Monday, April 16, 2012

Jagora Script Na Muhammad Sani Abdullahi Kaduna

1 INT. DAKIN BARCI - TSAKAR DARE 1
Hajiya Ladi na dan juyawa a gado, sai ta ji kururuwar mijintata faso daki. Ta tashi firigigi ta yi waje don ta ga ko mene ne.
2 INT. DAKIN ALH. ADO. DARE 2 A dakin Alhaji, ta iske shi cikin jini face-face. HAJIYA LADI (Ta fasa kuka)Lailaha, illallah! ALHAJI ADO Jummai! Jummai ce ta soke ni da wuka. HAJIYA LADI (Cikin kuka)Alhaji Jummai fa ke ce. WaceJummai? Mai aiki a gidan nan? ALHAJI ADO (Ya kada kai) Hajiya Ladi ta zo ta durkusa kusa da shi. HAJIYA LADI To tana ina? Kuma me ka yi mata? ALHAJI ADO Yana magana da kyar Sata na farka na gan ta tanakokorin yi… HAJIYA LADI Cikin gaggawa ta lalubi waya, ta danna tana mai karawa a kunnenta. cikin shasshakar kuka ta yi magana Hello! Offishin ‘yan sanda ne. 3 MONTAGES 3 Yan sanda na gwaje gwaje da aune aune cikin gidan Alh. Ado. CUT TO:
2.
Hajiya Ladi tare da wasu cikin danginta a falo jugum a halinalhini, tana zubar hawaye
CUT TO:
‘Yan sanda na ci gaba da aune-aunensu da bincike a dakin Jummai. Sun dauki wukar dake yashe gefe guda mai dauke daalamun jini.
CUT TO:
Wata ‘yar sanda ta bugawa Jummai ankwa an fita da ita hawayedaga idanunta na zuba.
DISSOLVE TO:
4 EXT. BABBAN TITI - SAFE 3 4
Labari ya cika gari cewa wata 'yar aiki ta kashe mai gidan datake yi wa aiki. Ko'ina ga mutane rukuni-rukuni wasu darediyoyi a hannayensu cikin sauraron labarai, fuskokinsu nadauke da kakabin wannan al'amari.
DISSOLVE TO:
5 INT. OFISHIN ‘YAN SANDA 4 5
Jummai na fuskantar tuhuma da jami’an ‘yan sanda. Ta ki amsawata magana daga dukkan tuhumar da ake mata, babu komai saihawaye dake ci gaba da kwaranya bisa kumcinta.
DISSOLVE TO:
6 INT.BABBAN FALON. ZAMAN MAKOKI. SAFE 5 6
zaman makoki a gidan su Hajiya Ladi tare da wasu mata da yawa.
MATA
Hajiya Ladi ai sai hakuri, kuka ba
zai dawo da shi ba. Tsakaninmu da
shi yanzu sai dai kyakkawar addu'a.
HAJIYA LADI (Ta kara barkewa da kuka)
GAMBO LAUYA
(Ta tambayi wata)
'Yar uwa don Allah mene ne
takamaimen abin da ya faru?
3.
MATA
Wai da misalin karfe daya na dare
ne, marigayin ya farka ya ga 'yar
aikinsu mai suna Jummai tana
kokarin sata a dakinsa. Da ta ga ya
gan ta ya kuma gane ta, sai ta fice
da gudu. Abin kaddara shi kuma sai
ya bi ta. Da shigar sa, ashe dama
tana tare da wuka sai kawai ta soka
masa.
GAMBO LAUYA To yanzu tana ina?
MATA
Ai 'yan sanda sun zo sun yi awon
gaba da ita tun daren jiya.
7 INT. OFISHIN 'YAN SANDA - DARE 6 7
Gambo Lauya ta ziyarci ofishin 'yan sanda, ta gabartar dakanta a matsayin lauyar Jummai. An ba ta iznin ganawa daJummai. Wata 'yar sanda mace ta taso keyar Jummai zuwa indaaka zaunar da Gambo Lauya.
JUMMAI
Ta dubi Gambo lauya duban kurilla
cikin tunnin. Tunaninta ya koma
baya....
DISSOLVE TO:
8 INT. TSAKAR GIDAN JUMMAI SAFE 8
Jummai tana dakan kuli yaninda jikakken garin kwaki ke ajiyegefe guda yana shan isa.
9 EXT. TSAKAR GIDA. RANA 9
Wasu mata a wani gida suna bayar da maganin riga kafi ga yara.
10 INT. TSAKAR GIDA. RANA 10
Jumma ta gama dakan kulinta da ta dauki kwaki tanakwadantawa.
11 EXT. KOFAR GIDAN JUMMAI RANA 11
Mata masu rigakafi suna nufin shiga gidan Jummai.
MATA INT. TSAKAR GIDAN JUMMAI. RANA
4.
JUMMAI Daga ina? Kuma wa kuke nema?
DIJE Daga Ma'akatar Kiwon Lafiya tawannan jihar. Mu ne jami'an da kebi gida-gida don yi wa yara 'yanshekaru biyar zuwa kasa rigakafincutar shan-inna.
JUMMAI
(Ta yi dariya)To wai ku har yau ba ku fararigakafin yunwa da fatara ba ne?
KULU Yunwa da fatara kuma? Haba uwargida, ta yaya za a yirigakafien yunwa da fatara ban daabin ki?
JUMMAI Yo, mu talakawa manyan cututtukanda ke gallabar mu ke nan ba waicutar shan-inna ba. Saboda haka ku koma ku gaya musu cewa mu rigakafinyunwa da fatara muke so yanzu. 'Yan matan nan sai wannan ta dubi waccan, waccan kuma ta dubi wannan.
DIJE To, uwargida, in Allah ya yarda zamu isar da sakonki. Mu je Kulu.
KULU Sai an jima 'yar uwa.
JUMMAI Allah ya ba mu yini lafiya.
12 INT. HARABAR KOTU. RANA 8 12
MULTI-DOOR COURT rubuce a jikin wata kofa. Cikin wani ofishi, Gambo na zaune bisa kujera bayan wani tebur. Sauran mutanenna zazzaune a kan kujeru da a ka tanada cikin ofishin.
GAMBO LAUYA Gonar da a ka saye ta shekaraashirin da biyar da ta wuce, ammaba ku musanta wannan ciniki sai a yanzu?
5.
MUTUM 1
Ai ranki ya dade laifinsa ne. Da ya
so ai da tun tuni mun sasanta.
GAMBO LAUYA
Na tabbata da kuna da nufin
sasantawa ba abin da zai kawo ku
nan. Shawarar da zan ba ku itace,
ku je ku yi sulhu tun da kun nuna
kuna da bukatar sulhuntawa. Ta dubi
wanda ya kawo korafi. Kai kuma
Malam Sani sai ka je, nan da sati
biyu ka dawo min idan ba a sami
wani ci gaba ba.
13 EXT. TITI. RANA 9 13
Dije tare da abokiyar aikinta na tsaye a bakin titi sunajiran mota. A nan Gambo lauya ta riske su.
DIJE/KULU
Ba su ankara da ita ba sai da ta tsaya gabansu tukuna. Dije ta washe baki cikin murnar isowarta a wannan lokaci. Nan da nan ta shige gaban motar tana yafito abokiyar aikinta da tashige. baya, kana su ka yi gaba.
GAMBO LAUYA
Wai yaya sha'anin rigakafin naku
yake tafiya ne? Amma ina fata yanzu
mutane suna karbar shirin ko?
DIJE
Yaya Gambo, ke dai a yi sha'ani
kawai. Ai har yanzu ba wani abin da
ya canza na a zo a gani. Da yawa
dai abin da suke gaya mana shi ne
an riga an yi wa yaransu, alhali
kuma ba a yi ba.
GAMBO LAUYA
To ai kin san harkar mutanenmu sai
a hankali. Amma in dai aka nace,
ina ganin za a sami cikakkiya
nasara a nan gaba.
DIJE
Allah ya sa. Har kin sa na tuna da
wani gida inda muka je matar gidan
ta ba ni dariya kuma ta ba ni
tausayi.
6.
GAMBO LAUYA Dariya da tausayi kamar yaya?
DIJE Wai da muka ce mata mun zo mu yi wayaransu rigakafin cutar shan-inane, sai ta ka da baki ta ce wai su rigakafin yunwa da fatara suke so ba wai rigakafin cutar shan-innaba.
GAMBO LAUYA Ta yi dariya.
To ku wace amsar kuka ba ta?
DIJE Muka ce mata, to ina ta taba ganininda ake rigakafin yunwa da fataraban da abin ta?
GAMBO LAUYA Ashe ku ne ma abin a yi wa dariyaba wai ita waccan mata ba.
DIJE Mu ne abin a yi wa dariya kuma?
GAMBO LAUYA Kwarai, ko shakka babu. Amma mu ajiye wannan batun gefe guda. Hakakawai na ji ina da sha'awar haduwada wannan mata da kike magana.
DIJE Yaya duk lokacin da kika sa niyyartafiya ba sai in kai ki gidan nata ba?
