsaki, ta cigaba da
hirar ta da matan da suke tare.
Can jimawa wayar ta sake zuruftu a hannunta ta sake duba wa rai a
bace, amma wannan lokacin sai ta ga Dakta Umar ne. Ta dan yi murmushi, yayin
nan ta nemi uzuri cikin gaggawa ta bar cikin hayaniyar ta koma daga cikin gida
inda babu yawan hayaniya.
Helo Umar. Na fa ce maka ina wajen biki, ko mene
ne ba zan dawo ba.
Dakta umar (V.O.)
Na sani, kawai dai na kasa jurewa ne shi ne na
kira don na ji sautin muryarki, ranki ya dade.....
DAKTA HUSNA
Ban ce maka bana son ranki ya dade din nan ba.
DakTA UMAR (V.O.)
Ya kyalkyale da dariya.
Tuba nake yi ranki ya.... Af! Husna. Ni na rasa
irin wannan danyen hukunci, Allah ya baiwa mutum daukaka amma ya rinka gudunta.
DakTA HUSNA
Ta yi murmushi.
To na ji sai da safe idan na shigo....
Jimmai
Ta iso inda Husna take cikin gaggawa da alamun tashin hankali a
tattare da fuskarta.
DakTA UMAR (V.O.)
A'a, akwai maganar da nake so mu tattauna.....
JiMMAI
Husna! Don Allah kawo mana agaji wani yaro ne a
nan makwabtanmu babu lafiya don Allah yiwo azama ki zo mu je....
DakTA HUSNA
Umar ka yi hakuri sai dai da safen ma yi maganar,
sai na dawo.
Ta kashe wayar ta maida ta jaka sannan cikin sauri ta bi jimmai
suka fita.
EXT. kan
layi unguwa - eVENING
Jimmai na gaba Husna na biye da ita a baya, yara na yin ball a
layin. Yayin da suka iso daf da wajen, ball din ta fada cikin kwatami, kiris ta
bata su. Wani yaro ya je ya tsoma hannu ya fiddo da ball din ya goge ta a kasa
suka cigaba.
Layin kaca kaca yake da bola da kwatami. Ga wani famfo daf da
kwatamin yara sun yi layi da bokitai suna diban ruwa.
EXT. tsakar gidan su larai - eVENING
Tsakar gidan kaca kaca da shirgi iri iri ga wasu yara sun gewaye
kwano daya suna cin abinci, a can kofar bandaki wani yaro na zaune akan fo yana
kashi.
DakTA HUSNA
Duk ta lura da wannan ne cikin kallo daya yayin da take biye da
jimmai a baya suna nufar inda matar ke zaune rungume da yaron.
Salamu alaikum.
Larai
Amin wa alaikus salamu.
JiMMAI
Larai ga Husna din na kira miki don ta duba shi.
Babbar likita ce.
LaRAI
Ta dubi Husna cikin tashin hankali.
Sannu da zuwa.
DakTA HUSNA
Ta risina a gaban Larai tana duban yaron.
Me ke damunsa?
LaRAI
Zazzabi ne mai zafi a jikinsa kuma wuyansa ya
sandare.
DakTA HUSNA
Ta yi sauri ta dubi Larai.
Tun yaushe ya fara?
LaRAI
Tun shekaranjiya da rana bayan sun gama cin
abinci.
DakTA HUSNA
Kun je asibiti ne?
LaRAI
Ta girgiza kai.
Bamu je ba. Dede mai magani ce ta bayar da wasu
saiwoyi aka jika masa.
DakTA HUSNA
Ta kura mata ido cikin shakka da kaduwa
Lokacin da aka haife shi an yi masa BCG?
LARAI
BCG? Mene ne haka kuma?
DakTA HUSNA
Suka dubi juna ita da Jimmai sannan ta sake duban Larai.
BCG allura ce da ake yiwa jarirai daga ranar da aka
haife su zuwa sati daya, sannan akwai jerin allurai da ake yi wa jariri har
tsawon watanni tara na rigakafin kyanda da
shan inna da cizon sauro a yanzu har da na rikafin ciwon hanta.
LARAI
Ta girgiza kai.
Ba a yi masa ba. Ke ni fa rabona da zuwa asibiti
har na manta.
DakTA HUSNA
Digon baki fa an taba yi masa?
LaRAI
Ni 'yar gidan digon baki, mazajenmu sun ja
kunnenmu da kada mu kuskura mu bari
a yiwa 'ya'yansu. Digon bakin da aka ce makircin turawa ne na hana haihuwa.
DakTA HUSNA
Ta girgiza kai cikin takaici, yayin da ta waiwaya ta kalli yaran
dake gewaye da kwanon abinci suna ta ci.
Yara 'yan shekara biyar da wadanda basu kai biyar
ba nawa ne a gidan nan?
LARAI
Su bakwai ne maza uku har da shi mata hudu, wani
abu ne?
DakTA HUSNA
Ina mai fargabar kamar ya kamu ne da cutar shan
inna. Zazzabi, ciwon ciki, ciwon kai daga nan jijiyoyi su dauka, sai dandarewar
wuya ko hannu ko kafa. A karshe zazzabi ya tsanananta. Wannan duk alamomi ne na
cutar shan inna.
Ta ja numfashi.
Me ya sa ba zaki kai shi asibiti ya samu kulawar
likita ba? jinkiri a irin wannan yanayin na da matukar hatsari.
LARAI
Ta dan yi shiru cikin sanyin jiki da damuwa.
To, sai dai idan maigidan ya dawo na tambaye shi,
ban sani ba ko zai yarda.
DakTA HUSNA
Ta bude jakarta
ta fiddo da biro da takarda ta rubuta wasu maganguna ta mika wa Larai.
Ga wannan maganin ku saya ku bashi, zai dan
taimaka ga zazzafan zazzabin.
Yaro
Wanda ke zaune a kan
fo.
Umma na gama kashin.
Umma (V.O.)
To, Ladidi je ki zubar a masai ki yi masa tsarki.
Ladidi
Bamu gama cin abincin ba.
UmMA
Ku yi maza ku gama.
Dakta Husna da Jimmai suna fita daga gidan lokacin da yarinyar ta
tafi yiwa kanin nata tsarki tana tafe tana sude hannu. Suka dubi juna, Husna
cikin mamaki.
INT. asibiti ofishin dakta husna - mORNING
Tana tsaye a gaban kalanda tana dubawa hannayenta a harde a kirji
lokacin da wayarta ta yi kara ta nufi wajen wayar ta daga ta duba. Ta kurawa
wayar ido dan lokaci ba tare da ta amsa ba sai ta mayar da ita kan tebirin ta ajiye.
Wayar ta yi ta ruri har ta gaji ta daina.
Aka kwankwasa kofa.
Yes, shigo.
DakTA UMAR
(38) Ya turo kofa ya leko yana murmushi.
Baki yi min waya kin ce kin dawo ba.
DakTA HUSNA
Baka yi min waya ka tambaye ni ko na dawo ba.
Dakta uMAR
Ya shigo ya mayar da kofar ya rufe kana ya nufi inda take.
Jiya kin azabtar da ni a gidan nan. Dama haka aiki
biyu yake da wahala? Dana koma gida kasa moruwa na yi, in ban da Mama ta tashe
ni yau sai na makara.
DakTA HUSNA
Ka yi sa'a Mamanka mai tashin asuba ce.
Wayar ta sake yin kara karo na iyu ta je ta leka sannan ta ja
numfashi, ta ja baya ta kyale wayar na cigaba da kara.
Dakta uMAR
Ki amsa mana, ke ce fa kike ce min wulakanci ne
kin daga waya.
DaktA HUSNA
Ta dubeshi.
Gaskiya ne wulakanci ne. Shi nake yi a halin
yanzu.
Dakta uMAR
Ya soma kokarin yin magana amma ganin ta tsare shi da ido sai ya
bushe da dariya.
To na yi shiru wai yaro ya ga kara.
DakTA HUSNA
Ka kyauta.
Suka jira har wayar ta kare rurinta ta yi shiru.
Dakta uMAR
Jiya ina yi miki magana kika katse ni.
Ya sosa keya.
Dama..... Mama ce.....
DakTA HUSNA
Mama ce me? Ka fada mana.
Dakta uMAR
Ta ce na gayyato ki tana son ganin ki.
DaktA HUSNA
Ta harare
shi.
La! Ka gaya
mata?
Dakta umaR
To me za a jira?
DakTA HUSNA
Ta girgiza kai.
Yau na shiga uku. Ka cika gaggawa wallahi, yaya
zaka gaya mata
haka da wuri.....
Dakta uMAR
Mene ne abin boye boye a maganar aure? Mene ne don
ta sani? Husna ko dai alkunya kike yi min ne ba kya ra'ayina.......
DakTA HUSNA
Ta yi masa alama da hannu ma'ana ya yi shiru.
Ina sonka. Ko kana so na sauya ra'ayina ne.
InT. ofishin umar - mORNING
Dakta alIYU
Ya kwankwasa kofar.
Umar.
Da ya ji shiru sai ya tura ya shiga.
Umar....
Ya lura lalita na yashe a gabansa a bakin kofa, ya sunkuya ya
dauka, sannan ya dubi cikin ofishin wanda babu kowa a ciki.
INT. aSIBITI OFISHIN DAKTA HUSNA - mORNING
DakTA HUSNA
Dama a bikin nan da na je jiya wani abu ya faru da
nake so mu yi maganar da kai.
Dakta uMAR
Mene ne fa?
A daidai lokacin suka ji karar wadda ta katse su.
Mai tsohon ciki (o.S.)
Wayyo Allah na, ku cire min cikin nan na huta
bayin Allah, wayyo zan mutu....
Suka yi waje cikin sauri ya zuwa inda matar ke karaji.
INT. falon Asibiti - mORNING
Mai TSOHON CIKI
Da ritsetsen ciki tana ta juyi, wata mace na rike da ita. Maza
biyu saurayi da magidanci na tsaye cikin gidadanci suna kallon ikon Allah.
Nas 1
Ke don Allah ki rufe mana baki haka da ihun banza.
Wani ya ce kar ku zo asibiti da wuri. Idan ba zata yi shiru ba ku fita da ita
can waje ta kari ihunta.
Dakta husna/dakta umar
Suka iso wajen.
Me ke faruwa?
Nas 1
Kin ganta nan Dakta, ko awo bata taba zuwa asibiti
ba, ta zo ta cika wa mutane kunne da ihu.
DakTA HUSNA
To, ki bita a hankali, fadan ba zai maganta komai
ba.
NAS 1
Dakta ai dole ne mu yi fada, a ce ba zasu taba
zuwa asibiti ba sai sun shiga bala'i. Sai da haihuwa ta zo da matsala suka tuna
akwai asibiti, su kwaso ta rabe rabe su jibge mana alhalin bamu san halin da
cikin ke ciki ba.
DakTA HUSNA
Na fahimci damuwarki, amma fada ba zai yi maganin
matsalar ba. Ki bita a sannu.
Dakta uMAR
Wayarsa ta yi kara ya fiddo ta ya duba, ya ki amsawa.
Wane ne mijinta?
Mijin mai tsohon ciki
Ya matso gaba.
Gani nan likita.
Dakta HUSNA
Ta dubi wayar dake hannunsa sannan ta dube shi.
Dakta uMAR
Ko ya kalli inda take.
Me ya sa ba ku kawo ta da wuri ba?
MijiN MAI TSOHON CIKI
Ya share hawaye daga kunci.
Babata ce ta hana, likita, tun da ta fara nakuda
na ke ta nacin a taho asibiti.
Dakta HUSNA
Ba tare da ta daina kallon Umar ba.
Tun yaushe ta fara nakudar?
