Saturday, April 7, 2012

HAUREN MAYU - Faruk Sayyadi

 A yi hakuri da yadda format din ya hargitse amma dai shi wannan shafin an tanade shi ne don karatun labarin kawai ba wai don yin nazari akan Format ba. idan ana son mai format a sanar a group sai a turo da rich text na script din.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
EXT. hauren mayu (bikin nadin sarauta) - niGHT        (opening caption to be superimpose)
Sun jeru reras a layi gwanin sha'awa, dukaninsu sanye da bante babu riga, mata cikin daurin kirji da kallabi ko kuma dai sanye da wasu kaya masu yanayi guda dake nuna alamar bikin mayu. An haske wajen ne da wutar ice wadda ke rike a hannun wani rukuni na samari dake daga bangare daya.
Dattijo
Kimanin shekaru sittin yana tsaye gaban taron yana wasu irin zantuka na surkulle. ya dora hannunsa a kan sabon Sarkin Mayu.
SaRKIN MAYU
Durkushe gaba ga dattijon kansa kasa ya rintse ido, yana saurare.
DaTTIJO
Ya cigaba da surkullen sannan ya daga murya yayi wata irin kuwwa.
Jama'a
Suka yi amshi baki daya.
Mace3
Ta ratso daga cikin taron mutane dauke da wani irin kwarkwaro ta zo ta rusuna ta mikawa dattijon nan. Sannan ta mike ta koma da baya da baya har ta bace a cikin yama.
DaTTIJO
Ya dora kwarkwaron a kan sabon sarkin mayu.
Dorawarsa ke da wuya sai wata wuta ta kama bal a gefensu.
JAMA'A
Suka yi sowa baki daya nan da nan sai kida ya barke. Aka shiga rawa da murna.
DATTIJO
Ya kama hannun sabon sarkin mayu ya mikar da shi tsaye ya nuna shi ga jama'ar, tabbatar ya zama sabon sarkin.
EXT. KAUYEN KALBO (TSAKIYAR GARI)- DAY
Yara su na wasanni a filin tsakiyar gari. Wasu na langa. Wasu na kwallon kafa. Wasu na 'yar carafke. Wasu na zaune a gindin bishiya su na wasan kasa.
A can nesa kuma, GAMBO, dan shekara 35 zuwa 40, ya na zaune a karkashin bishiya mai inuwa kan gungume ya na ta kallon yaran nan cikin tunani. Ga gyambonsa da ke kwaurinsa na dama, kuda na ta bi. A gefensa akwai mutum zaune wanda ke ta faman gyangyadi. A halin tunanin GAMBO, sai wani yaro dan kimanin shekara goma sha-uku ya zo gabanshi ya durkusa.
HAMIDU
(ya sunkuyar da kai)
Baba. Wai ka zo. Talle ya ki ya sha magani.
Nan da nan hankalin GAMBO ya dawo kan HAMIDU. Ya dan kalli yaron cikin tunani sannan ya tashi cikin hanzari. Shi ma HAMIDU ya tashi. GAMBO ya tafi cikin sauri. HAMIDU ya na biye da shi.
EXT. TSAKAR GIDA- DAY
GAMBO
Ya shigo tsakar gida a fusace cikin sauri.
HAMIDU
Ya na biye da shi.
GAMBO
Ya bi gefen tarin sharar dake zube a tsakar gidan ya nufi inda suke, ya yi bal da wani fo dake kan hanyarsa ya isa ga inda suke yana muzurai.
TALLE
Yaro dan shekara hudu, wanda ke zaune a kan tabarma da kafarshi daya a mike, daya a tankware. Sannan ya na kuka ba hawaye, a galabaice. Ga dattijuwa a gefen TALLE na hagu. A gefen dama kuma, ga LARAI nan a tsaye, da hannunta daya a kugu. HAMIDU ya tsaya kusa da ita.
DATTIJUWA
(ga GAMBO)
Yauwa GAMBO. Mun yi mun yi yaron nan ya sha magani. Amma ya ki.
GAMBO
(ya zazzare ido)
TALLE? Me ya sa ka ki shan magani, eye?
TALLE
(kuka ba hawaye)
Ni ruwa zan sha.
GAMBO
Ba za ka sha ruwan ba?...
Ya kalli dattijuwa sannan ya kalli daya matar.
GAMBO (CONT'D)
...Na ce, wannan maganin, shi zai zama ruwansa. Na ce ya daina shan kowane ruwa sai wannan maganin...
GAMBO ya zauna a daman TALLE. Matar ta matsa. Ya kalli HAMIDU ya daka masa tsawa.
GAMBO (CONT'D)
...Kai! Matsa! Kar ka fama min ciwo na.
GAMBO ya sa hannu ya dau kwanon-sha, wanda ke cike da jikakken maganin gargajiya a gaban dattijuwa. Ya kafawa TALLE  a baki. TALLE ya ki bude baki. Maganin ya na zubewa a kasa. Ran dattijuwa ya baci. Matar nan ta matso cikin nuna tausayi.
LARAI
Don Allah ka yi mi shi a hankali.
GAMBO
(ya dago kai ya kalleta)
Ke! Ko mijinki, kin ga dai yaya na ne, to bai isa ya nuna min yadda zan yi da da na ba.
DATTIJUWA
(cikin bacin rai)
Haba GAMBO.  A gaba na kake fadar haka? Kai kullum ba ka girmama yayanka?
GAMBO
(ga DATTIJUWA)
Baba. Ai Larai ce ta ke janyo masa. Kawai don ni kanin mijinta ne sai ta din ka shiga harkoki na?...
(ya koma kan TALLE)
...Kai wallahi sai ka sha maganin nan.
TALLE ya dage baya so. GAMBO ya ci-gaba da kokawa da shi.
LARAI
GAMBO! GAMBO! Kai ma sa a hankali. Ka ga daya kafar ta sa ba ta da lafiya.
GAMBO
Baba! Ki na jinta ko? Ki gaya mata ta dai na shiga harkoki na!
Nan ne LARAI ta ja HAMIDU su ka shige wani bangare na gidan. Ita kuma dattijuwa ta na ta tausar GAMBO.
EXT. GINDIN BISHIYA- DAY
Mai gyangywadi a inuwar bishiya ya na ta gyangyadinsa. GAMBO ya dawo gurin. Ya kama guri ya zauna. Ya ga mai gyangydi bai ko san da zuwansa ba. Ya sa hannu ya taba shi. Mai gyangyadi bai yi ko kotsi ba.
GAMBO
(ya dake shi)
Malam SALE? Da Allah ka tashi!
Nan kuwa MALAM SALE ya tashi ya na muttsuke-muttsuken ido.
MALAM SALE
(ya na gyara zama)
Me ne ne MALAM GAMBO?
GAMBO
Maganar TALLE ce.
MALAM SALE
Jikin na sa ne?
GAMBO
Yanayin jikinsa na sa ne duk ya rikitar da mu. Mun kasa gane ko me ne ne. Ga shi mu na ta ba shi magani. Amma har yanzu abin...
MALAM SALE
(ya katse shi)
Wai meye hakikanin abin da ke damunsa?
GAMBO
Ka ga, zazzabi ya ke yi mai dan karan zafi. Sannan wani lokaci ya yi ta sanbatu. Ga daya kafar ma ba ta aiki. Kamar ta fara shanyewa.
MALAM SALE
Wane irin magani a ke ba shi?
GAMBO
Zai wuce na gargajiya ne? Maganin gargajiya mu ke ba shi.
MALAM SALE
To. Mai zai hana ka gwada asibiti, tun da har yanzu abin ya ki ci ya ki cinyewa?
GAMBO
MALAM SALE, wani lokaci ka na ban mamaki. Ina wannan ciwo ina asibiti? Ba ka ganin har sanbatu ya ke? Watalika mayu ne. Ko kuma aljanu, domin ga kafar shi daya kamar ta shanye.
MALAM SALE
To. Allah ya sauwake. Ni dai shawara ce kawai na ba ka.
GAMBO
(ajiyar zuciya)
A to. Na dai gaya ma ka.
MALAM SALE
(gyara zama)
Amma ka san labarin SARKIN MAYU?
GAMBO
SARKIN MAYU?
MALAM SALE
SARKIN MAYU. Wanda ke a can Hauren Mayu?
GAMBO
Ina jinka.
MALAM SALE
Ina jin in dai mayu ne ko aljanu su ka shafi wannan yaro, in dai ya ga yaron, to zai warke da iznin Allah.
GAMBO
(cikin hanzari)
A wane gari ya ke? MALAM SALE?
MALAM SALE
Na ce a can cikin Hauren Mayu ya ke. Ko ba ka san Hauren Mayun ba ne?
GAMBO
O ho? Wancan hauren da na ke jin labari? Ni ka san ban taba zuwa gurin ba.
MALAM SALE
Kwarai. Wannan shi ne Hauren Mayu.
GAMBO
Ka na nufin sai an haure wannan dutsen mai kama da ganuwa?
MALAM SALE
A a. Ba neman lafiyar dan ka ka ke ba? Ba wannan ne ma tashin hankalin ba. An ce gaskiya zuwa gurin nan ya na da mutukar hadari. Ina nufin kafin ka isa gun SARKIN MAYU, akwai abubuwan hadari da mutum zai iya haduwa da su.