14 INT. TSAKAR WANI GIDAN - HANTSI 10 14
Jummai cikin gida a bakin turmi tana surfan masara. Alhaji Dozin da Alhaji Sabo sun kutso cikin gidan ba tare da sallamaba. Ta tsayar dakan ta dube su, cikin girmamawa ta risuna tana mai gaisuwa, amma ko amsa ma ta ba wanda yayi.
ALHAJI DOZIN A wannan gidan, wannan ita kadai cetake haya. Yau an tasar wa shekarubiyar ke nan ba ta ba ni ko sisiba.
7.
JUMMAI Alhaji ai ka san halin da nakeciki. Ba da gangan na ki biya ba.
ALHAJI DOZIN Zancen banza, kina nufin ki ce duk tsawon shekarun nan ba ki cin abinci?
JUMMAI Alhaji muna ci da bakar wuya.
ALHAJI DOZIN Ko ma dai da me kuke ci, ai ba ruwan abincin ake miki ba. Kai ni mene ne ma nawa? Gida dai ya fitahannuna. Alhaji Sabo, ga ka ga tanan. Hukuncin gida yanzu yanahannunka.
ALHAJI SABO Alhaji Dozin wane kukunci ne ya wuce wanda na gaya maka kafin ma mu yi ciniki? Sai da na tambaye ka zansami gidana cikin kwanaki bakwai dayin ciniki? Ka ce da ni zan samu.To yau kwana nawa?
ALHAJI DOZIN Yau kwana biyu.
ALHAJI SABO To, ka ga ke nan, ina sa ran zan zoin fara aiki nan da kwanaki biyar.In kuma na zo ba zan saurara wa kowa ba.
JUMMAI Alhaji ka wa Allah, ka ba ni lokaciisasshe in nenmi wajen da zan koma.
ALHAJI SABO Ki nema cikin kwanaki biyar din nan da suka rage, uwargida!
JUMMAI Alhaji kwanaki biyar ba za su isheni ba. In da ka gan ni nan, ban ajiye ba ban ko ba kowa ajiya ba.
8.
ALHAJI SABO Uwargida, ba ni da wani abin da zaniya yi miki. Alhaji Dozin, ai inaganin sai mu tafi ko?
JUMMAI (Ta daga hannaye tana
roko)Alhaji ka ji kai na kamar yaddaAllah ya ji kan ka.
Ko sauraron ta bai yi ba suka fice abin su.
15 EXT. KOFAR GIDAN - HANTSI 11 15
Alhaji Dozin da Alhaji Sabo sun zo fitowa suka yi kiliya daGAMBO LAUYA ta zo tare da kanwarta, Dije za su shiga.
16 INT. TSAKAR GIDAN - HANTSI 12 16
JUMMAI
Na tsaye a bakin turmi tabarya rike a hanunta cikin zulumi.Sallamar da su ka yi kadai ta ankarar da ita shigowarsu.
Sannunku da zuwa
Ta nufi zuwa cikin dakinta, jimawa kadan ta fito da wasukujerun zaman mata guda biyu ta aje masu Bayan sun shiga sun gaisa da Jummai
DIJE/GAMBO LAUYA
Dukaninsu su ka zauna
DIJE Kin gane ni kuwa?
JUMMAI Ba ke ce jami'ar rigakafin cutarshan-inna ba? Wannan ce dai ban san ta ba, don ba da ita kuka zo ba ran nan.
GAMBO LAUYA
Ta yi murmushi tana mai duban Jummai
DIJE
Wannan yayata ce, Ina mayar matayadda aikin rigakafi ke tafiya ne, sai labarin ki ya shigo ciki.
(MORE)
9.
DIJE (CONT'D)
Shi ne ta ce, ita kuwa tana so ta
zo ta ga inda kike don ku saba da
juna.
JUMMAI
Allah Sarki, ke kuwa me kika ce da
ita ne har ta ji tana so ta zo ta
gan ni?
GAMBO LAUYA
Ba wani abu ba ne, illa maganar
hikima da na ji a wurin ta kuma ta
ce ke ce kika fadi wannan Magana.
Ta ce kin tambaye su, babu wani
shiri ne na rigakafin yunwa da
fatara? sunana Gambo Kuma ina aiki
ne da Hukumar da ke Samar wa Marasa
Galihu Taimako irin na sharia. Ina
kuma harka da kungiyoyin mata
iriiri.
JUMMAI
Ni kuwa sunana Jummai. Ita wannan
fa?
DIJE Ni, sunana Dije
GAMBO LAUYA
To malama Jummai, in kin yarda zan
so in san mene ne kika sani game da
yunwa da fatara?
Jummai ta yi jim kadan cikin tunani
Nice kuwa na san fatara da yunwa.Mijina Sale ma’aikacin gwamnati ne. A rayuwarsa ban da aikin nan baisan komai ba, don aikin gwamnatibai koyawa ma’aikaci wata hanyardogaro ba illa kashewa kadai. Watarana ya shigo gida cikin tashinhankali, tashin hankalin da ban taba ganinsa gareshi ba kamar wannan rana.....
DISSOLVE TO:
10.
17 INT. CIKIN DAKI. MARAICE 13 17
SALE Yanzu a ce wai Kantoman Mulkin Soja guda daya tilo, ya bushi iska ya cewai ya kori mutum sama da dubu dagabakin aikinsu, faf! Kamar an kyastaashana?
JUMMAI Kora? Wace irin kora kuma?
SALE Wai mahaukacin kantoman nan namu ne ya kore mu daga aiki a dalilinyajin aikin da muke yi. Kin san ya ce a koma ko ya yi kora. Muka ce baza mu koma ba sai an biya manabukatunmu.
JUMMAI Yanzu shi ke nan ku da ba ku je ba, kowa an sallame shi?
SALE Ga takardar ma kuma a hannuna. Ji maganar gadora wai, " a bisa karfinikon da dikiri na 24 na shekarar ya ba ni, na kori wane, daga aiki, korar kare".
JUMMAI
(Ta bugi kirji)Korar kare? Yanzu shi ke nan dan kudin Sallamar ma da ake bayarwa kuba ku da shi?
SALE Kudin Sallama ba sai an yi rabuwararziki ake bayar da shi ba?
DISOLVE TO
JUMMAI Bayan watanni bakwai. Gari ya farazama gari.Dukkan kayan daki na nasayar mun cinye a ciki. Gani na nakarshe da zan iya tunawa na yiwasale, shine, na san mun kwanta da
shi a wani dare, amma sai na wayigari ni daya, babu Sale babulabarinsa kawo ya wannan lokaci.
(MORE)
11.
JUMMAI (CONT'D)
Mafiyawanci abincina garin kwaki da
kuli ne safe da rana har ma dare.
Ta dan yi jim kadan kanta kasa sunkuye. Hawaye ya gangarobisa kumatunta wanda cikin sauri ta yi gaggawar share shi dagefen zaninta. cikin murya sassauka.
Malama Gambo wa ya fini saninfatara da yunwa kuwa. Yanzu hakamasu gidan nan ma sun bani wa’adinkwana biyar na bar musu gidansu.
CUT TO:
18 INT. KOTUN YAMMA - BAYAN LA'ASAR 14 18
Mai Shari'a yana magana da Alhaji Sabo. Sauran mutane sunasauraro. hakanan Gambo sanye da kayan lauya na wurin zamantaJummai na tare da ita.
MAI SHARI'A
Alhaji Sabo, a yanzu dai ka gane
cewa abin da ka yi niyyar aikatawa
ba daidai ba ne ko, kamar yadda
Barrister Gambo ta kalubalance ka a
kai?
ALHAJI SABO
Hakika na yarda cewa tun farko ban
biyo hanyar ka'ida da shari'a ba.
Amma don na ga matar ta dade ne ba
ta biya.
MAI SHARI'A
Amma ai ka gamsu cewa ba ta ki biya
da gangan ba ne. Yanzu abin da kotu
take so shi ne ka daure ka bi ta
hayar ka'ida da shari'a. Mu da ma
aikinmu shi ne mu taimaka a sami
maslaha tsakaninku da masu haya a
gidajenku amma ba wai don a tursasa
ko a ci mutuncin wani bangare ba.
ALHAJI SABO Mai girma na ba ta watanni uku.
MAI SHARI'A
To ke kin ji ya ba ki watanni uku,
amma fa za ki biya shi wadannan
watanni uku da za ki yi a gidansa.
12.
ALHAJI SABO Mai girma, ni na ma yafe mata kudinwadannan watanni uku.
Abin da dai nake so shi ne bayan kokafin watanni uku ta tashi ta bar mini gidana.
MAI SHARI'A Ka kyauta, kuma muna fata kafincikar wannan wa'adi a san inda aka dosa. Ke kuma Jummai kotu tana shawartar ki da ki gaggauta nemaninda za ki koma kafin cikar wannan wa'adi.
JUMMAI
Ta dubi Gambo cikin walwalar fuska tana mai godiya
GAMBO LAUYA
Ta yi murmushin gamsuwa ga Jummai.
