Monday, April 16, 2012

Farida Na Nasir Gwangwazo

1 EXT. KOFAR WANI GIDA A WANI KAUYE. SAFIYA 1
Maroka na kai kawo cikin zarya suna rusa roko da kirari, yayin da masu gangunan duma ke ragargarzar kida. Da yawanmutanen wurin na zaune ne bisa tabarmin dake shimfide a kofar gidan. Hakanan mutane ke ci gaba da zuwa kofar gidan sunazaunawa maroka na bin wadanda suka gane da kirari har dai a sallame su.
AHMAD
Yana tafe cikin motarsa ya shigo cikin kauyen shi daya batare da wani dan rakiya ba.
LIMAN
Liman da jama’arsa sun iso kofar gidan sun sami wuri sun zauna yayin da mutane ke ta zuwa suna gaisuwa gareshi.
AHMAD
Ya iso kofar gidan kana ya ja birki ya tsaya, maroka sun yo ca kan sa lokacin da yake fitowa. Sun biyo bayansa da kirarihar dai ya iso wajen da liman yake a a zaune tare da wasudattijai. Ya yi gaisuwa kana ya mike ya nufi shiga cikin gida amma marokan nan su ka tisa shi gaba abinda ya sanya shi dole ya tsaya ya sallame su kana suka rabu da shi suna godiya dayabo.
MAKADA
Makada gangar duma na ta faman kida da waka ana yi musu kari.
SANKIRA
Yana durkushe ya karkata kunnensa ga sauraren wani dattijokana ya daga ya kwarara kuwwar shela da neman kowa ya dakatacewar yanzu za a daura aure.
MAKADA
Sun ajiye gangunansu sun sami wurin tsugunawa sun tsugunayayin da sauran jama’a kowa hankalinsa ya koma zuwa gada’irar inda Liman yake tare da manyan gidan.
LIMAN
Tare da masu gidan an baje goro da sauran kayan al’adardaurin aure a gabansu ana kasafi. Wani dattijo ya debo kashingoro da alawa ya mikawa sankira,
SANKIRA
Ya karbi goro da alawa cikin hanun babbar rigarsa kana ya
juya zuwa ga jama’a yana rabawa.
2.

2 INT. DAKIN GOGGO.SAFIYA 2
GOGGO
Kai kadai na gani, ina sauran
iyalan gidan?
AHMAD
Kan sa kasa sunkuye cikin ladabi da girmamawaWallahi aiyuka ne su ka sha matakai da yawa. Ita ma ta so a ce daita a ka yi bikin nan.
GOGGO
Cikin damuwa Na ga alama dai kai kana neman kafitar da kanka daga cikin dangi. A yau ranar daurin auren nan dukhaular gidan nan ta taru amma a cesai iyalin gidanka ne kadai babu.Wallahi ni dai wannan lamari bai yimin dadi ba.

3 EXT. KOFAR GIDA. SAFIYA 3
Liman tare da sauran jama’a sun shafa fatiyar daurin aure.Sankira da maroka sun sake kaurewa da kururuwar roko. Wata mota karama ta iso ta tsaya a kofar gidan dauke da mata a ciki. Maroka sun nufo su tare da kirari suna ambatar sunayenwadanda suka shaida cikinsu. Sun biyo bayansu lokacin da sukafito daga motar suna masu shigewa cikin gida.

4 INT. DAKIN GOGGO.SAFIYA 4
AHMAD
Goggo na fada miki ba wai taki zuwa
ba ne. Ita kan ta ta so ace an yi
bikin nan da ita ba dan yanayin
aikinta ba.
GOGGO
Cikin bacin rai da fushi Bata isa ta raba mu da kai ba idan ma wannan ce manufarta. Ka san dai tun asali auren nan ba da son raina a ka yi shi ba.
(MORE)
3.
GOGGO (CONT'D)
Ba dan ka nuna ka isa da kanka ba
da dai ba a yi shi ba inda ka na
son dadin zuciyata. Haba, me za a
yi da auren kabila ba don dai
kaddara ba. To wallahi idan kana
son ka ci gaba da ganin sararin
fuskata lalle ne ka kara aure. kuma
ma a nan kauyen ba a wani wuri ba.
Ta buda wani dan karamin gwangwani da lalubo wani guntun gorota jefa a bakinta
Idan ba ka san bacin raina ba to wannan karon zaka sani matukar ka sabawa umarnina.
Sallama daga wajen dakin ta ratso abinda ya waiwayar dahankalinsu ga bakin da suke shigowa.
‘YAN BIKI
Sun shigo cikin dakin dauke da akwatunansu.
GOGGO
Cikin walwalar fuska ta yi musu marabaA’a mutanen Jas ne, sannunku da zuwa. Kai amma kun yi sammako.
Babbar cikinsu 45 ta amsa mata
AMINA
Wallahi kuwa, ai tun asubahi muka
baro gida
RUKAIYYA
Rukaiyya [28] ta dubi AhmadYaya Ahmad, idan na yi waya ma bakadaukar wayata.
Tayi murmushi.

5 EXT. DAJI. MARAICE 5
Ahmad tare da abokinsa Dauda cikin daji suna hawa bisa wani dutse har dai suka kawo wani wuri dake dauke da alamar kamar an tona wurin. Kana su ka tsaya yana nuna masa
DAUDA
Ka ga nan ma shi a ka tona. Idan
dai da hali yakamata ka zuba jari
cikin harkar nan.
(MORE)
4.
DAUDA (CONT'D)
Ba zai yiwu a ce ga dukiya tsibe a
karkararmu ba amma sai dai wasu
baki ne za su rika cin gajiyarta.
AHMAD
Ya yi shiru kadan kana ya dubi abokinsa
Gaskiya Dauda ba wai bana son zubajari bane, sai dai ka san dukharkar da ba ka santa ba tana da wuyar sha’ani. Amma daiinsha’allahu zan duba na ga abindazan iya yi.
Sun dan yi gaba kadan kana sun zauna bisa wani dutse dake kusa da su.
DAUDA Wai me ke damunka ne,
AHMAD
Ya dubi Dauda yana mai girgiza kansa cikin damuwa
AHMAD (CONT'D)
Wallahi Dauda matsalar Goggo ce ke
damu na. Ta uzzara min wai dole sai
na kara aure, kuma a nan kauyen ba
a wani wuri ba. Ta dauki karan
tsana ta dorawa matata. Na rasa
yadda zan yi na fahimtar da ita
yadda za ta gane larurar zamanmu na
maraya da kuma irin yanayin
aikinta.

6 INT - CIKIN KOTU 1 - RANA 6
Kotu na zaune cike da 'yan kallo, ga 'yan jarida da lauyoyikowanne a mazaunan su, SHITU, DANLADI da MATI na tsaye a gurin wadanda a ke tuhuma idanun su duk sun firfito cikin yanayi na fargaba, MALAM SALIHI da BABA RABI na zaune su namatsar hawaye a sashen 'yan kallo, FARIDA na tsaye rike datakardu a hannu ta na fuskantar ALKALI HABU, wanda ke da rawani a kansa, ta na magana, yayin da ya kan yi rubutulokaci-lokaci.
FARIDA
Ya Mai Shari'a, akwai kuskuren da
'yan sanda su ka yi wajen gabatar
da caji kan wadanda a ke zargi.
(MORE)
5.
FARIDA (CONT'D) Saboda haka Ina rokon kotu ta ba ni izinin sauya cajin da a ke yi mu sudaga zargin aikata fyade zuwa naaikata kisan gilla da hadin baki.Wadannan cajin guda biyu su ne kadai za su ba mu damar bin hakkin rayuwar Ummi Salihi, 'yar shekarabakwai, wacce ta rasa ranta a hannun wadanda a ke zargi.
Fuskokin 'yan kallo cike da yanayi na rashin fahimtar abin dake gudana. Akwai alamun karin damuwa a fuskar Malam Salihi daBaba Rabi. Yanayi na faduwar gaba ya bayyana a fuskar LAUYA GARBA. Ya mike da sauri.
LAUYA GARBA Ya Mai Shari'a, 'yan sanda sun rigasun gabatar da cajinsu ga kotu, harma an fara sauraron shari'ar. Sake sabon caji zai cigaba da tsawaitashari'ar nan, wanda hakan cutarwa ce ga wadanda a ke zargi.
Ya zauna. Farida ta numfasa.
FARIDA A bisa kundin tsari na gabatar dakararraki, kwamishinan shari'a na jiha, wanda shi nake wakilta a wannan kara, ya na da hurumin karbekara daga hannun 'yan sanda tare daikon sauyawa ko sabunta cajin dakwamishinan 'yan sanda ya yi tundafari a shari'a ta aikata miyagunlaifuka.
Alkali Habu ya gyada kai cikin yanayi na gamsuwa.
ALKALI HABU Kotu ta gamsu da bayanan ki.
'Yan surutan mutane kasa-kasa. Cikin yanayi na jin dadiFarida ta dukawa Alkali Habu.
FARIDA Na gode.
Alkali Habu ya yi rubuce-rubuce, sannan ya dago kai ya na maigyara tabaran idanunsa.
ALKALI HABU Kotu ta dage sauraron shari'ar zuwaranar talatin ga wata.
6.
Ya mike, a ka yi gaisuwar kotu, sannan ya bi dama ya fita.Mutane su ka fara ficewa daga kotun, jami'an tsaro su kasanyawa su Shitu ankwa su ka fita da su, yayin da Farida tatsaya ta hada takardun da ke baje a gabanta, sannan tadaukowaya ta na kokarin bugawa.

7 EXT. MARAICE 7
Yanayin garin irin na damina, ruwan sama na sauka a hankalicikin yayyafi yayinda mutane ke ta kai kawowarsu ba tare dadamuwa ba.