GAMBO
(idonshi ya firfito)
Haba?
MALAM SALE
Lallai ba ka da labarin abin da ke faruwa. Ai shi ya sa ba kowa ya ke iya zuwa ba.
GAMBO
Zan iya zuwa kuwa?
MALAM SALE
Za ka bar danka haka ne? In dai ba za ka kai shi asibiti ba, to dole ka gwada SARKIN MAYU.
GAMBO
Haka ne.
MALAM SALE
Sai dai dole ka tafi da wani ya raka ka, tun da dole da yaron za a tafi. Kuma ga wannan gyambon na ka. Shi ma ba ka je asibiti ba ko?
GAMBO
Ba wannan maganar mu ke ba. Yanzu ya ka iya raka ni?
MALAM SALE
Ban da ni. Ina da aikin gona. Me ya hana ka sami dan uwanka ya raka ka?
Su na wannan magana, sai hankalin GAMBO ya koma kan kofar gidansu.
GAMBO
(ya mike ya na nuni da hannu)
Kai! Kai!! Kar ku shiga nan! Ba a shiga nan!...
GAMBO ya yi maza ya riski ma su aikin digon maganin "polio", namiji da mata biyu, wadanda su ke kofar gidan.
GAMBO (CONT'D)
...Wai ku ba za ku gane ba ne? Ku yi sheda a gidan nan. Ba na son ku kara zuwa...
Nan ne namijin ya ce da matansu tafi. Nan su ka tafi su ka kyale GAMBO a tsaye ya na ta fada.
GAMBO (CONT'D)
...Haka kawai ku karasa min yaro? Abin da cuta kuke sa wa yara a ciki? Kun dauka ba mu sani ba?
A nan ya tsaya ya na tunanin maganar SALE ta hadarin Hauren Mayu.
EXT. BAYAN GIDA- DAY
HASSAN, dan shekara 40, sanye da 'yar shara, ya na daukan kirare daga wannan bangare zuwa wancan bangare. Ya na ta yin haka tsahon daan lokaci. Can sai ga GAMBO ya iso.
GAMBO
Salamu alaikum.
HASSAN
(bai waiwayo ba)
Wa alaikumus salamu.
GAMBO
Yaya. Barka da aiki.
HASSAN
(ya juyo)
GAMBO ne? Sannu.
GAMBO
Bara in taya ka, yaya.
HASSAN
Ai na gama aikin ma.
(ya na karkade hannunsa)
Ya ya? Lafiya?
GAMBO
Lafiya lau. Magana ce. Sai dai ta na da dan tsaho.
HASSAN
Ko mu samu guri mu zauna?
GAMBO
Hakan zai yi kyau.
Nan ne su ka matsa kusa da wata bishiya mai inuwa. HASSAN ya tsuguna sannan GAMBO ma ya tsuguna.
HASSAN
Yau na ganka a nutse haka. Shiru-shiru. Ina fatan dai lafiya.
GAMBO
Kalau, kalau. Da man maganar Talle ce. Ina nufin rashin lafiyarsa.
HASSAN
Na gane. Ya kara tsanani ne?
GAMBO
Mu na magana ne da MALAM SALE a kan rashin lafiyar, sai ya ke ban shawara da na gwada kai shi Hauren MAyu ma na gurin SARKIN MAYU ko a dace.
HASSAN
(ya kalli GAMBO)
Hauren Mayu?...To amma an ce gun ya na da wahalar zuwa...
GAMBO
(ya katse)
Shi ne na zo a kan ko za mu iya tafiya tare da kai. Ka san tafiyar mutum biyu ta fi ta daya. Musamman ma da ya ke akwai yaro.
HASSAN
(ya sun kui da kai)
Haka ne...Ba na ki ta taka ba. Amma idan mu ka rankaya gaba daya, wa zai kula da gida? Ga kuma aikin gona.
GAMBO
I...To. Haka ne. Sai dai...Amma...
HASSAN
(ya katse)
Ko ba ka fahimta ba ne? Tafiyarmu tare ba za ta yiwu ba.
Su na wannan hira sai ga wani mutum dan kimanin shekara 27 zuwa 30, siriri cikin kaya burum-burum.
GAMBO
(a zuci)
Yauwa. Ga ma gwauro nan.
Da isowarsa sai ya tsaya a gabansu cikin rusunawa.
ALTO
Salamu laikum.
HASSAN
MALAM ALTO. Kai ne haka da rana tsaka?
ALTO
(ya dan sosa keya)
Wallahi. Da man ...
HASSAN
Ko ka na so ka ga mutumin ne?
ALTO
Kwarai kuwa.wata 'yar magana ce ba mai tsaho bas kuwa.
HASSAN
(ya kalli GAMBO)
Ka dai ji abin da ke akwai. Je ka ka ganshi.
HASSAN da GAMBO su ka tashi. HASSAN ya yi tafiyarsa. Shi kuma GAMBO ya ci gaba da tsaiwaa a inuwar bishiyar nan ALTO ya tsaya tare da shi.
GAMBO
(ba fara'a)
Ina jinka.
ALTO
Ka san duk maganar ba za ta ...
GAMBO
Malam. Kai sauri. Sauri na ke.
ALTO
To. To. Ina bishiyar nan ta tsakiyar gonar da ka ba ni aro?..
GAMBO
E.
ALTO
To tsuntsaye ne su ke taruwa a kai. Kuma har sun fara yi min barna a gona. Shi ne na zo na nemi alfarma kamar yadda aka sabayi min. Ina so ne na sare ta. In ya so na sa a kawo maka itacen har gida.
GAMBO ya yi shiru na wani dan lokaci.
GAMBO
Ka je ka sare.
ALTO
(ya rusuna)
Allah ya saka da alheri. Allah ya ji kan mahaifa. Allah ya kara arziki.
ALTO ya juya zai tafi.
GAMBO
Amma ba ka ji ba...
ALTO ya juyo ya tsaya.
GAMBO (CONT'D)
...zan yi wata tafiya ta kwana daya. Ina so ka raka ni.
ALTO
(ya na dariya)
Haba MALAM GAMBO. Me zai hana? Gobe za ka tafi ko yau?
EXT. FILI- DAY
Fuskar GAMBO cikin murmushi, a lokacin da ya ke tsaye shi kaddai a katon fili. Can sai ya fara tafiya cikin sauri. Ya na kara nisa ya na kara sauri, cikin murmushi.
GAMBO
(a zuci)
Dole MALAM SHEHU ya ba ni daya daga cikin 'ya'yansa ko kuma na kwace gona ta.
Ya na ta tafiya abinsa.
EXT. KOFAR GIDAN MALAM SHEHU- DAY
MALAM SHEHU, dattijo, ya na zaune a kofar gida tare da IBRAHIM(GAGARAU) dansa, dan kimanin shekara 20 zuwa 25, a tsugune, wanda ke sanye da jeans burgijeje, T-shirt mai tsada, takalmin "Timberland" sannan da tabarau mai tsada a hannunsa ya rike ya na wasa da shi.
MALAM SHEHU
(cikin fada)
A ka  gaya maka zuwa kurmi hauka ne? Daga zuwa Ikko sau daya sai ka ce ba za ka yi noma ba.
GAGARAU
Baba. Ai na manta yadda a ke noma. Kuma hannuna duk kanta zai yi.
MALAM SHEHU
Abin da za ka ce ke nan?
GAGARAU
Kuma ga HALADU nan. Da ba na nan ai shi ya ke yi. Ni kuma ba dadewa zan yi ba a nan.
MALAM SHEHU ya sunkuyar da kai yana girgizawa don takaici. Nan ne GAMBO ya ke isowa.
GAMBO
Salamu alaikum.
MALAM SHEHU
GAMBO? Barka da zuwa.
GAMBO
Wallahi, wata 'yar matsala ce da ni. Shi ya sa ka ganni yanzu.
MALAM SHEHU
To. Sannu. Samu guri ka zauna, ko?
GAMBO
A a. Ba komai. A nan ma sai mu yi maganarmu. Ba dadewa zan yi ba.
GAMBO ya tsuguna.
MALAM SHEHU
(ya yi wa GAGARAU nuni)
Kai tafi. Je ka.
GAGARAU ya tashi zai tafi.
GAMBO
A a. Kyale shi mana. Kai da shi ai duk daya ne.
MALAM SHEHU
To.
GAGARAU ya koma gefe ya dan tsuguna.
GAMBO
Na zo neman wata alfarma ne a gurinka.
MALAM SHEHU
Haba GAMBO. Me za ka zo nema a gurina na hana ka, mutukar zan iya? Mutumin da ya ba ka aron gona ai ya yi ma ka komai.
GAMBO
(gyaran murya)
Tafiya ce ta kama ni kuma ina bukatar mataimaki. Shi ne na ke cewa ko za ka hada ni da daya daga cikin 'ya'yanka ya raka ni? Kwana daya kawai za mu yi.
MALAM SHEHU
Ba komai...
GAGARAU
(ya yi farat)
Baba, ni zan je. Wallahi ni zan je.