19 INT. GIDAN ALH. ADO FALO - SAFE 15 19
Dije, Jummai da Hajiya Ladi cikin falon zaune
HAJIYA LADI Jummai kin taba yin irin wannanaikin ne na gida?
JUMMAI Hajiya ban taba yi ba.
HAJIYA LADI Tun da kin ce ba ki taba yi ba, yanzu kina ganin in kin fara za kiiya jure masa? Aiki ne fa ba na maison jiki ba.
JUMMAI Ina fatan Allah ya agaza mini Hajiya
DIJE Hajiya Ladi, ai ta saba dakwaranniya. Za ta iya.


13.
14.


 
HAJIYA LADI Jummai aikin dai bai wuce wankin kayana da na yara ba. Sai kumawanke-waken kwanuka da sharar gida. Mai dafa abinci daban. Managar abinda za a biya ki kuma Dije za tagaya miki.        
DISOLVE TO        
20         20        
21     INT. OFISHIN ‘YAN SANDA     21        
    JUMMAI            
    Hawaye na gangara bisa fuskarta            
    Gambo, na gode game da irin kaunada damuwar da kuke nuna min. Amma don Allah ki yi hakuri kar kishigar da kanki cikin wannanlamari. Ki bari a yanke minhukumcin da ya dace            
    GAMBO LAUYA To mene ne shi wannan hukuncin da ya dace?            
    JUMMAI (Ta yi shiru)            
    GAMBO LAUYA In kina nufin a kashe ki ne, to sai in ce ba ki yi ma kanki adalci ba.Ni kaina ba ki yi mini adalci ba.Ke hatta ita shari'ar ma ba ki yimata adalici ba. Don kuwa ta ba ki damar in kin san kina da kwararan hujjoji, ki gabatar mata da su. In ta gamsu da su, sai ta wanke ki.            
    JUMMAI Yanzu shari'a za ta iya wanke ni?            
    GAMBO LAUYA Ko shakka babu. In dai kika ba ta hujjojin da suka gamsar da ita. Don haka ina so ki gaya mini gaskiyawai kin kashe Alhaji Ado ne sabodaya kama ki da laifin sata a dakinsa?         

JUMMAI Sata?! In ji wane makaryacin?
22 INT. GIDAN GAMBO. DARE 22
DIJE
Tana kicin bisa abincin da take dafawa
Yanzu da ba a kama Jummai ba ta jawo mana salalan tsiya ke nan, don ni za a kamo tun da ni na kai ta. Gaskiya yanzu nake ganin rashinlaifin wadanda ke kin taimako. Mutum! Lalle mutum mugun ice ne.
GAMBO LAUYA
Rike da wani littafin a hannunta ta na dubawa ya yin da take
sintiri cikin falo. A dayan hanunta karas ne. Ta gatsi karas
din kana ta dubi nahiyar kicin inda Jummai take.
Amma kada ki manta a shari'ance, ana tuhumar ta ne, ba wai an tabbatar da laifin a kan ta ba ne.
DIJE
Ta juya miya da ludayi
Haba yaya! Wace tabbatarwa kuma, bayan ga shaidar 'yan sanda nan kuru-kuru. Kuma har yanzu ba tafito ta karyata zargin da ake yimata ba.
GAMBO LAUYA
Duk da cewa ba ta karyata ba, to
amma kuma ba ta fito fili to
bayyana amincewa da zargin ba. Kuma
kada ki yi mamakin kubutar ta in
dai har ta sami kwararren lauya ya
tsaya mata.
DIJE To a ina za ta same shi?
15.
GAMBO LAUYA Hukumar da nake aiki da ita, za ta iya taimaka mata da lauya. Bamamaki ma a ce ni ce zan kare ta.
23 INT. OFISHIN ‘YAN SANDA. MARAICE 23
Hajiya Ladi tare da Jami’in ‘yan sanda yana ma ta jawabi. Da alamun ko me yake baiyana ma ta bai yi mata dadi, ba, fuskacikin rashin walwala ta fito daga ofishin ranta a bace.
24 EXT. TITI. SAFE 24
Hajiya Ladi a baya cikin mota shehu direba na tuka ta sun isogidan Lauya Gambo
25 INT. HARABAR GIDA - SAFE 25
Gambo ta fito rungume da wasu manya-manyan littafai ta nufiinda motarta take cikin harabar gida. Ta bude kofa ta zube su gefe a kan kujerarta ta gaba. Hajiya ladi ta shigo daidailokacin da goshin motarta ya nufi kofa tana kokarin fita.
GAMBO LAUYA Hajiya Ladi ke ce haka da sassafe?Lafiya dai?
HAJIYA LADI Rufe mini baki, matsiyaciya maciamana! Algunguma! Ai ni ban sankina farin ciki da mutuwar mijinaba sai jiya da 'yan sanda suka kirani. Gambo ki rasa wanda za ki yi wawannan rashin mutuncin da cin zarafin sai ni?
GAMBO LAUYA Hajiya Ladi me ya faru
HAJIYA LADI Yanzu Gambo har za a ba ki kudi ki tsaya wa wacce ta kashe mini miji?
GAMBO LAUYA Oho! Kina nufin Jummai? Wallahi, ni ba wanda ya ba ni ko sisin kwabodon in kare ta.
HAJIYA LADI Kwadayin ki ci mutuncina ne ya sa kika yanke shawarar tsaya mata kenan ko?
16.
GAMBO LAUYA
Haba Ladi, wace sha'awa zan yi na
in ci mutuncinki?
HAJIYA LADI
To in dai ba kudi kika karba ba
kuma ba nema kike yi ki ci
mutuncina ba, to ina so ki wanke
hannunki daga al'amarin Jummai.
GAMBO LAUYA
Ladi, ina so ki yi mini adalci, ki
fahimci cewa hannayena a daure suke
game da wannan sha'ani. Abin da
kuka fada ba shi Jummai take fadi
ba. Kin ga ke nan dole a nemi mai
gaskiya a cikinku.
Sai kawai Hajiya Ladi ta daga hannu ta tsinke Gambo Lauya damari, tas! Maimakon Gambo ta fusata, a'a sai kawai ta kalli Ladi ta yi murmushi.
26 INT. BABBAR KOTU - SAFE. 26
PROSECUTOR
Ranar 19 ga Yuli, 2007. A gida mai
lamba 19 da ke kan titin Ado
Avenue. Da misalin karfe 2:30 na
dare, wata mata mai suna Jummai da
ke aiki a wannan gida ta kashe mai
gidan mai suna Alhaji Ado ta hanyar
suka da wuka, lokacin da ta shiga
tirakarsa da niyyar yin sata.
MAI SHARI'A
(Ya dubi Jummai)
Ko kin amince cewa kin aikata
wannan laifi da ake tuhumar ki da
shi?
JUMMAI
Ta girgiza kan ta cikin nuna alamar rashin yarda da abin da a ke son dora mata.
A’a
17.
MAI SHARI'A
To tun da wacce ake tuhuma ba ta
amsa laifin da ake tuhumar ta da
shi ba, wannan kotu za ta dage
sauraron wannan shari'a ha zuwa nan
da sati biyu. A lokacin da za a yi
wa karar cikakkayar sauraro. Kafin
wannan lokaci wacce ake tuhuma za
ta ci gaba da zaman 'riman' a gidan
kaso.
GAMBO LAUYA
(Ta mike)
Ya Mai Shari'a, ina rokon kotu ta
taimaka ta bayar da belin wacce ake
tuhuma.
LAUYAN GWAMNATI
(Shi ma ya mike)
Mai shari'a, ban yarda da abin da
lauyar wacce ake tuhuma take nema
ba. Don wannan mas'ala ce ta jini.
Bayar da belin wannan mata na iya
ba ta zarafin gudu kafin nan da
sati biyu. Baya ga hakanan nan,
wanda a ka kashe na da dangi da
masoya ma su tarin yawan gaske
wadanda har yanzu su na cikin
alhinin mutuwarsa. Bayar da belin
na iya sanya su jahiltar manufar
shari’a su dauka an sake ta ne,
hakan na iya tunkuda su daukar
matakin shari’a a hanunsu. Domin
tsaro da kare lafiyar wacce a ke
tuhuma bai kamata kotu ta bayar da
belinta ba a wannan hali.
MAI SHARI’A Kan sa kasa duke yana rubutu kana ya daga ya dubi kotu
Kotu ta karbi inkarin mai lauyanmai kara.
Ya daga gudumarsa ya bugi teburi da ita.
27 INT. FALO. RANA 27
Gambo tare da wata yarinya[MARTHA]mai matsakaicin shekarusuna tattaunawa. Bayan kammalawarsu ta ci gaba da aikin goge­goge kamar dai yadda a ka san ‘yar aikin gida.
18.
28 INT. OFFISHIN GAMBO RANA 28
Tare da shehu direban gidan Alhaji Ado, yana bayani tanarubutawa tare da sauraronsa. Bayan nan ta ci gaba da yi masawasu bayanai shi kuma na sauraronta tare da gyada kansa cikin alamar amincewa a gaba dabam dabam cikin zancenta.