8 INT. GIDAN AHMAD. KICIN. MARAICE 8
Farida na kicin ta na faman girki, ludayin miya a hannunta tana juyawa. Ta daga kai ta dubi agogon dake rataye jikin bangokarfe 7:00 daidai kana ta rufe tukunyar miyar
9 INT. GIDAN AHMAD FALO. MARAICE 9
Surayya (10) na zaune ita kadai ta na faman wasan video game. akwai sauran kayayyakin wasa baje kusa da ita.
FARIDA
Ta shigo falon, ta dubi Surayya, cikin tausasawa ba tare da
hantara ba Suraiyya wasan nan ya isa haka, kije ki Home work din ki.
SURAIYYA
Ta yi wani tari dan kadan amma ba mai zafi ba, cikin shagwaba
irin ta yara da nuna rashin jin dadin katse wasan da take.Umma, ni ban gane aikin ba ne, saidai ki zauna ki taimaka mini.
FARIDA
Ta dauki wata riga mai kauri ta jefa mata
To je ki debo littatafan mu gani.
SURAIYYA
Ta dauki rigar tana kokarin sanyawa lokacin da take kokarinshigewa cikin wani daki
7.
10 EXT. GIDAN AHMAD HARABA, DARE 10
Gari ya fara duhu daga waje fitulun gidan dukansu a kunne
TALATU
Talatu (40) tana daka doyar sakwara cikin wani dan karaminturmi.
11 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 11
Farida da Suraiyya zaune tana taimaka mata aikin home work dinta.
TALATU
Tana kai da kawowa dauke da kwanukan abinci tana jerawa bisateburin cikin abinci.
FARIDA
Ta dubi agogon hanunta kana ta rufe littattafan da sukekaratun, ta kama hanun suraiyya su ka nufi inda teburin abinci yake. Suna zaune bisa teburin cin abinci ta dauki wayata na kokarin bugawa.
12 EXT. OFFICE BLOCK DARE 12
Rubuce jikin ginin sunan kamfanin kamar haka: ZAMANI GEOTECHNICAL SERVICES.
13 INT. OFISHIN AHMAD. DARE 13
Yana zaune kan teburinsa, komfuta laptop na bude a gabansa.Bisa komfutar wani shafin kasuwancin internet ne bude. yanarike da waya a hanunsa suna zantawa kana ya ajiye wayargefensa. Ya dubi agogon ofishinsa ya karanta masa karfe 9:30 lokacin da wayarsa ke bugawa. Ya dauki wayar yana mai amsawalokacin da ya mike tsaye cikin harhada kayayyakinsa shirintashi. Ya ci gaba ta rufe komfutarsa yana mai sanyata cikin jaka, wayarsa na kafadarsa ya matse ta da kansa yana mai cigaba da magana ba tare da ya bar abinda yake yi ba.
14 EXT. TITI.DARE 14
Yana cikin motarsa bisa titi, wani sautin na tashi cikin motar a hankali kasa-kasa.
8.
15 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 15
Yana zaune rike da wata mujalla yana dubawa, talabijn gabansaa kunne ba tare hankalinsa na kan ta ba.
16 INT. GIDAN AHMAD KICIN DARE 16
Farida na dakan sakwara cikin wani dan karamin turmi, bayanta kammala ta debe ta zuba cikin mazubi, kana ta fara shiryasu bisa wani tray.
17 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 17
Ahmad na nan zaune inda yake hankalinsa ya tafi bisa dubamujallar da ke hannunsa, yayinda farida ta shigo dauke dakayan abinci ta fara jerawa bisa teburin abinci.
FARIDA
Honey, ga abincin ka fa ya kammala.
Ka yi hakurin jinkirin da a ka
samu.
AHMAD
Ya ajiye mujallar bisa kujerar da ya zauna kana ya nufi wajenteburin abinci.
18 EXT. GIDAN AHMAD TSAKAR GIDA DARE 18
Babu alamar motsin kowa cikin gidan, fitilar dake waje tadan haske tsakar gidan amma ba haske mai karfi ba. Har yanzuruwan sama na sauka yif-yif-yif a hankali ba da karfi ba.
19 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 19
Yana zaune bisa teburi yana cin abinci a hankali, Farida nada ga gefe guda zaune ta zuba masa idanu tana kallonsa.fuskarsa babu alamar walwala, kamar dai wani abu na damunsa.
FARIDA
Honey, ka na jiran na tambayeka ne
ko me ke damunka.
BAYAN WATA UKU
RANA - CIKI: KOTU 1 - DAKIN SHARI'A
9.
LAUYA GARBA
A madadin wadanda a ke tuhuma Ina
mika rokona ga kotu da ta yi
sassauci yayin yanke hukunci, domin
wadanda a ke tuhuma matasa ne da
idan a ka ba su dama za su iya
amfanar al'umma a nan gaba, kuma
wannan shi ne karo na farko da a ka
taba kama su da laifi makamancin
wannan a rayuwarsu. Na gode.
Ya duka ya yi gaisuwar kotu ya zauna. Farida ta mike.
FARIDA Cikin girmamawa ga kotu,
Ina rokon kotu ta da ta hukunta wadannan masu aikata laifi bisa dalilai kamar haka: Na farko, domin ya zama darasi ga masu aniyaraikata danyen aiki makamanci nasu.Sannan wadanda ke da hakkin bin jinin Ummi, wato iyayenta, su ji a ransu cewa, 'yarsu ba ta rasu a banza ba. Kuma Ina fata kotu ta yila'akari da yanayin yadda gari ya dauki zafi a kan wannan shari'ar, wanda idan a ka bar masu laifin su ka cigaba da rayuwa za a iya saminballewar hatsaniya. Hakika barinirin wadannan azzaluman a rayebarazana ce ga rayuwar mata bakidaya a wannan zamani. Don haka Ina rokon kotu da ta gaggauta yanke mu su hukunci, makamancin abin da su ka aikata ga Ummi Salihi, waccce take 'yar karama ce, ba ta ma sanlaifi ba a duniya. Na gode.
Ta duka ta yi gaisuwar kotu ta zauna. Alkali Habu ya yi danrubutu, sannan ya numfasa ya na mai karantowa bayanai datakardun gabansa jawabin yanke hukumci bayan sauraronhamzarin lauyoyi. Yanayi na farin cikin ya bayyana a fuskarMalam Salihi da Baba Rabi da 'Yan Kallo. Daga zaune a inda take, bakin Farida ya bude a hankali fuskarta dauke da alamar gamsuwa.
ALKALI
Alkali Habu ya mike, a ka yi gaisuwar kotu, sannan ya fice.Mutane su ka shiga yiwa juna barka tare da ficewa daga cikin kotun. Jami'an tsaro su ka sanyawa su Shitu ankwa su ka fitada su. Lauyoyi su ka dinga zuwa su na taya Farida murna.
10.
20 EXT. HARABAR KOTU RANA 20
Farida lullube da ‘yan jaridu suna faman yi mata tambayoyibisa nasarar da ta samu.
21 EXT. BAKIN TITI MARAICE 21
Rukaiyya rike da wani akwatin kaya mai taya tana gara shibisa titi har ya zuwa wurin tsayawa. Ta dubi wayarta kana cikin nutsuwa ta danna lambobinsa.
22 INT. SUPERMART MARAICE. 22
Ahmad tare da Suraiyya suna saye-saye, yana rike da wani kwandon zuba kaya ciki suna gewayawa. Dukkan wanda ya ga wani abin so suna dauka su saka cikin wannan kwando. Karshe sun iso wajen Ice cream an sayawa Suraiyya.
23 EXT. BAKIN TITI MARAICE 23
Rukaiyya na nan tsaye ta na faman nemansa a waya cikin damuwasaboda rashin samun layinsa a kan lokaci. Bugawarta ta karsheda ta yi ta sami sa’ar samunsa.
RUKAIYYA Hello!
24 INT. CIKIN MOTA MARAICE 24
Ahmad na tuki Suraiyya na gefe cikin walwala na zukar ice cream.
AHMAD Yanzu kina daidai ina?
Ya saurara kadan cikin sauraronta.
AHMAD (CONT'D)
To ki jira ni nan inda kike, zan
iso cikin dan lokaci kadan.
25 EXT. BAKIN TITI MARAICE 25
Ya tsaya daidai inda take, cikin sauri ya fito ya bude boot din motar suna ma su zuba kayanta ciki, kana suka zagaya zuwaga kofar shigar mota cikin hamzari.
11.
26 INT. GIDAN AHMAD. KICIN. DARE 26
Farida na kicin tana kokarin shirya abincin da ta dafa.
27 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 27
Rukaiyya tare da Ahmad bisa teburin abinci suna shan apetisergabannin a kawo musu abinci cikin raha. Za mu ga Ahmad nadariya yayin da ita kuma Rukaiyya ke dauke da wani murmushimai yalwa a fuskarta ta na mai yiwa Ahmad kallo irin kallondake dauke da sakon zuciya boyayye.
28 INT. GIDAN AHMAD KICIN DARE 28
Farida ta ji lallausar dariyar Ahmad abinda ya sanya talekowa don ta ga ko me ke faruwa. Yanayin murmushin Rukaiyya da irin kallon da take masa ya bugi zuciyarta, nan take fuskarta ta dan sauya zuwa ga alamar damuwa.
29 FALO 29
AHMAD Yanzu wa ke nan ki ka jajubo mana.
RUKAIYYA Ko dai wa ku ke son jajubowa
AHMAD Mu ne ma ma su jajubo miki.
RUKAIYYA Ba ka ji abinda da Goggo ke cewa bake nan? Tace ban isa na kawo musu wanda ba su ne su ka zabo mini ba.