EXT. KOFAR GIDAN SU GAMBO- MORNING
A-kori-kura a tsaye. GAGARAU da ALTO su na tsaye a gindin wata bishiya. ALTO ya na dauke da buhu karami. GAGARAU kuma na rataye da jakar baya. GAMBO, dauke da TALLE da HASSAN su na tsaye a kofar gida su na wasu maganganu. Ga mahaifiyarsu, LARAI,wadda takewa mahaifiyar tasu magana da HAMIDU, wanda ke rike da wata tsohuwar "Ghana-must-go" a tsattsaye a kofar gidan. Can sai GAMBO ya yi sallama da HASSAN. GAMBO ya taho gurin mota. HASSAN ya na kusa da shi. GAGARAU da ALTO su ka biyo su a baya. HAMIDU ya taho da jakar a bayansu. HASSAN ya bude KOFAR GABA. GAMBO ya fara sa TALLE ciki, sannan ya shiga ya zauna kusa da shi. GAGARAU ya yi tsalle ya hau bodin motar. Shi kuma ALTO da kyar ya hau bodin. HAMIDU ya dago jakar ya miko. ALTO ya yi sauri ya karbi jakar, duk ya na rike da duhu. Sai ya ajiye su gaba daya. Direban ya shiga gaban motar. Nan ne direban ya tashi motar. Ya ba ta wuta sannan ya ja ta. HASSAN da sauran mutane da su ke gurin su ka daga mu su hannu su na cewa "Allah ya kiyaye". Motar ta tafi ta bar HASSAN DA HAMIDU a tsaye su na kallon in da ta bi. Su kuma mahaifiyarsu da LARAI, wacce ta ke hawaye su na tsaye har yanzu a kofar gida.
I/E. CIKIN MOTA- DAY
GAMBO cikin mota, a lokacin da ta ke tafiya a kan titi mara kwalta. TALLE ya na jingine da shi, ya na bacci. Direba kuma ya na ta tuki. Radio na aiki. Ba wanda ya ke magana da wani.
EXT. BODIN A-KORI-KURA- DAY
GAGARAU ya na zaune ya na sanye da "head phone". Sanna ga bakin tabarau kato ya kwama. ALTO kuma ya na ta gyangyadi a zaune. Ga rana ta fara zafi. Ga gargadar hanya mara kwalta.
EXT. TITIN KWALTA- DAY
Motar ta taho ta wuce. Ita ba sauri ba kuma ba gudu ba.
EXT. TITIN KWALTA (WANI)- DAY
Hoton hanyar kwalta. Can sai ga motar ta taho daga nesa. Ta zo ta wuce.
EXT. TITIN KWALTA (WANI)- DAY
Motar ta wuce a guje.
EXT. TITI MARA KWALTA- DAY
Motar ta na ta da kura cikin gargada.
EXT. BODIN A-KORI-KURA- DAY
GAGARAU da ALTO su na ta bacci. ALTO ya rufe kansa da kwali. GAGARAU ya rufe kansa da jaka.
I/E. MOTA- DAY
Motar ta na dosar katon dutse mai kama da ganuwa. GAMBO ya na yi wa direban magana. Direba na amsa masa, duk da ba ya kallonsa.
EXT. BODIN A-KORI-KURA- DAY
GAGARAU da ALTO su na baccinsu alhali motar ta na tafiya.. Ba su sani ba sai kawai mota ta tsaya cak. Nan-da-nan su ka farka firgigit. su ka tashi su na dube-dube.
GAGARAU
Anzo? Mun zo?
ALTO
(ya na muttsuke ido)
Ina jin munzo.
GAMBO ya bude kofar mota ya fito. Sannan ya leka ya daauko TALLE ya rungume shi. Nan GAGARAU ya dau jaka jakarsa ya rataya a baya, ya na mai mikewa. Ya dira waje daga bodin. Shi kuma ALTO ya na ta kici-kici da buhu da "Ghana-must-go". Da kyar ya sauka daga bodin motar. A lokacin GAGARAU ya kame don mamakin dutsen da ya gani a gabansu. Shi ma ALTO ya tsaya ya na kallon sarautar Allah. Mota ta yi ribas. Ta buda musu kura. Ta tafi. Ta bar su nan su na kallon dutse.
EXT. BAKIN DUTSE- DAY
Babban dutse. GAMBO, wanda ke dauke da TALLE ya zo ya tsaya a bakin dutsen. Ka na iya jin karan mota kadan-kadan ta na barin gurin. GAGARRAU da ALTO su ka zo su ma su ka tsaya su na kallon dutsen. Duk sama su ke kallo don su ga karshen dutsen. ALTO ya na ta fama da kaya niki-niki. Can sai su ka fara maganganu.
GAGARAU
Ni gaskiya ba a gaya min nan zan zo ba.
ALTO
Haba. Ni ma fa na ga sai tafiya mu ke yi. Na ce sai ka ce wadanda za su bar duniya.
GAMBO
(ya kalli ALTO)
Wallahi in ka sa ke magana zan kwace gonata. Kuma ka buda jakata ka dauko igiya.
ALTO
(ya sa hannu a baki)
To, na yi shiru, wai yaro ya ga kara.
Ya bude jakar GAMBO ya dauko igiyar. Ya mikawa GAGARAU. GAGARAU ya karba.
GAMBO
Kar ka ban kunya ma na. Wanda ya ke zuwa kudu ci-rani, me ne ne bai gani ba. Tafiyar kwana daya da rabi ce kawai. Muna tsallake dutsen nan shi ke nan wahalar ta kare.
Nan ne GAGARAU ya juyo ya yi ajiyar zuciya. Ya rataya igiya a wuya sannan ya daga kai ya kalli tsahon dutsen. Sai ya ke nunawa GAMBO wani abu a saman. Duka su ka hadu su na shawarwari. Nan GAGARAU ya sunkuya ya na kwance takalminsa.
EXT. KAN DUTSE- DAY
GAGARAU a makale a jikin dutsen ya na hawa da igiya da takalmasa a rataye a wuyansa. GAMBO da TALLE da ALTO kansu ya na sama su na kallon shi. Can ya isa saman dutsen. Sai ya zuro igiyar. Su ka kama. A ka daurawa TALLE  kirjinsa, bayan an yi masa gunzugu na tsummma a cikin nasa. GAMBO ya dauke shi a baya sannan ya kama dutsen a hankali har ya isa sama. Sannan su ka sake zura igiyar. ALTO ya kama ya daura a kayansu na buhu da Ghana-must-go. Sannan ya daura igiyar a jikinsa. Ya kama dutsen ya hau. Duk su ka tsattsaya  su na haki. Can sai su ka juya.
EXT. DUTSEN HAUREN MAYU (TA CIKI)- DAY
GAMBO, wanda ke dauke da TALLE, GAGARAU, wanda ke sa tabaranshi baki da kuma ALTO, wanda ke fama da kayansaa da na GAMBO, su na tsaye a kan dutsen. Can sai su ka gangara su na sauka wata matattakala.
EXT. FILI- DAY
Su na tafiya a wani fili. Ba komai sai yashi. Ga rana ta kwalle. Gambo ya lullubawa TALLE da abin sallah a kansa. GAGARAU a yanzu ya na sanye da "face cap". Shi kuma ALTO ya sa malafa. GAMBO kuma sai gumi ya ke. Can tafiya ta yi tafiya, sai GAMBO ya tsaya ya na bude kan TALLE.
GAMBO
(ya na taba jikinsa)
Zo ku ji. Jikinsa zafi.
Nan da nan ALTO ya zo ya taba jikin TALLE. Sai yai sauri ya dauke hannnunsa. A nan ya ajiye kayan da ya ke dauke da su. Ya bude buhunsa ya dauko ruwa ya kwarawa TALLE a jiki. Take ya karar da ruwan da ke jarkar.
GAMBO (CONT'D)
Akwai wani ruwan ma a jakata.
ALTO
Ina ji ma wannan ya isa.
(ya kara taba jikin)
Kai. A kara ruwan nan.
ALTO ya sa hannu ya bude jakar GAMBO ya dauko ruwa a jarka. Ya jika abin sallar, ya rufa a kan TALLE. Sauran ruwan kuma ya bawa TALLE ya sha. Sannan su ka ci-gaba da tafiya. Haka har su ka yi nisa.
EXT. BISHIYOYI- DAY
GAMBO ya na jan GAGARAU da ALTO sallah a cikin wani guri mai inuwa sabo da bishiyoyinsa. Ga TALLE can a zaune a gindin wata bishiya da kosai a gabanshi. Ya dau daya ya na ci da kyar. A gefensa ga roba nan ta ruwa cike da maganin gargajiya jikakke. Ga moda nan cike da maganin. Lokacin da su  ka idar da sallah, sai ko GAMBO ya zo kusa da TALLE.
GAMBO
Ya ba ka ci? Ka sha maganin kuwa?
TALLE ba ya ko magana. GAGARAU kuwa ya na ta cin kuli-kuli. Haka ma ALTO, ya na cin kuli-kuli. Can sai GAGARAU ya kalli ALTO.
GAGARAU
Ni da na san haka tafiyar nan take, da ban biyo ku ba.
ALTO
Ni ce min ya yi, za mu yi tafiya ta kwana biyu. Amma na tanaji ruwa sabo da ruwan rijiyoyin kauyen nan a kakkafe su ke...
GAGARAU
(ya katse)
Wai kuwa ka san in da za mu tafi?