MiJIN MAI TSOHON CIKI
Tun shekaranjiya.
DakTA HUSNA
Ta isa ga mai cikin ta kama
hannunta tana dubawa, kana tana dudduba kwayar idonta.
Mai TSOHON CIKI
Ta sake yin kara.
Wayyo Allah cikina! Ku agaje ni!
Sai jini ya balle.
Dakta uMAR
Subhanallahi! Don Allah wani ya samo kura a
dauketa.
Dakta HUSNA
Ta fiddo wayarta ta kai kunne.
Helo, Azumi. Me kike yi? Don Allah yi maza ki zo.
Dakta uMAR
Wayarsa ta sake yin kara.
DaktA HUSNA
Umar kiranka ake a waya fa.
Dakta uMAR
Ina sane, ni ma koyi nake yi dake.
DakTA HUSNA
Ta kura masa ido. Bai kalle ta ba ya mayar da hankalinsa ga Mai
kurar daukar maras lafiya ya nufo su har ya iso. Aka dauki mai cikin aka dora
ta aka tura ta zuwa ciki.
Wayarta ta amsa ta duba sannan ta kai kunne.
Hello dakta, ina kwana? ba gajiya. An tashi
lafiya? Eh muna tare. To.
Ta dan kawar da wayar yayin da ta dubi Umar.
Dakta Aliyu ne ke magana. Ya ce a gaya maka yana jiranka a ofishinka.
Dakta uMAR
Me ya sa kika ce masa muna tare?
DakTA HUSNA
Karya kake so na yi masa.
Dakta uMAR
Wallahi zuwa zai yi ya uzzura min. Da aikina zan
ji ko da nasa.
DakTA HUSNA
Ta ja numfashi.
Umar, ya kamata ka gode Allah. Kai kadai ne
likitan laka a asibitin nan, me ya sa bai nemi wani ba ya zo wajenka. Bayan
haka ma ai abokinka ne.
Dakta azumi
Ta iso. Suka gaisa da Dakta Umar.
Me ya faru ake nema na?
DakTA HUSNA
Wata mai doguwar nakuda ce ke zubar da jini. Ga
dukkan alamu sai an yi mata aiki.
DakTA AZUMI
Tana ina?
DakTA HUSNA
Yanzun nan aka shiga da ita. Shiga mana tana ciki
yanzun nan zan shigo.
A daidai lokacin da Dakta Azumi ke shigewa ciki. sai Mijin Mai
cikin ya yi yunkurin shiga shi ma. Wata Nas ta tare shi ta hana shi shiga.
Nas 2
Malam ina zaka? Ka jira a waje tukuna.
DakTA HUSNA
Ta waiwaya ga Dakta Umar.
Bayan sallar magariba.
Dakta uMAR
Ya dube ta cikin rashin fahimta.
Bayan sallar magariba me?
DakTA HUSNA
Ta yi murmushi.
Ba ka ce Mama na son gani na ba? Zan zo bayan sallar
magariba.
Dakta uMAR
Au, har na sha'afa wallahi. Bayan magariba?
DakTA HUSNA
Ta gyada kai sannan ta yi sauri ta shiga ciki ta bar shi nan a
tsaye yana murmushin farin ciki.
INT. asibiti falo - mORNING
NaS 2
Ta shigo cikin falon tana gaba.
MiJIN MAI TSOHON CIKI
Yana biye da ita. Har suka isa
inda Dakta Azumi ke zaune.
Dakta aZUMI
Ta dube shi.
Malam, matarka ta galabaita ainun, ta zubar da
jini mai yawa. Haka nan ba zata iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata aiki.
MiJIN MAI TSOHON CIKI
Ya kura wa Dakta Azumi ido cikin karaya.
To, likita mene abin yi yanzu?
DakTA HUSNA
Wadda ke fitowa daga dakin wayarta ta yi kara, ta fiddo ta ta
duba ganin mai kiran ta yi tsaki ta kashe wayar gaba daya.
Ta karaso ta tsaya yayin da suka yi musayen kallo da Dakta Azumi.
Dakta aZUMI
Ta mayar da hankalinta ga mijin mai cikin.
Za a iya yi mata aiki a fitar da dan, amma maganar
gaskiya babu tabbacin tserar da ranta.
MiJIN MAI TSOHON CIKI
Kamar yaya likita ban fahimta ba.
DakTA HUSNA
Ma'ana komai zai iya faru wa idan aka yi aikin.
MiJIN MAI TSOHON CIKI
Ya soma kuka kasa kasa cikin damuwa.
Ina son matata.
DakTA HUSNA
Zamu iya bakin kokarinmu mu ceci ransu gaba daya.
Amma dai yanzu akwai bukatar a kara mata jini har leda biyu cikin gaggawa.
Doguwar nakudar ta galabaitar da ita ainun.
Dakta aZUMI
Ku je kai da 'yan uwanka a gwadaku a sashen diban
jini.
Ta dubi Nas 2.
Kwatanta masa wajen diban jinin.
Lebura
Suna barin wajen shi kuma leburan ya yi sallama ya shigo. Ya dubi
dakta Husna.
Dakta, Alhaji Hamza ne yake magana dake
Dakta HUSNA
Ta dubi leburan cikin takaici, sannan suka yi musayen kallo da
Dakta Azumi.
Dakta aZUMI
Baban Hafsa ne yake ta kiranki a waya tun dazu?
Husna ta gyada kai.
Ke kawai ki je babu damuwa, ai akwai sauran lokaci
kafin su kawo jinin.
DaktA HUSNA
Wallahi bana son zuwa wajen mutumin nan.
Dakta aZUMI
Gwamma ki je, kin san nacinsa.
INT. oFISHIN UMAR - mORNING
Dakta Umar
Ya tura kofar ofishin ya shiga.
Ta ina ka shigo?
Dakta alIYU
(40)Zaune a kujera da jarida a hannu yana dubawa, ya cira kai ya
dubi Umar.
Ta taga na shigo.
Ya ajiye jaridar.
Albishirinka mutumina.
Dakta uMAR
Ya ki cewa komai.
Dakta alIYU
Kai dai ka amsa mana.
Dakta uMAR
To goro.
Dakta aliYU
A'a, ba goro ba, kaza.
Ya mike ya isa ga tebir ya janyo filet din cinyoyin kaza guda
biyu babba da karama.
Ina fata baka karya ba.
Dakta uMAR
Ya bushe da dariya.
Lallai yau za a yi ruwa da kankara,
duk matsolancin nan naka.
Ya isa ga tebirin ya mika hannu zai dauka.
Bari
na dauki karamar.....
Dakta alIYU
A'a, dauki babbar, ni karamar ta ishe ni.
Dakta uMAR
Allah mutumina, wane irin imani ne ya zo maka haka
ne.
Dakta alIYU
Haba, sai imani ya zo min zan ciyar da abokina. Ni
ba ma haka ba, me kuke ciki ne da mutuniyar.
Dakta uMAR
Ya dauki cinyar kazar ya figa.
Yau zasu gana da Mama, ta ce zata je bayan
magariba.
Dakta alIYU
Ah har maganar ta shiga gida kenan? ka ce ciniki
ya kusa fadawa.
Dakta uMAR
Ka ga yi min bayani, mene ne sadakin wannan
hidimar ne, na san dai ungulu ne kai baka jewar banza.
Dakta alIYU
Yarinya budurwa 'yar shekara goma sha tara na kashin jini
Dakta uMAR
Gastrointeritis ne da dehydration.
Dakta alIYU
Ya girgiza kai yayin da ya isa ga tebur ya dauko takardar ya
duba.
Bana zaton haka, don kuwa tana gani dishi dishi,
kuma ta kan
shiga rudu na wucingadi.
Dakta uMAR
Ya karbi takardar sannan ya matsa bakin taga ya janye labule kana
ya nazarci rubutun. Ya ci naman cinyar kaza.
An yi scanning din kanta?
Dakta aliYU
A'a. Me zai sa a yi scanning din kanta?
Dakta uMAR
Bugawar zuciyarta fa?
Dakta alIYU
Stable, babu wata matsala. Ina ganin me zai hana
mu je ka ganta da kanka.
Dakta uMAR
Wai baka sayo ruwa ba ne?
Dakta alIYU
Ya rike baki.
Af! Na manta wallahi. Ba komai sai wani jikon,
idan irin wannan ta faru zan tabbatar na sayo har da ruwa.
Dakta uMAR
Ya shafa aljihunsa.
A'a, a ina na bar walet dina ne?
Dakta aliYU
Ita ce wannan?
Yana rike da ita a hannunsa.
Dakta uMAR
Ya dubi hannun Aliyu.
A ina ka ganta?
Dakta aliYU
A bakin kofa ka yar, a nan na ganta lokacin da na
shigo.
Ya cilla wa Umar.
Dakta uMAR
Ya saki takardar yayin da ya cafe wallet din. Yana
kokarin sa ta ne a aljihu lokacin da ya kura wa tagar ido.
Dakta Husna tare da wani mutum a tsaye a kusa da wata mota suna
magana. Ya waiga ya dubi Aliyu.
Ina zuwa.
Bai jira amsa ba ya fice cikin sauri. Ya je ya leka yana dubansu.
EXT. asibiti haraba - mornING
Dakta HUSNA
Da hausa fa nake gaya maka ba da wani yare ba. Na ce maka kada
ka sake zuwa wajen aikina.
Hamza
To, idan ban zo ba yaya zan yi? Na buga miki waya
kin ki dauka a karshe ma kin kashe min
waya. Na je gida kin ki saurarena. Yaya kike so na yi da raina.....
DakTA HUSNA
Ba abin da ya dame ni ba ne wannan. Kuma idan kai
maye ne to kurwata da daci. Zan gaya
maka magana ta karshe, daga yau ka fita harka ta. Kada ka sake zuwa wajena.
Ta juya a fusace ta bar shi nan a tsaye.
HaMZA
Maman Hafsa! Maman Hafsa!
Bata ko waiwaya ba, ya zura hannu a aljihu ya fiddo wata kwalbar
magani ya zazzaga ya afa a baki ya zura hannu cikin motarsa ya fiddo robar ruwa
ya kora ya dafe kansa.
Dakta Umar
Na tsaye yana kallon abin da ke faruwa.
InT. asibiti korido - mORNING
Dakta Husna ta mike cikin sauri a fusace da nufin komawa bakin
aiki.
Dakta uMAR
Husna!
Ta waiwaya da ta ga Umar ne sai ta tsaya. Ya isa gare ta.
Wane ne wancan kuke tankiya?
Dakta HUSNA
Ta dube shi dan lokaci.
Mijina ne.
Dakta uMAR
Cikin rashin fahimta.
Mijinki kamar yaya?
DakTA HUSNA
Baban Hafsa ne. Tsohon mijina. Shi ne ya yi ta
bugo min waya dazu na ki amsa wa, har kake cewa na yi wulakanci.
Dakta uMAR
Ya saki baki cikin mamaki.
Ah! To me ya zo nema kuma, ba kun dade da rabuwa
ba?
Dakta husna
Haka ne. Ya zo ya roke ni ne a mayar da aurenmu.
Suka kura wa juna ido dan lokaci yana mai kasa gaskata abin da ya
ji.
Ta yi murmushi.
Ka kwantar da hankalinka. Bayan sallar magariba
alkawarinmu yana nan. Zan zo mu gana da sirikata.
LeBURA
Ya iso cikin sauri.
Ranki ya dade, Dakta Azumi ta ce a gaya miki sun kawo jinin.
Dakta uMAR
A'a, dakata dakata! Ban gane ba. Ranki ya dade?
Wannan wane irin kabilanci ne, an yarda wasu su fada amma ba a yarda wasu su
fada ba?
