A yi hakuri da yadda format din ya hargitse amma dai shi wannan shafin an tanade shi ne don karatun labarin kawai ba wai don yin nazari akan Format ba. idan ana son mai format a sanar a group sai a turo da rich text na script din.
EXT. ESTABLISHMENT SHOT OF A REMOTE VILLAGE - mORNING
Alh. Musa (V.O.)
Da yawa wasu kan dawwama a cikin kuncin rayuwa komai kokarinsu.
Kauyen kayau. Yan gine ginen garin tsalli-tsall. Mutanen garin cikin yanayi na kunci tun daga gidaje, Hanya, rijiya da dabbobi da sauran abubuwa.
EXT. local govt. Head quater - dAY
Alh. Musa (V.O.)
Wasu kuwa su kan iya samun abin da bai kai ya kawo ba.
Mutane na harkokin su yayin da muke ganin yan abubuwan ci gaba jefi jefi. Wasu na aiki wasu kuma a lalace.
EXT. state head quater - aFTERNOON
Alh. Musa (V.O.)
Wasu kuwa, kan iya samun jin dadi daga lokaci zuwa lokaci.
Matsakaicin birni na jiha. kai da kawon abubuwan hawa, da cunkoson jama'a ko ina. Kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama'a. Makarantu da sibitoci, kamfanoni, da maikatun gwamnati.
EXT. babban birni head quater - eVENING
Alh. Musa (V.O.)
Yayin da lalaci ko kokari, ba sa samar da dawwamammen jin dadi na har abada.
Dogayen gine gine da kai da kawon abubuwan hawa na zamani. Kayan more rayuwa da abubuwan kyale kyale ko ina.
EXT. gidan alh. Musa (kofar gida) - eVENING
Katafaren gida, bene, na babban mai kudi, da babban kyaure.
Wata karamar mota mai tsada kirar zamani, ta karaso ta tsaya a bakin kofar gidan.
Alh. Musa
Mai shekaru (50-55) a bene a tsaye, ya yaye labulen tagar, yana kalonsu fuskarsa cikin damuwa.
A cikin motar a zaune, Hafsat ce (22-24) cikin kaya na ado, ta gama duba wata takardar dake hannunta, ta mikawa Ahmad cikin murmushi. Ahmad (33-35) mai matsakaicin kammani cikin shiga ta masu kudi.
Adamu
Mai gadi bayan ya leko, ya gane motar, yayi kamar zai bude babban gate din, Hafsat ta dakatar da shi.
HAFSAT I
Ba sai ka bude ba, tafiya zai yi.
AHMAD
Ya karba cikin sakin fuska ya duba, kafin ya dauki biro yayi rubutu akan takardar, ya sake mikawa Hafsat wadda ke binsa da kallon abin da yayi.
Hafsat I
Ta karba cikin sauyin fuska tana kallon takardar
Yaya ka chanja ranar?
Ahmad
Saboda tafiyar da zan yi, yiwo sayayya a China.
HAFSAT I
Karin damuwa a fuskarta
Amma da tuntuni ka sanar, ba sai yanzu da ya rage yan kwanaki a daura auren mu ba.
AHMAD
Ba tare da ya kalle ta ba
Kaya ne suka yanke a kasuwa. Shi yasa na ga ya dace naje na kawo.
HAFSAT I
Tayi shiru tana kallonsa
Gaskiya ba zan iya tunkarar Abba da wannan maganar ba.
AHMAD
To yaya kike so a yi?
Ya juya ya kalleta.
HAFSAT I
Ba ka san yanda za'a yi ba?
AHMAD
Shi yasa na tambaye ki.
Tayi jim tana kallonsa kafin ta fice daga motar cikin fusata.
AHMAD (CONT'D)
Hafsat! Hafsat!!
Ba tare da ta saurare shi ba, ta tura babbar kofar ta shige ciki, fuskarta kamar zata yi kuka.
Ahmad yayi jim kafin ya ja motar ya bar wajen daidai lokacin da Alhaji Musa ya ke barin inda yake a tsaye.
INT. gIDAN ALH. MUSA (falo) - eVENING
Falo na babban mai kudi komai a tsare. Babban hoton Alhaji Musa da Hafsat a makale ajikin bango. Sannan wani hoton na Hasiya ita da mijnta Sadiq. Shafafiyar talabijin ta zamani a ajiye.
Hafsat ta shigo cikin yanayi na damuwa daidai lokacin da Alhaji Musa ya ke saukowa daga benen fuskarsa cikin damuwa. Hafsat ta yi jim tana kallon mahaifinta ganin yar damuwar da fuskarsa ta nuna.
HAFSAT I
Abba, lafiya?
ALH. MUSA
Me ya faru?
Yana karasa isowa kusa da ita.
HAFSAT I
Naga kamar ranka a bace.
ALH. MUSA
Yayi yar dariya a wayance
Ke ce dai kike ciki yanayin damuwa duk da cewar Ahmad ne ya kawo ki gida.
Ya nufi wajen talabijin ya kunna.
Mutumin da za'a daura aurenku tare nan da kwanaki shida masu zuwa.
Hafsat ta zauna a kujera cikin sanyin jiki.
HAFSAT I
Ahmad din ne ya bata min rai. Ko sallama ba mu yi da shi ba.
ALH. MUSA
Dalilin me?
Ya tsaya yana kallonta
HAFSAT I
Yanzu don Allah Abba, idan aka sami sauyi akan sha'anin bukin nan, wa ya kamata a sanar?
ALH. MUSA
Magabatanku.
HAFSAT I
Don me Ahmad ba zai turo a sanar da kai cewa za'a daga bukin ba, sai dai yace zai fada mini na sanar da kai. A gaskiya ni naga take takensa kamar akwai wani abu a zuciyarsa.
Yayi jim kafin ya nufo wajen da take.
ALH. MUSA
shi yasa har yanzu zuciyata ta kasa amincewa da shi.
Hafsat ta bishi da kallo har ya zauna suna fuskantar juna.
ALH. MUSA (CONT'D)
Amma dole tasa na kyale ki saboda na fuskanci kina cikin shaukin kaunarsa.
HAFSAT I
Abba, yanzu kana son ka ce min tun da farko ba ka son mu'amala ta da Ahmad amma ba ka nunamin ba?
ALH. MUSA
A lokacin za ki iya ganin kamar na hanaki zabin zuciyarki ne.
Ta yi shiru ta zira masa ido tana kallonsa cikin mamaki.
HAFSAT I
Abba.
ALH. MUSA
'ya ta, Hafsat.
HAFSAT
ina son ka kaini wajen Umma ta.
Mamaki ya bayyana a fuskarsa.
ALH. MUSA
Kina son ganin mahaifiyarki?
HAFSAT I
Saboda na fuksanci Umma ta ce kadai zata iya nunamin so da kauna na hakika. Ba kai da kake bin son zuciya ta, dan kawai kada na zarge ka da laifin da ba lallai ne ya zama yanda nayi zatonsa ba.
Ta mike tsaye tana kallonsa cikin yanayi na karaya, tana ja da baya.
HAFSAT I (CONT'D)
Shi yasa shekara da shekaru kaki yarda ka kai ni wajen Umma ta. Ka hana ni sanin inda take. Biyayya da kauna ta gare ka, ba ta sa ka tausayamin a matsayina na 'yarka ba. Ka ki ka kulla rayuwata da ta mahaifiya ta. Maimakon haka, sai ka gadar da katanga ta dindin tsakanina da wadda tayi goyon ciki na har zuwa haihuwa.
ALH. MUSA
Saurara Hafsat. Mahaifiyarki ita ta guje ki a lokacin da tayi tsammanin hanyar da muka dauka ta gina rayuwarmu ni da ita, ba zata bulle ba.
Yanayin tausayi a fuskarsa
A lokacin da ni da ke muke da bukatarta don dorewar rayuwarmu tare. Tayi fushin da na tabbatar wata rana zata yi da na sanin yin sa.
Hafsat tayi shiru tana kallonsa cikin hawaye. Shi kuma ya tsare ta da ido cikin yanayi na matukar damuwa.
ALH. MUSA (CONT'D)
Ba ni ke da alhakin gadar da katanga tsakanin ku ba. Mahaifiyarki ce tayi hasashen kasa kaiwa gaci ga abin da muka sanya a gaba.
Yayi ajiyar zuciya yana kallonta idanuwansa cike da kwalla.
ALH. MUSA (CONT'D)
Auren soyayya muka yi da Zainab.
EXT. giDAN MUSA (KOFAR GIDA) - mORNING
Gida na bahaushe da bai wuce na miji da mata da yayan da basu wuce uku zuwa hudu. Babur din acaba a kafe a kofar gida da dan mukulli/sarka.
INT. gIDAN MUSA (cikin GIDA/falo) - mORNING
Alh. Musa (V.O.)
Duk da wasu daga iyaye na da nata, ba su so auren mu ba. Amma ta zama mace mai kokari wajen kula da gida da kuma nuna kauna gare ni.
Hoton Musa da na Ummi a makale, agogon bango na nuna bakwai da rabi ta wuce, muryar radiyo a kunne dake kusa da matsakiciyar talabijin da ke falon. Warin safa ta yara guda daya akan kujera a yashe. Ummi (27-30) na tattara kayan karin kumallo zuwa wajen wanke wanke/kicin. A hannunta rike da wani littafin Hausa tana yi tana karantawa.
Musa
Daga cikin daki
Ummi, warin safar Hafsat.
Ummi ta kai wasu kayan ta dawo daukar wasu.
Ummi
Ka ganta nan a falo.
Ta sake kwasar wasu kayan, Musa ya fito rike da hannun Hafsat (3-4) sanye da kayan makaranta, takalmi da safa a kafa daya, warin takalminta daya a hannu. Suka nufo inda jakar makarantar take ya dauka ya rike. Ummi ta dawo su kuma zasu fita, Musa ya saki yarinyar ya nufi wajen talabijin ya dauki dan mukullin.