ALTO
Sai dai ka tambayi MALAM GAMBO.
GAGARAU
(ya kalli GAMBO)
MALAM GAMBO. Har yanzu akwai sauran tafiya ne?
GAMBO
(bai dago kai ba)
Ba ka ganin jikin yaron nan ya kara zafi?
Nan da nan ALTO ya tashi ya isa gurin GAMBO. Ya taba jikin TALLE.
ALTO
Jikinsa ya kara zafi. Ko za a sake zuba masa ruwa?
(ya kalli GAGARAU)
Ko za ka ba da ragowar ruwanka a zuba masa a jikinsa?
GAGARAU
A a. Gaskiya. Ka na ganin yanzu naci kuli-kuli ban sha ruwa ba. Kuma tafiyar nan ban san lokacin da za ta kare ba.
Fuskar GAMBO ta canza da bacin rai.
ALTO
Haba GAGARAU, ba ka ganin ni ma na ci kuli-kulin? Ba za mu bar yaron nan haka ba.
ALTO ya taso ya dauki ruwan da ke kusa da GAGARAU. Ya koma gurin TALLE.
TALLE
Ruwa! Ni ruwa zan sha!
ALTO ya ba wa TALLE ruwa a baki. TALLE ya sha. Ya sha har ya koshi. Sannan ALTO ya zubawa TALLE ruwan a fuskarsa. Ya dau jarkar ya kai kusa da GAGARAU ya ajiye. GAGARAU ya taba jarkar. Ya ji ba komai. Sai ya buge ta da hannu ya na kun kuni. GAMBO ya ci-gaba da kula da TALLE.
EXT. YASHI- DAY
GAGARAU ya na tafe a gaba. GAMBO ya na biye ya na dauke da TALLE. ALTO ya na baya. Duk sun galabaita. Ga rana. Ga rashin ruwa. Can sai ALTO ya zabura a guje. Ya yar da kaya.
ALTO
(ya kwalla)
Rijiya! Ruwa! Alhamdu lillahi.
ALTO ya shige GAMBO a guje. Ya tarar da GAGARAU. Shi ma GAGARAU ya diba a guje har ya wuce ALTO, da jakarsa rataye a baya.
EXT. RIJIYA- DAY
GAGARAU ya na gudu ya wuce ALTO sosai. Ya fuskanci rijiya. GAGARAU ya sa hannu a jakarsa ya dauko igiya a halin ya na gudu. Ya isa bakin rijiyar. Ya ja ya tsaya. A wnnan lokacin ne su ka ji wani irin kara kamar na kwari. Nan kowa ya tsaya ya yi cirko-cirko. GAGARAU na bakin rijiya. ALTO da GAMBO,wanda ke rike da TALLE su na baya. Sun fara rufe kunnuwansu sabo da  kara. Nan ne wasu kwari su ka fito su ka mamaye ko'ina tsakanin GAGARAU da  su ALTO. ALTO ya na so ya taho amma kwari sun hana shi. GAGARAU ya na kallon rijiya ya na kallon kwari. Ga igiya a hannunsa amma ba guga. GAMBO da TALLE sun yi tsuru-tsuru.
GAGARAU
(ya ce da ALTO da karfi)
Jefo min jarka.
ALTO
(ya kwalla)
Mun bar jarkokin mu a baya.
GAGARAU
(ya kwalla)
Jefo min wani abu na yi guga.
GAMBO
(ya kwalla)
Akwai kwano a cikin jakata.
Nan ne ALTO ya fara bibbincika kayan GAMBO a tsaye, saboda tsoron kwari. Kuma ya na ta tsalle-tsalle ya na tattaka kwarin. GAMBO ma ya na tattake kwarin. ALTO ya binciko langar kwano. Ya yi sauri ya jefawa GAGARAU langar. GAGARAU ya yi tsalle ya cafe lamgar. Ya yi sauri ya daddaura igiyar a hannuwan langar, sannan ya zura a rijiyar. ALTO ya daka tsalle ya haye wata bishiya. Shi kuma GAMBO ya na ta tsalle ya na take kwarin. Yaron ya na cikin tashin hankali. GAGARAU ya na ta jujjuya igiyar don gugar ta kwanta. Can sai ya ji kamar ta makale.
GAGARAU
(da karfi)
Ta makale! Wayyo Allah ta makale!
A wannan lokaci ne wani kara mai kamar na gyare da kuma gurnani ya fara fitowa daga rijiyar. Da jin karar, duk kwari su ka gudu. TALLE ya sa kuka. Sai ga ruwa nan ya na diga ta wandon ALTO. Kokarin GAGARAU da ya janyo guga daga rijiya sai ta tsinke. Ya tafi taga-taga ya leka rijiyar. Ya sa kansa ya leka. GAMBO da ALTO su ka yi sak. GAGARAU ya dan bata lokaci kan sa a rijiya. Can sai ya fito da kansa. Ya dawo da baya a guje. Nan ne karan ya kara fitowa da karfi. Duk sunka tsaya kallon rijiyar. Can sai wani abu ya fito daga rijiyar kato ya yi sama. Duk su ka bi shi da kallo. Ashe katuwar maciiiya ce. Kusan rabin jikinta ya na waje a sama. Macijiyar ta yi ruri ta yi kara ta na mai zallako da harshe. GAGARAU ya rike guntuwar igiyarsa ya na wulwulawa. ya na kokarin kai mata duka. Nan macijiya ta zallako da harshe kamar za ta lashe GAGARAU. Ya ja da baya. A wannan hali ne, sai su kaji "daram", karan bindiga, kuma ya sami macijiya. Nan ne ALTO ya fado daga kan bishiya don tsoro. GAGARAU ya waiga ya ga daga ina harbin ya taho. Sannan ya kalli macijiyar, ta na wani irin kara. GAMBO a tsorace ya ke da yaro a rungume. Nan ne a ka kara harbin macijiyar. Macijiyar ta yi sama sannan ta koma cikin rijiyar, ta na juye-juye. Haka su ka yi ta jin kara har tsahon wani lokaci. can sai su ka ji shiru. Duk su ka yi ajiyar zuciya. GAGARAU ya kalli in da harbin nan ya taho. GAMBO da ALTO, wanda ke kokarin daukan kaya, su ma su ka bi gurin da kallo. Kawai sai su ka hangi bindigar gargajiya ta bayyana a hannun mace budurwa, 'yar shekara 18 zuwa 20, wacce ke sanye da atanfa tare da dammara ta fata. Akwai dan kwali a kanta.. Ta taho tinkis-tinkis har gaban GAMBO da ya ke rike da TALLE. sai ta kalli yaron.
BUSHARA
(ta cewa GAMBO)
Ya ya sunanshi?
(ta taba TALLE)
Ya jikinsa zafi?
GAMBO
(cikin magana a hankali)
Ba si da lafiya ne.
BUSHARA
(ta karbi TALLE)
Akwai hadari tafiya da yaro a gurin nan.
GAMBO
Wa ce ce ke?
BUSHARA
(ta na murmushi)
Suna na BUSHARA.
Sai su ka ci-gaba da tattaunaawa mai dan tsaho tare da su gaba daya.
EXT. HANYA (DAJI)- DAY
BUSHARA na tafiya dauke da TALLE. GAMBO ya na kusa da ita. Fuskarsa sak. Ba fushi sann ba fara'a. GAGARAU da ALTO su na biye da su a bayansu. ALTO niki-niki da kaya. BUSHARA ta kalli GAMBO cikin fara'a.
BUSHARA
Mahaifina maharbi ne. Ya kan yi wata shida a gun farauta. Amma yanzu ya kusa dawowa.
GAMBO
Farautar me ya ke yi? Macizai?
BUSHARA
(ta yi dariya)
Farautar manyan namun daji.
GAMBO
Na ga alama.
BUSHARA
Shi ya sa na iya harbi. Tun ina karama na koya...Mun ma zo gida.
A gabansu ga wata bukka mai 'yar danga a gefenta. Ga wata tsohuwa a zaune, ta tsiro mu su ido. Da bishiya a kofar bukkar. Sannan ga hauren giwa guda biyu, an kakkafe a kasa. Duwatsu da guma-gumai ne kuwa abubuwan zama. GAGARAU na ta kalle-kalle. Su ka isa gurin bukkar. GAMBO ya rusunaawa dattijuwar nan.
GAMBO
Sannu baba. Ina yini?
Tsohuwa kawai ta kallee shi. Sai ta tashi ta shige cikin bukkar, ta bi BUSHARA ke nan wacce ta shige da TALLE ciki. GAMBO ya canza fuska don mamaki.
GAGARAU
(ya ce da GAMBO)
Ya ba ka santa ba za ka barta ta shiga da TALLE ciki? Ka san me za ta yi ma sa?
GAMBO
Da za ta cuce mu, da ta cuce mu tun farko. Cetonmu ma ta yi.
GAGARAU
Ka sani ko gadar zare ta shirya ma na?
GAMBO
Haba! Dan ka ne ne? Ai ba dan ka ba ne, ko? Ka kyale ni!