AHMAD
(murmushi)Kai! Su Goggo ke nan. Ita har yanzuba ta san zamani ya canza ba.
RUKAIYYA
(murmushi)Mai yiwuwa kuma ta na da gaskiya.Sha’anin na ku ne na mazan wannan zamani na da wuya.
Hankalinsu ya juya zuwa ga Farida da ke isowa. Tana jerekayan abinci bisa teburin fuskarta babu alamar walwala.
12.
SURAIYYA
Tana sanye da wata riga yar karama maras duhu gaban talabijintana wasan video game. Ta dan fara tari kadan sama sama bamai tsanani ba.
30 FALO TEBURIN CIN ABINCI 30
Sun natsu ga cin abinci, cikin kawaici, ba bu mai magana dajuna.
RUKAIYYA
Lokaci lokaci Rukaiyya kan yi satar kallon Ahmad amma shi batare da ya lura ba.
FARIDA
Farida ta kula da abinda ke wakana na wannan satar kallon da murmushin ta take gareshi. Hakan ya sake duhunta fuskartabisa duhun da take da shi gabanni. Abincin da ba a kare ci bake nan ta bari, cikin rashin jin dadi ta tashi daga teburin ta shige ciki. Ahmad ya dube ta da fuskar tuhuma.
AHMAD Honey! Lafiya dai?
31 EXT. TITI SAFIYA 31
Zirga zirgar mutane da ababan hawa cikin safiya. Gefen titi ginin ofishin SAUKI CHAMBERS ne.
32 INT. CHAMBER SAFIYA 32
BABBAN LAUYA
Ba za ki iya wannan case din ba, me
ya same ki?
FARIDA
Barrister, ba na cikin nutsuwar da
zan iya rikon case din sosai har a
samu adalcin shari’a.
BABBAN LAUYA Ko ki na bukatar taimakona?
FARIDA
Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba zuwa wani lokaci kadan.
13.
Matsalar cikin gida ce. Ka baiwaA’isha case din, za ta iya.
BABBAN LAUYA
Yayi shiru yana duban ta kamar yana neman wata amsa dagafuskarta, kana ya mumfasa.
O.k ki tattauna da ita sai ki ba ta. Ki taimaka mata don gobe ne zaa fara sauraren case din.
33 EXT. GIDAN AHMAD. RANA 33
Yana kokarin parking din motar cikin gida lokacin da Rukaiyya ke lekowa ta taga
34 INT. GIDAN AHMAD FALO RANA 34
Rukaiyya ta shigo falo lokacin da Ahmad ke shigowa dauke dajakarsa a hannu. Wayarsa ta buga lokacin ya dauke ta zuwa gakunnensa.
AHMAD
O.k Honey, ba damuwa zan je nadauko ta.
RUKAIYYA
Yaya Ahmad, yau a gida haka da
wuri, ko ka yi mantuwa ne?
AHMAD
(murmushi)
A,a ba mantuwa na yi ba. Mun barki
a gida cikin kadaici ga kuma
bakunci. Shi ya sa na dawo don na
debe miki kewa kafin Farida ta
dawo.
RUKAIYYA
Ta yi masa wani irin kallo tare da murmushi
Wallahi Yaya babu ruwana idanFarida ta shake ka a wuya. Ba kalura da yadda ta yi bane jiya?
AHMAD
Rabu da ita, ta cika yawan zargi.
Sauri ki shirya mu fita, za mu je
dauko surayya daga makaranta.
14.
35 INT. CHAMBER RANA 35
FARIDA
Farida rike da waya a hanunta cikin tunani.
AISHA
A’isha [28] tana duban Farida fuskarta dauke da son nemanbayanin halin da take ganin abokiyar aikinta.
Farida, wai me ke damunki ne. Gaba daya cikin kwanakin nan ba ki danutsuwar hankali. Ina tsoron wannan na iya shafar nagartar aikinki.
FARIDA
Ta yi shiru ba ta ce mata kome ba, kana ta numfasa.
Aisha, matsala ce da ni a gida. Allah ya jarrabe ni da kishi. Ina tsoron dangantakar Ahmad da watayarinya da ta bakumce mu. Duk dadai kanwa ce gare shi amma komai naiya kasancewa don babu haramci a tsakaninsu. A yanzu haka ta daukihankalinsa fiye da ni.
AISHA
Farida ni ban ga wani abin damuwa
ba cikin wannan lamari. Har yanzu
kamar ba ki fahimci al’adar
zamantakewar jama’armu ta Hausa ba.
sha’ani ne kawai na zumuncin ‘yan
uwa.
FARIDA
Hakane Aisha, ba ni bukatar zama
bahaushiya kafin na fahimci zuciyar
namiji. Al’adar zuciyarsu duka daya
ce walau ta bahaushe ko waninsa,
babu bambamci.
Ta mike tsaye tana tara kayayyakinta, sannan ta rataya
jakarta tana kokarin fita.Zan koma gida ne, idan kina bukatartaimakona bisa wani abu, ko a wayakya iya kirana.
15.
36 EXT. MAKARANTA RANA 36
An tashi daga makaranta, wasu yara na jira wasu kuma na shigamotocin da aka zo daukarsu wasu kuma na wasanin bisa kayyakinwasa kafin a zo daukarsu. Suraiyya na cikin yara wadanda suke jira.
37 EXT. TITI. RANA 37
Ahmad tare da Rukaiyya cikin mota sun iso makaranta. Tana rike da waya a hannunta suna magana da wata.
RUKAIYYA
Na kwana biyu a garin, amma don
Allah ki yi hakuri gobe zan zo.
Ta dan saurare To na gode sai kin ganni.
Ta rufe wayar kana hankalinta ya koma ga Ahmad yana tuki tana mai murmushi lokacin da yake tsayawa kofar makarantar.
SURAIYYA
Ta hango motar ta taso a guje da jakarta goye a bayanta zuwamotar. Da zuwanta ta bude ta shiga ciki da sauri.
38 INT. GIDAN AHMAD RANA 38
Talatu mai aiki na ajiye abinci bisa teburi
TALATU
Sun fita tare da Alhaji dauko
Suraiyya. Amma ina ganin sun kusa
dawowa don sun jima da fita.
FARIDA
Fuskarta ta sauya ya zuwa nuna damuwa
39 EXT. KOFA GIDAN AHMAD RANA 39
Kofa ta bude Suraiyya ta fito rike da jakar makarantarta a hannu ta shige cikin gida a guje, kana su kuma su ka koma batare da sun shiga cikin gidan ba.
16.
40 INT. GIDAN AHMAD. 40
FARIDA
Ta leko ta taga ta hangi motar lokacin da ta juya suna masukomawa fuskarta dauke da karin damuwa.
SURAIYYA
Ta shigo a guje zuwa ga mahaifiyarta ta na mai rungumetacikin murnar dawowa gida.
41 EXT. FILIN SHAKATAWA MARAICE 41
Rukaiyya tare da Ahmad zaune bisa wani teburi dauke dakayayyakin abinci da na sha suna tattaunawa.
AHMAD
Rike da kofin lemo a hanunsa ya na mai duban Rukaiyya cikin
alamar kulawa. Ban taba tsammanin zan iya fahimtarhikimar Goggo ba sai yanzu. Mu baiwa fahimtarsu dama mu gwada mu gani ko mai Allah zai yi.
RUKAIYYA
Cikin taruwar hankali sosai Yaya ban ki ko me za ka ce ba, ammadai yakamata a yi takatsantsan.Kana zaune da matarka lafiya ba nison na zama sanadiyar tashinhankali a gidanka.
AHMAD
Ya kurbi ruwan lemo Kamar yaya tashin hankali. Na sanba za ta so ba, amma ai hakuri ya zama dole. Ina fata dai ba kokarin ture gwamnatina kike son yi ba.
RUKAIYYA
(Murmushi.)Har yaushe ka kafa gwamnatin dakake tsoron tunkude ta? Kai! Su Yaya ke nan, to gwamnatin Faridankuma fa?
17.
42 INT. DAKIN BACCI GIDAN AHMAD DARE 42
Agogo rataye jikin bango na daidai lokacin karfe dayan dare. maganarta na tasowa yayin da kyamara ke zagaya dakin har tadawo kan su suna zaune bisa gado.
FARIDA’S VOICE
Na hakura ne duk tsawon lokacin nan
don kar ka ce ina neman shiga
tsakaninka da ‘yar uwarka. To amma
na ga lamarin naku ya wuce makadi
da rawa, abin na neman tsallake
alakar jini ya zuwa kafuwar wata
dangantaka ta dabam da na kasa
ganewa.
FARIDA
Ahmad, ina son na san me ke gudana
tsakaninka da Rukaiyya?
AHMAD
Yayi shiru zuwa wani lokaci ba tare da yace mata komai ba. Ya nutsa cikin tunani kawai cikin shiru ga barin magana.
FARIDA
Ta dube shi da fuska dauke da tashin hankali cikin damuwa.
Ahmad, sauraronka nake.
AHMAD
Yayi ajiyar zuciya kana ya dube ta.
Me zan fada miki game da ita wanda ba ki sani ba. Rukaiyya ‘yar uwatace ba ya ga wannan me ki ke son sani kuma?
FARIDA
Ta yi shiru ta tsura shi da idanu ba tare da tace uffan ba.
AHMAD
Ya dubeta ya ga irin kallon da take masa, kana ya sunkuyar dakansa kasa. Ba tare da ya dube ta ba.
Farida, za mu yi aure ni daRukaiyya. Amma a gaskiya wannan bayi na bane.
(MORE)
18.
AHMAD (CONT'D) Tun daga gida a ka kulla shi. Ina so ki yi hakuri na san hakan ba zaimiki dadi ba.