UMMI (CONT'D)
Ki yi karatu da yawa, kin ji Hafsa ta?
HAFSAT
To.
Ta shafa kanta Musa ya kama hannun Hafsat za su fita. Ummi ta kalle shi ta yi murmushi.
MUSA
Ni zan fita.
UMMI
Allah Ya bada sa'a. Amma ka dawo da wuri, saboda ina son ka karasa min labarin da ka fara bani jiya kafin mu yi bacci.
Yayi murmushi kafin ya ja yarinyar su nufi kofa.
MUSA
Na fuskanci kin ji dadin labarin.
UMMI
Tana karasawa wajen kwanukan abincin
Gaskiya yayi. Inda zai yiwu da ka yi littafinsa.
Ya kai bakin kofa ya saurara ya juyo ya kalleta.
MUSA
Kina ganin za'a so labarin?
Ta daga masa littafin da ta ke rike dashi tana kallonsa.
UMMI
Ya fi irin wannan labarin da na ke karantawa ma'ana sau goma.
Ya sake yi mata murmushi, agogo yayi kara kafin ya fara buga takwas.
HAFSAT
Abba karfe takwas.
Cikin gaggawa ya bude kofa ya fita.
EXT. gIDAN MUSA (KOFAR GIDA) - mORNING
MUSA/hafsat
Sun fito tare ya ciro karamin tabarau na yara a cikin jakar makarantar ta ya bata ta sa. Bayan ya hau, ya dora ta a gabansa kafin ya tashi babur din.
EXT. akan hanya (cikin unguwa/babban titi) - mORNING
alh. Musa (V.O.)
Tun bayan kammala karatun jami'a ta, na fara sana'ar Acaba. Wanda yana daga cikin abin da ya ja hankalin Ummi ta yarda da ni mai kokarin neman na kaina ne.
MUSA/HAFSAT
Hafsat akan tankin babur a zaune sanye da tabarau, Musa yana tukawa cikin matsakaiciyar tafiya.
Hasiya (26-28) fara mai sigar fulani cikin kayan kamala, rataye da jaka, tana tsaye a bakin titi, tana jiran abin hawa, cikin yanayin da ke nuna ta dade ko sauri ta ke yi ta je inda za ta.
Musa ya taho, Hasiya ta fara daga masa hannu tun kafin ya karaso inda take a tsaye. Ganin sa da Ummi da ya kusa sai ta daina tsayar da shi. Musa ya gilma, kamar ba zai tsaya ba, sai kuma ya tsaya, ya dawo inda take.
Yana kallonta yana baiwa mashin din wuta kadan kadan.
MUSA
Ina za'a kai ki?
HASIYA
(Ta fada masa) Zan baka arba'in.
MUSA
Hau mu je.
Hasiya ta yi maza ta hau, suka nausa suka yi gaba.
Muryar Hasiya
Naga yarinya zaka kai makaranta. Ba zata makara ba?
Muryar MUSA
'Ya ta ce. Makarantar babu nisa da inda zan kai ki.
Suka sha wata kwana.
EXT. bakin hanya (kusa da plaza) - mORNING
Musa ya tsaya, Hasiya ta sauka tana gaggawar dauko kudin da zata bashi daga cikin jaka. Fuskarta cikin yanayi na zakuwa. Sannan ta fiddo da kudin daya naira dubu, daya dari biyar sai kuma naira ashirin. Ta kalle shi cikin yanayi na gazawa.
HASIYA
Bawan Allah gashi.
Tana mika masa dari biyar
Nayi zaton chanjin nawa sun kai ne. Amma don Allah ka yi hakuri ka dauki hamsin.
MUSA
Fitowa ta kenan. Ke ce ta farkon dauka.
Hasiya tayi galala da kudin cikin karin damuwa.
HASIYA
To yanzu yaya za'ayi?
Ta fara hange hangen yanda za'a yi.
Interview zan shiga karfe takwas da rabi, ga shi saura minti uku ta cika.
Yayi jim yana kallonta cikin yanayi na tausaya mata.
MUSA
Allah ya bada sa'a. Ba ni ashirin din.
Ta yi jim kafin ta mika masa, ya karba.
HASIYA
Na gode madalla.
Ya ja baburinsa ya tafi, ita kuma ta gaggauta inda za ta je.
EXT. makaranta (waje) - mORNING
MUSA
Yana kafe babur kafin ya sauke yarinyar ya shiga da ita.
HAFSAT
Tana kallonsa goye da jaka
Abba ka tahomin da buiskuit.
MUSA
Har da alewa zan hado miki, amma kiyi karatu yafi na kullum.
Hafsat ta yi cikin makaranta da gudu tare da suaran, ya buga babur yayi gaba.
EXT. akAN HANYA (KARAMI/BABBAN TITI i) - dAY
ALH. MUSA (V.O.)
Kullum haka na ke yi, kafin na fara sana'a ta ta acaba.
MUSA
Akan babur dinsa yana gudanar da sana'arsa ta daukar fasinja daga unguwa zuwa unguwa.
Mutum i
Wani matsakaicin dan kasuwa ya fito zai tafi wajen sana'arsa.
Musa ya ajiye shi ya biya shi, wani dan makaranta ya tare shi.
Dan makaranta
A bayan babur din, suna tafiya suna hira sun tsaya a bakin danja.
A wani shataletale, wani mai mota yayi musu a rubta, dan makaranta yayi zagi.
INT. giDAN MUSA (tsakar GIDA) - dAY
Bakin allo a tsaye, matan aure a zazzaune, wasu da hijabi wasu babu. Wasu na rubutu a littafi, wasu kuma suna saurare.
UMMI
A matsayin malama, a tsaye gaban allo tana koyar da su.
EXT. cikin kasuwa - dAY
MUSA
Yana yin cefane, har ya zuwa wajen mai kayan tireda ya tsaya sayawa Hafsat buiskuit da alewa. Ya saya ya sake buga babur yayi gaba.
EXT. mAKARANTA (WAJE) - dAY
Musa ya kafe babur dinsa yana kai a zaune. An tashi daga makaranta, Hafsat ta fito tare da sauran yara. Musa ya dauke ta suka tafi.
HAFSAT
Abba ka sayomin biscuit din?
MUSA
Na sayo miki.
Ya dauko daga aljihu ya nuna mata
Ke kuma fadamin na ki karatun da kika yi yau sai na baki.
Ta bude jaka ta dauko littafi ta nuna masa cikin littafin duk tayi zane a ciki.
HAFSAT
Gashi.
Ya rungume ta yana dariya sannan ya dora ta a babur ya tuka.
Muryar hafsat
Abba bani guda daya.
Muryar musa
Bari muje gida. Ba a cin abinci a waje.
Sun nufi wajen gidan cikin matsakaiciyar tafiya.
EXT. gIDAN MUSA (KOFAR GIDA) - dAY
MUSA/HAFSAT
Musa ya ajiye ta, ya mika mata biskuit da alewa, tayi masa "a dabo" kafin ta shige gida a guje rike da ledar biskuit din. Shi kuma ya sake buga babur ya juya.
EXT. bakin kasuwa - aFTERNOON
Wata mace a tsaye da faggon kaya, ta tare Musa.
Mace i
Tasha zaka kaini.
Musa ya leka kayan sannan ya kalleta.
MUSA
Naira dari da ashirin.
Mace i
Babbar tasha fa? Saba'in dai zan bayar ni da kayan.
Ya sake kallon kayan.
MUSA
Haba Hajiya daga nan fa har babbar tasha ke da wannan kayan?
Ya fara girgiza kansa yana kokarin bugawa zai tafi.
Gaskiya naira dari.
MACE I
To tamanin.
MUSA
A darin ma sauki na yi miki.
MACE I
Dora mu tafi.
Ya gama dora kayan, ta hau ta zauna, ya duba, ya nuna mata ta gyara zamanta da kuma gyara zaninta inda sharabarta ta fito.
ALH. MUSA (V.O.)
A kullum na kan auna yanayin fasinja na kafin na yi tsada shi. Saboda wani zai iya cewa ka yi masa tsada ko da ba haka ne.
Abubuwan hawa tare da sauran kai da kawon mutane kowa yana kokarin komawa gida. Rana tayi kasa zata fadi.
INT. gIDAN ALH. MUSA (cikin gida) - eVENING
ALH. MUSA (V.O.)
ummi ta san yanda ta ke yi wajen yin abincin da ya dace da mu.
UMMI
Tana kwashe abinci daga wajen da ke girki zuwa cikin falo.
EXT. majalisar yan acaba (kusa da masallaci) - eVENING
Kiran salla a bayan fage. Akwai taron baburan acaba, wani na barin wajen da fasinja wasu akan baburan a zaune, wasu sun fara alwala.
ALH. MUSA (V.O.)
Da yawan mu ba mu faya sakaci da addinin mu ba. Mu kan zama masu tsayawa a duk lokacin ibada dan gabatar da ita.
MUSA
Ya gama alwala ya mike ya nufi cikin masallaci.
INT. gIDAN ALH. MUSA (FALO) - nIGHT
Littafin a yashe akan kujera. Talabijin a kunne. Musa da Ummi da Hafsat suna cin abinci. Ummi rike da littafi tana karatu, tayi tsaki tayi wurgi da littafin. Musa ya kalleta.
MUSA
Yaya haka?
UMMI
Sai azabtar da kaina nake yi sai ka ce dole.
Ta tashi da na farantin abincin
Labarin ba dadi.
Ta dauko ruwa ta dawo ta zauna
Sake bani labairn da ka fara bani jiya.
Musa yayi murmushi yana ci gaba da cin abincin. Ummi ta lura da Hafsat ta gama cin nata abincin.
MUSA
Kina son labarin.
Ummi ta dauki kwanon gaban yarinyar ta mika mata ruwan sha.
UMMI
Allah na fada maka inda zaka buga shi mutane za su so shi.
MUSA
Ni kaina tun lokacin da na fara tunaninsa, na ji zuciya tana aiyana min na mayar da shi littafi.
Ummi
Don Allah Yaya Babba, ka buga labarin nan.