Nan BUSHARA ta fito da ruwa a kwarya. Nan da nan kuwa ALTO ya zabura ya wafce ta. Ya kafa kai. Ya sha. Ya sha. Ya zuzzuba a fuskarsa. GAGARAU ya na kallo kamar bai amince ba. Can shi ma sai ya zabura ya kwace kwaryar. Ya sha. Ya zuzzuba a jikinsa. Sai haki ya ke yi shi da ALTO. GAMBO da BUSHARA su ka tsaya su na kallonsu. Su na dariya.
BUSHARA
Kai ma tsaya a kawo ma ruwan.
GAMBO
Ya TALLE? Jikin na sa, da saukin zafin ice ko?
BUSHARA
(ta juya zuwa bukka)
Zo ka gan shi...
GAMBO ya bi ta a baya har zuwa cikin bukkar. Sai ga TALLE ya na kwance ya na bacci.
BUSHARA (CONT'D)
(ta na diban ruwa a randa)
...Bacci ya ke. Zazzabin ya sauka.
GAMBO
Madalla. Sai dai kin san a kan hanya mu ke.
BUSHARA
(ta miko ma sa ruwa)
Haba?... ...Sai kun bar yaron nan ya huta. Ya sha wahala. Kuma gashi akwai kawa-zucin rabuwa da uwarsa.
GAMBO
(ya sha ruwa)
TALLE bai san uwarsa ba. Ta na haihuwarsa ta mutu.
BUSHARA
Allah Sarki. Ashe maraya ne...Shi ya sa ku ke kiransa TALLE? To don Allah ku kwana a nan. Ku dan huta zuwa gobe sai ku karasa. Ai kun kusa zuwa tsallaken.
GAMBO
(ya mika mata koko)
Amma ni ina tsoron dajin nan.
BUSHARA
(ta karba)
Kar ku ji komai. Kamar a gida ku ke.
GAMBO ya juyo ya na murmushi ya fito daga bukkar. Ya tarar da GAGARAU da ALTO sun tsuro masa ido. Sai su ka kalli junansu sannan su ka samu guri su ka zauna.
EXT. GINDIN BISHIYA- NIGHT
GAMBO ya na zaune a kan dardumar sallar. GAGARAU kuma ya na zaune a kan gungume. ALTO kuma na zaune a kasa. Nan ne BUSHARA ta ke zuwa da kwano a rufe, ta ke ajiyewa a gaban GAMBO. Ta yi murmushi sannan ta juya zuwa bukka. GAMBO ya tashi ya bi ta.
GAMBO
BUSHARA? Ya jikin TALLE?
BUSHARA
(ta juyo)
Af. Bacci ya ke tun dazu da ya ci abinci. Ya na ta samun saukin zazzabin.
GAMBO
(cikin sanyin murya)
BUSHARA, na gode. Na gode BUSHSARA.
BUSHARA
(ta yi fari)
Hnm.
GAMBO
(ya dan zabura)
Kin ga.
BUSHARA
(ta tsaya ta jayo)
Me ne ne?
GAMBO
(kasa-kasa da magana)
Da Allah wace ce wannan dattijuwar da ku ke tare?
BUSHARA
(ta dan yi tunani)
Kanwar...mahaifiyar babata ce.
(ta kalle shi)
Me ne ne?
GAMBO
A a. Ba koai. Kawai na ga ya kamata na sani sabo da irin taimakon da ku ke yi mana.
BUSHARA ta juya ta shige bukka, shi kuma ya dawo cikin su GAGARAU da ALTO. Su ka tsura ma sa ido.
GAGARAU
Ni fagida zan koma don ban amince da wadannan matan ba.
GAMBO
Amma ka san zan iya kwace gonar da na bawa babanka aro,ko?
GAGARAU
Wannan tsakaninku. Da man na dauka tafiyar ba haka ta ke ba.
ALTO
GAGARAU, a yi hakuri. Ko don tsoho ai ka hakura a ci-gaba da tafiyar nan.
GAGARAU
To ya mu da za mu tafi gurin mai magani, sai mu bige da zama a gun mutanen da ba mu san su ba? Watakila ma aljanu ne.
GAMBO
(ransa a bace)
Kyale shi ya tafi.
Nan kuwa GAGARAU ya sa takalminshi sannan yadau jakarshi ya saba a baya. Ya tsaya a kansu.
GAGARAU
Allah ya ba da sa a. Gwara na koma gida na yi noma.
GAGARAU ya juya ya tafi har ya kule cikin duhu. ALTO ya yi shiru ya na tunani.
GAMBO
A wace gonar?
ALTO
(a zuci)
To. Ni kuma sai yadda Allah ya yi da ni kawai.
GAMBO ya kwanta abinsa a kan dardumar Sallah ya na tunani. Sai bacci ya kwashe shi.
EXT. KAN DUTSE MAI KYAU- DAY
GAMBO da BUSHARA su na kan wani dutse mai kyau su na waka. Sun yi shiga mai kyau.
EXT. KAN GADA- DAY
GAMBO da BUSHARA su na tafiya a kan wata gada da ta ke kan wani rami. Su na ta waka.
EXT. KAN FARFAJIYAR GIDA MAI TSAHO- DAY
GAMBO da BUSHARA su na kallon kasa dawatsu. Sun ci-gaba da waka.
INT. CIKIN WATA FADA- DAY
GAMBO da BUSHARA da TALLE su na tsaitsaye a cikin farin ciki. Su na waka. A nan su ka gama wakar.
EXT. GINDIN BISHIYA- NIGHT
GAMBO da ALTO su na bacci. Can sai motsi ka ke ji kamar wani mutum ya zo gurin. Nan ne ALTO ya farka. Idonsa a bude amma ya kasa tashi. Can dai ya tashi ya na dube-dube. Bai ga kowa ba. Can sai ya tashi GAMBO GAMBO ya tashi.
GAMBO
Me ne ne?
ALTO
(a rada)
Motsi na ke ji.
GAMBO ya tashi ya na tafiya a hankali a gefen bukkar.
GAMBO
(a hankali)
Wa ne ne? ...Wa ne ne?
Ba a yi magana ba.
GAMBO (CONT'D)
Wa ne ne?
ALTO
(kasa-kasa)
GAMBO, kai shiru. Ka sani ko ba mutum ba ne?
Nan ne GAGARAU ya ke fitowa ta cikin duhun dare. Ya tsaya a gabansu, su kuma su na kallon shi.
GAMBO
(tsaki)
Ya ka dawo?
GAGARAU
Ai wallahi sabo da baba kawai na dawo. Don na sanka ba ka da tausayi. Za ka iya kwace gonar da ka ba shi aro. I ma na. Don mai tausayi ba zai iya sa mu cikin wannan garari ba.
ALTO ya kalli GAGARAU sannan ya kalli GAMBO wanda kawai ya ke tsaye ya na cije baki.
ALTO
(ya bushe da dariya)
Ba kuwa wani abu ka gani ba? Kai dai ka fadi gaskiya.
GAGARAU ya kai wa ALTO duka. ALTO ya ci-gaba da dariya. GAMBO ya kwanta kawai ya kalli sama har bacci ya dauke shi, alokacin su kuma GAGARAU da ALTO su na ta ce-ce-ku-ce.
EXT. GINDIN BISHIYA- DAY
GAGARAU ya na yin sallah a kofar bukka. ALTO ya na harhada kaya. GAMBO ya na zaune a kan wani dutse ya sunkuyar da kai. GAGARAU ya yi sallama. Ya tashi tsaye. A dai dai wannan lokacin BUSHARA ta ke fitowa dauke da TALLE. Ta kalli GAGARAU.
GAGARAU
Sai yanzu kai sallah?
GAGARAU ya kalleta kawai ya na motsa baki kamar mai addu'a.
GAMBO
Ke ma kya fada...Ina kwana, BUSHARA?
BUSHARA
Lafiya lau. Kun tashi lafiya?
GAMBO
Alhamdu lillahi...To lokaci ya yi. Za mu tafi. Na ga yaron ma ya dan yi kuzari.
BUSHARA
A. Sosai. Me ya sa ma ba za ku bar shi a nan ba Ku je ku karbo maganin?
GAGARAU
Mu yi tafiya biyu ke nan? Haba. Da Allah ku zo mu tafi.
BUSHARA
Watalika ba ku san SARKIN MAYU ba ne. Shi ba ya bukatar dole sai an je da mara lafiya. Takalmin TALLe kawai, in a ka kai masa zai iya yi masa magani, ko a ina ya ke a duniya.
GAMBO
Haba?
ALTO
Tabbas akwai mutane ma su irin wannan baiwar. To amma...
GAMBO
(ya katse)
In dai haka ne, a iya barinshi a nan. Yanzu ba ni takalminshi.
BUSHARA
(ta yi dariya)
Kai amma ka kyauta. Ka ga kafin kudawo yaraon nan ya kara hutawa sosai. Haka a ka ke son uba ya zama mai tasayin 'ya'ya.
GAMBO ya yi murmushi. BUSHARA ta sa hannu ta ciro takalmin TALLE ta jefawa GAGARAU. GAGARAU ya cafe ba shiri. Ya kalleta. Ita kuma ta bata ranta.
GAMBO
To mun tafi. Don Allah ki kula da TALLE.
BUSHARA
Haba. TALLE fa kamar da na ne. Ai kamar a gida ya ke. Ni ma ina tuananin na sami da kamarshi nan gaba.