FARIDA
Fuskarta ta sauya nan take cikin alamun karuwar tashinhankali, hawaye na kwaranya daga idanunta.
RUKAIYYA Ahmad, na san idan namiji ya sa ransa zai yi aure sai ya yi. Ba zaniya hana ka aure ba, amma baRukaiyya ba.
43 EXT. A KOFAR WANI GIDA MARAICE. 43
Gida ne karami matsakaici, yanayinsa ya saba da na al’adarHausa. Wata mace mai girman shekaru na kofar gidan tana tuyarkosai da, dankali ayaba da sauransu.
44 INT. FALO 44
Farida tare da BABA KUDU ta, da kuma wata mace mai girmannshekaru, da wasu mata mabambanta shekaru kamar uku. Gefe gudajakarta ce dauke da kayayyakinta ciki Suraiyya na gefentazaune hawaye na zuba daga idanunta.
BABA KUDU Ai dama can mun fada miki, amma kika nace sai kin aure shi. Idan dai auren bahaushe wani abin kirki ne, to ga shi nan dai kin gani.
FARIDA
Cikin wata karin damuwa. Ba maganar bahaushe ce ba..
INNA
Ta katse ta cikin gwasalewaHmm, rufa mana baki karyar banza.Wa yake haka idan ba bahaushe ba.Da a cikin yarenmu ki ka yi aurehaka ta faru?
Ta dubi wata mai matsakaicin shekaru.
Ke Molaji ke ce a ke rigima dakekema sai kin auri bahaushe.
(MORE)
19.
INNA (CONT'D)
To kin ga dai abinda ya faru a kan
‘yar uwarki, idan ba ki ji maganar
manya ba saura ke.
MOLAJI
Molaji [25]ta yamutsa fuska cikin rashin jin dadi.
BABA KUDU
Ni yanzu ban  ma san abinda zan
fadawa babanki ba.
45 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 45
Ahmad rike da waya a hannunsa ya kai gwauro yakai mari yanasauraro ba a amsa ba.
46 INT. GIDAN BABA KUDU FARIDA DARE 46
Farida cikin wani daki kwance bisa gado suraiyya na gefenta.Wayarta na ajiye tana rurin kuka amma ta ki kula ta har ta gama.
47 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 47
Yana ci gaba da sintirinsa ya sake danna wayarta cikin kirakana ya kara a kunnensa cikin sauraro
48 INT. GIDAN BABA KUDU FARIDA DARE 48
Wayar ta sake rurin kuka, sunnan Ahamad bisa screen ya fito.Ba tare da ta duba ba ta sa hannu ta dauko wayar ta kasheta.
49 EXT. KOFAR GIDAN BABA KUDU FARIDA MARAICE 49
Ahmad na zaune cikin mota a kagauce yana duba agogon hannunsalokaci lokaci, kana ya mayar da hankalinsa ga kofar gidan.
50 INT. GIDAN BABA KUDU FARIDA MARAICE 50
Farida daga cikin gida daga taga bayan labule na lekensa, fuskarta dauke da damuwa. Dubanta na kai kawowa tsakaninsa da matan gidansu dake zaune wata nahiya suna shewa. Lokacilokaci ta kan kai hannunta fuskarta ta na sharar hawayen.Hawaye ya sake tunkudowa lokacin da ta ga ya ja motarsa gabarin kofar gidan cikin damuwa.
20.
51 EXT. FILIN TSAKAR GIDA A KAUYE MARAICE 51
Guda da sautin dukan turmi cikin lugude ya kaure gidan. Matana ta kai da kawowo cikin sha’anin Biki.
52 INT. DAKIN GOGGO.MARAICE 52
Rukaiyya da Ahmad na gurfane a gaban Goggo, sautin guda dalugude na ratsowa cikin dakin a hankali.
GOGGO Kin ga dai Amadu dan uwanki ne, idan ma babu aure kina da hakkin kulawa a kansa yana da shi gareki.Don Allah ku zauna lafiya. Ku bani damar komawa ga ubangijina cikin gamsuwa. Allah ya yi muku albarkatun da dai har ku ka cika min burina.
RUKAIYYA
Cikin kankan da kai da girmamawa.Ba komai Goggo, idan Allah ya yardaba abinda zai faru. Na yi hakuri dacan a gidan wani ma ballatana wandaya zame min dole na.
Ta dubi Ahmad cikin murmushi.
GOGGO
Hankalinta ya juya zuwa ga AhmadIdan ka koma lalle ne ka je kadauko yarinyar nan. Don ba zai yiwuta tashi a gabansu cikin irinal’adunsu ba.
AHMAD Hakane, idan Allah ya so zan je nadauko ta da zarar mun isa gida.
53 INT. BABA KUDU’S HOUSE (PREMISES) - MORNING 53
AHMAD
Na jingine da garun kofar gidan cikin halin jira.
21.
BABA KUDU
Ya fito ya dubi wanda ke sallama dashi.A aha, Ahmad. Kai ne dama ke sallama?
AHMAD I ni ne Alhaji.
Ya durkusa suka gaisa.
BABA KUDU Lafiya dai haka da sassafe?
AHMAD Dama na zo ne akan maganar Farida.
BABA KUDU Ai ta tafi aiki.
AHMAD I na sani, dama kai na zo ganiAlhaji. Ina so don Allah ka sa bakia maganar nan, ko Farida ta hakurata koma dakinta.
BABA KUDU
Jinjina maganar cikin shakka.Babbar magana. To, ka san halinyaran zamani, ban san yaya zan yida ita ba, ko a lokacin ma da ta kafe sai ta aure ka ba ta jimaganar mu balle yanzu da ta kafeba zata zauna ba. Ina ganin dai ita din ya dace kasamu ku daidaita.
AHMAD
Ya dubeshi cikin mamaki. Ina rokon alfarma ne, a taimaka a shiga maganar nan. Don sam takiyarda ta ko ganni ballentana mu yi maganar....
BABA KUDU
Ya duba agogo.Bana jin akwai abin da zan iya yi.Ita din ya kamata ka samu.
Ya juya zai koma ciki.
22.
Ka yi hakuri zan je wata unguwa ne na dan makara.
AHMAD Alhaji don Allah a taimaka...
Ya tafi ya bar shi nan a kofar gida cikin tunani.
54 EXT. BABA KUDU’S HOUSE - MORNING 54
MOLAJI
Na wanke kwanuka a daidai rariya.
BABA KUDU
Ya shigo cikin gidan.
INNA Waye ne haka da safe ke sallama?
BABA KUDU Alhaji Ahmad ne don rashin hankaliya zo wai na sa baki a maganarFarida. Da can bai tunanin mu ba sai da yanzu ta hado su.
MOLAJI
Ta dan saci kallon su, sannan ta yi sauri ta kawar da kai tawayance da aikin tana saurare.
INNA Ooh oh! In ban da kaddara ma me zai kaita wannan gidan, Yaron da baisan mutuncin kowa ba.
BABA KUDU
Ya nufi cikin daki. Ai an gama, Farida ba zata komagidansa ba, in ban da taurin kan tama na tsiya duk a dangi ta rasawanda zata aura sai kwashe kwashe. ki dai kara ja mata kunne, babuabin da zai mayar da ita wannangidan.
55 EXT. FARIDA’S CHAMBER PREMISES - EVENING 55 FARIDA
23.
Tana tsaye a wajen ajiye littafai tana duddubawa har ta zokan littafin da take so ta mika hannu ta zaro shi. Ta zagayagaban kujerar ta soma tattara sauran littafan ta dauki kwatdinta da hular lauyoyinta a daidai lokacin da ta ji ana kwankwasa kofa.
Yes wane ne?
AHMAD
Ya yi sallama yayin da ya shigo.
Suka dubi juna dan lokaci sannan ya mayar da kofar ya rufe.Farida me na yi miki ne kike yi minirin wannan wulakanci, a ce ko wayata ki kasa dauka, na je gidan ku kin ki yarda ki ganni. To ganina zo tun da haka ne mu yi ta takare.
FARIDA
Me kuma zamu yi ta kare? Ai tuntunimun yi ta ta kare.
Ta rungumi littafan a kirjinta yayin da take kokarin sabekwat din.
Na gaya maka ba zan koma gidankaba, ko dole ne. Ko da can da na aure ka ai ra’ayi na yi ba dole aka yi min ba. Zan maimaita maka Ahmad, bana yi, ka je ka zauna daRukaiyya.
AHMAD
Farida.
FARIDA
Na fa rufe shafinka tun tuni, saboda baka don Allah ka san na yitun dare bai yi maka ba.
AHMAD Shi kenan na ji. Game da zama nidake na hakure wa zuciyata, ina so na shaida miki na sawwake miki, saboda haka ina jiran ki dawo minda duk abubuwan da kika san mallakina ne.
FARIDA
24.
Jan numfashi. Igiyar aure hakkinka ce, kana daiko ka saki ko ka rike, maganar namaido maka da abubuwan da suka kasance mallakinka ne na kasa fahimta.
AHMAD Suraiyya nake nufi, ko ba hakkinaba ce?
FARIDA
Ta kura masa ido dan lokaci cikin kallo na natsuwa. Idan da zaka dauki shawara ta sai na ce kada ka kuntata zuciyar ka gabukatar da ba zaka taba samu ba.
AHMAD Suraiyyan ce ba zan samu ba ko kuwame?
Ya yi dariyar mamaki.Kin manta ne? ‘ya ta ce fa.
FARIDA Kwarai kuwa na san haka. Kana zaton akwai hukumar da zata iya karbarmaka ita daga gareni ne?
AHMAD
Ya dube ta dan lokaci cikin nazari. Bana bukatar hukuma don zan karbi Suraiyya. Kin sani na sani baki dawadataccen lokacin kula da ita saboda yanayin aikin ki. Rukaiyya zan kaiwa ta lura da ita.