DaktA HUSNA
Matsayinka ne bai kai ba tukuna.
Ta yi dariya ta juya ta tafi ta barshi nan a tsaye.
Har Adamu Lebura ya soma tafiya sai Umar ya kirashi.
Dakta uMAR
Don Allah Malam Adamu zo ka sayo min ruwan sha
mana.
Ya fiddo wallet dinsa zai fiddo kudi, idanunsa suka fito alamar
gane lalatar da Aliyu ya yi masa. Ya zaro 'yan ragowar kudin dake cikin wallet
din ya jujjuya su sannan ya dubi Adamu.
Shi kenan ma jeka abin ka na gode.
Ya dan yi tunani cikin girgiza kan takaici.
InT. asibiti falo - mORNING
Ana kara wa mai cikin jini yayin da mijinta ke sa hannu a
takardar amincewa a yi mata aiki. Husna na shigo wa a daidai lokacin.
INT. asibiti dakin tiyata - aFTERNOON
Dakta Husna da Dakta Azumi na daura kayan tiyata.
Dakta aZUMI
Ke, Na ji an ce Umar ya ganku a tsaye lokacin da
kika je wajen Hamza.
DakTA HUSNA
Gaskiya ne ya gan mu.
Dakta aZUMI
Wai yaya kika ga hawan jini wajen Umar.
Suka kyalkyale da dariya.
DaktA HUSNA
Ai kuwa jinin nasa ya hau. Ko kin san bai taba
ganin Hamza ba sai yau.
Dakta aZUMI
Ke don Allah!
Dakta HUSNA
Mhm! Yau dai zan je mu gana da mahaifiyarsa.
Suka nufi cikin dakin tiyatar.
Dakta aZUMI
Ki ce magana ta yi karfi. Lallai mun kusa amarce
wa.
Suka sake bushe wa da dariya yayin da suke kulle dakin tiyatar.
INT. asibiti dakiN TIYATA - aFTERNOON
Suna yi wa mai doguwar nakudar tiyata suka fito da dan sai kuka
yake yi. Sannan suka taru a kan
uwar suna ta kokarin ceto ranta. A karshe rai ya yi halinsa.
Suka dubi juna.
DaktA HUSNA
Ta dubi agogon bango.
Ta rasu da karfe 12.33
Sannan ta waiwaya ta dubi wani dalibin dakta da suka shiga
tiyatar da shi.
Dakta Kabiru, je ka sanar da mijinta.
Dakta kabiru
Ya gyada kai cikin fahimta sannan ya fita daga dakin.
Dakta aZUMI
Ta girgiza kai, yayin da suke fita daga dakin suna kwance daurin
bakinsu sun bar nas biyu na karasa aikinsu.
Allah ya gani mun yi iya kokarinmu.
Dakta HUSNA
Kada ki zargi kanki, daman kafarta daya a duniya
daya a lahira aka kawo ta asibitin nan. Wannan ce matsalar doguwar nakuda.
Dakta aZUMI
Allah sarki, wannan yaro zai ga maraici.
EXT. gidan su Umar kofar gida - nighT
Dakta uMAR
Yana tsaye a kofar gida yana
duba agogo yana ta hange hange cikin kaguwa da karaya.
Dakta HUSNA
Ta iso a motarta, ta tsaya a kofar gidan yayin da ya isa cikin
sauri da zumudi ya bude mata kofa.
Ta ziro kafarta waje ba tare da ta fito ba.
Dakta uMAR
Har kin sani fargaba. Na zaci ba zaki zo ba.
Dakta HUSNA
Ko na koma ne?
Dakta uMAR
Ya harareta.
Ba sai na ga ta inda zaki bi ki koma din ba.
Suka tuntsure da dariya.
Dakta HUSNA
Ta ja dogon numfashi.
In gaya
maka gaskiya, wallahi ji nake yi kamar na koma din. Wata irin kunya nake ji a
raina. Wai yau zan yi gaba da gaba da Mama.
Dakta uMAR
Kin ga ki kwantar da hankalinki. Babu wani abu.
Fito mu shiga.
DakTA HUSNA
Ta goge fuskarta ta gyara daurin dan kwalin ta fito daga motar ta
sake yafa mayafin.
Yaya ka ganni?
Dakta uMAR
Ya dubeta daga sama zuwa kasa ya yi murmushi.
Komai ya ji.
EXT. gidan dakta Husna haraba - niGHT
HamZA
Ya danna hancin motarsa cikin harabar gidan ya shiga a daidai
lokacin da wani yaro ke kokarin shiga cikin gidan.
Kai yaron nan don Allah zo mana.
Yaro dan aike
Ya zo ya tsaya yana duban Hamza.
Gani.
HamZA
Don Allah idan ka shiga ka ce ana sallama da
Husna.
Ya jira a cikin mota yayin da yaon ya shiga gidan, jim kadan sai
ga yaron ya dawo.
Yaro DAN AIKE
Wai tana asibiti ba ta dawo ba.
INT. gidan su umar falo - niGHT
Zannira
Ta shigo falon dauke da tire, da lemo da kufuna a kai.
Ina yayar tawa? La! ke ce Dakta Husna. Sannu da
zuwa.
Ta isa gareta ta zauna kusa da ita ta ajiye tiren.
Dakta HUSNA
Sannun ki.....
ZANNIRA
Barista Zannira, bai gaya miki sunana ba?
Dakta HUSNA
Au! Ke ce Barista Zannira?
Dakta uMAR
Ya shigo dakin.
Zannira kawai sunan ta, bata zama barista ba.
ZaNNIRA
Yaya faruku, saura fa shekara daya kawai na tafi Law School.
Dakta uMAR
Ya nuna ta da dan yatsa.
Kin gan ta nan doki har doki amma kofaton sakaina.
Duk gidan nan ma'aikatan lafiya ne, ita kadai ta fitar da kanta daga dangi don
fitinar tsiya.
ZANNIRA
Wallahi na ki jinin asibiti idan mutum ya shiga ya
yi ta tuna mutuwa.
Ta dubi Husna.
Yi hakuri ba fa bakar magana nake yi ba.
Dakta HUSNA
Ta kada kai.
Kina da 'yanci ki fadi ra'ayinki.
Dakta uMAR
Sai ki zauna ki yi gadin duniya tunda ba kya son
mutuwa.
ZANNIRA
Idan na zama lauya kawai ka je ka taro rigima na
tsaya maka.
Dakta umAR
Ke don Allah tashi ki fice kin ishe mu.
DaktA HUSNA
A'a kyale ta ta debe min kewa kafin Mama ta fito.
ZANNIRA
Ta yi zumbur ta mike tsaye.
Don ma ka samu a shigo din, shi ne sai ka yi min
wulakanci. Na fita din da me zan ragu.
A fusace ta fice daga dakin.
Dakta HUSNA
Gaskiya baka kyauta ba, ba a yin haka.
Dakta uMAR
Rabu da ita kawai, tana kara minti biyar nan sai
duk ta gundure ki. Ga Maman nan shigowa yanzu.
Dakta HUSNA
Ta sake gyara daurin kanta ta dan tattaba fuskarta. Sannan ta ja
dogon numfashi. Kana ta sake gyara lullubin kanta.
Dakta uMAR
Don Allah ki sa ranki a inuwa.
Ya samu kujera dake can gefe ya zauna.
Kofa ta bude, Mama ta shigo, Husna ta mike tsaye cikin girmamawa
da jin kunya.
Mama
Salamu alaikum.
Ta shigo ta cakare kamar wata yarinyar mace, ta bi Husna da kallo
yayin da ta nufi kujera da kwamfuta laptop a rike a hannunta.
Barka da zuwa sirikata ta kaina.
Ta isa ga kujera ta zauna.
DakTA HUSNA
Ta durkusa daga inda take tsaye.
Ina wuni?
Mama
A'a, matso nan kusa da ni mu ga juna sosai. Ai kin
yi nisa.
Dakta uMAR
Mama kunyarki fa take ji. Ki bi a hankali.
Mama
Babu kunya a tsakaninmu, matar da zata aure min
da, gwamma dai ta matso kusa dani.
Husna ta mike cikin sanyin jiki ta koma kusa da sirikarta ta
durkusa, Mama ta ajiyer kwamfutar sannan ta kama
hannunta ta zaunar da ita akan kujera kusa da ita.
"yata, yaya sunanki?
Dakta uMAR
Sunanta Husna.....
Mama
Ta dube shi.
Bana son surutu, ko kai na tambaya?
Ta mayar da hankalinta ga Husna.
DakTA HUSNA
Sunana Husna.
Mama
Husna.
Ta dubeta daga fuska har kafa, sannan ta kura wa zanin ido dan
lokaci ta mika hannu ta kama zanin ta dan
murza.
Wannan yadi da kyau yake.
Sannan ta dubi Husna wadda ke cike da kunya.
Ga kuma tsada, ko?
Ta kai kallonta ga agogon hannun Husna.
Omega Gold.
Hankalin Umar ya tashi ainun ya saki baki a daidai lokacin da ya
ga ta kai zanin hancinta ta sansana.
Mhm! Marvin xtra. na ga alama kina son kayayyaki
masu tsada.
Har yanzu kan
Husna na kasa bata ce uffan ba ta rasa yadda zata yi saboda kunya.
Dakta uMAR
Mama don Allah ki bi a sannu.....
Mama
Wai da ita nake magana ne ko da kai? Bana son
rashin kunya.
Ya dafe kai yayin da ya mike tsaye ya shafa fuska kana ya juya
baya. Yayin da Mama ta mayar da hankalinta ga Husna.
Kin taba yin aure?
DaktA HUSNA
Ta gyada kai.
Na taba yi.
Mama
Kin taba haihuwa?
Dakta HUSNA
Ta cira kai a hankali ta dubi sirikarta.
Ina da 'ya 'yar shekara takwas.
Sannan ta waiwaya suka hada ido da Umar kana ta sake sad da kai.
Dakta uMAR
Mama cewa kika yi fa na kawo ta ki ganta ba wai ki
tuhumeta ba.....
Mama
Faruku kai dana ne, ita kuma matar da zaka aure, a
matsayina na uwarka ina da hakki na san komai game da ita kafin ku yi aure.
Ta sake mayar da hankalinta ga Husna.
'Yata, yana da muhimmanci yin nazari kafin a yi
aure. Na san kin san Faruku dan albashi ne ba dan kasuwa ba. Sai dai ina fata
kin kuma san Faruku saurayi ne bai taba aure ba.
Husna da Mama suka kura wa juna ido dan lokaci. Umar dake tsaye
yana duban su hankalinsa a tashe.
DaktA HUSNA
Wayar ta ce ta cece ta, lokacin da ta yi kara. Ta ciro wayar ta
duba sannan ta dubi Mama.
Don Allah ina neman afuwa, ana nemana ne.
Ta mike tsaye.
Zan tafi, na bar ki lafiya.
Ta nufi kofa ba tare da ta dubi Umar ba. Har ta je kofa.
Mama
Husna.
Ta waiwaya ta dubi Mama.
Na gode da kika samu lokaci kika zo, kin karrama
ni. Ki gaida gida.
Husna ta fita Umar ya bita a baya.
Mama (CONT'D)
Ta bi kofar da kallo dan lokaci tana mai yin murmushin nasara
sannan ta mika hannu ta dauki kwamfutarta ta dora a cinya ta ta zaro tabarau ta
kwama ta cigaba da aiki.
ExT. gidan su UMAR KOFAR GIDA - niGHT
Ya bude mata kofar motarta ta shiga, suka jima basu ce da juna
komai ba.
Dakta uMAR
Husna, don Allah ki yi hakuri, ban san abin da
zata yi miki kenan ba, da babu dalilin da zai sa ki zo.