Yayi jim yana kallonta cikin gane abin da ta ke nufi.
MUSA
Kin ga fa haka ne. Babu mamaki ya zama hanyar arziki na.
UMMI
Ko dai arzikinmu.
Cikin raha suka kwashe da dariya gaba dayansu.
INT. gIDAN MUSA (cikin DAki) - nIGHT
Musa da Ummi suna kwance, agogo ya buga sha biyun dare.
ALH. MUSA (V.O.)
Tun daga lokacin, fadi tashin yanda za' a buga littafi ya fara, kasancewar ba kudin bugawa ne da ni ba.
Ummi ta farka sannan ta tashi Musa, da akwai alamar gajiya a tare da shi. Ta bude bed-side-drawer ta dauko littafin exercise da biro ta mikawa Musa, yayi jim yana kallonta.
UMMI
Yi rubutu.
MUSA
Ya karba yana mai kallonta cikin mamakinta.
ALH. MUSA (V.O.)
A ranar Ummi ba ta bari mun sake runtsawa ba, sai da na karasa rubuta labarin gaba daya. Na mika mata. Ta karba ta fara karantawa, ni kuma na fita yiwo alwala.
Ummi ta karba tana karantawa shi kuma ya dauki doguwar rigarsa ya fice daga dakin.
I/E. gIDAN ALH. MUSA (cikin GIDA) - mORNING
ALH. MUSA (V.O.)
Da safe Ummi ta bani shawarar na je na sami mijin Yayarta, Dan Garba, mai sayar da littattafai mu yi yarjejeniya ya bugamin, ko kuma na sayar masa shi ya buga.
Kayan wanki a zube a kasa, Musa ya fito daga falon rike da Hafsat cikin kayan makaranta, Ummi na biye da su rungume da sauran kayan ta zo ta hada da ragowar kayan. Suka yi waje ita kuma ta koma cikin falon.
ALH. MUSA (V.O.) (CONT'D)
Na yarda da shawararta ta farko. Amma maganar sayarwa tun a lokacin na ji zuciya ta bata amince ba.
INT. gIDAN ALH. MUSA (FALO) - mORNING
A Radiyo ana hira da wani shahararren murubuci, exercise book din akan kujera.
UMMI
Ta shigo zata wuce cikin daki, idanunta suka kan littafin.
INT. gIDAN ALH. MUSA (kofar GIDA) - mORNING
Musa rike da hannun Hafsat sun fito har ya zasu tafi, sai Ummi ta fito da sauri dauke da littafi, tazo ta bashi, ya karba yana sokewa a jikin babur yana kokarin tashin babur.
UMMI
A falo ka manta.
MUSA
Da karshenta sai na tafi na yi ta tunanin a ina na barshi?
Ta juya tana komawa cikin gida.
UMMI
Yaya Babba, ka fa daure ka je.
MUSA
In sha Allahu.
I/E. sHAGON GARBA MAI LITTAFI - dAY
Babur din Musa a waje a kafe, kusa da wata karamar mota.
Littattafai iri dabam dabam a cike a shagon, wani matshin saurayi na kokairn gyara wasu. Musa a zaune suna fuskantar juna da Dan Garba (45-47) cikin kyakykyawar shiga fuskarsa cikin rashin walwala ya gama sauraren bayanin Musa.
Dan garba
Muga littafin.
Cikin ladabi ya mika masa yana fara'a, shi kuma ya karba.
DAN GARBA (CONT'D)
Da daddare sai ka same ni a gida mu tattauna yanda za'a yi.
MUSA
Allah Ya kaimu. A tashi lafiya.
Musa yayi godiya suka yi sallama ya fito, ya hau babur dinsa ya tuka ya tafi dai dai lokacin da Dan Garba ya taso ya bude mota ya jefa littafin a cikin dashboard ya kulle.
INT. gidan dan garba (falo) - nIGHT
Baraka yayar Ummi cikin fara'a, tana kwashe kwalabe lemon da ta kawowa su Musa da Ummi wadanda ke a zaune a kujeru kusa da juna. Baraka ta mike da kwalaben a hannunta.
Baraka
Ina zuwa.
Ummi
Ki ce shi fa muke jira.
Cikin raha ta jawo Hafsat jikinta wadda ke tsaye a kusa da ita. Dan Garba ya Fito daga cikin daki dauke da littafi fuskarsa babu walwala.
Dan garba
Salla na idar.
Ya zauna akan babbar kujerar suna fuskantar juna.
UMMI
Kada fa ace za'a buga mana yan copy kadan. So na ke a buga shi yanda kowa zai gane cewar fitowar murucin kan dutse muka yi.
Dan Garba ya ajiye littafin ya kalle ni cikin yanayin gazawa. Baraka ta dawo ta zauna kusa da mijinta.
ALH. MUSA (V.O.)
Daga yanayin fuskarsa nasan za'a sami akasin maganar da Ummi ta fada.
Dan Garba yana magana fuskarsa cikin rashin walwala, yayin da muke ganin damuwa a fuskar Musa da Ummi, wadda kafin ya kare tuni ta dauki Hafsat ta yi sallama da Baraka ta fita.
ALH. MUSA (V.O.) (CONT'D)
Daga karshe dai na gane dalilin da zai hana Dan Garba buga littafin, bai wuce na cewar babu wanda ya sanni a rubutu. Babu tabbas kudinsa zai dawo.
INT. gIDAN ALH. MUSA (FALO) - nIGHT
Ummi fuskarta cike da takaici ta shigo falon dauke da Hafsat wadda ke bacci, Musa na biye da ita wanda ya fara zama kafin Ummi ta shimfide Hafsat sannan ta zo ta tsaya a kansa.
UMMI
Yaya Babba.
Musa ya daga kai ya kalleta.
UMMI (CONT'D)
Mai zai hana ka yiwa chairman din kungiyar ku magana a ara maka kudi kai ka buga da kanka?
MUSA
Yayi shiru yana kallonta cikin fahimtar abin da tace da shi.
INT. oFISHIN ACCOMORAN (CIKI) - mORNING
ALH. MUSA (V.O.)
Ko da naje, ban sami shi Chairman ba. Amma sanayyar da ke tsakanin mu da sakatariyar, yasa na yi mata bayanin littafi na rubuta, na ke son kungiya ta taimaka, ko ta dauki nauyin bugawa, ko kuma ni a bani rance na buga da kaina. Bayan na sayar kungiya ta dauki kashi 60% ni kuma na dauki 40% na ribar. Sannan na bar sallahun cewa zan dawo.
Fuskar Sakatariya cikin fara'a a inda ta ke a zaune, ganin shigowar Musa da ya shigo rike da rubutaccen labarin.
MUSA
Suka gaisa da ita sannan ya mika mata littafin.
Sakatariya
Ta karba, suka yi sallama ya juya ya fita.
EXT. ofishin accomoran (waje) - dAY
Yan acaba wasu a zaune kan baburansu suna hira. Musa ya karaso da babur din sa ya kafe, suka gaisa da wasu kafin ya wuce ya nufi cikin ofis din.
INT. oFISHIN ACCOMORAN (ciki) - dAY
Akan kujara a zaune, Mallam Mudi ne yana duba littafin. A gabansa an ajiye wata yar roba wadda aka rubuta "COMRADE MUDI S. BABA Chairman ACCOMORAN". Musa yayi sallama ya shigo ya nutsu.
MUSA
Comrade barka da aiki.
Comrade mudi
Musa Abba.
Ba tare da ya daga kansa ba, ya nunawa Musa kujera ya zauna. Musa ya zauna yana washe baki musamman da ya lura da yadda Comrade ya nutsu yana karanta rubataccen labarin, har ya gama.
ALH. MUSA (v.O.)
Wani dadi ya cika ni, ganin irin yadda ya kwafule yana kokarin sai ya kai karshe, wanda na tabbata a cikin kashin karshe na littafin yake. Ni kaina idan nazo wajen, ba na son ko magana a yi min. Nan da nan na dokanta da ya gama ya saurare ni.
Sannan ya daga kai ya kalli Musa cikin fara'a ya mika masa hannu suka gaisa.
COMRADE MUDI
Kai Musa gaskiya labarin nan ya burge ni matuka.
MUSA
Yana washe baki
Godiya nake Comrade.
COMRADE MUDI
Saboda ya zo da ma'ana da kuma sako mai kyau.
MUSA
Na gode.
Fuskar Comrade ta sauya, yayi jim yana kallon Musa cikin yanayin gazawa.
COMRADE MUDI
Jiya mun zauna da sauran shugabannin Exco akan maganar littafin. Sai dai ni kaina, da ina da dama, ni ya kamata na dauki kudin ko nawa ne na baka ka buga. Saboda Exco sun ki yarda da bukatarka wai matsalarka ce kadai. Ba abin da kungiya zata yi saurin amfana ba ne.
Musa ya mike cikin sanyin jiki yana mai kallon wani waje.
EXT. oFISHIN ACCOMORAN (WAJE) - dAY
Musa ya fito jikinsa a sanyaye, yazo ya haye kan babur din ya zauna kamar yana tunani.
ALH. MUSA (V.O.)
Sauran maganganun da ya ci gaba da yi min na kwantar da hankali ne, don kawai na gane ya so ya taimaka min, amma babu yanda zai yi ne.
INT. gIDAN MUSA (falo) - eVENING
Musa da Ummi a doguwar kujera a zaune cikin yanayi na damuwa.
UMMI
Mai gida ya zo dazu maganar kudin haya.
Bai ce komai ba, yayi shiru kamar bai ji ta ba.
UMMI (CONT'D)
Yace zai dawo gobe.
Musa yayi a jiyar zuciya
MUSA
Da daddare za muje wajen Malam Sale.
Ummi ta juyo ta kalle shi cikin rashin fahimta.
UMMI
Waye haka?
INT. gIDAN sale Umar (falo) - nIGHT
MUSA/uMMI
Musa da Ummi zaune kan kujera, Hafsat a tsakiyar su. Kofuna da kwalaben lemo akan teburin tsakiya. Sale Umar (45-50) a zaune kan kujera suna fuskantar juna, yana duba shafukan littafin.