FARIDA
Da can da babu Rukaiyyan waye kekula da ita. Malam bari na gayamaka, ko me zaka yi wallahi ba zanbaka ita ba.
AHMAD A a fa, bana son ki fara abin da ba zai haifar da da maras ido ba.
FARIDA Kana da ja kenan? Zaka iyajarrabawa.
25.
Ta duba agogon hannunta, yayin da ta baro tebirin nata tanufo kofa rike da makulli.
Zan fita idan iya maganar dake tafeda kai kenan.
56 INT. BABA KUDU’S HOUSE - EVENING 56 FARIDA Ta shiga dakin ta ajiye littafan a kan dan tebiri kana tajefa kwat din ta kan gado. SURAIYYA Ta shigo a guje ta rungume Farida. Sannu da zuwa Mama. FARIDA Yawwa Suraiyya, yaya makaranta, ana yin karatun dai ko? SURAIYYA I, an bamu ma homework. MOLAJI Ta shigo cikin dakin a hankali tana waiwaye don ta tabbatarbabu wanda ya ga shigowarta dakin. Farida. FARIDA Ta waiwaya ta dube ta. Molaji, yaya aka yi? MOLAJI Dazu bayan kin tafi wajen aikiAhmad ya zo. FARIDA Ta dan yi shiru sannan ta dubi Suraiyya. Je ki wajen Inna ina zuwa. Bayan Suraiyya ta tafi sai ta dubi Molaji. (MORE)
26.
FARIDA (CONT'D)
Ya je ofis ma ya same ni. Me ya
faru?
MOLAJI
Don Allah ni dai zan rokeki Farida,
ki rufawa kan ki asiri ki koma
dakin mijinki.
FARIDA
Na kallonta ba tare da ta ce komai ba.
MOLAJI
Wai kin manta halin gidan nan ne,
daurin gindin da Alhaji da Inna
suke baki akan kar ki koma dakin
mijinki don fa bukatar kansu ne ba
wai don soyayyar su gareki ba. In
da yau a ce suna amfanar Ahmad
wallahi ba za su hana ki ki koma
ba.
FARIDA
Ta ja numfashi gami da lumshe ido. can ta dube ta.
Molaji na fahimce ki, ammawulakancin da mutumin nan ya yi minna rasa yadda zan yi na manta.
MOLAJI Ai ba akan ki aka fara kishiya ba.
FARIDA
To amma ya rasa wadda zai aura sai
Rukaiyya?
MOLAJI
Farida kishiya duka kishiya ce. Me
Ahmad ya rage ki. Yana son ki, yana
son Suraiyya kamar yadda kike son
ta, idan babu me jin tausayinki me
zai hana ki ji tausayin kanki. Idan
ma ke ba kya tausayin kanki to don
Allah ki tausayawa Suraiyya.
Ta juya ta fita daga dakin ta bar Farida cikin tunani.
57 INT. DAKIN FARIDA - NIGHT 57
FARIDA
27.
Na zaune a gefen gado tana duba littafan shari’a, amma tunanida zulumi ya hana ta maida hankali ga karatun.
SURAIYYA
Kwance a gado rabin jikinta a lullube tana bacci.
FARIDA
Ta kura mata ido cikin tunani, sautin maganar Ahmad na ya sauwake mata na bijiro mata. Sannu a hankali hawaye nakwaranya daga idanunta.
58 INT. FALON GIDAN BABA KUDU - MORNING 58
FARIDA/SURAIYYA
Suna karin kumallo.
FARIDA
Ta dauki wayarta ta buga wata lamba ta kai kunne. Jim kadan
aka amsa. A’isha ina kwana, ina gajiya, yayaweekend. Don Allah yau kina gida ne ko zaki je wata unguwa?To don Allah zan zo in an jima dahantsi. A’a babu komai wata ‘yarmagana ce. To sai na zo. Na gode.
Ta katse wayar.
SURAIYYA Mama, wace ce?
FARIDA Anti A’isha ce ta wajen aikin mu. Yi maza ki gama karya kumallon nayi miki wanka.
Ta mike ta nufi cikin daki.
59 INT. FARIDA’S CHAMBER PREMISES - DAY 59
(Flash back) Lokacin da A’isha ke bata shawara a kan auren daAhmad zai yi.
60 INT. AHMAD’S HOUSE - EVENING 60
RUKAIYYA
28.
Ta tsiyaya ruwa ko lemo a kofi ta mikawa Ahmad yayin da takoma ta jingina da kujerar tana duban sa.
Yaya aka kare?
AHMAD Wai Farida ce zata rike Suraiyya.
Ya kurbi ruwan, sannan ya dubi Rukaiyya dan lokaci sannan ya
kawar da kai. Amma gaskiya ni ban gamsu ba.Suraiyya ‘ya ta ce babu wanda ya isa ya raba ni da ita ina da hakkia kanta kamar yadda take da’awarhakki akanta. Babu makawa sai na karbo ta ko da tsiya tsiya ne.
RUKAIYYA
Ta matso gaba ta zauna a kujerar a hankali tana fuskantar sa.
Bai kamata a yi haka ba. Ina rokonda ka bar ni na je mu gana daFarida ni da ita.
AHMAD Zaki bata lokacin ki ne a banza. Farida ba zata saurare ki ba.
RUKAIYYA Ni dai ka bani dama abin da kawai na roka kenan.
61 EXT. GIDAN BABA KUDU - EVENING 61 RUKAIYYA Ta shiga harabar gidan. Salamu alaikum. INNA Daga cikin kicin Off scene. Amin wa’alaiku salamu, wane ne? SURAIYYA
29.
Na wasa a can karshen katangar gidan ta waiwayo ta gaRukaiyya. Cikin farin ciki ta taso ta runtumo a guje zuwa gareta.
Anti oyoyo sannu da zuwa Anti.
Ta zo ta rungumeta.
Anti kin zo ki kai ni wajen Abba nane?
RUKAIYYA
Ta rike hannun Suraiyya tana dariya, ta dubi Inna lokacin data shigo cikin falon, kana ta durkusa ta gaishe ta cikin girmamawa.
SURAIYYA
Inna anti Rukaiyya ce fa, ba ki san
ta ba?
INNA Af! Ke ce amaryar Ahmad?
RUKAIYYA
Cikin murmushi kan ta kasa sunkuye.E, nice. Na zo ganin Yaya Farida ne.
INNA
Ai tana ciki, Suraiyya kai ta
dakinta mana.
62 EXT. KOFAR GIDAN BURUKU MARAICE 62
Ahmad na zaune cikin mota yana jiran fitowar Rukaiyya.
63 INT. CIKIN GIDAN BURUKU MARAICE 63
Inna ta leko ta kafar kofar gida ta hangi Ahmad zaune cikin mota ya na sauraro. A hankali ta koma cikin gida ta nazunburar baki nuna alamar halin ko oho.
Naci, naci dambun kuturu, wannan da shegen nacin tsiya yake.


30.
31.

Text Box: 64  INT. GIDAN BURUKU DAKIN FARIDA MARAICE  64 
 RUKAIYYA To idan kuwa hakane sai ki bani Suraiyya na tafi da ita.  
 FARIDA  
 Ta zumburi baki,  
 Wata dabam ke nan in ji ‘yan caca.  
 RUKAIYYA Ba wani maganar wata dabam Yaya Farida. Ai Suraiyya Yaya Ahmad ce, jini da tsoka, idan dai har ba kison shi to mai za ki yi da ita?  
 FARIDA (Cikin hasala)Kin ga malama, wallahi daurewazuciyata na yi har nake maganadake. Amma ji nake kamar na tashina yi miki tsinannen duka.  
 RUKAIYYA (murmushi)Ai zan iya hakuri da dukanki tundadukan girma ne, amma idan ba hakaba ki dubi zatina ki gani zan dakua wajenki?  
 FARIDA  
 Cikin karin hasala ta fara daga murya.  
 To tashi ki fice mana daga gida. Nabar gidan naku ma dai ba za a kyaleni ba sai an biyoni ana cusa minbakin ciki?  
65  EXT. AHMAD LAWYER’S HOUSE - DAY  65 
 LAUYAN AHMAD  
 Suka nufi inda Ahmad ya ajiye motarsa.  
 Ita ke da hakkin kula da ita, amma a irin case din ku kana da hurumin karbar yarinyar a kotu.
AHMAD Yauwa Barista ni ai abin da kawai nake so na ji kenan. Don a gaskiyaba zan iya bar mata ‘ya ta ba....
Wayar sa ta buga. Ya fiddo ta ya kai kunne.
Hello Sweetie, yaya aka yi?No, babu damuwa amma dai matsalar kawai ita ce bana kusa da gida, idan zaki iya bani kamar mintitalatin zan iso. Yaya kawar takiina fata dai lafiya kika same ta?To to, ina amsawa, sai na zo.
Ya kashe wayar ya dubi Barista.
To Barista na gode, bari na koma.Sai ka ji daga gare ni.
LAUYAN AHMAD Babu damuwa sai mun hadu.
Ahmad ya shiga mota suka dagawa juna hannu ya tuka ya tafi.
66 EXT. ON THE ROAD - AFTERNOON 66 FARIDA Na tafe a kan titi tana tuki, yayin da shiga wata kwana.
67 EXT. A’ISHA’S HOUSE PREMISES - AFTERNOON 67 AHMAD Ya iso a mota yayin da yake kokarin tsayar da motar, yanamagana a wayar dake kunnensa. Ki fito mu tafi, na iso.