Dakta HUSNA
Babu komai Umar, na ji dadin zuwa na. Ko babu
komai dai na karu.
Dakta uMAR
Kin karu kamar yaya?
Dakta HUSNA
Da ta maido ni cikin hankalina. Umar mahaifiyarka
bata sona.
Dakta umar
A'a, kada ki ce haka Husna. Ba wai sonki ne bata
yi ba, haka yanayin maganarta yake.
DaktA HUSNA
Ta tashi motar.
Shi kenan, sai dai mun gamu goben. Na tafi.
Ta ja motar ta tafi. Ya
tsaya nan yana dubanta cikin damuwa har ta bace sannan ya koma cikin gida.
INT. gidan su umar fALO - nIGHT
Mama
Ta bude shafin facebook tana hira kamar wata 'yar budurwa.
Dakta uMAR
Ya dawo cikin dakin ya dubi mahaifiyarsa.
Mama don Allah me yasa kika yi mata haka? Husna na
ganin girmanki, tana jin nauyinki, kin san abin da ta ce: wai ba kya sonta.
Mama
Bata dauke kanta daga kallon allon kwamfutar ba.
Faruku, mafarki a bacci kadai ake yin sa, yayin da
mutum ya farka ya kare.
Sannan ta dube shi a hankali.
Lokaci ya yi da ya dace ka wanke idonka, ko ka
nutsu, wannan yarinyar ta fi karfinka.
Dakta uMAR
Ta fi karfina kamar yaya.
Mama
Ta girme ka.
Dakta uMAR
Husnan ce ta girme ni?
Mama
Ina nufin ta girme ka da aure. Na farko dai bazawara
ce, na biyu dubi shigarta da zubinta, ba matar talaka ba ce.
Dakta uMAR
Mama babbar ma'aikaciya ce tana da hali, ba wai
don kudi take sona ba.
Mama
Faruku tana da 'ya budurwa. Ba tsarar ka ba ce.
Dakta uMAR
Ya dubi mahaifiyarsa dan lokaci.
Na sani Mama, amma ina sonta haka.
Mama
Ta dauki kwamfutar yayin da ta mike tsaye ta kalle shi.
To, Allah ya barku tare.
Ta shige cikin gidan ta bar shi nan a tsaye cikin damuwa. Ya
zauna a kujera ya dafe kai cikin tunani.
ZANNIRA
Yaya Faruku, har Dakta Husnan ta tafi ko ka kira
ni mu yi sallama.
Ya cira kai ya dubi Zannira bai iya cewa komai ba. Ta isa kusa da
shi ta zauna.
Ka san wani abu kuwa, wallahi ta yi min. Ashe ka
iya zabe. Allah ya sa ita zaka aura.
Dakta uMAR
Ya kura mata ido cikin tunani.
EXT. gidan dAKTA HUSNA HARABA - night
DaktA HUSNA
Ta iso gida ta tuka motar ta shiga harabar gidan ta yi fakin, ta
dan jingina da makarin siddin motar ta dafe kanta dan lokaci ta ja numfashi.
Sannan ta bude kofa zata fita sai ta lura da motar Hamza a tsaye
yana ciki yana dubanta. Tana zuro kafa tana fito wa yayin da shi ma ya fito ya
nufo wajenta. Ta rufe kofar motar zata shige cikin gidan ta barshi.
HamZA
Maman Hafsa! Maman Hafsa!
Bata tsaya ba balle ta waiwayo. Ya yi sauri ya tari gabanta.
Wajen ki na zo.
DaktA HUSNA
Ba na bukatar zuwan ka tuntuni na riga na shaida ma....
HamZA
Ina Hafsa?
DakTA HUSNA
Ta kura masa ido cikin tsarguwa.
Kana nufin ka dawo da bara bana ne? Ka san dai
baka da hakkin karbar ta, tuni ma mun gama da wannan shafin a kotu....
HamZA
Ni ba ina maganar karbar ta ba ne. Ina so ne kawai
na ganta.
Dakta HUSNA
Ta kura masa ido dan lokaci. Sannan ta ja numfashi.
Bata nan, na maida ta wajen Hajiya.
InT. asibiti koRIDO - mORNING
Dakta HUSNA
Ta biyo korido tana tafe suna gaggaisawa a hanyarta ta isa ofis.
Ta isa kofar ofishin ta tura zata shiga sai ta ji ana yi mata magana, ta
waiwaya.
Wata mata ce dauke da yaro wani mutum na biye da ita.
Ta dubi matar dan lokaci cikin rashin fahimta sannan ta tuno
matar.
Ko Larai ce?
LaRAI
I, ni ce.
DakTA HUSNA
Ta dubi yaron.
Lafiya me ya faru?
LARAI
Likita abin da kika fada min ne ya faru wuyansa ya
sandare. Dazu kafin mu taho har suma ya rinka yi.
DaktA HUSNA
Ku zo mu je ciki.
Ta fiddo wayarta ta yi kira.
Kana ofis ne? To, don Allah ka same ni a dakin
karamar tiyata mana.
INT. asibiti wani daki - mORNING
Ta shiga dakin, wasu nas su biyu suna diban kayan aiki a dakin,
ta karbi yaron daga hannun Larai ta kwantar da shi a wani dan gado.
Nas Nas din na gaishe ta.
DakTA HUSNA
Sista Amina zo nan don Allah.
Dakta uMAR
Ya shigo da sauri.
Husna lafiya dai?
DakTA HUSNA
Wani yaro aka kawo babu lafiya.
Dakta uMAR
Jikin sa ya yi dan sanyi, amma ya isa gareta ya kalli yaron.
Me ke damunsa?
DakTA HUSNA
Zazzabi da sandarewar wuya. Jiya na fara baka
labari game da zuwa na gidan biki hankalina ya yi wani waje.
Dakta uMAR
I na tuna.
Larai/mijin larai
Sun tsaya a gefe suna kallon ikon Allah.
DakTA HUSNA
Wannan yaron ne dalilin da ya sa ban saurari wayar
ka ba. Ina mai fargabar idan ba zazzabin sha inna ne a jikinsa ba.
Dakta uMAR
Ya isa ga yaron.
Me yasa kike zaton hakan?
Kamar amsa ga tambayar tasa, sai numfashin yaron ya shake.
Numfashin sa ya soma dauke wa.
Nan da na ya kinkime shi.
Mu shiga da ciki, sai an sa masa respirator....
Sista amina
Dakta bari
na karbe ka.
Ya mika mata shi ta yi sauri ta shiga cikin dakin, yana biye da
Nas din.
DakTA HUSNA
Ta bi bayansu, su Larai har sun biyo ta sai ta waiwayo.
Larai ku dan jira a nan, muna fitowa.
Ta ja labule.
INT. asibiti daki na musamman - mORNING
SisTA AMINA
Ta nufi gado ta kwantar da shi.
Dakta uMAR
Ya yi sauri ya dauko respirator ya isa ga yaron ya sanya masa. A
daidai lokacin da Husna ta isa gare shi.
DaktA HUSNA
Akwai matsala a rigakafin shan inna din nan Umar.
Dakta uMAR
Ya dubeta.
Kin ga wani abu ne?
DaktA HUSNA
Gidan da na je duba yaron nan baka ga kazanta ba.
Yaro na kashi a fo, yara na cin abinci
daf da shara. Ka san abin takaici dana tambayi uwar yaron ko an taba yi masa
digon baki sai ta ce wai mazajen su sun hana su saboda maganin hana haihuwa ne
turawa suka kawo.
Ta ja numfashi.
Ka san fargabar da nake yi. Da wuya in yaran nan
duk ba su dauke da kwayar cutar shan inna.
InT. asibiti wani falo - aFTERNOON
LARAI
Zaune cikin tagumi.
Mijin larai
Jingine da bango kansa kasa cikin zulumi.
Dakta husna/DAKTA UMAR
Suka fito daga dakin.
Larai/MIJIN LARAI
Suka yi sauri suka tashi suka nufi inda likitocin suke.
Yaya me ake ciki? Yaya jikinsa?
DakTA HUSNA
Ta dubi Umar ya gyada mata kai sannan ta dubi iyayen yaron.
Kyakkyawan labari dai shi ne: Numfashinsa ya dawo,
an yi masa allurai duk da dai ya galabaita da yawa, amma zai warware nan da dan
wani lokaci.
LaraI
Ta lumshe ido ta daga hannu sama.
Alhamdu lillahi! Har na ji dadi....
Dakta husnA
Mummunan labari shi ne: Saboda jimawa da ya yi
yana fama da ciwon a tsaitsaye hannunsa na dama ya nakasa ma'ana ba zai kuma
amfani ba. Sai dai hakuri, idan irin wannan matsalar ta faru, don bata da
magani.
Larai/MIJIN LARAI
Ta fara kuka yayin da mijin ta ya shiga salallami.
Dakta uMAR
Abin da ya faru gare shi ya riga ya faru, amma kuna da damar taimakawa a
rage faruwar hakan a nan gaba.
Mijin lARAI
Ya dubi likitan.
Ta wacce hanya kenan?
Dakta uMAR
Danku ya kamu ne da cutar shan inna, ita kuwa tana
faruwa ne ta hanyoyi kamar yin tsarki ba tare da wanke hannu da sabulu ba, cin
abinci ba tare da wanke hannu sosai ba, ko barin kazanta misali bayan gida idan
kuda ya hau kai ya tashi ya sauka a kan abin ci to da zarar an ci abincin za a
iya dauka. Duk wadannan hanyoyi ne da ka iya haddasa cutuka iri daban daban.
Mijin lARAI
Ya kurawa likitan ido cikin sauraro da nutsuwa.
Dakta uMAR
Na samu labari kun hana iyalanku su bari a yi wa 'ya'yanku
digon baki. Wanda shi ne rigakafin kare yaduwar ita wannan cutar. Yanzu ta yaya
zamu iya tabbatarwa bai harbi sauran yaran dake gidanku ba kai har ma da yaran
makwabta?
Ya kasa hada ido likitan saboda kunya da nadama.
Gyara kayanka ba zai zama sauke mu raba ba.
Mijin lARAI
Ya gyada kai.
Gaskiya na yarda kuskurena ne ya jefa dana cikin
wannan mawuyacin hali. Wallahi na yi matukar nadama.
Ya dan yi shiru na wani lokaci.
Zamu iya ganinsa?
Dakta HUSNA
Zaku iya ganinsa mana.
Ta nuna musu cikin dakin.
Ku shiga zaku ga wata ma'aikaciya ta nuna muku
gadon da yake kwance.
Bayan sun tafi sai Umar da Husna suka soma tafiya.
Dakta uMAR
Yau me ya faru ne? Zuwa na biyu ofishinki da safe
na tarar ba kya nan.
DakTA HUSNA
Makara na yi, wani abu ne?
Dakta uMAR
A'a, dama ina so na baki hakuri ne a kan abin a ya faru
jiya.....
DakTA HUSNA
Me ye kuma ya faru?
Dakta uMAR
Wayarsa ta yi kara ya fiddo ta ya kai kunne.
Helo Malam, kana ina yanzu? Dakin abinci? Okay, to
gani nan, ka saya da ni.
Suka tsaya a kofar ofishinta yayin da ya duba agogonsa.
Lokacin cin abinci ya yi, ko zamu wuce wajen cin
abincin ne?
DaktA HUSNA
Ta girgiza kai.
Ina da aiki da yawa a ofis je ka kawai abinka.
Wayar ta ta yi kara ta ciro ta duba.
Dakta uMAR
Ko na taho miki da take away?
DakTA HUSNA
Ta girgiza kai.
A koshe na fito daga gida.
Ta yi sauri ta shiga ofis.
Dakta umaR
Ya yi murmushin karfin hali ya juya ya wuce zuwa wajen cin
abinci.