ALH. MUSA (V.O.)
Sale Umar, malami na ne. Kuma shine senior master din mu a lokacin da nake Secondary. Mutum ne mai son wasannin motsa jiki, karance karance da kuma bukatar harkar fasaha. Musamman abin da ya shafi kirkira. Shi yasa ko da Dan Garba mai littafi, yaki yarda da shawara ta, babu wanda tunani na ya kawo sai Sale Umar.
sannan ya mikawa Musa ya karba. Ya yi jim cikin gajeren tunani. Musa da Ummi suna kallonsa cikin sauraronsa. Sannan ya binciko complementary card da biro yayi rubutu.
Mal. sale
Kaje unguwar Rimin lada, Ka tambayi gidan Alhaji Sani Mai Dab'i. Ka kai masa wannan.
INT. gidan sani mai dab'i (babban falo) - dAY
Takardu da sauran fastoci ko ina, wasu a like, wasu a zube a kasa. Wasu ma'aikata na ta aikin karasa hada wasu litattafai.
Musa ya shigo wajen cikin yanayi na bakunta. Ya sami wani daga cikin ma'aikatan yayi tambaya, ya nuna masa wata kofa.
MUSA
Musa ya nufi wajen yana kallon yanda ake tafiyar da aikin.
ALH. MUSA (V.O.)
Ganin yanda wajen yake shi yasa ni tunanin aikin zai iya yiwuwa.
INT. gIDAN SANI MAI DAB'I (cikin ofis) - dAY
Gaban wani makeken teburi mai cike da takardu da sauran tarkacen aiki, Alh. Sani ne (55-60) Karan sigari a bakinsa, ya juya yana bincike a cikin wani kwali mai cike da takardu. Musa ya shigo.
MUSA
Salamu alaikum.
Alh. Sani na ci gaba da ya ke yi bai dago ya kalle shi ba.
Alh. Sani
Malam daga ina?
MUSA
Daga wajen Sale Umar.
Alhaji Sani ya dago kai a hankali ya fara karewa Musa kallo kafin ya nuna masa kujerar da ke gabansa alamar ya zauna yana karkade tokar sigarin a cikin farantin da ke gabansa. Musa ya tafi zai zauna da sauri.
ALH. SANI
Yi hankali wajen zama.
Musa ya zauna a hankali kamar zai zauna akan kwai. Yana zama kujerar ta zame da shi yayi maza ya mike yana kokarin zama.
MUSA
Zamewa tayi.
Alhaji Sani yayi zuru yana kallonsa.
ALH. SANI
Me ke tafe da kai?
Musa
Ya mika masa katin cikin yanayi na girmamawa.
Alhaji Sani ya karba, yana karantawa, sannan ya mikawa Musa hannu ba tare da ya kalle shi ba.
ALH. SANI
Bani rubutun.
MUSA
Cikin nuna rashin fahimta yana fara'a
Wane rubutu fa, Yallabai?
ALH. SANI
A lokacin ya dago kai ya kallle shi a kurace
Rubutun da kake so a mayar littafi.
Musa yana kallonsa ya mika masa littafin, ya karba ba tare da ya dauke idanu daga kansa ba.
ALH. SANI (CONT'D)
Zan baiwa matata ta duba. Idan ta ce labarin yayi zance maka yayi.
Ya jefa cikin wani kwali mai dauke da wasu takardu da ke a hargitse. Ya kalli wata kalanda da ke rataye a bango.
Ka dawo ranar sha tara ga wata.
Musa yayi shiru yana kallon wani waje cikin yanayi na tunani.
ALH. SANI (CONT'D)
Ko da wani abu ne?
MUSA
Cikin Yake ya girgiza kansa
Nan da mako guda za'a fara aikin kenan?
ALH. SANI
Cikin dagawar murya
Ba haka na ce ba!
Ya juya ya dauko littafin daga inda ya jefa shi
Cewa nayi matata zata duba, kafin nasan ko zan iya mayar da shi littafi.
Ya tsare shi da ido ta cikin tabarau.
ALH. SANI (CONT'D)
Saboda kowane mutum daga talauci ya dame shi, sai ya dauki biro da takarda ya fara rubuta karya da gaskiya. Ya dauko ya kawo, yace ka saka ka kudin ka, ka buga masa, ya je ya kai kasuwa. Mai yiwuwa ma irin labarin da ke gurbata tarbiyyar mutane ne.
Ya mika masa littafin, karan sigari a bakinsa.
Musa
A yi hakuri. Ban fahimce ka bane. Duk da dai nawa labarin ba karya ba ne, ba kuma talaucin ne yasa na keso na buga ba. Sai dai nima matata, a matsayinta na mai yawan karanta littattafai, ta ke ganin zai karbu a wajen jama'a.
Alhaji Sani yayi shiru yana kallonsa har ya dauki littafin ya juya zai fita, sannan ya kira shi, Musa ya dawo ya sake zama.
ALH. SANI
Babu abin da Sale Umar zai nema a waje na ban yi masa ba. Amma tuni na daina irin wannan aikin Baban giwan. Wanda daga karshe za'a rabu dutse hannun riga.
Cikin sakin fuska ya karbi littafin ya mayar da shi inda ya jefa shi da farko.
ALH. SANI (CONT'D)
Ka dawo rana i ta yau.
ALH. MUSA (V.O.)
Haka na tashi na fita zuciya ta na tunanin yiwuwar aikin.
EXT. gIDAN SANI MAI DAB'I (kofar gida) - nIGHT
Sautin kiraye kirayen salla na ratsowa ta ko ina, babur din Musa a ajiye a kofar gidan.
MUSA
Ya fito fuskarsa babu walwala, ya dauki babur din ya tafi.
ALH. MUSA (V.O.)
Cikin karyewar murya
Gaba dayan nasara ta zata dogara ne, idan Furera matarsa, tace labarin yayi. Idan kuwa ta fadi akasin haka ko ta soki labarin, to duk duniya babu wanda ya isa yasa Sani mai dab'i, yin abin da yake sabanin ra'ayin matarsa.
INT. gIDAN MUSA (CIKIN DAKI) - nIGHT
UMMI/hafsat
Ummi a kwance, Hafsat a kusa da ita. Musa ya shigo cikin yanayin gajiya.
ALH. MUSA (V.O.)
Ganin ta yi bacci ban tashe ba. Na bari sai da safe zan fada mata yanda muka yi.
MUSA
Ya zauna a gefen gado yayi jim kamar yana tunani sannan ya kinkimi Hafsat ya dawo da ita akan shimfidarta kafin ya je ya kashe fitilar dakin.
EXT. gIDAN MUSA (TSAKAR GIDA) - mORNING
Ummi a zaune tana hada tana shara fuskarta babu walwala, Musa ya fito yana karasa sanya hularsa.
MUSA
Ni zan fita.
UMMI
Mai gida ya sake zuwa jiya da magariba. Ya bar sallahun zai dawo da safen nan.
Musa yayi jim kafin ya kofa ya fita. Ta bishi da kallo fuskarta cikn karin damuwa.
EXT. gIDAN ALH. MUSA (KOFAR GIDA) - mORNING
Musa na kokarin tashin babur, Mota ta tsaya a kofar gidan.
Mai gida
Musa!
Gane muryar wanda ya kira shi, yasa fuskar Musa ta sauya tun kafin ya waigo daidai lokacin da yake fitowa daga mota.
MUSA
Barka da zuwa Alhaji.
Yana fara'a. Shi kuma cikin daurewar fuska ya riske shi.
MAI GIDA
Ba ka samu sako na ba ne?
MUSA
Na samu.
MAI GIDA
To yaya a ke ciki?
MUSA
Ina sane, dan hakuri za'a ka kara yimin Alhaji.
Ya dakatar da shi da hannu.
MAI GIDA
Babu wani hakuri da zan kara wanda ya wuce na watanni ukun da na yi. Na baka sati daya. Ko kudi na, ko kuma ka tashi. Kawai.
Ya juya zai koma cikin mota.
MUSA
Don Allah Alhaji ka yi hakuri.
MAI GIDA
Mako guda na baka.
Ya shige mota ya tuka ya tafi, Musa yayi jim yana bin motar da kallo kaifn ya buga babur din ya tafi.
EXT. cikin gari - mORNING
Kai da kawon mutane da sauran abubuwan hawa, daga kasuwanni, makarantu asibiti, har zuwa ma'aikatu da gidan man da aka yi dogon layi saboda wahalar mai.
ALH. MUSA (V.O.)
Makon da ba zan taba mantawa da shi ba saboda wahalar man da aka shiga, sai ya zama duk abubuwan da na sa a gaba a cikin satin, ban sami damar aiwatar da su ba. Tun daga kudin haya har zuwa aikin littafin.
MUSA/UMMI
Suna tafiya a kasa suna hira, Ummi rungume da Hafsat. Musa ya karbe ta yayi mata dokin wuya suka ci gaba da tafiya.
EXT. gIDAN SANI MAI DAB'I (KOFAR GIDA) - nIGHT
MUSA/UMMI
A kofar gidan, wani saurayi yana yi musu bayani, fuskar Ummi cikin damuwa ta fara juyawa tana barin wajen kafin Musa ya bita.
ALH. MUSA (V.O.)
Dan ko gidan Mai dab'i da muka je, ni da Ummi da Hafsat, sai aka ce yayi tafiya, sai bayan mako biyu zai dawo.
INT. gIDAN MUSA (FALO) - nIGHT
Sun dawo a gajiye, Musa dauke da Hafsat tayi bacci. Musa ya shimfide ta akan kujera. Ummi ta nufi daki zata shiga sai ta saurara a kusa da kofa, fuskarta kamar zata yi kuka.
UMMI
Musa.
Ya kalleta cikin yanayin mamaki da saurare.
UMMI (CONT'D)
Ni fa na fara gajiya.