68 EXT. A’ISHA’S HOUSE PREMISES - AFTERNOON 68 A’ISHA/RUKAIYYA Suna fitowa daga cikin gidan suna magana cikin raha. Sun nufoinda Ahmad yayi fakin. FARIDA Hancin motarta ya bullo kan layin, ta nufo gidan su A’isha.
32.
AHMAD
Ya bude kofar motarsa ya fito suna gaisawa da A’isha.
RUKAIYYA
Na bude kofar motar.
FARIDA
Ta hangesu, ganin A’isha tare da Ahmad da Rukaiyya ya tayarda hankalinta. nan da nan ta taka birki ta tsaya. Ta kuramusu ido dan lokaci cikin kaduwa. Ba shiri ta yi sauri ta sa ribas ta yi baya ta bar layin ba tare da sun ganta ba.
69 INT. GIDAN BURUKU FARIDA’S ROOM - AFTERNOON 69
FARIDA
A zaune cikin tagumi idanunta sun yi ja, hawaye na kwaranya a kuncinta.
MOLAJI
Zaune a gefen gado tana kallon Farida.
FARIDA A ce aminiyata, makusaciyata tamunafunce ni. Ashe kabilancin Hausawa da ake fada gaskiya ne.
MOLAJI Wai me ya faru ne haka? Ki gayamin.
FARIDA Ashe duk wannan abin da ake yiA’isha ta san Rukaiyya, shi ne tanuna kamar bata santa ba. Dagagidan nake yanzu, na ga sun fitotare, Ahmad na waje yana jira.
MOLAJI To mene ne don A’isha ta san Rukaiyya.
FARIDA Ah! Mene ne ma zaki ce? Lallai yarinyar nan baki da hankali.
(MORE)
33.
FARIDA (CONT'D)
Matar nan fa ita ta yi ta tausa ta
na hakura, ashe bakin su daya da
Rukaiyya saboda ‘yar uwarta ce
bahaushiya. To wallahi ba zata yiwu
ba, ba zan taba komawa gidan Ahmad
ba, ko me za a yi.
70 INT. FARIDA’S OFFICE - DAY 70
A’ISHA/FARIDA
Suna zaune kusa da kusa suna nazarin wasu takardu.
FARIDA
Lokaci lokaci ta kan dubi A’isha fuskarta a hade gami dakwafa.
A’ISHA
Ta dubi Farida. Farida! Na yi miki ba daidai bane, naga alama kamar kina fushi dani, don ko gaisuwata ba ki amsa ba tun isowarki office. Ina son na tambayeki ko jiya lafiya? kin ce zaki zo amma shiru na jira ban gan kiba.
FARIDA
Ta yi tsaki kana ta mike tsaye cikin shirin barin wurin.
Ki je can ki karata da munafuncintsiyarku.
Ta bar A’isha nan cikin mamakin ko me ya faru.
A’ISHA
Jim kadan cikin tunani gami da juyayi, can alamar farga tabaiyana a fuskarta, nan da nan ta dauki wayarta ta lalubowayar Rukaiyya.
Rukaiyya ko kin san wata abokiyaraikina mai suna Farida, E, Farida G. Ahmad.
Tana sauraron wayar Rukaiyya can za mu inda ta dan bude bakicikin mamaki abinda da ta jiyowa kunnenta.
(MORE)
34.
A’ISHA (CONT'D)
Nagode Rukky, sauran magana sai mun
hadu zancen ba na waya bane.
71 INT. RESTAURANT - DAY 71
A’ISHA/FARIDA
Suna cin abinci suna tattaunawa.
FARIDA
Ta kurbi lemo cikin wani kofin tangaranA whole learned sister kamarki ace har yanzu kina dauke da akidarjahiliyya, kabilanci, wallahi kin bani kunya A’isha. Don me za kimunafunce ni idan kin san Rukaiyya? Saboda ni ba bahaushiya bace ko?
A’ISHA
Ta dubi Rukaiyya ba tare da tace mata komai ba ta ci gaba da
cin abincinta. Idan nace miki ban san Rukaiyya itace amaryar mijinki ba, ba za kiyarda ba. Rukyy classmate dina ce.Tare muka gama sakandire da ita, ajinmu daya. Rabona da ita tun damuka gama service, yau shekarabiyar kenan. Saduwa tsakaninmu saidai ta waya kadai sai fa dawowartagarin nan.
FARIDA
Da alamar dukkan maganar da A’isha ke yi bai shige ta ba. Tadauke fuskarta ga barin kallonta kamar ma dai ba ta son maganar.
A’ISHA
Ta lura cewa maganarta ba ta gamsar da Farida ba
Ba wai gamsuwarki nake nema ba. Ina dai fada maki zahirin abinda na sani ne. Idan dai har na ci amanarki kamar yadda kike zato, to Allah shine masani, amma yau dagobe, lokaci zai baiyanar dagaskiyar zancena. Ina sa zuciyarkarbar afuwar da za ki zo nema a wajena yayinda kika gane gaskiya.
35.
Mai aikin restaurant ta zo da bill dinsu, A’isha ta karbe ta duba adadin kudin kana ta zuge jakarta ta biya gaba daya.Gama biyanta ta mike ta bar Farida a wurin.
FARIDA
Ta bi ta da kallo har zuwa ficewarta daga cikin dakin cin abincin.
72 INT. HOSPITAL - DAY 72 DOCTOR ADAM Yana gwada Suraiyya da kayan gwajin likitoci. Ya sa a
kirjinta yana saurare a kunnensa. Ya soma rubutu a kan katin. FARIDA Zaune a kujerar dake fuskantarsa tana rike da Suraiyya. Tana bin abin da yake yi da kallo cikin kyautata fata. SURAIYYA A zaune a cinyar Farida yayin da ake dubata. DOCTOR ADAM Kuna bari tana shan ruwan sanyi ne da dangoginsa irinsu kankara daaskirin? FARIDA Ta girgiza kai. DOCTOR ADAM Akan dauke ta a babur ne? FARIDA Ba a daukanta a babur.
DOCTOR ADAM Sai ku yi hattara don kuwa nimoniyata yi karfi a jikinta. A halinyanzu tana bukatar kulawa sosai. FARIDA Ta girgiza kai cikin damuwa.
36.
73 EXT. GINDIN BISHIYA BAKIN MAKARANTA. RANA 73
Ahmad na gindin wata bishiya cikin mota yana jiran tashi dagamakaranta.
74 EXT. KOFAR MAKARANTA. RANA 74
Maigadi ya bude kofar yara na fitowa , wasu na fadawa cikin motocin da suka zo daukarsu. Suraiyya ta fito na dube-dube.
75 EXT. GINDIN BISHIYA 75
Hayaniyar yara lokacin da suke fitowa ne ya ankarar da shi.Ya fito daga cikin motar ya nufi kofar makarantar. Can ya hangota tsaye goye da jakar makarantarta a baya tana dubedube. Ya daga hannu yana kadawa domin ya karkato hankalintagare shi amma ba ta kula ba har sai da ya daga murya ya kira sunanta.
SURAIYYA
Ta hango shi, kana ta nufo inda yake a guje cikin murna dadoki, bata wata wata ba ta fada cikin motar tana dariya.
76 EXT. TITI RANA 76
Farida cikin mota ta nufo makarantar su suraiyya. Ta taras an tashi ragowar yaran da suka rage ‘yan kadan ne. Ta ci gaba dadubawa ko za ta ganta amma ta ba ganta ba kana ta ci gaba datambayar yara har ta nufi mai gadi.
MAIGADI (bayan gaisuwa)Makara ki ka yi ne,
FARIDA
Wallahi kuwa, ga shi kuma ban ganta
ba.
MAIGADI Ai an zo an dauke ta.
FARIDA
Alamar fargaba tana mai dafa hanunta bisa kirji.
MAIGADI
Ai dama shi yake zuwa daukarta idan
ba ki samu damar zuwa ba.
(MORE)
37.
MAIGADI (CONT'D) Yau kuwa tun da wuri yazo. A can wajen bishiyar can ya tsaya lokacinda ya zo ya taras ba su ta shi ba.
FARIDA
Alamar dan sassauci ga zuciyarta kana ta juya tana maikomawa. To na gode maigadi.
77 EXT. KOFAR GIDAN AHMAD RANA 77
Ya iso gida yana kokarin parking din motarsa lokacin da ya jibugun karar waya ya dube ta kana ya kai ta ga kunnensa ya namai amsawa.
AHMAD Hallo
Yaci gaba da sauraen
78 EXT. TITI RANA 78
FARIDA
Cikin mota tana tafiyaMenene dalilin zuwanka ka dauki Suraiyya ba tare da ka sanar da niba.
79 EXT. KOFAR GIDAN AHMAD RANA 79
AHMAD Ya ta ce, ni ma ina da hakki a kanta. Ina da damar daukarta kamar yadda kike zaton kina da ita. Hakanan tana da damar zama a gidanakamar yadda kike da’awar zamantawurinki.
Ya kashe wayar ya ajiye ta gefe guda
80 EXT. TITI RANA 80
Farida ta dubi wayar rike a hanunta kana ta jefar da ita kujerar gefenta , cikin fushi ta juya kan motarta.
38.
81 INT. GIDAN AHMAD FALO RANA 81
SURAIYYA Suraiyya na zaune cikin annushuwa tana wasan video game
RUKAIYYA Tana kai kawowar shirya abinci bisa teburi
82 EXT. KOFAR GIDAN AHMAD RANA 82 FARIDA Ta iso gida cikin hamzari ta tsayar da motar. Ta fito a gaggauce ta shige cikin gidan TALATU Tana wanke-wanke, ta dube ta cikin kokarin yi mata sallamaamma yanayin da ta gani ya sarar da ita, ta bita da kallocikin mamaki da aljabi. AHMAD Ya fito daga cikin wani daki zuwa cikin falo, inda suka yikicibis da Farida. FARIDA Ta dube shi fuskarta a murtuke kana ta mai da kallo zuwa gaSuraiyya ta daka mata tsawa, Tashi mu tafi, Ta nufi inda take. AHMAD Ya sha gabanta ya tare ta.