DakTA HUSNA
Helo, ka ga kowace irin magana ce ke tafe da kai
bai dace ka rinka zuwa ofis kana damuna ba. To na ji, na ji ka same ni a gida
da dare idan na koma....
HamZA
Yana tuka mota.
Maman Hafsa, ba zan iya jira har dare ba, ni dai
ina rokonki da ki daure ki ara min 'yan
mintuna a cikin lokacinki.
DakTA HUSNA
Ta dan yi tunani dan lokaci.
To, shi kenan ka zo amma ka yi sauri.
HamZA
Ai na shigo cikin asibitin ma a halin yanzu. Ina
kusa da ofishinki.
Dakta uMAR
Ya dan tsahirta yayin da motar ta wuce a hankali ta gabansa. Ya
shaida Hamza wanda ke waya yana tuki.
DaktA HUSNA
Ta yi ajiyar zuciya.
To gani nan zuwa.
EXT. asibiti hARABA - aFTERNOON
Suna zaune cikin mota.
HamZA
Ko Allah ma ana saba masa ya yafe, me yasa ni ba
zaki yafe min ba.
DakTA HUSNA
Da me zaka amfana don na yafe maka, mun riga mun
rabu. Ko ka manta ne kai ba mijina ba ne?
HamZA
Yawwa, wannan shi ne abin da nake magana. Ki yafe
min mu maida aurenmu.
DakTA HUSNA
Ta dube shi kawai dan lokaci.
Ka san abin da nake so da kai, ka fadi abin da ke
tafe da kai, idan kuma ba haka ba zan fita na yi tafiya ta.
HamZA
Saurare ni ki ji. Na yarda kin kama ni ina cin
amanarki da kawarki a dakinki, amma laifina ne ni kadai, ba ke ce kika jefa ni
cikin kadaicin da na aikata hakan ba. Kada fa ki manta ni namiji ne ina da
kishi, ta yaya zan amince ki rinka aurenmu mu biyu.
Dakta HUSNA
Na rinka aurenku ku biyu kai da wa?
HamZA
Kina aure na kina auren aikinki, kuma na lura ma
aikin naki ya fi ni muhimmanci.
DakTA HUSNA
To, ai yanzu ta yi kai tun da mun rabu ka yi aure
ba shi kenan ba. Me kuma kake nema?
HamZA
Ke kin sani na yi aure ne saboda halittarmu ba
daya ba ce. Kin sani ba zan iya zama babu aure ba. Tun da ni ba kamar ke nake
ba. Amma kin sani duk duniya babu matar da nake so kamar ki ko da ko mata dubu
zan aura. Wannan al'amari ne da ban isa na canza a zuciyata ba. Saboda haka
Husna don Allah ki daure ki sake bani dama, na yi miki alkawari wannan karon ba
zan baki kunya ba.
DakTA HUSNA
Ta kura masa ido cikin takaici da mamaki sannan ta bude kofar
motar zata fita.
HamZA
Ya girgiza kansa sannan ya dafe kan cikin alamun damuwa sannan ya
yi dan tari.
DakTA HUSNA
Ta sake dubansa wannan karon kallon likita ga maras lafiya.
Lafiya dai kuwa? Ko wani abu ke damunka?
HamZA
Ya girgiza kai.
A'a, babu komai. jiya zuwa yau ne da dan gaji.
DakTA HUSNA
Ta cigaba da kallonsa har ya dube ta.
Shi kenan, bari na koma ofis.
Ta fita daga motar.
Dakta uMAR
Na can daga kan kwana a jingine da bango a tsaye ya ga Husna na
fitowa daga motar Hamza.
INT. asibiti OFISHIN DAKTA HUSNA - aFTERNOON
Ta bude ofishin ta shiga ta mayar ta rufe sannan ta nufi kujerar
maziyarta ta zauna.
Zamanta ke da wuya ta ji an kwankwasa kofa. Umar ya turo kofa ya
shigo.
DakTA HUSNA
Baka tafi cin abincin ba ne?
Dakta uMAR
Ya rufe kofar ya shiga har inda take ya tsaya a gaba gareta.
Hamza ne?
DakTA HUSNA
Wa kake magana?
Dakta uMAR
Wanda na ga kin fito daga motarsa yanzu.
DakTA HUSNA
Ta dauke kai daga kallonsa.
Shi ne.
Dakta uMAR
Wai me yake kawo shi ne? Ni fa na soma tsarguwa.
Ta mike tsaye a hankali tana duban Umar.
Wai me ke faruwa ne Husna? Yau duk kin wani sauya
min. Ko abin da ya faru jiyan ne har yanzu baki huce ba.
DaktA HUSNA
Ni ce na sauya maka? Me ka yi min?
Yana shirin yin magana sai aka kwankwasa kofa.
Hajiya umma
Salamu alaikum.
Tana da tsohon ciki ta shigo.
DakTA HUSNA
Ah, Hajiya Umma ce? Lafiya dai?
HajIYA UMMA
Ta dubi Husna yayin da ta dafe bayanta.
Dakta cikin nan ya matsa min da ciwo.
DakTA HUSNA
Ta dubi Umar suka hada ido dan lokaci sannan ya juya ya fice daga
ofishin.
INT. gidan su UMAR FALO - night
Kwamfuta Laptop a kunne a gefensa yana kwance rigingine a tsakar
falon ya afka a tunani.
ZanNIRA
Ta shigo falon rike da littafi sai ta ganshi a kwance bai ma san
ta shigo ba.
Yaya faruk, tunanin me kake yi ne?
Dakta uMAR
Ya dawo daga tunanin ya dubeta. Bai amsa ba ya mayar da kansa ya
kwanta.
ZANNIRA
Ta shigo ya zuwa inda yake, ta zauna a kujera.
Na san me kake tunani. Dakta Husna kake tunani.
Bai tanka ba bai ko kalle ta ba.
Na tambayeka mana? Tun fara soyayyarku da ita sau
nawa ka taba zuwa zance ne?
Dakta uMAR
Ya bude ido cikin mamaki.
Zance yana kara dankon sayayya ga masoya.
ZANNIRA
In da kana sonta kamar yadda na zata ba kwanciya
ce ta kamace ka ba.....
Ya sake afka wa a tunani yana mai amince wa da shawarar tata.
EXT. gidan DAKTA HUSNA HARABA - nigHT
Dakta uMAR
Ya isa kofar gidan a motarsa yana shirin shiga harabar sai ya
hangi motar Hamza.
Dakta husna/hamza/hafsa
Shi a jingine da mota, ita a tsaye a gabansa suna zance, ga
karamar yarinya wadda Umar ya gane Hafsa ce.
Dakta uMAR
Ya tsaya nan daga cikin mota yana dubansu cikin damuwa. Sannan ya
tuka motar a hankali ya bar wajen.
INT. asibiti dakin marasa lafiya - moRNING
DakTA HUSNA
Na zagayen duba marasa lafiya.
Nas 2
Na tare da ita tana taya ta.
Suna fito wa ne suka yi kicibis da Dakta Umar. Nas Amina ta gaishe
shi ta wuce ta barsu.
Suka jera suna tafiya.
Dakta uMAR
Jiya na je gidanki da dare, amma ban shiga.
DakTA HUSNA
Me ya sa?
Dakta uMAR
Na hange ku a tsaye ke da Hamza.
DakTA HUSNA
Ta gyada kai.
Haka ne, ya je ganin Hafsa.
Dakta uMAR
Ya dube ta dan lokaci.
Dakta HUSNA
Ta ja ta tsaya suka dubi juna.
Wai Umar me ke damunka ne? Kishi?
Dakta uMAR
Gaskiya ne, kishi ne ke damuna. Kin san wani abu
Husna, wallahi na gaji. Ina so yau na san matsayina tun ban kamu da ciwon
zuciya ba. Kin ce kina sona amma kullum sai na ganki da Hamza. Ta yaya
hankalina zai kwanta irin wannan na faruwa?
Dakta HUSNA
Ta yi shiru dan lokaci, daga karshe ta ja numfashi ta cira kai ta
dubeshi.
Gaskiyar magana Umar na rasa abin da ya dace na
shawarta wa zuciyata game da wannan lamarin.
Dakta uMAR
Yanzu yana cikin damuwa.
Me kike nufi?
Dakta HUSNA
Kwakwalwata ta toshe, na rasa shawarar da ya
kamata na yanke. Shin gidan tsohon mijina zan koma ne ko kuwa kai ya kamata na
aura.
Dakta uMAR
Ya kura mata ido cikin damuwa ya kasa cewa komai dan lokaci.
Kina nufin ba zaki aure ni ba, Husna?
DaktA HUSNA
Me ke damunka ne? Da bakina ka ji na ce ba zan
aureka ba. Ra'ayina ka nema na kuma na gaya maka. Amma ban sani ba ko kana so
ka kirkiro laifi ne don ka kafa hujjar rabuwa da ni.
Suka dubi juna dan lokaci.
EXT. gidan DAKTA HUSNA HARABA - nIGHT
Dakta husna/hamza
Suna tsaye jingine da motar Husna suna zance.
Dakta uMAR
Zaune a cikin motarsa ya bude kofa ya zuro kafa waje yana cikin
damuwa yana duba agogon hannunsa.
Hamza
Suna sallama ya baro Husna ya nufi motarsa.
Dakta HUSNA
Ta yi wa Umar inkiya da hannu cewa ya zo ya fita daga motarsa ya
nufi wajenta. A hanya suka yi kiliya da Hamza suna yi wa juna kallon biyu ahu.
HamZA
Ya bude kofar motarsa zai shiga ya ja ya tsaya ya waiwaya yana
duban Umar da Husna yayin da ta yi masa jagora ya zuwa cikin gidan. Bayan sun
kule sai ya shiga motar ya tashe ta.
INT. gidan dakta husna falo - night
Dakta HUSNA
Ta nuna masa kujera.
Zauna ina zuwa.
Dakta uMAR
Ya zauna ya dan jira yayin da ta je ta dawo da lemo, ta zo ta tsiyaya
masa a kofi ya kurba.
Dakta HUSNA
Ta zauna ita ma yayin da ta tsiyaya wa kanta.
Oh! Umar. Wai yau kai ne a gidan nan. Lallai za a
yi ruwa da kankara.
Dakta umar
Dole ce ta sa. Irin wannan kalubale. Gani na yi
gwamnatina zata gigita.
Ya kishingida yayin da ya sake kurbar lemon.
Gaskiya na ji kunya. Wai a ce na kasa daukan haske
har sai Zannira ta dora ni a hanya. ita ce ta gargade ni na rinka zuwa zance
don kara dankon soyayyarmu.
Dakta HUSNA
Amfanin samun lauya a gida kenan.
Dakta uMAR
Har ta zama lauyar ne?
Dakta HUSNA
Na ji kana maganar kalubale wanne kalubale kake da
shi. Hamza kake nufi.
Dakta uMAR
Kwarai kuwa.
Suka yi shiru dan lokaci. Sannan ya yi murmushi ya dube ta.
Na dade ina zolayar kaina cewa zan same ki cikin
ruwan sanyi. Ban taba tsammani Hamza zai dawo ba.
Dakta HUSNA
Umar wai me ya sa duk ka damu ne?
Dakta uMAR
Dole na damu Husna, ai duk abin da mutum ya sa ran
samu idan a karshe ya fahimci samuwar abin ta zama kila wa kala to dole akwai
damuwa.
Sannan ya dubeta.
Husna, na tambayeki mana.
Dakta HUSNA
Me?
Dakta uMAR
Ya mike zaune sosai.
Shin kina sona har cikin zuciyarki?
Dakta HUSNA
Me ya sa ka yi min wannan tambayar? Saboda kana
tamtamar soyayya ta gareka?