GAMBO
Allah ya sa...Allah ya kaddara saduwarmu.
BUSHARA
Amin. Allah... Sai kun dawo.
Nan ne GAMBO ya ja-gaba ALTO na biye shi sannan GAGARAU, wanda bai bi su ba sai da ya dan tsaya ya na kallonsu. ya na rataye da jakarsa a baya. Can sai ya bi su. ALTO da GAMBO kuwa ba su dauko kaya ba sai abin ruwa da ALTO ke rike da shi.
EXT. HANYA (DAJI)- DAY
GAMBO na tafiya. GAGARAU da ALTO su na biye da shi. GAGARAU ya kara sauri ya tarar da GAMBO.
GAGARAU
Ni fa ban yarda da BUSHARA ba.
GAMBO
(da fada)
Me ya sa ka ke haka ne?
GAGARAU
Gaskiya na ke gaya ma ka. Ga kuma wata irin tsohuwa.
GAMBO
Wannan matar kanin...ka ga na manta..kanin babarta ne. Kaka ce dai kawai a gunta.
GAGARAU
Kai dai kawai son BUSHARA ka ke.
ALTO
(ya sa baki)
Haba GAGARAU. Ba fa sa'anka ba ne.
GAGARAU
Ai gaskiya na fada.
GAMBO ya nuna bacin rai a fuskarsa. Can sai ya yi murmushi. Ya kalli ALTO.
GAMBO
(ya kira ALTO da hannu)
Zo ka ji. In na ganin kai za ka fi fahimta ta.
ALTO ya matsa kusa da GAMBO.
GAMBO (CONT'D)
(ya na murmushi)
Jiya na ganni a mafarki a gurare ma su kayatarwa. A gurare ma su ban sha'awa. Kamar ba a duniya ba. Ko kuma ka ce aljannar duniya.
ALTO
(ya karfafawa)
Daga ji wannan mafarkin alheri ne.
GAMBO
(ya na murmushi)
Amma ba ni kadai ba ne... Ni da BUSHARA ne. Sannan ga TALLE a kusa da mu. Kai ka ce mata da miji ne.
ALTO
(ya kau da kai)
To. Allah ya zaba abin da ya fi alheri.
GAMBO
Ai wannan shi ne alherin.
Su ka ci-gaba da tafiya har su ka kule. GAGARAU kawai kallonsu ya ke wanda shi ne a bayansu.
EXT. MAKABARTA- DAY
GAMBO da ALTO su na tafiya a cikin daji. GAGARAU ya na biye da su. ALTO bai sani ba sai ya taka wani kabari. Ashe makabarta ce. Su dan yi nisa sai kawai wani kwarangwal ya fito daga cikin kabarin. Karangwal ya biyo su. Can sai ALTO ya waiwayo ya ganshi. Nan kuwa ya sa ihu sannan ya zura a guje. GAMBO ma ya bi shi. Shi kuma GAGARAU ya tsaya. Ya dauki wani itace a gefen hanya. Ya tsaya su ka dinka rigima. Su GAMBO sun kule. GAGARAU kuwa ya yi ta rigima da kwarangwal har tsahon lokaci.
EXT. HANYA (DAJI)- DAY
GAMBO da ALTO su na tsere. Wannan ya wuce wancan, wancan ya wuce wannan. GAMBO ya na gudu ya na duba kafar shi sabo da ciwonsa. Har su ka iso gurin wata rijiya. Su ka tsaya su na haki. GAMBO ya na duba ciwonshi ya na dan yi masa firfita da hannu. Can sai ga GAGARAU nan ya taho a hankali ya na dan waige-waige. Har ya iso gurinsu. Ya tsaya tare da su ya na haki, amma ba sosai ba. GAGARAU ya kalli rijiya. Ya tsaya tsai ya na kallonta. Sai ALTO ya yi murmushi.
ALTO
(ga GAGARAU)
Za ka sha ruwa ne? Ga guga.
GAGARAU
(ya dago kai)
Wa ya gaya ma ka ina jin kishin ruwa?
Ya  yi tsaki. ALTO da GAMBO su ka koma gefe su na gintse dariya.
EXT. BAKIN RUWA- DAY
GAMBO, ALTO da GAGARAU su na tafiya a galabai ce. Sun yi kura. Can sai su ka hango wani ruwan kogi. Nan ne su ka tsaya su na kallon ruwan. Su ka lura ashe akwai wani kwale-kwale a gabar ruwan ta in da su ke. Nan ne su ka ci-gaba da tafiya har su ka isa gurin jirgin. GAGARAU ya gangara ya jawo jirgin ya gyara shi yadda za a iya hawa. GAMBO ya hau sannan ALTO. GAGARAU ya cire takalminsa 'Timbeber land' sannan ya shiga ruwan ya tura jirgin sannan ya hau.
EXT. CIKIN RUWA- DAY
Su na cikin kwale-kwale. GAGARAU ke tukawa da sanda a can baya. GAMBO ya na zaune a gaba sannan ALTO a bayansa. Sun fara ganin hayaki ya na turnuke gurin.
EXT. CIKIN RUWA(WANI)- DAY
Har yanzu su na cikin ruwan amma sun yi nisa yanzu. Sai dai ga wasu duwatsu a warwatse cikin ruwa da wuta a kan kowanne ta na ci a hankali. Hayaki a gun sama da kasa. Su na ta kalle-kalle cikin tsoro. GAGARAU ya na ta tuki ba abin da ya dame shi. Can sai ya sa hannu a ljihu ya dauko tabaransa ya kwama a fuskarsa. Sannan ya ci-gaba da tukinsa har su ka kule.
EXT. GABAR RUWA- DAY
GAMBO, ALTO da GAGARAU sun iyo gabar ruwa. GAMBO da ALTO su ka fito. Sannan GAGARAU ya dauko takalmansa ya fito a bayansu. Su ka tsaya shi ya na sa takalmin a tsugune. Su kuma su na kallon gabansu. GAGARAU ya gama daura takalmi. Ya mike. Nan ne su ka hangi wani kauye can nesa mai manya- manyan rumbuna. GAGARAU ya yi ajiyar zuciya.
GAGARAU
(ya kalli GAMBO)
Mun zo ne?
GANBO ya girgiza kai cewa "e". Nan GAGARAU da ALTO su ka yi da dariya ta farin ciki. A wannan hali ne wani mutum ya zo wucewa. Sai GAMBO ya tsayar da shi su ka gaisa. GAMBO ya tambaye shi, shi kuma ya ba da amsa tare da yi masa nuni da hannu zuwa cikin kauyen. Shi kuma GAMBO ya bi in da ya nuna da kallo ya na girgiza kai. GAMBO ya yi sallama da mutumin. Mutumin ya shige ya tafi.
EXT. KOFAR GIDAN SARKIN MAYU- DAY
GAMBO, GAGARAU da ALTO suna tafiya su na kalle-kalle. Su na dagawa duk wanda su ka gani hannu. Duk da GAGARAU, wanda ke sanye da tabarau, bai cika daga hannun ba. Jim kadan su ka iso kofar gidan SARKIN MAYU. Ba su yi aune ba sai su ka ga mata biyu sun fito daga gidan da riguna da kayan aikin digon magani na "polio". Su ka wuce su kuma su GAMBO su ka bi su da kallo. Can sai ga wani babban mutum mai matsakaicin tsaho, kamar dan shekara arba'in zuwa hamsin, sanye da rigar saki, shi ma ya fito daga gidan. Da ya ganinsu a tsaye, sai ya karaso gurinsu.
SARKIN MAYU
(yana mika musu hannu)
Sannnunku da zuwa.
GAMBO
Yauwa. Sannu...A. Nan ne?...Mu na tambayar gidan SARKIN MAYU ne.
SARKIN MAYU
Nan ne. Kwarai. Na san kun sha tafiya. Ya hanyar.
GAMBO
Mun gode Allah. Mun zo ne a kan wata matsala.
SARKIN MAYU
(ya na yin nuni da hannu)
To sai mu matsa daga inuwa ko?
GAMBO
Ba komai. Madalla.
SARKIN MAYU ya wuce gaba. Su kuma su na biye da shi. GAGARAU ne a karshe. Ya na tafiya a hankali. Su ka zazzauna a kan tabarma karauni. GAGARAU bai cire takalmansa ba. Ya bar kafafuwansa kan kasa.
SARKIN MAYU
(ga wasu yara su na wasa)
Kai Ibrahim, jeka ka samo mana ruwa,ruwan sha.
Yaro ya tafi a guje ya shige gidan SARKIN MAYU.
EXT. INUWAR BISHIYA- DAY
GAMBO da ALTO suna zaune suna dan firfita. Shi kuma GAGARAU sai shan ruwa ya ke. Yanzu ya gama. Ya ajiye kwanon ruwan a gabansa. Ba komai a ciki. SARKIN MAYU ya gyara zama.
SARKIN MAYU
Me ke tafe da ku?
GAMBO
(ya gyara zama)
To...Maganar rashin lafiyar yarona ce ke tafe da mu. Amma...Ko da yake...In yi tambaya?
SARKIN MAYU
Haba. Yi ma na. Mene ne?
GAMBO
(ya gyara zama)
A lokacin da mu ka iso sai na ga wani abu da ya daure min kai.