29 INT. BABBAR KOTU - SAFE 29
Bayan sati biyu da fara sauraron kara, lauyan gwamnati ya cigaba.
LAUYAAN GWAMNATI
Ina so in gabatar wa kotu wukar da
aka aikata wannan aika-aika da ita,
gami da cikakken rahoton gwajin
'yan sanda wanda ya tabbatar da
cewa zanen yatsun da aka samu jikin
wannan wuka, sun yi daidai da hoton
zanen yatsun hannun Jummai da ke
hannun 'yan sanda. Bayan wannan ga
kuma rigar da aka soki Alhaji Ado a
cikin ta nan face-face da jini.
Akawun Kotu ya karbi wadannan kayayyaki ya mika wa Mai Shari'a. shi kuma ya sami lokaci yana dubawa.
MAI SHAIRI’A
Ya dubi Gambo, Ko kuna da inkarin shaidar da a ka gabatar.
GAMBO LAUYA Babu ya mai shari’a
MAI SHAIRI’A
Ya dubi lauyan Gwamnati
Ci gaba
LAUYAN GWAMNATI
Ina rokon kotu ta amince sai a zama
na gaba zan kara gabatar da wasu
shaidun
19.
MAI SHARI'A
Kotu ta amince. An dage ci gaba da
wannan shari'a sai nan da wasu
makonni biyu.
30 EXT. MARARRABA KADUNA STATE MARAICE 25 30
Hada hadar mutane na kai da kawowa, manyan motoci da dama sun yi parking. Wata mota kirar bus ta tsaya a bakin titi, shehuya fito daga ciki. Ya tsaya ya yi dan dube dube kana ya tsallaka titi ya shiga ciki. Daga kasa kasa sautin kidankuntigi [dan indo] na tasowa
31 INT. GIDAN WASA MARAICE 31
Gidan wasa ya cika, Dan Indo na cashewa ana ta faman yi masakari
FATI
Tana tsaye can gefe guda da karan shigarinta a hanu cikin
alamar tunani. Babu alamar hankalinta na tare da wasan da
abubuwan da ke faruwa.
SHEHU
Ya shigo cikin gidan wasan yana dube dube. Ya hango ta can
gefe tana feso hayakin sigari daga bakinta, cikin sauri ya
nufi inda take.
FATI
Ta ankara da shi lokacin da ya karaso gareta, nan da nan
cikin washewar fuska ta yi masa karbar maraba, daga nan suka
fice daga gidan wasan zuwa waje.
32 INT. DAKIN FATI 32
Shehu zaune kan kujera, Fati na daga bakin gado, kwalbar lemoa gabansa da wani kofi guda daya. Daki ne matsakaici, babukomai a ciki banda gadonta sai ‘yan kujeru guda biyu. Gefeguda kuma talbijin ce tare da VCD bisa wani dan karaminteburi. Hotunanta da na Alhaji Ado na makale jikin bango.
33 INT. BABBAR KOTU - SAFE 33
Hajiya ladi na tsaye cikin kewayen shaida tana bayar dashaida,lauyan gwamnati na fuskantarta cikin sauraro
HAJIYA LADI
Ranar 19 ga Yuli, 2007 da misalin
karfe 2:30 na dare, ina kwance sai
na ji kururuwar mai gidana yana
neman gudunmawa. Na fito na same
shi da wuka kafe a cikinsa, jini na
zuba.
(MORE)
20.
HAJIYA LADI (CONT'D)
Da na tambaye shi abin da ya faru, sai ya ce mai aikinmu ce, Jummai tashigo dakinsa da niyyar sata. Da ya farka ya gan ta, sai ta fice. Shikuma ya bi ta. Da fitowarsa, asheta labe. Bai Ankara ba sai kawai ya ji an luma masa wuka. Mun yikokarin kai shi asibiti amma kafin 'yan sanda su zo ya cika. Abin dana sani ke nan.
MAI SHARI'A
Ko lauyar wacce ake tuhuma tana da
wata tambaya da za ta yi wa shaidar
nan ta mai gabatar da kara?
GAMBO LAUYA
(Taje wajen Ladi)
Ina so ki gaya mini sunan ki da
irin dangantakar da ke tsakanin ki
da shi wannan mai rasuwa.
HAJIYA LADI
Ni sunana Ladi, kuma shi mai rasuwa
miji ne a wuri na.
GAMBO LAUYA
Ya Mai Girma, ina so kotu ta yi
kyakkyawar la'akari da irin
dangantakar da ke tsakanin wannan
shaida da kuma shi mai rasuwa. Mai
Shari'a ya gyada kai
GAMBO LAUYA (CONT'D)
Lokacin da kike yi wa kotu bayani,
kin ce kin fito kin same shi da
wuka a cikinsa. A ina ne takamaimai
kika same shi din?
HAJIYA LADI A dakinsa ne na same shi.
GAMBO LAUYA
Dakinsa ba dakinku ba? A kwai
sabani kenan tsakaninki da marigayi
kafin rasuwarsa.
HAJIYA LADI Ta harari Gambo
A’a, ala’adarsa ce kwana a dakinsa shi daya. Ba na zuwawajensa har sai ya nemi ni.
21.
GAMBO LAUYA
To shi Alhaji Ado, da ma al'adarsa
ce rashin kulle kofar dakinsa in
zai kwanta?
HAJIYA LADI A iyakar sanina yana kullewa
GAMBO LAUYA
Tun da kin ce yana kullewa, ko za
ki iya gaya wa kotu inda kike zaton
Jummai ta samo mabudin da ta bude
dakin Alhaji da shi a wannan dare?
Haiya Ladi ta yi shiru.
GAMBO LAUYA (CONT'D)
Ya Mai girma, iyakar tambayoyin da
zan yi wa wannan shaidar ke nan.
Tare da fatan kotu ta ji dukkan
amsoshin da ta ba ni.
MAI SHARI'A
Lauyan gwamnati sai ka ci gaba da
gabatar da shaidun ka.
LAUYAN GWAMNATI
Shaida na biyu, shi ne Sufeto
Tukur.
Sufeto Tukur ya fito aka rantsar da shi.
LAUYAN GWAMNTI
Sufeto, a matsayin ka na jami'in da
ya gudanar da bincike, muna so ka
gabatar wa kotu irin binciken da
kuka yi da abubuwan da kuka gano.
SUFETO TUKUR
To ranar 19 ga Yuli, 2007 ne da
misalin karfe 2:45 na dare muka
sami waya daga gida mai lamba 19 da
ke kan titin Ado Avenue inda wata
mata mai suna Ladi, ta nemi Hukumar
'Yan Sanda ta kawo musu dauki
saboda an yi ta'adi a gidan. Da
muka isa mun tarad da mutane 'yan
kadan wadanda muka umurta da su bar
wurin saboda gudun kada a jirkita
muhimman abubuwan shaida da ke
wurin. Mun sami wacce ake tuhuma a
dakinta haka shi ma wanda aka soka
yana dakinsa. Binciken likitan mu
ya nuna ba ta da ciwon hauka.
(MORE)
22.
SUFETO TUKUR (CONT'D)
Kuma babbar shaidar da ta bayyanaita ce ta wukar da aka yi wannankisa da ita. An riga an gabatar dawannan da sauran muhimman abubuwan shaidu.
LAUYAN GWAMNATI Ina fata kotu za ta yi la'akari dawannan shaida ta Sufeto Tukur, musamman sakamakon likita wanda ya nuna cewa wacce ake tuhuma ba ta da hauka. Wannan ya nuna kisa ne taaiwatar na ganganci.
MAI SHARI'A Ko lauyar wacce ake tuhuma tana daabin da za ta ce?
GAMBO LAUYA
(Ta je wajen S. Tukur)Ina so ka gaya wa wannan kotu shekarun da ka yi kana aiki dahukumar 'Yan Sanda.
SUFETO TUKUR Bana shekaru na goma sha tara
GAMBO LAUYA Sufeto lokacin da kuka gudanar dabincike ran 19 ga Yuli, 2007, a inakuka sami wannan wuka da aka gabatar a matsayin kayan shaida?
SUFETO TUKUR Mun same ta ne lume a cikin Alhaji Ado
GAMBO LAUYA To ba wani abu da kuka samu baya gawannan wuka?
SUFETO TUKUR Babu wani abu
GAMBO LAUYA Koda dan mabudi ba ku samu ba?
SUFETO TUKUR I, mun sami dan mabudi na dakin Jummai.
GAMBO LAUYA Me ya sa ba ku hada da shi ba cikin jerin kayayyakin shaida?
23.
SUFETO TUKUR Saboda… saboda… saboda babu zanen yatsun wacce ake tuhuma a jikinsa.
GAMBO LAUYA Ta yaya kuma mabudin dakinta zai rasa samun zanen yatsunta a jikinsa? Ke nan babu komai na zanenyatsun kowa a jikinsa?