MUSA
Kin fara gajiya? Me kika nufi Ummi?
Ba tare da ta bashi amsa ba ta bude kofar daki ta shige ta rufe kofar har da sakata. Musa yayi shiru yana mai bin kofar dakin da kallo.
EXT. aKAN HANYA (cikin gari) - nIGHT
Musa ya tsaya daukar wani yaro matashi ya tsayar da shi. Bayan sun yi tsada ya dauke shi har ya zuwa inda zai a jiye shi. Yana dan yin gaba ya sake daukar wani shima.
EXT. baKIN HANYA (wajen masu bunburutu) - nIGHT
Ya sayi rabin galan na mai ya zuba har da mix. Ya fara duba lokaci sannan ya biya yayi gaba.
MUSA
Yana tafiya kawai sai fitlar babur din ta dauke. Musa yayi yayi fitilar ta ki kunnawa. Ya hau a haka ya tafi.
EXT. aKAN HANYA (junction) - nIGHT
Yan sanda suka fara haska Musa da cocilan tun kafin ya karaso ya tsaya.
Dan sanda i
Yaya ba fitila.
MUSA
Yanzun nan ina tafiya ta dauke.
DAN SANDA I
Ya kara hannunsa jikin fitilar
Yaya ban ji da zafi ba. Anya ma babur din ka ne? Ina particulars?
Yana kokarin sake tare wani mai mota da ya kawo kai.
DAN SANDA Ii
Yi parking mana ka tsaya a hanya. Ka hawo babur ba fitila. Ina hular kwanonka? Kawo takardun babur din.
Musa ya shafa kansa yana fara'a.
MUSA
Yallabai ai suna gida tunda ba a yi yawo da su da daddare ba.
Dan sandan ya kalle shi a wulakance.
DAN SANDA II
Copral zo ka wuce da shi station.
DAN SANDA I
Yes Sir!
EXT. aKAN HANYA (KARAMI/BABBAN TITI) - nIGHT
Musa ya goyo Dan Sandan suna tafiya.
MUSA
Yallabai a taimakamin. Kasan yanayin sana'ar nan.
DAN SANDA I
Kaga kawai ka yi belin kanka.
Musa ya koma gefen hanya ya kashe babur din. Ya kwakwulo Naira dari da hamsin din da suka rage ya wari dari ya mika masa.
MUSA
Yallabai ga wannan.
DAN SANDA I
Nawa ne?
Musa yana mikawa Dan Sandan ba tare da ya karba ba.
MUSA
Naira dari ce.
DAN SANDA I
Naira dari? Wato cin hanci ma ka bani kenan. Wallahi sai na kai ka.
MUSA
Dan Allah Yallabai ka karba.
DAN SANDA I
Kawai Malam ka buga mu tafi.
Musa yayi jim, sannan ya sake buga babur din.
INT. police station (ciki) - nIGHT
Sergeant ya tura wani matashi takarda ya sa hannu akai, zai karbi belin wata yarinya. Musa a bayan canta a zaune shi da yarinyar. Matashin ya gama sanya hannun, sergeant ya juya.
Sergeant
Ya dan waiga
Sai ki taso ku tafi.
Yarinya
Ta kalli Musa ta yi masa fari da ido
Sai anjima.
Sannan ta tashi ta je ta sami saurayin suka fita tare. Musa ya tashi ya zo ya tsaya kusa da Segeant.
MUSA
Yallabai don Allah alfarmar wayarka na keso ka bani na kira wata lamba.
SERGEANT
Waya ta kuma, wa za ka kira?
MUSA
Matata zan kira Yallabai.
Sergeant yayi jim kafin ya dauko ya mika masa.
SERGEANT
Minti daya.
Musa ya karba da rawar jiki, ya danna lambar kana ya kai kunnensa cikin saurare ta fara kara har ta yanke. Ya sake kira a karo na biyu sannan aka dauka.
Muryar ummi
Salamu alaikum. Hello.
MUSA
Ummi nine.
Shiru na dan lokaci.
MurYAR UMMI
Sai aka yi yaya?
MUSA
Cikin karaya
Ummi a police station na ke.
MURYAR UMMI
Police station? Lafiya?
Musa
Kama ni aka yi, babur dina babu fitila. Ki taimaka ki zo, ina jiranki.
Wayar ta yanke kudin ya kare. Fuskar Musa cikin damuwa.
SERGEANT
Sai ka bani tunda kudin ya kare.
Musa ya koma ya zauna cikin takaici yana mai rike kansa. Babu dadewa wayar ta sake kara.
SERGEANT (CONT'D)
Hello.
Yayi saurare kafin ya juya ya kalli Musa, daidai lokacin da Musa ya dago kai suka hada ido.
INT. gIDAN MUSA (CIKIN GIDA/FALO) - nIGHT
Suka shigo, Ummi na gaba, Musa na biye da ita, ya cika da matukar mamakin ganin babu komai a falo ya juya ya kalli Ummi suka hada ido.
UMMI
Na kai gidan Baraka.
MUSA
Dalili?
UMMI
Saboda zaman mu ya zo karshe.
MUSA
Wato dan nazo na ga wannan wulakancin, yasa kika yiwo beli na?
UMMI
Saboda Hafsat ne. Dan nasan zaka so ka ganta kafin mu tafi.
Musa ya kura mata ido yana mai matsawa kusa da ita, ita kuma tana ja da baya
MUSA
Ummi fadamin laifi na.
UMMI
Tana girigiza kanta cikin nadama
Gaskiya na gaji. Ba zan iya ba. Abubuwa sun ki sauyawa. Ka tsaya ka kafe akan abu daya. Ka ki ka sauya sana'a.
MUSA
Ba ga littafi na nan za'a buga ba.
UMMI
A yaushe? Tun yaushe ake ta yin abu daya.
Suka yi jim suna kallon juna
Babu tabbas! Musa ba zan ci gaba da rayuwa akan kila wa kala ba. Ya isa haka.
Ta juya ta shiga daki ta dauko wata jaka ta fito, ta yar a tsakiyar falon ta zauna a gefen shimfidar da Hafsat ta ke a kwance. Musa ya je Ya leka dakin, babu ragowar komai sai katifa a jingine. Ya juyo ya kalleta a inda take.
MUSA
Ba za dai ki fita yanzu ba?
UMMI
Sai da safe zan biya gidan Baraka kafin na wuce garinmu.
Ya koma gefe ya zauna ya harde, zuwa wani lokaci ta tashi ta koma ciki ita da yarinyar ta mayar da kofa ta rufe.
INT. gIDAN MUSA (CIKIN GIDA/FALO) - mORNING
Har yanzu Hafsat na bacci, Ummi ta fito ta nufi inda yarinyar take zata dauke ta.
MUSA
Kada ki dauke ta.
Ya gargade ta yana mai mikewa tsaye daga inda yake a zaune. Ummi ta dakata tana kallonsa cikin mamaki.
Ummi
Ban gane ba.
Musa ya tsaya tsakanin Ummi da Hafsat suna kallon juna.
MUSA
Ba da ita kika zo ba.
Tayi jim na wani lokaci kafin ta juya ta kinkimi jakar ta yi waje, Musa ya bita.
EXT. gIDAN MUSA (KOFAR GIDA) - mORNING
Ta fito cikin bacin rai, Musa ya biyo ta.
MUSA
Bazan fa neme ki ba.
UMMI
Nima ba zan dawo gunka ba.
Ba tare da ta juyo ko ta saurare shi ba ta ci gaba da tafiya. Musa ya tsaya yana kallonta har ta tsayar da Dan acaba ta hau ta tafi, sannan Musa ya koma cikin gida jikinsa a sanyaye.
ALH. MUSA (V.O.)
Tun daga lokacin ba mu sake ganin juna ba.
INT. gIDAN MUSA (CIKIN GIDA/FALO) - mORNING
Musa yana dawowa ya tarar da Hfsat a zaune ta tashi.
HAFSAT
Abba ina Umma ta?
Yayi jim yana kallonta sannan ya nufo wajenta.
MUSA
Ta tafi wajen Ummanta. Tashi muje na yi miki wanka.
Hafsat ta tashi tana kallonsa ya kama hannunta zuwa ciki.
ALH. MUSA (V.O.)
Saboda haka matsala ta ta farko a lokacin bayan na kai ki makaranta, sai na nemi Lawan dan nasan shi kadai ne zai iya kurda kurdar da zai samo min wajen da zan zauna ko da shago ne.
EXT. mAJALISAR YAN ACABA (KUSA DA MASALLACI) - dAY
Sauran yan Acaba na harkokinsu, Musa da Lawan sun kebe suna tattaunawa yana bashi labarin abin da ya faru. Lawan yana saurare cikin yanayi na tausayawa da nuna damuwa.
HAFSAT
A kusa da Babur din Musa cikin kayan makaranta tana wasa.
lawan
Dama akwai wani shago irin na saukar baki da magidanta ke yi, kusan ni ke kula da gidan.
MUSA
Ni yayi min.
LAWAN
Matsala daya. Lallai ne a sati nan mu nemi kudi ko da rabi ne mu dankawa Mai gidan.
MUSA
In Allah Ya yarda za ayi kokarinsu.
ALH. MUSA (V.O.)
A wannan ranar na tarkata komatsai na na koma sabon shagon da na samu. Na mayar da hankali na wajen kokarin na cimma burin rayuwata. Na ci gaba da na cin zuwa wajen Sani Mai dab'i har dai na same shi.
INT. gIDAN SANI MAI DAB'I (CIKIN OFIS) - mORNING
ALH. SANI
Ta karanta, ta kuma ce labarin yana da ma'ana.
Musa yayi dan murmushi.
Sai dai bayan ni kaina na karanta, na ga akwai tulin gyare gyare. Don haka sai dai mu rinka zama ni da kai muna aikin tare. Saboda yarinyar da ta ke yimin typing bafillatana ce ba ta san adabin Hausa ba.
MUSA
To ai ni ban san aikin ba.