SARKIN MAYU
Me ne ne fa?
GAMBO
Yauwa. Ka san mu wannan digon bakin da a ke yi wa yara...
SARKIN MAYU
(ya katse)
Maganin "polio" ke nan?
GAMBO
Haka a ke kiransa ko? To ka san mu mun dauka cututtuka a ke durawa yara wadanda za su hana su haihuwa, sabo da turawa sun ga mutanen mu, ba ma son tsarin iyali, sai a aka fito da wannan tsari, ya zamana duk wanda a ka yiwa digon ba zai iya haihuwa ba.
SARKIN MAYU
(dariya)
Daman har yanzu akwai masu irin wannan tunani?
ALTO
(ya dan matso)
Wasu kuma cewa su ke kanjamau a ke sa wa yara a ciki.
SARKIN MAYU
Babbar magana. Ina ganin ya kamata na wayar mu ku da kai.
Ya nuna wasu yara.
Kun ga yaran can?...
Su ka kalli yara guda wajen hudu.
...Duk yara na ne. Ya ku ka gansu?
GAMBO/ALTO
Lafiyayyu. Ga su nan sai wasansu su ke yi.
SARKIN MAYU
To...Ba wanda ba a yi wa digon maganin "polio" ba a cikinsu. Abin da na ke so ku gane shi ne, wannan magani da ake digawa yara ba shi da wata illa sai ma taimakon yara da ya ke.
GAMBO
Taimako?
SARKIN MAYU
Kwarai. Taimakonsu ya ke da gaske. Ka san jiki ya na da wata garkuwa da ta ke kare mutane daga cututtuka. To ta yara ta na da rauni. Shi ya sa cutar shan inna, wato "polio" ta ke kama yara kanana wadanda ba su shige shekara biyar a duniya ba. Amma idan ana yi musu digon nan, garkuwar jikin na su ta na kara karfi kwarai ya za ma ko da cutar ta shigo jikin sai garkuwar ta kore ta, ta tashe ta.
ALTO
Domin yanzu ta yi karfin da za ta iya kare jiki ke nan, ko?
SARKIN MAYU
Haka ya ke. Ashe ka gane.
GAMBO ya na kallon SARKIN MAYU kawai. Shi kuma GAGARAU ran sa a bace. Kamar ba ya son hirar.
SARKIN MAYU (CONT'D)
(ya cigaba)
Maganarka da kace a na sa kanjamau a cikin digon nan na baki...
ALTO
(ya yi farat)
Ran ka ya dade, haka na ji a na fada.
SARKIN MAYU
(ya na dariya)
Ko ma ya ya ne, ba zai yiwu a sawa yaro cutar kanjamau ba kuma ya rayu har ya wuce shekara daya bai mutu ba. Haba. Ku kalli 'ya'ya na mana.
GAGARAU
(da dan fada-fada)
Da Allah mu yi abin a ya kawo mu mana. Yamma na yi.
SARKIN MAYU
Shi ma wannan na da muhimmanci. Sai dai don daga nesa ku ke. Ina yaron? Da kun zo da yaron da yafi?
GAGARAU
(ya yi farat)
Haba! Me na gaya mu ku?
GAMBO
Yallabai. Ai mun zo da takalminsa.
SARKIN MAYU
Takalmi? kamar ya ya?
GAMBO
An ce, idan ma mun zo da takalmin yaron za ka iya yi ma sa magani sabo da baiwar da Allah ya ba ka.
SARKIN MAYU
(dariya)
Wa ya gaya muku haka?
GAMBO
Akwai wacce mu ka gani a hanya, BUSHARA. Yaron ma ya na gurinta.
SARKIN MAYU
Wace ce? A ina?
GAMBO
A tsallaken ruwa.
SARKIN MAYU
(ya tashi tsaye)
Yaron ya na gurinta? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!
GAMBO
(ya tashi)
Lafiya? Me ya faru?
ALTO ya tashi da sauri. GAGARAU kuwa ya tashi da sanyin jiki, kamar abin bai dame shi ba.
SARKIN MAYU
Kai, wannan tsohuwa? Wannan tsohuwar mata?
GAMBO
Ba tsohuwa ba ce BUSHARAR. Budurwa ce.
SARKIN MAYU
Ba budurwa ba  ce. Mayya ce kamar ni. Amma ita muguwa ce kuma matsafiya don ta na aiki da miyagun aljanu. Ita ce duk ta kori mutanen da su ke cikin kauyen nan. Duk wani mugun abu da ya ke hauren nan, ita ce ta kawo shi. Ko ni ma na rabu da shigewa ta gurin. Sai yau, sabo mu ceci yaron nan, dole ne mu tafi tare.
GAMBO
Me ne ne yallabai? Na ce BUSHARA...
SARKIN MAYU
(ya katse ya na tafiya zuwa gidansa)
Ka na son danka kuwa?
GAMBO da ALTO da GAGARAU su ma su ka bi shi a baya. GAMBO ya kasa magana. SARKIN MAYU ya shiga gida. Su ka tsaya cirko-cirko. GAMBO ya kasa tsayawa guri daya. Can sai ga SARKIN MAYU nan ya fito da wata kibiya da kwari-da-baka a rataye.
SARKIN MAYU (CONT'D)
(bai kalle su ba)
Ku zo mu tafi.
Wata mace ta leko da yaro a hannunta.
MACE2
Allah ya kiyaye, maigida!
ALTO
(ya na biye da GAMBO)
Amin, baiwar Allah.
Haka SARKIN MAYU ya ja su. Su kuma su na biye da shi. GAGARAU ya dauko tabaran shi ya sa.
EXT. HANYA (KAUYE)- DAY
SARKIN MAYU ya na tafe, GAMBO, ALTO da GAGARAU su na biye da shi. Idan mutane su ka gan su sai su kauce. Har su yi nisa.
EXT. BAKIN RUWA- DAY
Sun iso bakin ruwa. Yanzu GAMBO ne ya ke kokarin janyo kwale-kwale, sai SARKIN MAYU ya dakatar da shi. Nan ya rike wani itace a gefen gabar ruwan ya juya har sau hudu ko biyar. Sannan ya dawo ya tsaya. Su ma su ka tsaya tare da shi. Nan ne wata gada ta ke fitowa daga cikin ruwa, wacce ta fara daga wannan gaba zuwa tsallake. Su ka tsaya su na mamaki a lokacin da shi ya hau ya yi nisa a kan gadar. GAGARAU ya bi shi sannan GAMBO da ALTO.
EXT. GINDIN BISHIYA(GIDAN BUSHARA)- DAY
Sun iso gurin gidan BUSHARA. GAMBO, ALTO da GAGARAU sun tsaya sun yi cirko-cirko cikin mamaki. Sai SARKIN MAYU ya kalle su.
SARKIN MAYU
Ya ku ka tsaya?
ALTO
Kalli gurin wayam.
GAGARAU
Nan ne in da gidanta ta ya ke. Daman na ce ni ban amince da ita ba. Ga shi nan.
GAMBO ya koma gefe ya hada kan shi da bishiya don takaici.
SARKIN MAYU
(ga GAMBO)
Ba kuka za ka tsaya yi ba.
ya juya ya fara tafiya
Ku biyo ni.
GAGARAU da ALTO su ka bi SARKIN MAYU a baya cikin sauri. Sai GAMBO da ke bayansu cikin sanyin jiki.
EXT. SURKUKI- DAY
Sun iso wani surkuki, wanda rassan bishiyoyi sunka rurrufe ko'ina. Sai hanyar da take tsakiya kawai. Su ka bi wannan  hanya a bayan SARKIN MAYU. Su ka fita wani fili. Sai su ka tsaya su na kalle-kalle. Sai su ka ga wani katon gini mai tsahon gaske.
ALTO
Wannan ginin fa?
SARKIN MAYU
Na tsafi ne. Nan za mu hau. Ta na can tare da yaron.
SARKIN MAYU ya doshi ginin da sauri. Su na biye da shi. Duk kansu ya na kallon tsahon ginin.
EXT. JIKIN GINI- DAY
SARKIN MAYU a makale a jikin ginin ya na hawa. GAGARAU ya na biye da shi. Sannan GAMBO. Sai ALTO a bayansu.
EXT. KAN GINI- DAY
SARKIN MAYU ya hawo kan ginin sannan GAGARAU ya biyo shi. Sai GAMBO da ALTO. ALTO ya tsaya kusa da GAGARAU. Shi kuma GAMBO ya tafi kusa da SARKIN MAYU. Duk su ka tsaya cikin mamaki. Nan ne su ka ga BUSHARA, mai sanye da wasu dogayen kaya ma su ban tsoro, na kokarin cire kurwar TALLE, wanda ke kwance a kan wani gadon dutse. Kurwar har ta fara rabuwa da jikinsa. GAMBO ya zaburo. SARKIN MAYU ya tare shi. Nan da nan ya ciro kwari-da-bakarsa ya dana kibiya sannan ya harwa BUSHARA. BUSHARA ta juyo, a lokacin da kurwar TALLE ta ke komawa jikinsa. Kibiyar nan ta taho kai tsaye saitin goshinta. Daf da za ta cake goshita, sai BUSHARA ta goce ma ta. Kibiyar ta wuce. Ran BUSHARA ya baci. Sannan ta kyalkyale da dariya irin ta mugunta. Kawai sai ta rikida ta koma kamar wannan tsohuwar da ta ke gidanta. Duk sun tsorace amma ban da SARKIN MAYU. Nan ta yi wani yunkuri ta daga hannunta, sai ta jefo dunkulalliyar wuta. SARKIN MAYU ya goce. GAMBO ya sunkuya. Wutar ta je ta sami ALTO da GAGARAU. Ba wuta ba ce ashe. Ya yi kama da wuta ne. Karfinsa ya sa ALTO da GAGARAU su ka fada ta kan ginin. Sai karansu kawai ka ke ji tare da amsa kuwwa. SARKIN MAYU ya taso ya kara dana kibiya.