SUFETO TUKUR A'a akwai amma dai ba su yi daidaida na ta ba.
GAMBO LAUYA Shi wannan mabudi da kuka samu, wani ne ya nuna muku shi?
SUFETO TUKUR A dakin wacce ake tuhuma muka same shi.
GAMBO LAUYA Ya Mai Girma, iyakar tambayoyi nake nan ga wannan shaidar. Da fatankotu ta kiyaye da irin amsoshin daya ba ni.
MAI SHARI'A Lauya mai wakiltar gwamnati, munaso mu gama da sauraron shaidun kayau. Sai ka ci gaba da gabatar da su.
LAUYAN GWAMNATI Ya Mai Girma, shaidun da zan gabatar iyakar su ke nan.
MAI SHARI'A Da yake shaidun mai gabatar da karasun kare, za mu dage wannan shari'asai bayan sati biyu, inda za mu dawo mu saurari hujjoji da shaidunbangaren masu kariya.
Mai Shari'a ya fara fita sannan kowa ya fice.
24.
34 EXT. NIGHT 34
Areal view of kaduna in the night
DISSOLVE TO:
35 EXT. HARABAR BABBAR KOTU - SAFE 35
Harabar kotu ta cika da motoci da sauran abubuwan hawa na masu zuwa sauraran shari’a
36 INT. BABBAR KOTU 36
Kotu cike take makil fiye da kowacce rana. Gambo Lauya natsaye cikin yi wa kotu bayani.
GAMBO LAUYA
Ya mai shari’a, da farko zan so
kotu ta saurari jawabi daga bakin
wacce ake tuhuma kan gaskiyar abin
da ya faru har Alhaji Ado ya rasa
ransa. Bayan ta gama za mu gabatar
da shaidu ko hujjojin da za su
gaskanta abubuwan da za ta fada.
MAI SHARI'A Ci gaba.
Gambo Lauya ta dubi Jummai ta yi mata isharar ta fito.
JUMMAI
Ta fito zuwa cikin kewayen shaida ta tsaya. Ta dubi kotu ta
kowacce kusurwa sannan ta dan saryar da kan ta kasa ta
fara...
Sunana Jummai. An dauke ni aikin wanke-wanken na kaya a gidan Alhaji Ado, Na fara aiki kamar abin arziki. Wata rana Hajiya Ladi ba ta nan..
DISOLVE TO
37 EXT. GIDAN ALH ADO - RANA 37
JUMMAI
Tana bakin famfo tana fama da wanki
ALHAJI ADO
25.
Sanye da doguwar riga kai ba hula, ya leko daga cikin faloyana kallon Jummai sunkuye tana wanki cikin alamar sha’awa.Yayi gyaran murya kana ya kira ta
Ba kowa ne a gidan sai ke kadai?
JUMMAI E, ni kadai aka bari.
ALHAJI ADO Yanzu ke kadai ce kawai?
JUMMAI I, ni kadai ce Alhaji.
ALHAJI ADO Ko za ki shigo ki taya ni duba wasutakardu da na rasa inda na saka su?
JUMMAI Alhaji ina kuma zan shigo?
ALHAJI ADO A'a dakina mana. Ai in mun yi sa'a yanzu za mu gan su.
Ta bi shi suka shiga ciki.
38 INT. BEDROOM 38
ALHAJI ADO Jummai da ma wata magana nake so nafada miki ta asiri, amma sai kin yialkawarin babu mai jin ta.
JUMMAI Alhaji kada fa Hajiya ta dawo tasame ni a dakin nan.
ALHAJI ADO In ta dawo ta same ki, sai me? Ba ni na kira ki ba? Wato Jummai na dade ina fakon lokacin da zan gayamiki cewa tun da kika kama aiki a gidan nan, na ji kin kwanta mini a rai na.
JUMMAI (Ta sunkuyar da kai)


26.
27.


 
ALHAJI ADO wannan kuma ba laifi na ba ne. Sai ki zargi kyau da cikar halitta daAllah ya yi miki.        
JUMMAI Alhaji ni dai zan koma.        
ALHAJI ADO Za ki koma ina?        
JUMMAI Wajen aikina.        
ALHAJI ADO Yo ai ba mu gama magana ba. Ammatun da kina nema ki daburce, bari in yanke miki duk wani dogonturanci. Ni so nake kawai mu yiabota da ke. Ki zama kawata, ni kuma in zama abokinki.        
JUMMAI (Ta zaro ido)        
Alhaji me ka ce?        
ALHAJI ADO (Ya yi tsaki)Ashe ke 'yar kauye ce. Da ina ganinki kamar wata wayayyiya? Je ki yitunani. In kin amince, to ranar da Hajiya ta sake fita kuma na jiamsar ki.        
39     EXT. GIDAN ALH ADO DARE     39        
    Ya iso gida cikin motarsa da dare,            
    MAIGADI            
    Cikin gaggawa ya ya tashi ya bude kofa kana Alhaji Ado ya shige cikin gida.            
40     INT. DAKIN BARCI - DARE 33     40        
    HAJIYA LADI Sanye da doguwar riga maras nauyi, irin kayan barci.            
    Alhaji yau fa muna da babbar matsala a gidan nan.         

ALHAJI ADO (Ya tsorata)Matsalar me ce ce kuma?
HAJIYA LADI Tun da na dawo na iske matar nan ba ta komai sai aikin rusar kuka.
ALHAJI ADO Wace mata?
HAJIYA LADI Jummai mana, mai aikinmu.
ALHAJI ADO To kin tambaye ta abin da ya dame ta?
HAJIYA LADI Ai ta ki magana sam-sam, sai famankuka kawai.
ALHAJI ADO Ina ganin damuwa ce kawai.
HAJIYA LADI Alhaji damuwa kamar yaya?
ALHAJI ADO Matar da mijinta ya gudu ya bar taa rasa damuwa tare da ita? ki dan ba ta dama ta huta, za ki ga komaiya daidaita. Ki ba ta maganin barcita sha don ta sami yin bacci. Hakan zai taimaka mata sosai.
41 INT. WANI BABBAN FALON - RANA 34 41
Gambo Lauya ta ziyarci Hajiya Ladi a gida.
GAMBO LAUYA Assalamu Alaikum
HAJIYA LADI Wa alaikumussalam. Ah Barrister, sannu da zuwa!
GAMBO LAUYA Sannu kadai. Kwana biyu ba ki ganni ba, aiki!
HAJIYA LADI In dai lafiya kalau ne ai ba komai
28.
GAMBO LAUYA Haka ne. Kada ki so ki ji irindadin da na ji, da kika dawo damatar nan Jummai gidanki. Tana nan?
HAJIYA LADI Tana nan, sai dai cikin 'yankwanakin nan ba ta cika walwala ba.
GAMBO LAUYA Jummai da rashin walwala? Ko ba ta lafiya ne?
HAJIYA LADI Farkon abin, kin magana ta yisamsam, amma daga baya-bayan nan koka tambaye ta sai ta ce laifyartalau.
GAMBO LAUYA To kira ta mu gaisa.
HAJIYA LADI Tashi dai mu je dakinta kawai
GAMBO LAUYA Mu je.
ALHAJI ADO
42 INT. GIDAN ALH. ADO. DAKIN JUMMAI MARAICE 42
Suka je dakin Jummai suka iske tana barcin karya. gefengadonta kabewa da a ka ferewa, wukar yankan kabewar na yashejikin kafar gado.
HAJIYA LADI Jummai! Jummai! Ga Barrister Gambo! Ina ganin barci take yi.
GAMBO LAUYA Kyale ta, in ta tashi sai ki sanar mata cewa na zo.
HAJIYA LADI To mu je daki mu tattauna.
Ta sunkuya ta dauke kabewar, kana su ka yi waje.
29.
43 INT. DAKIN ALH.ADO DARE 36 43
ALHAJI ADO Shi kadai yana sintiri cikin dakin sanye da doguwar riga zulumbu.
44 INT. DAKI FALLE DAYA-TSAKAR DARE 44
JUMMAI Da misalin karfe daya na dare, Jummai tana kwance sai ta jimotsi ana kokarin bude kofa daga waje. Tsoro ya kama ta. Tatashi ta sa hannu jikin bango ta kunna fitilar daki lokacinda kofar ke budewa suka yi arba da Alhaji Ado.
ALHAJI ADO Ya sa yatsa kan bakinsa, ka na ya mika hannu ya kashe fitilardakin
Na ga amsar taki tana nema ta dauwani dogon lokaci ne. Ni kuwa kin gan ni nan ba ni da hakurin jira.
JUMMAI Alhaji na gama ka da Allah kada katilasta ni cikin saba masa.
ALHAJI ADO Jummai shi fa Gafurur-rahim ne.
JUMMAI (Tana ja da baya)Alhaji ka ji tsoron Allah!
ALHAJI ADO Haba Jummai, wa'azi ai sai ido na ganin ido. Tashi mana ki gyara kadagari ya waye mana muna cacar baki.