ALH. SANI
Cikin kosawa
Wai wa ya ce maka har an zo bugu. Ina yi maka maganar a tafa shi a cikin komputa tukuna, ya tashi daga rubutun hannu ya koma na littafi kafin a zo a tsara shi zuwa shafuka da kashi kashin da zai zama sannan kuma a shiga jan aikin sosai.
Musa yayi tsai yana kallonsa cikin yanayin saurare.
ALH. MUSA (V.O.)
Lallai kuwa jan aiki. Dan tun daga ranar sai da na ji kamar na hakura da zuwa gidan. Dan sai da ta kai duk lokacin da na ga dama zan je saboda rashin tsayayyen lokacin da zan same shi, har wata rana na yanke shawarar zama na jira shi komai dare na fda masa ya bani littafina na hakura.
EXT. gIDAN SANI MAI DAB'I (KOFAR GIDA) - aFTERNOON
Musa akan babur dinsa a zaune alamar ya dade a haka. Hasiya ta fito daga cikin gidan rataye da jaka, Har zata wuce sai ta gane shi ta dawo shima ya gane ta.
HASIYA
Malam kamar mun taba haduwa?
MUSA
Yana fara'a
Kwarai kuwa. Na kai ki wani waje da za kiyi interview da safe.
Tana murmushi tana kallonsa.
HASIYA
To sakamakon interview ne aka dauke ni aiki anan.
MUSA
Cikin mamaki
Da gaske anan kike aiki, amma ba mu taba haduwa ba. Ai kusan kullum sai nazo gidan, a kalla sau biyu.
HASIYA
Kullum tun takwas ina nan. Sai biyar na ke tashi. Kana da aiki anan ne?
MUSA
Wani rubutaccen labari ne na kawo za'a buga amma wata da watanni har yanzu ba a fara ko tafawa ba.
HASIYA
Wane labari ne?
MUSA
Rai da buri.
HASIYA
Cikin mamaki
Ai na karanta labarin. Daman naka ne? Amma labarin yayi dadi da ma'ana.
MUSA
Yace shi da kansa zai zauna, amma na ma kasa samunsa, balle mu zauna mu yi aikin. Shi yasa na yanke shawarar na hakura kawai ba yi zai yi ba.
Ya kawar da kansa cikin damuwa. Hasiya tana kallonsa cikin mamakin jin shine ya rubuta labarin.
HASIYA
Yanzu don Allah kai ka rubuta?
Musa ya juyo ya kalle ta cikin daurewar fuska.
MUSA
Ni da za ki taimaka ki shiga ofis dinsa ki dauko ki bani abina na tafi. Na hakura da aikin.
HASIYA
Ba na wuce karfe biyar anan, amma saboda kai gobe ka zo bayan biyar, sai mu rinka zama zuwa goma na dare har mu gama typing din sannan a shiga wani abin.
MUSA
Yayi jim yana kallonta
A gida Babarki za ta barki?
HASIYA
Yaya ta ce. Idan na yi mata bayani ba za ta damu ba.
Musa yayi shiru cikin yin ajiyar zuciya ita kuma tana kallonsa cikin murmushi.
HASIYA (CONT'D)
Ni zan tafi. Zan fa jira ka goben.
MUSA
Muje mana na kai ki.
Yana kokarin tayar da Babur din.
HASIYA
Da ka bari na hau tasi.
MUSA
Kin daina hawa acaba ne?
HASIYA
Ni awa? Kare da gudun layya.
Musa har ya tashi Babur din yana bashi wuta.
MUSA
Hau mu tafi.
Hasiya ta hau suka juya suka tafi.
INT. gIDAN SANI MAI DAB'I (wajen typing) - eVENING
Karar taba key board na tashi.
MUSA/HAsiya
Suna zaune kusa da juna. Hasiya na typing, Musa na bi da karatu da yi mata gyara a wani lokaci.
Musa ya fara hamma, Hasiya na ci gaba da typing akwai alamu na jajircewa a fuskarta. Ta dan saurara, ta waiga ta kalli Musa wanda tuni yayi bacci. Tayi murmushi sannan ta kashe computer ta tashi Musa suka fita tare.
INT. shagon musa (ciki) - nIGHT
MUSA/HAFSAT
Suna kwance, Musa na munshari alamar gajiya. Hafsat na daga gefe. Sautin kiran salla na ratsowa cikin daki.
INT. gIDAN SANI MAI DAB'I (WAJEN TYPING) - evening
Musa ya shigo wajen rike da ledar snack. Mamaki ya cika fuskarsa ganin Hasiya na ci gaba da typing abin da yasa ya duba agogon hannunsa.
MUSA
Na yi latti ko?
Hasiya na ci gaba da abin da ta ke yi.
HASIYA
Ni ce na zo da wuri.
Musa ya zo ya zauna ya ajiye mata ledar a kusa da ita.
MUSA
Ga snack nan na taho miki da shi.
Ta dan saci kallon ledar tayi murmushi
HASIYA
Madalla na gode.
Sannan ta dakata da abin da ta ke yi tana kallon Musa.
HASIYA (CONT'D)
Musa na tambayeka mana.
MUSA
Ina jin ki, Hasiya.
Yana karanta abin da ke screen din.
HASIYA
Wa ya baka labarin nan?
Ya juyo da sauri ya kalle ta cikin mamaki.
MUSA
Kamar yaya fa, Hasiya?
Fuskarta cikin nufin abin da zata fada.
HASIYA
Labarin ne yayi matukar kama da abin da ya faru a lokacin aure na.
EXT. kauye (bayan gari/rugar fulani) - dAY
Babbar ruga ce, Hasiya tana tsaye tana kula da shanunsu. Daga dan nesa da ita mahaifnta ne, Ardo Bello tare da aminnisa Atiku suna tattauna maganar hada auren Hasiya da Sadiku dan shi Atiku wanda ya dawo daga karatu.
Muryar hasiya
Sadiku kamar Yaya yake a waje na saboda amincin da ke tsakanin mahaifanmu. Amma maganar soyayya tsakanin mu babu ita, saboda ina da Bashir wanda muke soyayya tun da dadewa.
EXT. kAUYE (dandali) - eVENING
Mutane na harkokinsu, masu sana'a sun kasa kayayyakinsu.
Daga gefe dan nesa da wajen, Hasiya ce tare da Bashir suna tattaunawa cikin yanayi na alhini.
HASIYA
Ta sunkuyar da kanta tana saurarensa cikin yanayi na damuwa.
Bashir
Yana yi mata bayani cikin lallashi da kwantar da hankali.
MURYAR HASIYA
Bashir mutum ne mai hankali da nutsuwa. Irin mijin da kowace mace mai hankali zata yi fatan aurensa. Dan ko da buki na ya kusa, sai ya rinka lallashi na tare da rokon na bi zabin iyaye dan samun ribar rayuwata duniya da lahira.
INT. gIDAN SANI MAI DAB'I (wajen typing) - eVENING
Fuskar Hasiya kamar zata yi kuka.
HASIYA
Babu dadewa aka fara samun matsaloli a auren, saboda mahaifyar Sadiq ta na da wata yar uwarsa da ta ke so ya aura.
Musa yayi shiru yana kallonta cikin yanayi na tausayawa.
HASIYA (CONT'D)
Haka aka ta kai ruwa rana, har sai da mahaifina ya raba auren. Ganin Sadiq ya dawo neman Kome, sai na baro gida na taho wajen Yayata da ke nan garin, mijinta ya nema min wannan aikin kafin sakamakon ko an dauke a Jami'a ya fito.
Ta saurara kamar tana jinjina wani abu a cikin zuciyarta.
MUSA
Cikin fara'a yana kallonta
Gashi kuma daidai wajen kike rubutawa.
Ta juyo ta kalli Musa cikin murmushin karfin hali. Suka yiwa junansu murmushi, ta juya ta ci gaba da typing.
EXT. cikin gari (unguwa/kofar gida) - nIGHT
ALH. MUSA (V.O.)
Tun daga ranar sai muka zama kamar yan uwa ni da Hasiya.
MUSA/Hasiya
Musa ya goyo Hasiya suna tafe suna hira cikin nishadi, suka iso bakin kofar gidan ya sauke ta, suka yi sallama ya juya ya tafi. Hasiya a tsaye tana kallonsa cikin fara'a har ta daina hango shi sannan ta shige gida.
EXT. akan hanya (junCTION) - mORNING
Cunkoson motoci ya hadu.
Hasiya
A bayan Dan acaba ta duba agogo cikin yanayin zakuwa. Suka juya suka dauki wata hanya.
EXT. sHAGON MUSA (waje) - mORNING
Musa sun fito da Hafsat yana yi mata brush a bakin kofar shagon, sai ga su Hasiya sun biyo ta wajen. Ganin Musa da yarinyar yasa bayan sun gilma ta sauka ta sallami mai babur din ta dawo wajen sa fuskarta cikin mamaki.
HASIYA
Salamu alaikum, Musa.
MUSA
Wa alaikis salam.
Ya dakata da abin da ya ke yi ya daga kai suka hada ido. Murmushin karfin hali ya bayyana a fuskarsa.
HASIYA
Yaya haka?
MUSA
Ai anan nake.
Hasiya cikin karin mamaki tana kallon Hafsat.
HASIYA
Ban gane anan kake ba. Ina babarta?
MUSA
Yana yin Yake
Ai ba ma tare.
Fuskar Hasiya ta sauya zuwa yanayin takaici.
HASIYA
Haba Musa. Me yasa zaka sake ta? Ko dan wannan yar marainiyar yar da ke tsakaninku.
MUSA
Ya karasa gogewa Hafsat baki yana fara'a
Ita tace na sawwake mata. Saboda ba za ta iya ci gaba da jure halin kuncin da muke ciki ba.
Hasiya ta sunkuyar da kanta cikin karin takaici. Musa ya shafa kan Hafsat.
MUSA (CONT'D)
Hafsat, gaishe da Anti Hasiya.
HAFSAT
Anit Hasiya, ina kwana?