SARKIN MAYU
(a hankali)
Bismillahi.
Sai ya harba kibiyar. Nan take ta shige mata kirji. BUSHARA ta yi kara ta yi gigiza. Ya kara dana wata.
SARKIN MAYU (CONT'D)
Bismillahi.
Ya harba. Ta sake shige ma ta ciki. Ta yi ihu mai ban tsoro.
SARKIN MAYU (CONT'D)
(ya na saita wata kibiya)
Bismillahi.
Sannan ya harba. Nan ta tafi saitin goshita. Nan BUSHARA ta kame ta na wani yunkuri da kakari. Sai ta fada ta saman ginin zuwa kasa, wanda ke da zurfi ainun.
SARKIN MAYU (CONT'D)
(da GAMBO a kusa da shi)
Muguwa, uwar mugaye. Sunanta Ladi Uwar mugaye, ba Bushara ba.
Nan ne suka yi sauri suka daga TALLE daga wannan gadon dutsen. GAMBO ya na dudduba jikin TALLE, kamar zai kuka. SARKIN MAYU ya na kallonsu.
SARKIN MAYU (CONT'D)
Mu yi sauri mu sauka daga nan. Komai zai iya faruwa.
EXT. JIKIN GINI- DAY
GAGARAU da ALTO su na makale a jikin ginin su na ta lilo.
ALTO
Na gaji. Ko na saki ne?
GAGARAU
Saki ma na.
EXT. CIKIN BISHIYOYI- DAY
SARKIN MAYU, wanda ke tsugune gaban TALLE, ya na duba shi. Ya na tattaba masa kafar da ba ta aiki. GAMBO ya na zaune a gefensu. GAGARAU da ALTO su na can daga baya su na kus-kus na gulma.
SARKIN MAYU
Ya na taba jikin TALLE
Jikinshi zafi zau. Sau nawa a kataba yiwa yaron nan digon maganin "polio"?
GAMBO
(ya kau da kai)
Ba a taba yi masa ba.
SARKIN MAYU
Ka san kafarsa daya ba ta aiki sosai?
GAMBO
Mun sani mana. Ai shi ya sa mu ka kawo shi.
SARKIN MAYU
Ni? Nai mishi me? Wannan ai cutar asibiti ce. A ka gaya maka ko wace cuta mu ke magani? Akwai cutar asibiti daban. Akwai kuma wacce mu ke maganinta da maganin gargajiya.
GAMBO
Ba shan inna ya ke ba ne? Ai cutar aljanu ce. Kuma ku na maganin cutar aljanu.
Nan ne SARKIN MAYU ya fusata. Ya tashi tsaye ya juya ya yi tafiyarsa. GAMBO ya bi shi a baya da sauri.
GAMBO (CONT'D)
Allah ya ba ka hakuri. Don Allah ka saurare ni.
SARKIN MAYU ya tsaya sannan ya juyo.
SARKIN MAYU
TALLE danka ne. Kuma ka fi ni son shi. Ni na gaya ma ka mastalarshi. Amma ba ka yarda ba. In ya zama gurgu, kai ya zamarwa gurgu ba ni ba.
ALTO
(cikin karyar da kai)
A dubi halin da yaron ke ciki. A taimaka don Allah.
SARKIN MAYU
(ga GAMBO)
Kawai ka ba shi hadin kai. Ka fa ba mu wahala wallahi.
GAMBO ya yi shiru ya na kallon yaron da ya ke can a zaune a kan dan dutse, jingine da bishiya. Abin tausayi.
SARKIN MAYU (CONT'D)
(ya yi ajiyar zuciya)
Ka ganni nan? Ni likita ne. Na san banbancin gargajiya da zamani. Na dawo gida ne sabo da na gaji mahaifina da ya mutu don ni kadai ne namiji. Kuma ba na so sarautar ta bar gidanmu. bugu da kari na karanci likitanci ne da burin na bunkasa harkokin maganin gargajiya kamar yadda kasashen sin da hindu suka yi.
GAMBO ya girgiza kai da sauri.
SARKIN MAYU (CONT'D)
Yanzu asibiti za a yi sauri a kai shi, domin ya na cikin hadari.
GAMBO
Akwai asibiti a kauyen ku ne?
SARKIN MAYU
Akwai. Amma ba babba ba ne. Daga ina ku ka zo?
GAMBO
Daga Kalbo.
SARKIN MAYU
Yauwa. Asibitinku ya fi na mu. Dole mu yi sauri sabo da yaron ya na cikin hadari. Idan cutar ta ci karfinsa duk kafafuwan za su shanye.
GAMBO
(Kamar ya yi kuka)
Yanzu ya za a yi mu je cikin kankanin lokaci?
SARKIN MAYU
Akwai yadda za a yi. Ina da mota. Maza ku dauko TALLE.
EXT. SAMA- DAY
Gajimare ya na tafiya.
EXT. HANYA (DAJI)- DAY
Ga su nan a mota kirar "gulf" tsohuwa, su na ta gudu. SARKIN MAYU ne direba. GAMBO a gefe rike da TALLE. GAGARAU da ALTO na baya.
EXT. BISHIYOYI- DAY
Motar ta na ke ta bishiyoyi a guje.
EXT. DUTSEN HAUREN MAYU (TA CIKI)- DAY
Motar ta doshi dutsen. Hankalin su GAMBO ya tashi.
ALTO
(ya na karkarwa)
Waiyo Allah. Allah ka sauke mu lafiya.
GAGARAU ya cire tabarau. ya tsirawa hanya ido. GAMBO ya na kallon hanya sannan ya kalli TALLE.
Ba abin da ya dami SARKIN MAYU. Kawai gudunsa ya ke izuwa dutsen. Nan ya bi ta matattakalar dutsen. Ya hau a guje ya yi tsalle, ya yi sama.
EXT. DUTSEN HAUREN MAYU (TA WAJE)- DAY
Motar a sama har tazo ta dire a kasa ta na mai gudu. Kararsu kawai ka ke ji. Sun yi murna ta karfin hali.
GAMBO
(daga can nesa)
Waiyo ciwona!
EXT. HANYA MARA KWALTA- DAY
Motar a guje a kan hanya. Sai kura ce ta ke tashi.
EXT. HANYA MAI KWALTA- DAY
Motar ta na gudu.
EXT. HANYA MAI KWALTA(WANI)- DAY
Motar ta na gudu.
EXT. HANYA MARA KWALTA- DAY
Mota ta na gudu cikin kura.
EXT. KOFAR ASIBITIN KALBO- DAY
Mutane biyu a tsaye. Sai su ka kalli in da karan motar ke zuwa. Kara ya na karuwa. Har da ya kusa zuwa kusa da su,sai su ka kauce. Nan ne motar ta yi boris.
INT. CIKIN ASIBITI- DAY
GAMBO ya na dauke da TALLE ragaje-ragaje. A garukan asibitin a lillika fastocin "polio immunisation". ALTO da GAGARAU su na biye da shi. Su ka shiga dakin emergency. Wata mai jinya ta dakatar da GAGARAU da ALTO. Sun tsaya a waje. Kofar dakin ta rufe.
EXT. cikin unguwa a kalbo - dAY
Iyaye sun fito da yaransu. Ma'aikatan polio na digawa yara maganin a baki.
EXT. GINDIN BISHIYA- DAY
RUBUTU: Bayan Wata Uku.
GAMBO, wanda ke cike da farin ciki na zaune kusa da GAGARAU, wanda ke sanye da 'yar shara, sannan da fartanya a kusa da shi. ALTO kuma ya na gefe ya na cin kuli-kuli. Duk su na kallon yara su na wasa. Sai ga TALLE nan ya na kwallon kafa da kafafuwansa, amma ya na dan dingishi kadan. Duk su na cikin farin ciki. Can sai hankalin GAGARAU ya yi wani guri. Nan ne GAMBO shi ma ya kalli in da GAGARAU ya ke kallo. Ashe ma su digon maganin "polio" ne su ka taho, namiji daya da mata uku. Tare da kayan aiki. Nan da nan GAMBO ya tashi a guje ya je ya dauko TALLE ya na dariya, ya na yi ma sa cakulkuli. Shi ma TALLE ya na darira. GAMBO ya taho da shi gurin masu aikin ya dire shi. GAGARAU da ALTO su na dariya. ALTO ya kware. Ya na tari. Mace daya daga cikinsu ta dauko maganin ta na digawa TALLE a baki. Hoton ya kame.
ALHAMDULILLAHI

No comments:

Post a Comment