Yana matsawa kusa da ita, tana matsawa nesa har wuri ya kureta fada kan gado. Alhaji Ado ya daka tsalle shi ma ya fada dadan mabudi a hannunsa.
JUMMAI Ta yi sauri ta sauko daga gadon, tana kasa cikin rarrafekokarin laluben wajen kofa cikin duhun daki. hanununta ya fada kan wukar da ta yi yankan kabewa ta rike ta
DISOLVE TO
JUMMAI (CONT'D)A lokacin ina cikin kidima, don ban taba fuskantar yunkurin faden danamiji ba sai a wannan lokaci.
(MORE)
30.
JUMMAI (CONT'D) Ba zan iya tuna wani abu da naaikata ba daga nan illa dai kawaikururuwar ihunsa da na ji yana cewa“waiyyo Jummai kin kashe ni”
JAMA’A Kotu ta yi tsit kamar ruwa ya cinye su bayan kammala jawabinJummai,
HAJIYA LADI Tana wurin zamanta a zaune, hawaye na gangara daga fuskarta.
MAI SHARI'A Lauyan gwamnati ko kana da abin da za ka ce?
JAMA’A Jama’a masu sauraron shari’a sun ankara, yawan kus kus din damutane ke yi a junansu ya sa Mai shari’a buga gudumarsa don jawowar hankali da ai shiru.
LAUYAN GWAMNATI Ya mike tsaye cikin kasalar jiki, kana ya fuskanci Jummai.
Lokacin da Alhaji Ado yake ta yimiki abubuwan da kika ce ya yi, me ya sa ba ki nemi wasu muhimmanmutane kin sanar da su abin da ake ciki ba?
JUMMAI Ai ba abu ne mai sauki ba talaka kamata ta je tana zargin mutumkamar Alhaji Ado, wa zai yarda dani?
LAUYAN GWAMNATI A daren da kika soke shi me ya sa ba ki yi kururuwar neman taimakoba. Kafin ki kai ga aikata wannandanyan aikin?
JUMMAI Ko na yi kururuwa an taru, ai mutane za su fi aiki ne da maganarsa. In ya gaya wa mutane cewabarayi ne suka shigo, kana ganin zasu saurare ni?
LAUYAN GWAMNATI To ko kin san azabar da rashin mijike iya jawowa ga mace da 'ya'yanta?
31.
JUMMAI
Hakika na sani. Rashin nawa mijin
ne ma sanadin kama aikina a gidan
Alhaji Ado tare da fadawa cikin
wannan musiba.
LAUYAN GWAMNATI
Dukkan wannan labari da ki ka bayar
ya fi kama da kirkirarki. Ko ki na
da shaida bisa da’awar alakar da
kike da’awarta tsakaninki da
Marigayi?
GAMBO LAUYA Ta mike tsaye cikin gaggawa.
Ya mai shari’a ina inkarin tambayarda lauyan Gwamnati ke yiwa abarwakilcina. Idan bai yarda dalabarinta ba yakamata ya kawohujjar raunana shaidar da ta bayar.
MAI SHARI’A Ya dubi Gambo kana ya girgiza kan sa.
Na’am, kotu ta amince da inkarinki.
LAUYAN GWAMNATI
Ya mai shari’a ina son gabatar da
shaida, karinar da za ta raunana
labarin abar tuhuma
GAMBO LAUYA
Ya mai shari’a, masu kara sun riga
sun kammala gabatar da shaidunsu.
Bai kamata kotu ta karbi wata
shaida da ya san yana da ita ya ki
gabatarwa ba.
LAUYAN GWAMNATI
Ya mai shari’ah, ina neman afuwar
kotu bisa neman gabatar da wannan
shaidar a halin yanzu. Bukatar haka
ta taso ne saboda Lauyar abar
tuhuma ta yi inkarin da’awarmu
saboda rashin karinar da za ta
tabbatar da cewa labarin da wacce
ake tuhuma ta bayar kirkirarsa ta
yi. Rashin gabatar da wannan shaida
na iya sa kotu ta ki karbar
da’awarmu, hakan kuma na iya kawo
cikas cikin adalcin shari’a.
32.
MAI SHARI’A Ya gyada kansa cikin amincewa,
Na’am ci gaba. Amma daga wannan karka sake gabatar da wata shaida daka san kana da ita ba ka baiyanarda ita ba tun farko.
LAUYAN GWAMNATI Ina kiran Alaramma Malam Hashimu ya baiyyana gaban kotu.
MALAM HASHIMU Ya fito zuwa cikin kewayen shaida.
MALAM HASHIMU (CONT'D)Sunana Alaramma Malam Hashimu. Ni limami ne a wani dan karamin masallacin dake kan titin Ado abanu
LAUYAN GWAMNATI Ko ka san marigayi Alh.Ado.
MALAM HASHIMU Kwarai na san shi kuwa farin sani. Masallacin da nake limanci na kusa da gidansa ne.
LAUYAN GWAMNATI Ko me za ka iya cewa game dahalayyarsa.
MALAM HASHIMU Mutumin kirki ne kwarai da gaske.
LAUYAN GWAMNATI Ina so ka yiwa kotu bayanin me kakenufi da cewa shi mutumin kirki ne.
MALAM HASHIMU To! Ai an ce duk wanda ka ga ya lizimci addini ko taimakon addini to a iya yi masa shaida ta gari. Idan kuwa hakane, to dole ne na ce Alhaji Ado mutumin kirki ne, dominshine ke daukar mafiyawandawainiyar masallacin da mukesallah.
33.
LAUYAN GWAMNATI Ko ka taba jin a na zargin sa dawani halin banza, ma’ana kamar dai wata harka da za mu iya cewashashanci ce.?
MALAM HASHIMU Kai! Anya, ba dai Alhaji Ado ba. Nidai ban sani ba, ban kuma taba jinwanda ya zarge shi da rayuwarsakarci ba.
LAUYAN GWAMNATI To Malam Hashimu mun gode.
Ya fuskanci kotu. Ya mai shari’a, da wannan shaida nake fatan kotu za ta gamsu cewaMarigayi Alh. Ado Mutumin kwaraine, ba zai yiwu mutum kamarsa ya salwantar da kimarsa da mutumcinsa ba har ta kai shi neman aikata fajirci da ‘yar aikin gidansa.Dukkan labaran da wacce ake tuhuma ta bayar kirkirarsa ta yi amma babuhakikanin gaskiya a cikinsa.
MAI SHARI’A Ya dubi Gambo.
Ko kina da wata tambaya a gare shi.
GAMBO LAUYA
Ta mike tsaye kana ta fuskanci Malam Hashimu.
Malam Hashimu kace ka san AlahjiAdo, har ka kara da farin sani.
MALAM HASHIMU Hakane, ranki ya dade.
GAMBO LAUYA Tun yaushe ka san Alhaji Ado?
MALAM HASHIMU
Ya dan yi tunani kana ya amsa
Yau shekara ta bakwai da saninsa.
GAMBO LAUYA Gidanka nan yake tare da masallaci?
34.
MALAM HASHIMU A’a, ni ba ma a unguwar nake ba.Harkar almajirci ce dai kawai kekawo ni, idan isha’i ta yi na komagida.
GAMBO LAUYA Daren da Marigayi ya rigamu gidangaskiya, ko za ka iya tuna kun yisallar magariba zuwa Isha’i tare dashi?
MALAM HASHIMU Kwarai kuwa, a ranar ba mu yisallolin guda biyu da shi ba.
GAMBO LAUYA Malam Hashimu ko ka san sana’ar marigayi Alhaji Ado?
MALAM HASHIMU
Ya yi shiru zuwa wani lokaci, kansa kasa cikin tunani, can ya daga ya dubi Gambo, tare da girgiza kan sa.
A gaskiya ban san sana’arsa ba, nikuma ban taba tambaya ba.
GAMBO LAUYA Wanda ka sani har tsawon shekara bakwai, amma ba ka san sana’arsa ba, yaya a ka yi har ka sanrayuwarsa, sanin da za ka iya bayarda shaidar halayyarsa.
MALAM HASHIMU
Ya shiru cikin alamar damuwa ba tare da ya iya cewa komai ba.
GAMBO LAUYA Ya mai shari’a, ina fata wannan kotu mai alfarma za ta yi watsi dawannan shaida domin rashin ingancinta. Sannan ina rokon dagewannan zama zuwa gobe domin ci gabada gabatar da kariyarmu.
45 EXT. KOFAR GIDAN YARI RANA 45 Shige da ficen mutane ciki da wajen prison.
35.
46 INT. PRISON. WAJEN GANIN MASU ZIYARA. RANA 39 46
Lauya Gambo tare da Jummai, suna tattaunawa zuwa wani lokaci.wata Jami’ar gidan yari ta iso tana fadakar da ita cewalokacin ziyarar ta ya kare.
GAMBO LAUYA
Ta mike tsaye suna sallama da juna, sannan ta kawo ‘yankayayyakin da take dauke da su ta mika mata, tana mai karbacikin godiya.
47 INT. KOTU. SAFE 47
MAI SHAIDA
Tana dauke da ciki dan kusan wata bakwai.