Hasiya ta dago kai ta kalli yarinyar cikin murmushin karfin hali, ta kamo hannunta zuwa gare ta.
HASIYA
Lafiya lau, Hafsat.
Suka yi musayar kallo da Musa kafin ya kama hannun yarinyar.
MUSA
Ina zuwa.
Suka shiga cikin shagon da Hafsat tare.
INT. gIDAN SANI MAI DAB'I (wajen typing) - mORNING
Computer a kunne, hular Musa da dan mukullin babur dinsa a kan teburin. Hasiya na rubutu akan wata takarda, ta gama ta ajiye gefe guda. Musa ya dawo ya zo ya zauna.
HASIYA
Na rubuta maka. Gobe kaje wajen da na kwatanta maka, kace su baka quotation din buga copy dubu uku, in yaso sai muzo mu san yanda za mu yi mu samu ni da kai mu buga.
MUSA
Hasiya a wajen wa zamu samu kudin?
Tana ci gaba da abin da ta ke yi.
HASIYA
Daga kudin acabar ka zaka rinka ragowa. Ni kuma duk karshen wata na rinka aje wani abu daga albashina. Muga abin da zamu samu.
ALH. MUSA (V.O.)
Hakika Hasiya mai kauna ta ce. Dan wannan shine digon dan ba na matakin arzikin da Allah Ya yimin.
I/E. a wani shago na kayan printing - day
MUSA
A zaune a cikin shagon gaban teburin mai shagon wanda yake rubutu akan wata takarda tare da yiwa Musa bayani daga lokaci zuwa lokaci.
ALH. MUSA (V.O.)
Washe gari a wajen na wuni sai da suka bani kididdigar abin da copy dubu uku na littafin zai ci.
INT. gIDAN SANI MAI DAB'I (WAJEN TYPING) - nIGHT
Computer a kashe babu kowa. Musa ya shigo yana fara'a.
ALH. MUSA (V.O.)
Ina doki na shiga wajen dan na fada mata yanda muka yi.
MUSA
Hasiya!
Yana nemanta ya zauna kan kujerarta. Alhaji Sani ya shigo fuskarsa cikin rashin walwala rike da wata takarda a hannunsa. Musa ya juya ya kalleshi yana kokarin gaishe shi.
ALH. SANI
Ta koma garinsu saboda an aiko mahaifnta ya rasu.
Ya mika masa takardar.
Ta ce na baka wannan.
Tsananin firgici a fuskar Musa yana mai kallon Alhaji ya mika hannu ya karbi takardar ya fara karantawa.
MURYAR HASIYA
Na tafi garinmu Musa, saboda rasuwar mahaifina da aka aiko min.
Karin tashin hankali a fuskar Musa.
Musa, rayuwa zahiri ce ka fuskance ta. Ina fatan rashi na, ba zai karyar da zuciyarka bisa kokarin cimma burin rayuwarka ba.
Ya gama karanta takardar kwalla ta cika idanunsa. Alhaji Sani ya matsa kusa da shi ya dafa kafadarsa cikin tausayawa.
ALH. SANI
Mun yi rashin Hasiya.
Ya yi ajiyar zuciya
Musa, Rai da Buri kullum tare suke.
Musa ya kalle shi yana mai share wasu hawaye da suka biyo kuncinsa ya nufi kofa zai fita.
ALH. SANI (CONT'D)
Ina quotation din?
Musa ya juyo da sauri yana kallon Alhaji cikin mamaki.
ALH. SANI (CONT'D)
Ni nace ta sa kaje ka binciko, dan kasan matsayin aikin da za'a yi. Nasan zuciya ba ta da kashi, Musa. Ya dace kasan ainihin abin da za'a kashe kafin a yi aikin.
Musa yayi shiru yana kallonsa sannan ya bude kofa ya fita.
EXT. akAN HANYA (KARAMI/BABBAN TITI) - nIGHT
Musa akan babur fuskarsa babu walwala.
ALH. MUSA (V.O.)
Ban faya yin aikin dare ba. Amma saboda matsalar da na ke ciki, na ki komawa gida da wuri. Na dade ina yawo ban sami fasinjan da zan dauka ba. Ga mai na ya kusa karewa. Ga babu kosisi a aljihuna. Saboda haka na yanke shawarar ba zan koma gida ba sai na sami fasinjan da zan dauka ko da kuwa zuwa ina ne.
Musa ya wuce cikin matsakaiciyar tafiya. Wani matashi ya tsayar da shi.
MATASHI I
Cikin yanayi na neman taimako
Ka taimaka ka kaini Sabon fegi. Nawa zan baka?
MUSA
Ya kalli saurayin
Dari biyu.
MATASHI I
Ka daure ka kaini a dari da hamsin.
Musa yayi masa wani irin kallo yana kokarin buga babur.
MUSA
Ba kowa ne zai kai ka wannan wajen a cikin daren nan ba.
Ya jefawa babur din giya zai tafi.
MATASHI I
Shikenan muje.
Matashin ya hau suka fara tafiya inda suka dauki tsawon titin cikin matsakaiciyar tafiya.
ALH. MUSA (V.O.)
Bayan mun fara tafiya, sai kawai na ji na fara da sanin daukarsa da nayi.
Babu zato ba tsammani, suka fara kokawa da Matashin suka tsaya suna kici-kici, babur din ya fadi. Wani Alhajin birni kosasshe, a cikin mota mai tsada, ta tsaya a kusa da su.
Alhaji
Kai ya haka?
Suna ci gaba da kici-kici.
MUSA
Babur di na ya ke so ya kwacemin.
ALHAJI
Kace barawo ne kawai. Rike shi da kyau na gyara fakin.
Musa ya rike matashin wanda ke ta kokarin ya kwace har boot din motar ya fara budewa kafin Alhaji yayi parking, ya fito da wani abu a hannunsa, ya fesawa matashin nan take ya suma. Alhaji ya kalli Musa wanda ke cikin mamakin abin da ya faru.
ALHAJI (CONT'D)
Kama min mu sa shi a boot. Yau a kulle zai kwana.
Suka yi kama-kama da Musa suka saka matashin a cikin boot. Alhaji ya mayar ya rufe sannan ya dauko daurin dubu hamsin ya mikawa Musa, ya karba yana mai kallon Alhaji cikin mamaki.
ALHAJI (CONT'D)
Dauki babur din ka ka tafi. Shi babur ya fito nema, ni kuwa mutum na fito sata.
Ya juya ya shiga mota, ya ja ya tafi cikin gitacciyar tafiya, ya bar Musa a tsaye cikin tsananin firgici ya bi motar da kallo kafin ya kalli kudin da ke hannunsa.
INT. sHAGON MUSA (CIKI) - nIGHT
HAFSAT
A kwance kan kuejra tana bacci.
MUSA
A zaune yayi shiru cikin tsananin damuwa. Ya rike kudin yana jujjuyawa sannan ya jawo katifa ya yar a kasa ya kwanta.
EXT. akan hanya (jUNCTION) - dAY
Musa tare da yan acaba da sauran abubuwan hawa, a tsaye suna jiran danja ta basu hannu.
HASIYA
Musa!
Musa ya waiga wajen kiran, ya hangi Hasiya a cikin wata karamar mota a gidan baya, tana daga masa hannu cikin fara'a.
Musa yayi mata murmushi, yayin da aka bayar da hannu ya tsallaka ya same ta suka gaisa suna kallon juna cikin mamaki.
MUSA
Hasiya, yaya haka?
HASIYA
Ka ganni sai yau Allah Ya hada mu.
MUSA
Hasiya yaya hakurin mahaifinki?
HASIYA
Hakuri, alhamdu lil lahi.
Fuskarta ta dan sauya
Ina Hafsat da kuma maganar littafi?
Ya dan yi jim yana kallonta.
MUSA
Hafsat lafiya, Hasiya. Maganar littafi kuwa tana nan yanda kika barta.
Hasiya tana fara'a ta bude jaka ta dauko kudi ta mika masa.
HASIYA
Ga wannan ka sha mai. In anjima ka zo ka saman a Beach Hotel.
Tana fara'a ta mika masa
Kada fa kaki zuwa, Musa. Dan nasan ka. Kada ka zaunar dani jira.
Musa ya karba yana murmushi.
MUSA
In sha Allahu zan zo. Na gode, Hasiya.
HASIYA
Ina jiranka. Direba muje.
Motar ta bar wajen cikin matsakaiciyar tafiya, Musa ya bi motar da kallo cikin yanayi na mamaki.
INT. sHAGON MUSA (CIKI) - aFTERNOON
Hafsat a zaune cikin kayan makarantar islamiyya. Musa yana gyara jikinsa, Hafsat tana kallonsa.
HAFSAT
Abba kwalliya kake yi?
MUSA
Kayana na sa Hafsat.
HAFSAT
Zaka je yawo ne?
Musa ya juyo ya kalli yarinyar ya dan yi murmushi.
MUSA
Islamiyya zan kai ki. Daga nan zan je wajen abokina.
Ya kama hannunta suka fita.
INT. hotel (cikin falo/daki) - aFTERNOON
Wayoyi biyu masu tsada da wasu takardu a zube. Musa yana zaune a falon, Hasiya ta fito da jaka sanye da hijabi/laffaya tazo ta zauna suna fuskantar juna.
HasiyA
Copy nawa muka ce za'a buga?
Ta bude jaka tana dauko check.
MUSA
Copy dubu uku.
Ta fara rubutu akan check din.
HASIYA
Yanzu za'a buga kwafi dubu talatin.
MUSA
Dubu talatin, Hasiya?
Cikin matukar mamaki. Ta mika masa check din tana kallonsa fuskarta cikin nufin abin da ta fada.
HASIYA
Buri na ne na ga na taimakawa rayuwarka, Musa.
Musa ya karba yana kallonta kafin wani karamin murmushi ya biyo fuskarta, shima haka. sannan ta sake dauko kudi ta bashi.
HASIYA (CONT'D)
Wannan ka biyawa Hafsat kudin makaranta. Amma check din sai jibi za ka je ka yi cashing.