Dakta uMAR
A'a, ina so ne na samu tabbaci ko na samu
kwanciyar hankali.
Dakta HUSNA
Ta kura masa ido cikin tunani.
Umar, ina sonka har cikin zuciyata. Baka bukatar
kalma ta fatar baki daga gareni, kafin ka tabbatar da hakan.
Dakta uMAR
Ya sadda kai kasa dan lokaci sannan ya cira ya dubeta.
Ban san irin zurfin son da kike yiwa Hamza ba,
amma zan yi abin da ban taba yi a rayuwata ba. Husna, don Allah ki taimake ni,
na roki alfarma ki zabe ni.
DakTA HUSNA
Ta kura masa ido cikin kaduwa.
Umar.....
Dakta uMAR
Ni dai alfarma na roka. Ki amince na turo
magabatana, na yi miki alkawari zan zamo miji na kwarai a gareki, irin mijin da
duk kike mafarki.
Ta mike tsaye a hankali ta yi kasake cikin tunani.
INT. asibiti wajen cin abinci - aFTERNOON
Dakta aZUMI
Tana zaune da abinci a gabanta tana ci.
Dakta HUSNA
Ta iso ita ma dauke da abinci.
Ke! Kwana biyu ina kika shiga ne.
Ta zauna suna fuskantar juna.
Dakta aZUMI
Ke ina nan, jiya ma na hange ku tare da hajiyar
nan mai tsohon ciki. Ina Umar naki? Kwanaki na ji kina zaki kaiwa mahaifiyarsa
ziyara.
Dakta HUSNA
Na kai mata, amma gamuwar ba dadi. Mahaifiyarsa
bata sona.
Dakta aZUMI
Yaya azancin bata sonki?
DakTA HUSNA
Ta yi mata bayani a takaice.
A halin yanzu kuma Hamza ya dawo ya uzzura min
akan maganar kome.
Dakta aZUMI
Ta kai cokali baki.
Kina so ki ce min Umar bai san makomarsa ba kenan?
Dakta HUSNA
Ba Umar ba ni kaina ba san makomata ba cikin
wannan sha'anin.
Dakta aZUMI
Wallahi ki yi a hankali kada ki karya wa dan
mutane zuciya, kin san sabon yanka rake ne.
DakTA HUSNA
Ta dauki nama ta kai bakinta.
Gaskiya Azumi, bana son koma wa gidan Hamza kamar
yadda bana son kiyayyar uwar miji.
EXT. gidaN DAKTA HUSNA HARABA - night
Dakta huSNA/HAMZA
Suna zance a farfajiyar gidan.
Dakta uMAR
Ya shigo a motarsa.
Ta yi wa Hamza sallama tun kafin ya tashi motarsa ya tafi ya ga
Husna da Umar sun shiga ciki.
INT. gidan DAKTA HUSNA FALO - niGHT
Dakta HUSNA/DAKTA UMAR
Suna zaune suna ciye ciye da shaye shaye suna tadi cikin farin
ciki.
Bayan sati biyu
InT. asiBITI FALO - moRNING
A katon falon Nas da ma'aikata sun taru suna duba katunan. Wasu
kuma a kan board suke duba wa, ana ta kus kus.
Dakta uMAR
Ya shigo falon ganinsa ya sa kus kus din ya yi kasa. Wasu na
gaishe shi.
Ya dubi wata Nas.
Me ke faruwa ne?
Nas
Ta girgiza kai.
Ni ma ban sani Dakta.
Har ya soma tafiya sai ya lura mutanen dake falon satar kallonsa
suke yi saboda haka sai ya fasa fita ya nufi board, ganin ya iso board din sai
ma'aikatan suka gaishe shi suka sace jiki suka bar wajen.
Ya dubi takardun dake kakkafe daya bayan daya har idonsa ya zo ga
dan katin daurin auren. Ya karanta.
Katin daurin auren Dakta Husna ne da Hamza.
Ya kura wa katin ido dan lokaci sannan ya yago shi ya rike a
hannu zuwa wani dan lokaci.
INT. asibiti OFISHIN DAKTA HUSNA - mORNING
Dakta HUSNA
Tana zaune a tebirinta ta yi tagumi kanta kasa.
Ta ji an turo kofa, ta cira kai a hankali ta dubi kofar. Bata yi
mamaki ba da ta ga Umar ne. Ta dubi hannunsa ta ga yana rike da katin.
Dakta uMAR
Ya shigo jiki a sanyaye, ya iso gaban tebirinta ya tsaya.
Na ga katin.
Ya nuna mata katin.
Na ga kin zabi Hamza. Husna laifin me na yi miki?
Bata yi magana ba bata cira kai ta dube shi ba.
Na ji matsayi na bai kai na ki aure ni ba, hakan
na nufin matsayina bai kai na ki gayyace ni ba kamar yadda kika gayyaci kowa a
asibitin nan.
Har yanzu bata amsa ba, bata daga kai ta dube shi ba. Ya juya ya
nufi kofa zai fita.
Dakta HUSNA
Umar.
Dakta uMAR
Ya waiwayo ya dube ta.
Dakta HUSNA
Hawaye na kwaranya a kuncinta.
Don Allah ka yafe ni, ka yafe ni. Ban san me zan
fada da zai iya kwantar da hankalinka ba.... don Allah ka fahimce ni.
Dakta uMAR
Na fahimce ki.
Ya juya ya fita, ta kura wa kofar ido yayin da ya rufe tana mai
damuwa.
InT. ofishin UMAR - mOMENTS LATER
Dakta uMAR
Yana zaune a tebirinsa yana rubutu yana dan tunani, ya gama
rubuta takardar ya nade ta ya dauki ambulan ya sa a ciki. Sannan ya ya mike
yana hada kayayyaki daga kan tebirin.
EXT. asibiti hARABA - mOMENTS LATER
Dakta uMAR
Ya fito ya hangi Musa Lebura ya kira shi ya mika masa kayan
hannunsa.
LEBURA
Ya bi Dakta Umar da kayan har wajen motarsa ya sanya masa a gidan
baya.
Umar ya mikawa Musa Lebura takardar ya rusuna ya karba ya tafi
shi kuma ya shiga motar ya tashe ta ya tuka ya bar wajen.
InT. asibITI OFISHIN DAKTA HUSNA - afTERNOON
Dakta HUSNA
Tana tsaye jingine da tebirin ta harde hannaye tana kokarin yin
waya.
Kofa ta bude Azumi ta shigo.
Dakta aZUMI
Husna wane irin wulakanci kika yi wa Umar haka?
Yanzu Hamza kika zaba kika bar shi? So kike ki haukata bawan Allan nan.
Dakta HUSNA
Daina yi min irin wannan kallon.
Dakta aZUMI
Wanne irin kallon nake yi miki?
Dakta HUSNA
Kallon kamar na zunguro sama da kara.
Dakta aZUMI
Ai kuwa saman kika zunguro da kara. Wallahi duk
abin da ya samu Umar ke ce.
DaktA HUSNA
Babu ma abin da zai same shi.
Dakta aZUMI
Ba ki ma da labarin abin da ke faru wa kenan.
Dakta HUSNA
Me ke faruwa?
Dakta aZUMI
Umar ya mika takardar barin aiki.
DaktA HUSNA
Ta dafe kirji.
Me?
Gidan su umar dakin umar - NIGHT
Dakta uMAR
Yana tsaye ya kura wa hoton Husna dake rataye ido, sannan ya isa
gare shi ya juya shi. Ya koma gefen gado ya zauna dan lokaci. Daga karshe ya
kwanta rigingine ya afka a tunani.
Int. Gidan su umar wani daki - mORNING
Mama
Da waya a kunnenta tana magana.
I yana nan a gidan Yaya, to don Allah ka zo na yi
na yi da shi ya ki yarda. To sai ka shigo din, zan gaya masa.
INT. gidan su umar fALO - MoRNING
Zannira
Tana shirya jakarta zata tafi makaranta, jin motsin fitowarsa ta
cira kai ta dubeshi.
Dakta uMAR
Ya nufi tebirin cin abinci debi shayi a kofi ya dauki burodi ya
juya zai koma dakinsa.
ZANNIRA
Ta tare shi.
Yaya Faruk, a gaskiya babu dadi abin da Husna ta
yi maka, amma ni ban ga hikimar kin zuwa aiki saboda wannan dalilin ba.
Dakta uMAR
Ya dube ta.
Zannira, kauce ki ban hanya.
Ta yi kamar ta yi magana amma ganin ya tsare ta da ido sai ta
fasa, ta bar shi ya wuce ta je ta dauki kayan littafanta.
Mama
Na tsaye a bakin kofa. Bayan Zannira ta yi mata sallama ta fice
sai ta leka dakin Umar.
Medical Director ya ce ka jira shi kada ka je ko
ina, ga shi nan zuwa yanzu.
InT. gidan su umar fALO - mOMENTS LATER
Dakta Hannafi
(62) Ya yi sallama ya shigo falon,
Mama
Ta fito daga cikin gida.
Sannu da zuwa yaya.
Dakta haNNAFI
Yawwa.
Ta gaishe shi. Sannan ya nemi waje ya zauna.
Ina farukun yake?
Mama
Yana daki.
Dakta haNNAFI
Kira min shi.
Ta tashi ta shiga jim kadan ta fito.
Dakta umar
Ya biyo ta a baya ya zo ya durkusa.
Sannu da zuwa Baffa. Ina kwana?
Dakta haNNAFI
Bai amsa ba, ya zura hannu a aljihu ya fiddo takardar.
Ba gaisuwa ce ta kawo ni ba.
Ya nuna masa takardar.
Kai ka aika da wannan takardar?
Bai amsa ba ya sadda kai kasa kawai.
Tambayarka nake yi.
Dakta umar
Ni ne.
Dakta haNNAFI
Ashe mahaukaci ne kai! Soyayya hauka ce da zaka
bar aiki don bata aureka ba?
Mama
Ta dafe kirji.
Barin aiki?
Ta yi salati.
Lallai yaron nan baka da hankali.
Dakta haNNAFI
In ban da shakiyancin banza, mene ne abin barin
aiki a cikin wannan maganar. yaran banza, dole ne sai kun yi wata uwa soyayya
in ban da bata wa kai lokaci. Mene ne amfanin kai ka makaranta in ba don ka yi
ilimin da zaka yi aiki da shi ba? shi ne zaka bata mana kudi ka bata wa kanka
lokaci.
Ya rusuna ya tsattsare Umar da ido.
Ba zan sake gargagadinka ba. Idan wani abu
makamancin wannan ya sake faru wa.
Ya kekketa takardar.
Sai na shigo har cikin gidan nan na ci zarafinka.
Ya watsa masa guntayen takardun a fuska yayin da ya mike.
Allah ya sa na shiga asibitin gobe na tarar baka
je ba ka ga yadda zamu kwashe da kai.
Bai yi sallama ba ya nufi kofa fita.
Mama
A sauka lafiya, Allah ya kara zumunci.
Sannan ta waiwayo ta dubi Umar cikin bacin rai.
INT. gidan su umar dAKIN UMAR - mOMENTS LATER
Dakta uMAR
Ya kai gwauro ya kai mari a dakin. Daga karshe ya tafi gado ya
kwanta ya jima nan yana kallon saman dakin.
Lokacin da wayar ta yi kara ya jima kafin ya ko kalli inda take,
sannan ya mika hannu ya dauki wayar ya duba sai ya ga Husna ce ke kira.
Ya kurawa wayar ido har ta kari kukanta sannan ya kawar da kai ya
cigaba da karatun wasikar jakinsa.