SURAIYYA Ta tashi a guje ta shige cikin wani daki ta kulle RUKAIYYA
Tana teburin abinci tana kallonsu babu alamar jin dadinabinda ke faruwa.
39.
AHMAD
Kowanne da na da hakkin zama gidan
ubansa idan ya so haka. Nan gidan
ubanta ne, tana da hakkin ta zabi
zama nan kamar yadda ki ka zabi
zaman naku gidan.
83 EXT. GIDAN AHMAD TSAKAR GIDA RANA 83
TALATU
Tana shanya kayan da ta wanke bisa wata igiya a tsakar gida.
84 EXT. KOFAR GIDAN AHMAD RANA 84
Motar ‘yansanda Farida na yi musu jagora sun iso kofar gidan suka tsaya kana suka fito.
85 INT. GIDAN AHMAD FALO RANA 85
Ahmad, Suraiyya da Rukaiyya na zaune bisa teburin abinci sunacin abincin rana, cikin raha da annashuwa. Suraiyya na dagagefen Rukaiyya tana yi mata wasa kana ta debi abinci ta karamata, Ahmad na binsu da kallo cikin murmushi. Sautin kararrawar gidan da a ka danna ta sanya shi waiwayawa, sannanya tashi a hankali ya nufi kofar ya bude suka yi ido hudu dayansanda Farida na gefe guda abinda ya sanya fuskarsa sauyawanan da nan.
86 EXT. GIDAN AHMAD TSAKAR GIDA RANA 86
Talatu na bin su da kallo ‘yansanda sun tisa shi gaba hardai zuwa shigar motarsu tare da shi, kana ta nufi cikin gidan da sauri.
87 INT. GIDAN AHMAD FALO RANA 87
Rukaiyya na kokarin tattare kwanukan abincin da suka ci tanagyara teburi yayinda da Suraiyya ta komawarta wajen vediogame din ta.
TALATU
Ta shigo gidan kamar a gigice tana mai kiran Rukaiyya
Amarya! Amarya!!
40.
RUKAIYYA
Ta dubi Talatu, ganin tashin hankalinta ta tambayeta
Talatu, me ya faru? Lafiya!
TALATU Yansanda ne, yansanda sun tafi daBaban Suraiyya.
RUKAIYYA
Fuskarta ta sauya ya zuwa yanayin damuwa,
Yansanda?
TALATU E, yansanda fa. Sune su ka zo tare da Maman Suraiyya.
RUKAIYYA
Wayar Rukaiyya ta buga nan da nan cikin hamzari ta kai hannugareta tana mai amsawa. Ta ci gaba da sauraron wayar tana maigyada kayinta cikin amincewa.
88 EXT. TITI RANA 88
Ahmad tare da ‘yansanda cikin mota yana rufe wayarsa alamarya kammala magana ke nan.
89 INT. GIDAN BURUKU FALO MARAICE 89
MOLAJI Amma a gaskiya Farida ba ki kyautaba. Ko ba komai ai uban ‘yarki ne. Yaya kike gani nan gaba zai iyaganinki da mutunci?
FARIDA Wacce kima ko mutumci kuma nake nema a wurinsa, Molaji. Mutumin daya sake ni ya wulakanta ni. Ya mance da alfarmar soyayyar da nakemasa ya tagaiyara ni. A yau na zamemasa bora ya wofintar da ni. Wannemutumci zan yi gare shi?
41.
MOLAJI
Farida, ina ilminki yake ne? Amfani
ilmi aiki da shi. Sam a ayau
ilminki bai miki amfani ba.
FARIDA
Ta dube ta kamar a wulakance.
Ki bari sai kin yi aure kin farasamun naki ‘yayan kafin ki ce za kimin nasiha bisa zamantakewar da ni na san ta baki da fari.
90 INT. OFISHIN ‘YANSANDA MARAICE 90
Ahmad tare da lauyansa suna tattaunawa da ‘yan sanda, sun karbi wasu takardu suna cikewa kana lauya ya sanya hannubisansu.
91 EXT. GIDAN AHMAD TSAKAR GIDA RANA 91
Suraiyya na rike da igiya tana wasan skipping lokacin daAhmad tare da lauyansu su ka shigo cikin mota. Suraiya ta yarda igiyar da take wasa ta ruga a guje gare shi tana mai rungume shi.
92 EXT. HARABAR KOTU RANA 92
Kai da kawowar mutane suna shige da fice cikin kotun. Farida sanye da kayan lauyoyi ta fito yayinda lauyan Ahmad tare daAhmad ke fitowa bayanta.
93 INT. DAKIN KARATU MARAICE 93
Farida na binciken wasu manyan littafan shari’ah, tare da ita akwai takardu da take rubuta dukkan abinda take bukatar daukarsa.
94 EXT. KOFAR GIDAN BURUKU MARAICE 94
Ahmad tare da lauyansa suna tattaunawa da Molaji.
42.
95 INT. KOTU SAFE 95
FARIDA
Ya mai shari’ah ina rokon wannan
kotu mai alfarma ta gamsu da
dalilai na cewa nice mafi hakkin
kulawa da Suraiyya fiye da babanta.
Ina fata kotu za ta sallama min
ita, sannan ta yi masa iyaka ga
barin sake daukarta ba tare da
iznina ba.
Ta yi risinawar kotu kana ta nemi wurin zama ta zauna.
ALKALI
Ya dube ta kana ya ci gaba da rubutu cikin wani littafin dakegabansa sannan ya dubi lauyan wanda a ke kara.
LAUYA
Ya mike tsaye tare da girmamawar kotu.
Ya mai shari’ah, babu jayayya bisahakkin da mai kara ke da’awa na riko da renon wacce ake kara a kanta. Kafin na ci gaba ina nemaniznin kotu don na bijiro mata dawani abin lura don shaidawarta.
ALKALI
Ya dube shi tare da gyada kansa alamar amincewa.
LAUYA
Ya kamo hannun Suraiyya ya tsayar da ita a tsakiyar kotu kana ya koma wajen tsaiwarsa.
Suraiyya!
SURAIYYA
Ta waiwaya ta dube shi.
LAUYA
Ya nuna mata Farida
Waccen ummanki ce, ga kuma abbankia can. Idan kina son komawa gidan Ummanki je ki wurinta ku tafi.
43.
SURAIYYA
Ta dubi Farida kana ta komar da ganinta zuwa ga abbanta. Tatsaya nan tsakiyar kotu ba tare da ta daga ko ina ba.
LAUYA
To idan kina son komawa gidan
Abbanki tafi wajensa.
SURAIYYA
Ta sake duban Farida kana ta kada kanta ta nufi wajen Ahmad.
FARIDA
Ta dube ta cikin takaici hawaye na zuba daga idanunta ta sadda kan ta kasa.
LAUYA
Ya mai shari’a, ina son kotu ta
fahimta cewa zaman Suraiyya wajen
mahaifinta ba zabinsa ne kadai ba,
zabinta ne. Hakkin reno da kulawa
hakki ne dake yawo tsakanin iyaye,
amma mafi girman hakki cikinsu
shine abin renon. Inda maslahar
rayuwar abin reno ta rinjaya nan
hakkin hadhana ke karkatuwa. Ya mai
shari’ah kasancewar Suraiyya ta kai
shekarun tamyizi, ta na da hakkin
zabin wajen zamanta domin itace
mafi sanin inda ya fiye mata
maslaha. Ta zabi zama wajen
babanta, ina roko wannan kotu mai
alfarma da ta yi watsi da wannan
kara, ta tabbartarwa Suraiyya
hakkin zabinta na ta zauna a hannun
mahaifinta ka da sabanin dake
tsakanin iyayenta ya zamana ya
cutar da ita. 
ALKALI
Alkali ya dube shi kana ya ci gaba da rubutu bayan ya
kammala, Kotu ta daga wannan kara zuwa nan da sati biyu domin ci gaba dasauraron wannan shari’ah
ya daga gudumarsa ya buga ta alamar kotu ta tashi.
44.
96 INT. SUPER MART. MARAICE 96
Ahmad, Rukaiyya da Suraiyya cikin wani babban kanti sunasayayya. suraiyya ta nuna wani ice cream an miko mata
97 INT. ZAUREN MALAMI MARAICE 97
Farida tare da wani malami cikin zaurensa. Manyan littafai nagefensa zube yayinda wani na bude gabansa suna tattaunawa, ita kuma na rubutawa cikin wani dan karamin littafi da take dauke da shi.
98 INT. ASIBITI SAFIYA 98
Likitoci na tsaye kan Suraiyya tana kwance bisa wani gado, numfashinta sama sama kamar zai fita.
AHMAD
Ahmad na waje cikin tashin hankali yana kai kawowa da waya a hannunsa yana ta kokarin kira.
99 EXT. KOFAR GIDAN BURUKU SAFIYA 99
Farida sanye da kayan lauyoyi rungume da wadansu littafai tafito daga gida ta nufi inda motarta ke ajiye. Wayarta ta bugata duba ta ga sunan Ahmad ne ta yi banza da ita har ta gama kukanta. Ta isa inda motar take ajiye lokacin da wayar tasake bugawa amma ba ta kula da ita ba.
100 EXT. HARABAR ASIBITI SAFIYA 100
Ahmad ya sauke wayar daga kunnensa da ya ji taki dauka. cikin damuwa nan da nan ya danna sako ya tura mata.