Wasu hawaye suka biyo kuncinsa yana mai yi mata murmushi. Tayi dariya tana mayar da wayoyin cikin jakarta.
HASIYA (CONT'D)
Zan je na yi salla. Zaka dawo da safe muyi sallama?
MUSA
Mai zai hana? Na yi zaton zaki dade.
HASIYA
Mun zo sayen wani abu ne.
Suka yi sallama tana tsaye tana kallonsa cikin murmmushi har ya bude kofa ya fita sannan ta shige daki.
INT. shaGON MUSA (CIKI) - niGHT
Dakin cikin matsakaicin haske. Hafsat tana bacci.
MUSA
A zaune yana rubutu.
ALH. MUSA (V.O.)
A daren ban runtsa ba, sai da na rubuta komai a takarda, tare da tsara yanda za'a yi bukin kaddamarwa.
EXT. hotel (WAJE) - mORNING
Motar Hasiya a waje, direba na sanya jakunkuna a cikin boot. Musa ya karaso wajen akan babur din sa. Ya tsaya suna gaisawa da direban daidai fitowar Hasiya rike da jakarta tana karasa yin waya. Ganin Musa ya bayyanar da murmushi a fuskarta, ta nufo wajensa.
HASIYA
Cikin fara'a tana kallonsa
Sauran kiris ka tarar mun tafi.
MUSA
Ai kuwa da na biku.
Suka yi dariya tana mai mika masa hannu ya bata takardar da ke hannunsa.
MUSA (CONT'D)
Kinsan ko ta mecece?
HASIYA
Ai tatsuniyar gizo bata wuce koki.
MUSA
Gaskiyane.
Ya bata takardar yana dariya ta fara karantawa tana murmushi.
Sunayen wadanda zan sa ne a shafin godiya. Shine na taho da shi ki gani.
Ta gama karantawa tana fara'a ta bude jakarta ta dauko biro ta soke sunanta. Musa fuskarsa ta sauya ganin abin da ta yi.
HASIYA
Ban yi maka dan a sani ba.
Tana kallonsa cikin murmushi daidai fitowar Sadiq (35-37) cikin shiga ta matashin mai kudi ya nufo wajensu fuskarsa a sake.
Sadiq
Malam Musa, ashe ka zo.
Musa cikin kallon rashin sani yayi murmushi kafin Sadiq ya mika masa hannu suka gaisa.
HASIYA
Allah Yayi za ku san juna.
Ta kalli Musa har yanzu cikin fara'a.
Sadiq, wannan shine Musa.
Cikin raha Sadiq ya sake mikawa Musa hannu ya karba.
SADIQ
Sunana Sadiq Atiku. Nine mijinta na da, da kuma yanzu.
Musa ya cika da mamaki kafin ya wayance da yin dariya.
MUSA
Musa Abba Mai lalle. Nine marubucin littafin Rai da Buri.
Suka yi dariya gaba daya, Sadiq na kusantar motar zai shiga.
HASIYA
Ai ba a buga ba tukuna.
MUSA
In sha-Allahu kamar an buga.
SADIQ
Gaskiya fa Musa, tunda ta bayar da damar bugawar a yanzu ba.
Suka sake yin dariya gaba dayansu Sadiq ya shiga ya zauna.
HASIYA
Ko kuma muka bayar ni da kai ba.
Musa ya sake kallonta tana murmushi.
HASIYA (CONT'D)
Shi ya bani kudin buga copy dubu talatin din da na rubuta maka check jiya.
Musa yayi shiru yana kallonta cikin matukar mamaki. Hasiya taci gaba da yi masa magana. Yanayi na mamaki da alhini, har suka yi sallama, suka rabu suna masu kallon juna cikin yanayi na taba zuciya yayin da wasu hawaye suka biyo kuncin Musa.
ALH. MUSA (V.O.)
A lokacin ta ke fadamin cewa, kasancewar ita kadai ce a wajen mahaifinta, sai ta tarar ya bar mata wasiyyar cewar ya fahimci abin da yayi mata wajen hada aurenta da na Sadiq. Amma shi kansa Sadiq ya gane kuskuren da ya faru tsakaninsu. Kuma ya yi da na sanin abin da ya faru a yayin zaman auren su da shi. Don haka yana rokonta da ta cika masa burinsa na alkawarin da ya yiwa Sadiq na komawarta gare shi.
INT. gIDAN ALH. MUSA (FALO) - eVENING
Alhaji musa na share ruwan hawayen da ya biyo kuncinsa, idanunsa na kallon hoton Hasiya da Sadiq. Hafsat a inda ta ke a zaune tana kallonsa cikin hawaye.
ALH. MUSA
Tallafawar da Hasiya ta ba ni, shine tushen nasarar dukkan matsayin da na kai a yanzu.
Suka yi shiru na wani lokaci.
EXT. gIDAN MUSA (KOFAR GIDA) - eVENING
Wani Dan acaba ya tsaya dauke da Ummi II a bayan babur.
UMMI
Gashi ban chanji.
Ta mika masa dari biyu Dan acabar ya kalla bai karba ba.
Dan acaba i
Amma Hajiya tun kafin ki hau sai da nace miki bani da chanji.
UMMI
To ita kenan da ni. Ba sana'a kake ba. Ko ni kake son na nemo chanji na baka. Idan ba zaka samo chanji ba shi kenan.
Ta nufi kofa, Dan acabar ya sha gabanta. Adamu ya fito.
DAN ACABA I
Malama sai fa kin bani kudi na.
ADAMU
Kai menene ya faru, lafiya?
UMMI
Dari biyu na bashi yace babu chanji.
DAN ACABA I
Tun kafin ki hau na fada miki ba ni da chanji.
Suka fara hayaniya, Adamu ya shiga tsakani.
ADAMU
Nawa kuka yi?
DAN ACABA I
Hamsin.
UMMI
Karya ne! Taltin na ce zan baka.
DAN ACABA I
Haba malama! Tun daga sabuwar tashar zan kawo ki nan a talatin? Ba za ta yiwu ba!
Adamu ya fito da hamsin daga aljihunsa ya mika masa.
ADAMU
Bai yi tsada ba. Gashi.
Ya karba yayi godiya ita kuma tana ta masifa.
INT. gIDAN ALH. MUSA (FALO) - eVENING
Alhaji Musa a jikin kafar bene a tsaye cikin alhini.
ALH. MUSA
Wannan yasa, bayan rasuwarsu ita da mijinta, a wani hatsarin mota na wajabtawa kaina roka musu gafara a wajen Allah Madaukaki. Na mayar da su ababen tunawa a koda yaushe.
HAFSAT
Karin tashin hankali a fuskarta.
Suka yi shiru na wani dan lokaci har ya zuwa lokacin da ya juya zai koma sama yana mai share hawayen fuskarsa daidai bude kofa da shigowar Adamu cikin falon.
ADAMU
Ya kalli Alhaji cikin ladabi
Yallabai, ka yi bakuwa.
Alhaji da Hafsat suka kalli juna cikin kokwanto.
ALH. MUSA
Bakuwa? Daga ina?
ADAMU
Bata fada ba. Tace dai a yi mata sallama da kai.
Yayi shiru na dan lokaci kamar yana tunani, ya kalli Hafsat.
ALH. MUSA
Hafsat jeki ki ga wace ce.
Hafsat ta tashi suka fita tare da Adamu.
EXT. gIDAN ALH. MUSA (KOFAR GIDA) - eVENING
Ummi na zaune akan benci tana rike da littafi a bayansa an rubuta RAI DA BURI tana bin gidan da kallo, Hafsat ta nufo wajenta tana binta da kallo.
HAFSAT
Sannu da zuwa.
Ummi
Ta yi maza ta mike tana kallon Hafsat cikin mamakinta
Abbanki na nan.
INT. gIDAN ALH. MUSA (FALO) - eVENING
Alhaji Musa zai hau bene, Hafsat ta shigo.
HAFSAT
Abba.
Alhaji Musa ya tsaya kafin ya juyo gare ta.
ALH. MUSA
Wace ce?
HAFSAT
Tace sunanta Zainab.
Alhaji musa yayi shiru yana kallonta cikin shakku.
ALH. MUSA
Yaya kamanninta?
Hafsat ta kwantata masa Ummi yayin da fuskarsa ke sauya zuwa yanayi na jin haushi.
ALH. MUSA (CONT'D)
Ummi ce mahaifiyarki.
HAFSAT
Umma ta, Abba?
Ta tambaye shi cikin mamaki. Ba tare da ya amsa mata ba, ya juya zai hau kafar bene.
HAFSAT (CONT'D)
Mafi cin nasara a rayuwa, shine wanda ya yafe kuskuren da aka yi masa.
Alhaji Musa ya saurara a inda yake a tsaye zuwa wani lokaci cikin karyewar zuciya, Hafsat ta na binsa da kallo.
ALH. MUSA
Jeki ki shigo da ita. Ki yi mata duk abin da ya dace.
Ya haye sama ita kuma ta juya ta fita waje da sauri.
EXT. gIDAN ALH. MUSA (harabA) - eVENING
Ummi fuskarta cikin yanayin gazawa rike da littafin ta mike ta nufi gate zata fita.
HAFSAT
Umma!
Ummi ta tsaya kafin ta juyo ta kalli Hafsat wadda ta runtumo a guje ta zo suka rungume juna kafin littafin ya fadi kasa.
UMMI
Hafsat na guje ki tare da mahaifinki, a lokacin da kuke da bukata ta a rayuwa. A yanzu gashi na dandani sakamakon abin da na yi.
Sun gurfana suna kuka tare. Hafsat ta sunkuya ta dauko, ta duba, taga sunan littafin, ta mikawa Ummi wadda hawaye ke bin kuncinta, ta karba tana mai kallon yarinyar.
A saman bene a tsaye gindin taga hawaye na bin kuncinsa, Alhaji Musa ne yana kallonsu kafin ya mayar da labulen tagar ya rufe.
End credit
No comments:
Post a Comment