Sunana Martha Audu, ni mutuniyarJihar plateau ce.
GAMBO LAUYA Ko za ki fadawa kotu abinda ya kawoki Kano,
MARTHA Na zo ne neman aiki domin na sami dan abin da zan biya kudin karatuna, kasancewar iyayena masu karaminkarfi ne.
GAMBO LAUYA Ko kin san marigayi Alh. Ado?
MARTHA Kwarai, na san shi, domin a gidansana yi aiki har tsawon wata uku.
GAMBO LAUYA An ce ganin gida ki ka tafi, tun daga nan ba ki dawo bakin aikinkiba ko hakane?
MARTHA
Ta girgiza kan ta cikin rashin amincewa.
A’a ba gaskiya ba ne.
36.
GAMBO LAUYA To menene dalilin barin aikinki a gidan Marigayin?
MARTHA
Ta dan yi shiru, kana ta dubi Hajiya Ladi.
Cikin saukin murya ta fara amasa tambayar da Gambo ta yi
mata. Wata safiya na tashi jikina badadi, ina ta faman amai... DISOLVE TO 48 INT. CIKIN DAKI SAFIYA 48 Hajiya ladi na tsaye bisanta, martha na faman kera amai cikinwata roba. Cikin wannan hali Alhaji Ado ya same su. ALHAJI ADO Ya dubi Hajiya, cikin alamar damuwa da tsarguwa, Me yake damunta, lafiya. HAJIYA LADI Wacce irin tambaya ce wannan bayankana ganin halin da mutum ke ciki. ALHAJI ADO Subahanalillah, maza je ki ki dubaidan Shehu ya zo ki ce ya fito damota, mu je na kaita asibiti. Bayan fitar Hajiya Ladi. Martha, me ya same ki? MARTHA Tambayar me za ka yi min, ai ka fikowa sani. ALHAJI ADO (Cikin kidima,) Kamar yaya na fi kowa sani, danAllah yi min bayani.
37.
MARTHA
(Ta dube shi)
Lafiya ta kalau, yau wata biyu
kenan ban ga al’ada ta ba. Ka san
kuma ba inda nake fita daga gidan
nan tun zuwana, ba kuma wani namiji
da yake da wata mu’amula dani idan
ba kai ba.
ALHAJI ADO
(Cikin in’inar dole,)
To to to, don Allah yi shiru kar
aji mu. Ki bari idan mun fita ma yi
zancen.
49 INT. CIKIN ASIBITI SAFIYA 49
Cikin wani karamin asibiti mai zaman kansa, Alahji Ado tare da Martha a gaban likita.
LIKITA
Ya daga wani dan karamin hoton scanning yana duddubawa, kana ya mayar da shi tare da sauran takardu cikin ambulam. Ya cigaba da rubutu bisa wata takarda kana ya dubi Alhaji Ado.
Alhaji, lafiyarta kalau. Ciki ne daita, dan kwana 49.
Ya mika masa takarda,
A saya mata wadannan magunguna, zasu taimaka ta daina yawan aman datake yi. Sannan ta rinka zuwaasibiti a kai akai ana duba lafiyarcikin da jaririn.
ALHAJI ADO
Ya karbi takardar da likita ya miko masa tare da abulan gabadaya. Sun mike tsaye cikin godiya kana suka fito.
50 EXT. WANJEN ASIBITI HANTSI 50
ALHAJI ADO Za mu je a zubar da shi,
MARTHA
A gaskiya ni tsoro na ke ji, ba zan
iya zubar da shi ba.
38.
ALHAJI ADO
To ke da kike son tafiya makaranta,
yaya za a yi ki sami damar karatu
kina dauke da ciki ko renon yaro.
Ki yi hakuri mu je a zubar da shi.
MARTHA
Ko yaya karatu yake da amfani a
gareni, ai bai kai rayuwata ba.
Gaskiya ni ba zan iya ba.
ALHAJI ADO To yanzu a ina za ki zauna?
MARTHA
Wannan ba wani abin damuwa bane,
zan iya komawa gida. Abinda nake so
kawai shine ka dauki nauyin kula da
ni da kuma renon yaro idan na haife
shi.
ALHAJI ADO
Yayi shiru, can zuwa wani lokaci ya nisa. Ya dauko littafinbanki [checque] ya na rubutu.
To shikenan, ga caki na dubu hamsinki je bankina ki karba. Idan kin jegida ki bude account ki aiko min dalambar. Kowanne wata zan yi mikitransfer kudi naira dubu talatin.
LIKITA (CONT'D)
GAMBO LAUYA
Tana rike da wata doguwar takarda mai kalmasa a hanunta. Ta
dubi alkalin kotu Ya mai shari’a, wannan itace Martha mai aikin gidan Alhaji Ado kafinzuwan abar wakilcina. Account din da take magana ta bude shi ne a bankin “Promise” da ke kan titin Yakubu Gowon cikin garin Jos Babbarbirnin jihar plateau. Wannan shine bayanan shige da ficen kudin dakecikin account din tun lokacin da aka bude shi kawo ya zuwa wannanlokaci Ta mikawa kotu takardar bayanin banki [statement of account]
39.
HAJIYA LADI Hawaye na zuba daga idanunta cikin bacin rai da damuwa.
MAI SHARI’A
Ya karbi takarda daga hanun akawun kotu, yana dubawa. Ya dubi
Lauyan Hukuma
Ko kana da karin tuhuma ga wannanshaidar.
LAUYAN GWAMNATI
Rike da kofin takardun shaidar da mai bayar da shaida ta
gabatar mike yana mai fuskantar kotu.
Ya mai shari’a, hujjojin mai bayarda shaida ba su da karfin da za a iya tabbatar da alakar nema tsakanin Marigayi da wannan mai bada shaida. Dukkan takardun da ta bayar na asibiti da sauransu babuwanda ke nuna cewa Alhaji Ado ya dauki alhakin cikin da mai shaida ke dauke da shi. A shari’ance dukkan wadannan ba za su iya zamashaidar abinda take da’awa ba. Ya mai shari’a ina so kotu ta sani cewa Marigayi Alhaji Ado Mutuminkirki ne, wanda ke da kimar mutumci a idanun al’umma. Don haka yakamatakotu ta yi taka tsan tsan da dukkanshaidar da za ta iya raunanamutumcinsa, saboda nakasu da kuma tawayar da hakan ka iya zaikewaiyalinsa cikin al’umma.
MAI SHARI’A Ya gyada kansa ga Gambo cikin isharar cewa ta ci gaba.
GAMBO LAUYA
Ina bukatar baiyanar Malam Shehu a gaban kotu.
SHEHU
Ya fito ya zuwa cikin kewayen shaida ya tsaya. Akawun kotu ya
rantsar da shi kamar yadda yake al’adar kotu.
GAMBO LAUYA
Ko za ka iya fadawa kotu sunanka
sana’arka da kuma alakarka da da
Marigayi?
40.
SHEHU Sunana shehu, ni direba ne, nine ke tuka shi har ranar da Allah ya karbi ransa.
GAMBO LAUYA Shekararka nawa kana tuka Alhaji Ado?
SHEHU Shekara ta biyar ina aiki tare dashi.
GAMBO LAUYA Me za ka iya tunawa game dahaduwarka ta karshe da maigidanka?
SHEHU Ina tare da shi har wajen karfegoma na dare, lokacin da na dawo dashi gida.
GAMBO LAUYA Ko za ka iya fadawa kotu inda ku kaje a daren wannan rana ta 19 gawatan yuli?
SHEHU
Ya yi shiru kadan, ya daga idanu ya dubi Hajiya kana ya saddakansa kasa ba tare da yace komai ba.
GAMBO LAUYA Malam shehu, kotu tana son ta jiina ku ka je da Marigayi Alhaji Ado a daren 19 ga watan yuli.
SHEHU
Kansa kasa ba tare da ya sake daga dubansa ba ya amsatambayar da lauya Gambo ta yi masa.
Mun je unguwar low cost ne?
GAMBO LAUYA Wajen wa ku ka je?
SHEHU Na kai shi wajen Fati ne?
41.
GAMBO LAUYA Wacece Fati?
SHEHU Yarinyarsa ce.
JAMA’A Masu sauraren shari’a suka nuna alamar mamaki, guna guni ya yawaita, har sai da mai shari’a ya jawo hankalin su, kotu tayi tsit.
GAMBO LAUYA
Ta dubi lauyan gwamnati, ba tare da tace komai ba ta yi masanuni ga Shehu dake tsaye cikin kewayen shaida.
HAJIYA LADI
Hankalinta a tashe, tana zubar hawaye.
LAUYAN GWAMNATI
Ya mike kana ya dubi Shehu direba,
Ka taba ganin wacce kake zatonwajenta ka ke kai shi.
SHEHU Ba zato nake ba, abinda nake fada tabbas ne, na san ta domin yanaaike na wajenta.
LAUYAN GWAMNATI Yanzu ke nan idan ka gan ta za kaiya shaida ta?