Can jima wa wayar ta sake ruri ya duba ya tabbatar Husna ce sai
ya jira har ta gama rurin sannan ya kashe ta gaba daya.
Yana kwance har yanzu cikin damuwa.
ZANNIRA
Ta yi sallama ta shigo, ta mika masa wayarta.
Yaya Faruk, Husna ce ke magana da kai.
Dakta uMAR
Je ki abin ki.
Ta tsaya tana kokarin ta yi masa bayani.
Na ce ki je abin ki ko kuwa yaya ne.
ZANNIRA
Ta fice daga dakin babu shiri.
Can jima wa sai gata ta sake dawo wa rike da wayar.
Ya nuna ta da hannu.
Sako ne ta aiko ni da shi. Ta ce a cikin biyu ka
zaba, ko dai ka karbi wayar ku yi magana ko ita ta zo gidan nan da kanta, duk
wanda ka zaba a cikin biyun ta ce ya yi mata.
Dakta uMAR
Ya jima nan a kwance bai ce komai ba. Daga karshe ya mike zaune
ya mika hannu cikin damuwa ya karbi wayar ya kai kunne.
Me kike so?
Ya saurara zuwa wani dan lokaci.
To, Allah ya kaimu.
Ya mika wa Zannira wayarta. Ta karba ta fita daga dakin ta bar
shi nan cikin tunani.
INT. oFISHIN UMAR - mORNING
Dakta umaR
Yana mayar da kayayyakinsa inda ya dauke su, a daidai lokacin da
Husna ta shigo.
DakTA HUSNA
Salamu alaikum.
Dakta uMAR
Amin wa alaiki salam.
Ya mika hannu ma'ana ta ba shi fayil din.
DakTA HUSNA
Ta cika da mamaki.
Haba Umar me ya yi zafi haka da ko gaisuwa babu.
Dakta uMAR
Yi hakuri, ranki ya dade. Ina kwana?
DakTA HUSNA
Ta yi shiru dan lokaci cikin tunani, yayin nan ta mika masa fayil
din tana mai girgiza kai.
Dakta uMAR
Ya mika hannu ya karba.
Ina maras lafiyar yake.
DakTA HUSNA
Wajensa zamu je yanzu.
Dakta uMAR
Ya buda fayil din ya karanta sunan maras lafiyar.
Hamza Mahdi dan shekara hamsin.... HAmza....
Ya cira kai ya dube ta.
Hamza? Wane Hamzan, ba dai mijinki ba?
Dakta HUSNA
Ta gyada kai.
Shi ne.
Dakta uMAR
Nan da nan ya jefar da fayil din a kan tebir. Ya sadda da kai
kasa shiru zuwa wani lokaci. Ta jira shi ya gama tunane tunanensa ya juyo ya
dube ta.
Me ya sa kike zaton zan karbi wannan case din?
DakTA HUSNA
Saboda kai na zaba.
Dakta uMAR
Me ya sa kika zabe ni?
Dakta HUSNA
Saboda kai kadai ne a duk likitocin da na sani
wanda zai iya taimakonsa.
Dakta uMAR
Idan ya mutu fa?
Bata amsa masa ba.
Amsar ita ce ni na kashe shi. Ko ba haka ba ne? Na
gane manufar ki, kina so na azabtar da kaina wajen ganin na ceto rayuwarsa don
kada a zarge ni da kashe shi dalilin zafin kishi.
Dakta HUSNA
Umar don Allah ka cire duk wani zargi daga ranka.
Yanzu don Allah bai kadarta aurenmu ba ba zan iya rokon alfarma daga gareka ba.
Ni fa ina daukar ka ne tamkar dan uwana.
Dakta uMAR
Ya kura mata ido dan lokaci sannan ya mika hannu ya sake daukar
fayil din.
Me ya same shi?
DakTA HUSNA
Muna tsaye da shi tari ya tirnike shi, kafin ka ce
me ye wannan sai ya yanke jiki ya fadi. Da fari na yi zaton......
Dakta uMAR
Kun gwada shi ba tarin fika ba ne?
Dakta HUSNA
An gwada, amma sakamakon bai nuna tarin fuka ba.
Dakta uMAR
Yana ina yanzu?
INT. asibiti daki na musamman - moRNING
Dakta HUSNA
Ta tura kofar suka shiga, Umar na biye da ita a baya. wani Nas na
daura wa maras lafiyar dirif.
HamZA
Yana yin waya daga kwance jin shigowar su Husna ya yi sallama da
wanda yake maganar. Ya waiwaya ga Husna.
Maman Hafsa ina kika shiga ne tun dazu ina ta
neman ki.
DaktA HUSNA
Na je na taho da likitan da zai duba ka ne.
HamZA
Ganin Umar ya sa shi zabura kamar wanda aka tsikara.
Wane ne likitan da zai duba ni? Kada ki ce min
wannan makiyin nawa ne zai taba ni. Ah don Allah ban son tsokana. Ke ma kin
san ba zata sabu ba.
Dakta HUSNA
Baban Hafsa, ba yadda kake zato ba ne, Umar ba
makiyinka ba ne, bayan haka bamu da wani kwararre akan irin rashin lafiyarka a
asibitin nan da ya kai shi.....
Dakta uMAR
Husna, yana da gaskiya, bai kamata na duba shi ba
tun da ni makiyinsa.
Dakta HUSNA
Ta ja Umar bakin kofa inda ke da 'yar tazara.
Wai zaka amsa bukata ta ne ko ba zaka amsa ba?
Yana da matukar muhimmanci na san wannan.
Dakta uMAR
Kina jin sa fa, ya ce bai yarda na taba shi ba.
Jikinsa ne, lafiyarsa ce, shin ma me ya sa kika damu akan dole sai ya rayu idan
shi bai bukatar rayuwar?
Dakta HUSNA
Kada ka manta ko babu aure tsakanina da shi akwai
haihuwa. Don Allah zan roke ka duba shi ba don shi ba. Idan kuma har zaka yi
hakan to yanzu ne lokacin da ya fi dacewa.
INT. asibiti WANI DAKI - mORNING
DakTA HUSNA
Tsaye a gefe tana duba wasu fayil.
HamZA
Zaune a kan kujera yana duban Umar.
Dakta uMAR
Yayin da yake bubbuga gwiwar Hamza da wata 'yar guduma. Ya
kwankwashi gwiwar dama, da ya gama da ta dama ya koma ta hagu, yana fara
kwankwasar ta sai bai ga Hamza ya motsa ba, ya sake kwankwasa wa shiru. Ya cira
kai ya dubi Hamza cikin shakka, sannan ya waiwaya ga Husna wadda har yanzu ke
ta duba fayil.
Husna.
HamZA
Lafiya dai, me ya faru?
DakTA HUSNA
Ta dubi Umar.
Dakta uMAR
Ya sake kwankwasa gwiwar karo na uku.
DakTA HUSNA
Ta yi sauri ta ajiye fayil din a razane. Ta nufo wajen.
Sake kwankwasa wa mu ga.
HamZA
Ya dube su cikin fargaba da rashin fahimta.
Maman Hafsa! Ku yi min bayani mana!
Dakta uMAR
Ya sake kwankwasa wa.
Umar da Husna suka kura wa juna ido cikin kaduwa.
Hamza ya shiga cikin rudu yayin da shi kuma ya yi ta duban Husna
da Umar.
INT. asiBITI OFISHIN DAKTA HUSNA - aFTERNOON
DaktA HUSNA
Na zaune a kujerarta ta yi tagumi.
Dakta alIYU
Na tsaye bangare daya.
Umar ya yi gaskiya, babu wata hanya illa a yi masa
brain biopsy din.
Dakta uMAR
Ya yi alama da hannu irin ta, 'ai dama na gaya miki'.
DaktA HUSNA
Ta girgiza kai cikin rashin amince wa.
Aliyu ka fa sani, brain biopsy na iya haddasa
matsalar laka ta dundundun.
Dakta uMAR
Haka ne, amma kada ki manta idan har Tumor ne a
kwakwalwarsa rashin yin zai iya bata dama ta girma ta mamaye kwakwalwar.
DakTA HUSNA
To idan bacterial infection ne fa?
Dakta alIYU
Na san dai ba kin kira ni ba ne don ki yi jayayya
da ni. maganar gaskiya yana da muhimmanci a yi masa, kuma cikin gaggawa.
Husna
A dai yi tunanin wata hanyar ba biopsy ba.
Dakta uMAR
Ya dan yi dafa kai cikin tunani.
To ko CT Scanning za a yi, ina ganin kamar ya fi
karancin hatsari.
Dakta alIYU
Ya gyada kai.
Shi din ma zai wadatar idan ana tsoron biopsy.
DakTA HUSNA
Ta mike tsaye.
A yi CT Scanning din ya fi.
INT. asibiti wani daki - aFTERNOON
Hamza
Na sanya riga irin ta asibiti.
Nas 1
Na gyara kujera mai taya a gaban gadon.
Aka dora Hamza aka tura aka fita da shi daga dakin.
INT. asibiti dakin scanning - aFTERNOON
Dakta alIYU
Yana yin hoton Cranial CT Scan na Hamza.
HamZA
Kwance a kan abin kwanciyar.
INT. asiBITI wani daki - aFTERNOON
Dakta alIYU
Yana rike da sakamakon CT Scan din a hannunsa.
Sakamakon ya nuna babu tumor, kuma babu infection.
Ya ja numfashi.
Sai dai yana da...Toxosplasmosis...
Dakta HUSNA/DAKTA UMAR
Suka dubi juna cikin sanyin jiki. Sannan suka dubi Aliyu.
Dakta uMAR
Ka tabbata toxos ne?
Dakta alIYU
Ya gyada kai. yayin da ya mika musu sakamakon.
Positive.
Dakta husna/DAKTA UMAR
Suka karbi sakamakon suna nazarinsa.
INT. aSIBITI OFISHIN DAKTA HUSNA - afterNOON
DaktA HUSNA
Tana kai gwauro tana kai mari a ofishin cikin rashin kwanciyar
hankali.
Daga karshe ta koma ta zauna a kujerar maziyarta ta kife kai a
tebir ta soma shisshikar kuka.
INT. asibiti waNI DAKI - aFTERNOON
Dakta uMAR
Na tsaye gaban Hamza ya sunkuyar da kai hannayensa duka biyun
cikin aljihun rigarsa, bai cewa komai.
HamZA
Wai me ke faruwa ne, ka yi min bayani mana.
Umar ya cira kai ya dube shi, har yanzu bai ce komai ba.
DaktA HUSNA
Jim kadan ta turo kofa ta shigo.
Dakta uMAR
Ina mai fargabar shaida maka ka kamu da cuta mai
karya garkuwar jiki, AIDS.
HamZA
Ya kura wa Umar ido cikin shakka da rudu, sannan a hankali ya
waiwaya ya dubi Husna wadda ta iso ita ma ta tsaya.
Fuskarta kadai ta tabbatar masa da maganar ba da gangan ake yi
ba.
AIDS? Ta yaya za a ce ina da AIDS? Ta yaya........
Ya mittsike fuska cikin rudewa.
Dakta uMAR
Ya dubi Husna sannan ya dubi Hamza.
Ka kwantar da hankalinka, mutane masu dauke da
wannan cuta kan rayu tsawon lokaci.....
HamZA
Ya daka wa Umar tsawa.
Kada ka raina min hankali. Ai daman kai abin da
kake so kenan. To wallahi ban yarda ba wannan sharri ne.
Dakta uMAR
Kana jin a halin da kake ciki, gardama zata
taimake ka? Yana da muhimmanci mu gaggauta dora ka a maganin
Antiretroviral......
HamZA
Ya girgiza kai.
Ba dai a kaina ba.
Ya waiwaya ga Husna.