101 EXT. KOFAR GIDAN BURUKU SAFIYA 101
Ta bude motarta lokacin da sakon yake fadowa cikin wayarta.Ta buda shi don ganin ko menene. Nan da nan fuskarta ta canzaya zuwa alamun tashin hankali. Ta zubar da littafan da take rungume da su bayan motar, cikin gaggawa ta shiga ta fizgimotar a guje.
45.
102 INT. ASIBITI SAFIYA 102
Ahmad ya kasa zaune ya kasa tsaye yana sintiri ya kai gwauroya kai mari tsakanin dakin da suraiyya take yana lekawa, yayin da Rukaiyya na zaune gefe guda ita ma cikin halindamuwa.
FARIDA
Ta shigo asibitin a kidime cikin gaggawa da damuwa. Ta dubeshi yana mai saryar da kansa kasa ka barin dubanta.
Yaya jikin?
AHMAD
Ya nuna mata dakin da suke ciki hawaye na gangara da idanunsa
Suna ciki, Suraiyya sai abindaAllah ya yi.
FARIDA
Ganin damuwar da yake ciki da tashin hankali ita ma ta kasadaurewa ta fashe da kuka. A hankali Rukaiyya ta taso zuwagareta ta kama ta ta rungume tana lallashinta kana  a hankali ta jawo ta zuwa wurin zama ta zaunar da ita.
103 EXT. HARABAR ASIBITI SAFIYA 103
Talatu dauke da kayan abinci cikin flask na kokarin shigowacikin asibitin.
104 INT. ASIBITI SAFIYA 104
Likita ya fito daga cikin dakin da suraiyya take, nan da nan Ahmad ya riske shi. Cikin dokantar ya san halin da take cikiyana tambyarsa.
AHMAD Likita yaya jikin nata dai?
LIKITA
Ya dube shi tare da wani murmushi mai karfafa zuciya.
Kar ku damu ba bu komai za ta warware nan ba da jimawa ba. Kunaiya komawa gida ku dan sami hutuita ma yanzu tana barci.
46.
Likita ya tafi inda ya shige cikin wata kofa.
FARIDA
Ta dubi Ahmad Ka dauki Rukaiyya ku koma gida, nizan zauna a wajenta har ta farka.Kuna nan tun cikin dare ba ku sami runtsawa ba.
AHMAD A’a ku dai tafi ni ku bar ni a nan.
FARIDA To idan ka zauna a nan me za ka yimata. Zaman jiyya ai na mata ne. Ka je ku samu ku dan rintsa indai ba so kake a yi da kwance uwa kwanceba.
AHMAD
Ya dubi Rukaiyya ya yafito ta da hannuTashi mu tafi.
RUKAIYYA
Ta mike ta bishi sun nufi kofar fita.
FARIDA Honey.
AHMAD
Ya waiwayo zuwa gareta cikin kidima da mamakin kiran
FARIDA Ka sanyawa zuciyarka hakuri, idanAllah ya karbi Suraiyya kayansa ceme za mu iya yi?
105 EXT. CALL CENTER DAY 105
Molaji rike da waya a hannunta tana magana da yaren nufancihar zuwa wani lokaci.
106 EXT. HARABAR ASIBITI. SAFIYA 106
Ahmad, Rukaiya, Farida da sumaiyya babanta na rike da ita suna fitowa daga cikin asibiti. Sun iso inda motocin su keajiye.
47.
FARIDA
Ba tare da ta dubi su ba ta nufi inda motarta take ajiye.
RUKAIYYA
Ta kalle ta kana ta nufi wajenta, ta riske ta tana kokarin
shiga cikin motarta.Ina za ki? Yau ba ki kwana ko ina sai cikin dakinki.
FARIDA
Ta dubi Rukaiyya kana ta sunkuyar da kanta kasa.Rukaiyya zan kai kaina gidan mijine ba tare da ya zo ba. Ke fa mace ce, ki na ganin hakan mai yiwuwa ne.
RUKAIYYA
Ta dubi Ahmad shi ma ya tsira idanu yana kallonsu
AHMAD
Ya sanya Suraiyya cikin mota kana ya nufi inda suke.
RUKAIYYA Yaya don Allah ina neman arzikiwajenka, ka je wajen kawun Farida yau ka dawo da ita gida.
AHMAD
Ya dubi Rukaiyya kana ya dubi Farida ya girgiza kan sa.Gaskiya ba zan iya komawa ba. Ita ma kuma ta san dalilin. Babanta bai wulakanta ni ba, ba zai yiwu wani can da yake amfani da damar wakilcinta da a ka danka a hannunsa ya rinka wulakanta ni ba. Zan iyajure kome amma ban da wulakanci.Idan za ta dawo gida ta dawo inamaraba da ita, amma ba dai na sake gurfana gaban Buruku ba.
FARIDA
Ran ta a bace Yanzu nan kana nufin na dauki kai na na kai gidanka ke nan. Lalle, wallahi ba za ta sabu ba, ai ba dan gwal bane kai.
48.
RUKAIYYA
Ashe yanzu wannan halin da yarinyar
nan ta shiga bai isa ya tausasa
zuciyarku ba. Yakamata ku sani cewa
a matsayinku na iyaye ba ku da
wadatar bin ra’ayi ko bin soye
soyen ranku. Arzikin suraiyya dake
tsakaninku shi yakamata ya zama
alkiblar zuciyarku. Gareta za ku
karkata, ku kuma bijirewa dukkan
abinda zai kawar daku ga barin
fuskantarta. Yaya Farida, Suraiyya
na bukatarki, bai kamata ta dauki
farashin azabar sabanin dake wakana
tsakaninku ba.
FARIDA
Rukaiyya kece ki ka san hakan, ai
shi ko a jikinsa.
Ta shige cikin motarta, Mu hadu a kotu jibi.
107 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 107
Ahmad na zaune Laptop dinsa na gefe kan kujerar da yake zauneyayinda da Suraiyya ke kwance gefensa ta yi matashi dacinyarsa.
108 INT. GIDAN AHMAD KICIN DARE 108
Rukaiyya na kicin tana faman girkin abinci.
109 EXT. GIDAN AHMAD TSAKAR GIDA. DARE 109
Molaji Farida dauke da kayanta wasu kuma a hanun Molaji tare da Gimba [55] suna kokarin shiga ciki
110 INT. GIDAN AHMAD FALO DARE 110
Rukaiyya ta fito daga kicin lokacin da suke shigowa tare dasallama.
RUKAIYYA
Ta dube su tare da murmushi. Yaya Farida ce, sannunku da zuwa.
AHMAD
49.
Ya waiwayo cikin sauri, ganinsa ya sa ya mike tsaye cikin
girmamawa Alhaji barka da zuwa,
Ya nuna musu wurin zama
SURAIYYA
Ta iso wajen mahaifiyarta ta rike hannunta kana suka isokujerar zamansu gaba daya.
GIMBA
Ya zauna kana Ahmad ya zauna Molaji ku ta koma can gefe guda.
AHMAD
Ya sake yin gaisuwa bayan zamansa.
GIMBA
Ya dubi Ahmad. Na ji dukkan abinda ya farutsakaninka da Farida. Yanzu ke nan ba dan yarinyar nan Molaji ta yihankali ta sanar da ni ba haka za ku zauna lamura duka su lalace tsakaninku. Babu wani babba da zai iya tsawatar da ku ku kuma ba za kuiya yiwa kanku fada ba ko?
AHMAD
Ya sunkuyar da kai kasa cikin girmamawa.A gaskiya Alhaji na so yi makamagana amma kuma sai na kasa. Ina tuna wasicin da ka bar mana ne na cewa ka da mu neme ka cikin dukkan abinda ka iya tasowa tsakaninmu, gawakilinka nan. Ina tsoron ka da ka dauka cewa ban girmama umarninkaba.
GIMBA
Na ji duk abinda ya gudana
tsakaninka da Buruku. Ban ji dadi
ba, amma ka yi hakuri. Ni babu wani
abu tsakanina da kai sai godiya,
Allah yayi maka albarka. Ka rike
min ‘ya ta babu wulakanci, to ni
kuwa me zan ce da kai?
50.
Ya juya zuwa ga Farida.Ke kuma daga yau ba ni son sake jinwata fitina. Ban yarje miki sake fita daga cikin gidansa ba nan gaba.
Ya nuna suraiyya dake kwance jikin Ahmad
Idan ba ku yi hakurin zama ba don kanku ai kwa yi ko domin wannanyarinyar. Tana da hakki bisakowannenku, yakamata hakkinta ya taraku wuri guda. kamar yadda kikejin tana da bukatarki hakanan ma tana da bukatar kulawar mahaifinta kafin ta sami ingantacciyar rayuwa.A matsayinku na iyaye baku dayalwar bin zabin zuciyarku ba tare da la’akarin cikas din da hakan ka iya samarwa ga ‘yayanku ba. ‘Ya’yaamana ce ku sauke amanar da Allah ya dora muku ta hanyar yin hakurinzama da juna.
AHMAD/FARIDA
Sun kalli juna kana kowannensu ya zo da dan wani murmushi mairauni, kana ta kawar da idanunta ga barin kallonsa cikin kunya. Ta sauka kasa guiwarta biyu a durkushe.
FARIDA
Abba ka yi hakuri mun taso ka tun
daga Bida cikin tafiya mai nisa.
Ta dubi Ahmad, Baban Suraiyya kai ma ka yi hakurika gafarce ni bisa dukkan abinda nayi ma. Na san ban kyauta ba, hankalina ya fada min amma girmankai irin namu na mata ya hana niamsa laifina.
AHMAD
Idan kin yi min ba daidai ba ni ma
na yi miki, ina fata Allah ya yi
mana afuwa baki dayanmu.
(CONT'D)
51.

No comments:

Post a Comment