SHEHU Kwarai kuwa, tana ma cikin kotun nan a yanzu haka.
LAUYAN GWAMNTI Ko za ka iya nuna wa kotu ita.
SHEHU Ya yi duba cikin jama’ar dake cikinkotu kana ya yi ishara ya zuwa indatake zaune
Ga ta can mai sanye da koren leshi
JAMA’A Hankulan kowa ya karkata zuwa ga inda ya yi nuni, cikinrudani da hayaniya. Mai shari’a ya sake buga gudumarsa yana
42.
jan hankalin jama’a.
GAMBO LAUYA (Ta mike tsaye.)
Ya mai shari’a, ina rokon kotu ta bamu damar gabatar da shaidarmu takarshe, wacce itace Fati yarinyarAlhaji Ado.
FATI
Ta fito, ta tsaya cikin kewayen shaida, ita ma akawu ya rantsar da ita kamar sauran shaidun.
GAMBO LAUYA Ko za ki iya gabatar da kan kigaban kotu.
FATI Sunana na Fati, ni mutuniyarMaiduguri ce.
GAMBO LAUYA
Ta dauko wani hoto wanda ke dauke da fati tare da Alh. Ado
Da alama wannan hotonki, ne, ko za ki fadin wanene kuke tare da shi.
FATI
Ta karbi hoto to duba,
Shine Marigayi Alh. Ado. Mun daukiwannan hoton kusan farkon haduwarmu tare da shi.
GAMBO LAUYA To yaya a ka yi kuka hadu?
FATI Na san shi ne ta hanyar waniabokinsa wanda da shine saurayina.
GAMBO LAUYA Ki na ina Ranar 19 ga watan yuli?
FATI A ranar muna tare da shi tun
misalin Magriba har.....
DISOLVE TO
43.
51 INT. RESTAURANT DARE 51 Alhaji Ado tare da Fati suna cin abinci 52 INT. SHOPPING COMPLEX DARE 45 52 Tare cikin wani kantin kayayyaki suna shopping 53 EXT. TITI. DARE 53 Suna bayan mota tare shehu na tuka su cikin gari bisa titi sun nufi gida. 54 INT. FALO DARE 54 Tufafinsa na zube bisa wata doguwar kujera, hakanan kayanFati na zube a wuri guda, rigar mamanta na rataye samanmajinginar kujerar. Sautin dariyarsu cikin nishadi gamisaukar ruwa na fitowa daga kofar wani bandaki dake da rufe 55 EXT. KOFAR GIDAN FATI. DARE 55 Motar Alhaji Ado na tsaye, shehu direba na gaban gidan motaryakwantar da kujerar baya yana kwance. Sautin rediyo kasakasana tasowa. Agogon motar ya nuna karfe goma daidai, lokacin daAlhaji Ado ya fito tare da Fati sanye da zani falle daya kaiba dankwali tana rako shi. DISOLVE TO 56 CIKIN KOTU 56 FATI Hawaye na gangaro mata, cikin sauki ta sa hannu ta share. Wannan itace ranar haduwarmu ta karshe, washegari na ji labarinmutuwarsa a rediyo. Kotu ta yi tsit kamar an dauke ruwa, sauran jama’a duka sun tsirawa Fati idanu. GAMBO LAUYA Cikin rusunawar girmamawar kotu Ya mai shari’a wadannan sune shaiduna. MAI SHARI’A
44.
Yaci gaba da rubutu cikin fayil din dake gabansa. Bayan ya gama ya dubi Lauyan hukuma.
Ko kana da wani abin cewa?
LAUYAN GWAMNATI
Babu, ya mai shari’a, tsokacinmu
bisa wannan shaidar kamar sauran da
Lauyar abar tuhuma ta gabatar ne
MAI SHARI’A
Ya juya ga Gambo. Menene rokonki ga wannan kotu.
GAMBO LAUYA
Ya mai shari’a ina fatan kotu za ta
gamsu cewa tuhumar da ake yi wa
wacce nake karewa a kan ta kashe
Alhaji Ado da ganganci ba gaskiya
ba ne. Alhaji Ado ya gamu da
ajalinsa ne a sakamakon yunkurin
kare mutumcin kai da ita Jummai ta
yi lokacin da ya so ya yi mata
fyaden karfi da yaji. Shaidar farko
ta tabbatar da cewa Jummai ba ta je
dakin Alhaji Ado ba a daren 19 ga
Yuli, domin matar sa Hajiya Ladi ta
tabbatarwa kotu cewa ba al'adarsa
ba ce barin kofa a bude lokacin da
zai kwanta. Babu kuma wata shaida
da ta nuna an karya kofar tasa a
wannan dare. Shaida ta biyu wacce
ta yi nuni karara da cewa Alhaji
Ado shi ne ya yi takakkiya zuwa
dakin da Jummai take kwana, ita ce
dan mabudin dakinsa da 'yan sanda
suka iske a dakin Jummai. Hoton
zanen yatsun da ke jikin wannan
mabudi bai yi daidai da hoton zanen
yatsun Jummai ba, amma kuma cikin
dakinta. Tambaya, zanen yatsun wane
ne a jikin wannan dan mabudi?
Shaidun da muka gabatar a gaban
wannan kotu sun tabbatar mana cewan
babu nagartar halayya a rayuwar
Marigayin. Abinda wacce ake kara ke
da’awa na cewa ya neme ta halinsa
ne sananne.
(MORE)
45.
GAMBO LAUYA (CONT'D)
Ina so kotu ta yi izna da cewa har
kawo ya wannan gaba cikin wannan
shari’a wadanda ake kara sun kasa
baiyanar da shaidar nagartar
halayyar Marigayi kakkarfa da za ta
gamsar da kotu cewa Marigayi ba zai
iya aikata abinda abar wakilcina ke
da’awar aikatawa ba. Shaidunmu, duk
da sukan da Lauyan mai kara ke yi
na ba su cika sharadan shari’a ba,
amma dai za su iya zama karina mai
karfi bisa da’awar wacce ake kara
saboda gazawar shaida mafi karfi
daga bangaren wadanda ke kara.
Ya mai shari’a muna rokon wannan
kotu mai alfarma ta gamsu da cewa
Jummai ba ta shiga dakin Alhaji Ado
ba kamar yadda ake tuhumarta,
hakanan ba bu tabbacin tuhumar
yunkurin sata da a ka dora mata,
sannan ba ta kashe Marigayi Alhaji
Ado kisan ganganci ba kamar yadda
masu kara ke da’awa. Ina rokon kotu
ta yi watsi da wannan kara domin
dalilai guda biyu. Na farko,
gazawar shaidar tuhumar da ake
mata, na biyu, kariyar da take da
ita a karkashin shari’ar musulumci,
shari’a ta baiwa dukkan wacce a ka
nemi keta mutumcinta damar kare
kanta koda da makami ne kamar yadda
ya tabbata a karkashin Hadisin
Sa’ad Bn Zaid cikin ruwayar Abu
Dawud, Nisa’i da Ibn Maja.
57 EXT. CIKIN GARI MARAICE 50 57
Mutane a wurare dabam dabam suna sauraron radiyo
58 INT. GIDAN GAMBO FALO MARAICE 51 58
Babu kowa cikin falon, radiyo na kunne, sautinsa na baiyyanaa matsakaicin sauti. Dije na kicin tana aikin girki. Sautinradiyon na isa gareta. Ta yi kasake da kunnenta lokacin daaka fara labarai da jin cewa ga labari da dumi duminsa dagawakilin babbar kotu
46.
RADIO VOICE
A yau Mai Shari’a alkalin babbar
kotun Jiha, Malam Mubasshar ya kawo
karshen mashahuriyar shari’ar nan
ta kisan kai da aka yiwa wani
attajiri mai suna Alhaji Ado. Ana
tuhumar ‘yar aikin gidansa mai suna
Jummai cewar itace ta kashe shi ta
hanyar suka da wuka a lokacin da
take kokarin yin sata a dakinsa.
Kotu ta kori wannan shari’ar saboda
gazawar shaida kwakkwara daga
bangaren masu kara. Wakilinmu ya yi
hira da Lauyar wacce ake tuhuma
bayan shari’ar kamar haka:
59 A HARABAR KOTU 59
DANJARIDA V.O
Yaya ki ka ji game da wannan nasara
da ki ka samu a cikin wannan
shari’a?
GAMBO LAUYA V.O
Da farko godiya ta ga Allah SWT
take wanda ya ba ni wannan dama.
Ina fata wannan nasara ta zama
tafarkin sauya tunanin mutane na
ganin shari’a ta mai karfi ce.
Yakamata jama’a su sani, a gaban
shari’a gaskiya itace mafi karfi.
Idan kana da gaskiya jagoranci
kadai ka ke nema. A shirye muke mu
daga nan kungiyarmu karkashin
shirin MULTI-DOOR COURT mu baiwa
talakawa da duk me neman hakki
jagorancin shari’a a duk lokacin da
bukatar hakan ta taso..

No comments:

Post a Comment