Yanzu Maman Hafsa, dake za a hadu a yi min wannan.
Haka kawai a kala min AIDS ban ji ba ban gani ba. Ko jinina baku gwada ba ku ce
ina da AIDS.
Dakta uMAR
Zamu gwada jininka, amma yana da muhimmanci ka
fara shan maganin tun kafin sakamakon ya fito, jinkiri na da hatsari......
HamZA
Babu maganin da zan sha idan ba gwada ni aka yi
ba.
Husna da Umar suka dubi juna.
DaktA HUSNA
Dauki jinin nasa a gwada, mu daina bata lokaci.
Umar ya je ya dauki sirinji ya farke shi, sannan ya nufi wajen
Hamza, Husna ta harde hannu a kirji ta kura ido cikin damuwa.
INT. asibiti waNI DAKI - eVENING
Agogo yana nuna lokuta mabanbanta.
Dakta uMAR
Ya turo kofa ya shiga dakin ya isa ga Hamza ya mika masa takardar
dake hannunsa.
Positive.
HamZA
Ya mika hannu ya karba ya duba hannunsa na rawa.
Dakta uMAR
Ya dauko ruwa da magani ya mika masa.
Karbi ka sha.
Hamza
Ya jima nan yana duban ruwan da maganin sannan a hankali ya karba
ya kai bakinsa ya sha.
Dakta umar
Ya zauna yana fuskantar Hamza.
Ina son ka gaya min matan da kake hulda dasu.
HamZA
Me kake nufi matan da nake hulda dasu?
Dakta uMAR
Muna so mu tuntube su ne da wuri, domin Cell count
dinka ya nuna ta yi karfi a jikinka.
Hamza
Malam bana kula kowace mace sai matata. Kuma sai
da aka gwada jininta kafin mu yi aure.
Dakta uMAR
Zamu sake gwada ta. Saboda haka ka yi mata waya ta
zo yau din nan idan da hali.
Ya mike tsaye.
HamZA
Na lura farin ciki kake yi da faruwar abin da ya
faru. Ko?
Umar bai amsa ba ya juya ya fita daga dakin.
Hamza ya jima yana jujjuya wayar a hannunsa daga karshe ya jure
ya buga ya kai kunnensa.
Hannatu.
INT. asiBITI wani daki - eVENING
HamZA
Daga kwance a gado yana yi mata bayani.
Hannatu
Tana saurarensa, cikin karayar zuciya da fargaba, ta kife kai
tana kuka yana rarrashinta.
Dakta HUSNA
Na tsaye daga bakin taga tana lekensu ba tare da sun ganta ba. Ta
kawar da kai cikin damuwa.
INT. asibiti wanI DAKI - eveNING
Hannatu/nas
Ana diban jininta da sirinji don gwaji. Har yanzu tana cikin
damuwa.
InT. aSIBITI OFISHIN DAKTA HUSNA - night
Dakta HUSNA
Zaune a kujerarta har yanzu cikin damuwa.
NaS 1
Ta shiga a firgice.
Dakta, yi sauri ki zo..... jikin Hamza ya
rikice.....
Ta yi sauri ta mike cikin rude wa, ta bi Nas din suka fita daga
ofishin.
InT. asibiti wani daki - nIGHT
dakTA HUSNA
Ta shiga dakin biye da Nas a daidai lokacin da ma'aikata ke
daddane Hamza wanda ke ta fuffuka a gado.
Ina dakta Umar yake?
NaS 1
An je kiransa shi ma.
Dakta uMAR
Gani nan, me ke faruwa?
A daidai lokacin da yake shigo wa dakin.
HannATU
Haka kawai ina zaune kusa da shi na ga ya fara karkarwa.
Suka waiwaya suka dube ta tana tsaye a bayansu cikin kaduwa.
Me ya same shi ne?
DaktA HUSNA
Ta yi mata wani irin kallo na bacin rai.
Ki jira a waje tukuna.....
HannATU
Ku yi min bayani mana bayin Allah, me ya same shi.
DaktA HUSNA
Ki jira a waje na ce.
Ta yi wa Nas din alama, sannan ta juya ta koma ga Hamza yayin da
Nas ta je ta tisa Hannatu a gaba ta fitar da ita daga dakin.
Dakta uMAR
Ya dauko abin numfashi ya sanya wa Hamza a hanci, cikin dan
lokaci sai ya daina fuffukar, bacci ya kwashe shi.
Int. Asibiti OFISHIN DAKTA HUSNA - niGHT
Dakta HUSNA
Na zaune tana wasa da biro a hannunta amma tunani kawai take yi.
Dakta uMAR
Tsaye ya zura hannu a aljihu shi ma cikin tunani.
Hakan na nufin kwayoyin maganin basu yi aiki ba
kenan.
Dakta HUSNA
Na kasa gane me wannan ke nufi, shin me ya sa basu
yi aiki ba?
Ya fi kama da magana maimakon tambaya. Sun yi shiru cikin tunani
an rasa mai magana.
Nas
Ta shigo gami da sallama. Ta zo ta mika wa Umar takardar.
Dakta ga sakamakon gwajin jinin matar Hamza.
Dakta uMAR
Ya mika hannu ya karba, ya soma duba wa.
DakTA HUSNA
Yayin da ita ma ta taso ta nufo inda yake. Nas din ta fita ta
barsu.
Dakta uMAR
Alamun mamaki ya bayyana a fuskarsa.
Me zan gani haka!
DakTA HUSNA
Mene ne sakamakon?
Yayin da ta isa ta karbi takardar ta duba. Mamaki ita ma ya
bayyana a fuskarta. Ta dubi Umar.
Dakta uMAR
Ya juya baya yana kokarin ya fahimci lamarin sannan ya mika hannu
ba tare da ya juya ba.
Ina sirinji.
DakTA HUSNA
Bata yi wani jinkiri ba ta binciko sirinji a cikin kayanta ta
mika masa.
InT. asibiti wANI DAKI - night
HamZA
Kwance a gado cikin rashin kwarin jiki.
HannATU
Zaune a kusa da shi. Lokacin da Umar ya shiga dakin da sirinji.
Dakta uMAR
Sannu. Yaya jikin nasa?
HanNATU
Da sauki, me kuma za a yi masa?
Dakta uMAR
Zan debi jininsa ne.
Ya farke sirinjin ya matsa kusa da shi. Hannatu ta bishi da kallo
yayin da yake diban jinin.
ExT. Wayewar gari - mORNING
Daga duhun asuba zuwa hudowar rana.
INT. ofishin umar - morning
Gari ya waye, yana tsaye a gaban wani dan allo wanda wata babbar
farar takarda ke like a jiki yana rubutu, ya kurawa rubutun ido dan lokaci
sannan ya ajiye pen din ya fita.
InT. asibiti waNI DAKI - morNING
Hamza
Yana daga kishingide.
HannATU
Na kokarin bashin maganinsa.
Dakta uMAR
Kada ki bashi maganin nan.
A daidai lokacin da yake shiga dakin.
HamZA
Ya dubi Umar dake shigowa.
Kamar yaya kada a bani magani, kai ne fa kake cewa
na gaggauta shan magani......
Dakta uMAR
Na janye. Saboda baka dauke da kwayar cutar AIDS.
HannATU
Ta dafe kirji cikin alamun kwanciyar hankali.
HamZA
Ya kurawa Umar ido dan lokaci. Sannan ya tuntsure da dariya.
Jiya ina da AIDS amma yau bani da ita. Wannan abin
mamaki da yawa yake.
Dakta uMAR
A kan samu haka a duk cikin mutum dubu biyar.
Sakamakon farko ya yi karya, sakamako na biyu ya tabbatar baka da AIDS. Amma
dai har yanzu bamu tabbatar da abin dake damunka ba.
Ya ja kujera ya zauna ya dubi Hannatu.
Ki yi hakuri Hajiya, tun jiya ya kamata mu sanar
dake. Sakamakon gwajinki ya nuna ke ma ba kya dauke da ita.
HannaTU
Ta gyada kai alamar fahimta.
Dakta umar
Ya dubi Hamza.
Ina so na tambaye ka. Kana da wani maras lafiya
dake fama da Tarin fuka ne?
HamZA
Ya gyada kai.
Mahaifiyata tarin fuka ne ya yi ajalinta, mun yi
magani sosai amma muka yi rashin sa'a tarin ya gamu da tsufa da wasu cutukan.
Dakta uMAR
Kai ne ka yi jiyyar ta?
HamZA
Ya girigiza kai.
Ba ni ba ne, amma dai kullum ina zuwa wajen ta na
dan jima. Kada ka ce dai tarin fuka ne da ni, don su Maman Hafsa sun gwada tun
farkon kawo ni.
InT. asibiti dakiN TIYATA - aFTERNOON
Dakta HUSNA/dakta azumi
Suna yin tiyata a kan wata mai ciki
Dakta HUSNA
Wallahi na dauki alhakin yarinyar nan, saboda na
zaci ita ta shafawa Hamza kwayar AIDS din. Ban san da idon da zan kalle ta ba.
Dakta aZUMI
Idan kun hadu kawai ki roki gafarar ta. Ai dan
Adam Ajizi ne.
Mai ciki
Tana kwance a kan gadon tiyata.
NaS 1/nas 2
Suna taimaka wa yayin da aka fidda dan yana ta kuka.
INT. asibiti fALO - aFTERNOON
DakTA HUSNA
Ta fito daga tiyata har yanzu da kayan da ta shiga tiyata a
jikinta.
Dakta uMAR
Na zaune yana jiran fitowar ta. Ya mike ya tare ta.
DakTA HUSNA
Ta dube shi cikin sa rai.
Yaya mene ne sakamakon sabon gwajin?
Dakta uMAR
Nagetive,
DakTA HUSNA
Ta rintse ido cikin godiya ga Allah.
Alhamdu lillahi.
Dakta uMAR
Ya dan kawar da kai.
Za a sake gwada shi tarin fuka. Idan ba maganin ta
aka yi ba, ba zata bari a gane sauran abubuwan dake damunka ba.
ExT. asibiti hARABA - aFTERNOON
Harabar Asibiti.
INT. asibiti wajen DAKI - AFTERNOON
Dakta HUSNA/DAKTA UMAR
Suna tsaye tare a bakin kofa.
Na gode Umar, ban san da irin kalaman da ya dace
na gode maka ba. Sai dai na ce Allah ya musanya maka ni da wadda ta fini. Kuma
mai sonka fiye da yadda nake sonka.
Dakta uMAR
Ya kura mata ido yana mai kasa cewa komai.
Dakta HUSNA
Zo mu shiga, ko babu komai kana bin sa bashin
neman gafara.
Dakta umar
Ya girgiza kai cikin murmushin karfin hali.
Babu komai, ki shaida masa na yafe masa. ba sai na
shiga ba.
Ta gyada kai cikin fahimta. Sannan ta barshi ta shiga da takardar
a hannu tana farin ciki.
Barka! Umar ya yi gaskiya. Sakamakon ya nuna tarin
fuka ne. idan aka dora ka a kan magani na tsawon wata shida zaka warke sarai in
Allah ya yarda.
Ta zauna kusa da shi suka dubi juna.
HamZA
Ina Umar din yake.
Dakta umar
Ya tafi gida, kasan a asibitin nan ya kwana.
HamZA
Ya yi shiru cikin tunani yana duban saman dakin.
Gaskiya na yi masa mummunar fahimta. Ki ce masa
ina neman gafarar abin da na yi masa don Allah kafin mu gamu.
Suka cigaba da tattauna wa.
Dakta uMAR
Na daga taga yana dubansu cikin kishi da damuwa yayin da suke ci
gaba da zancen su. Sannan ya juya a hankali ya bar wajen.
(Tamat)
No comments:
Post a Comment