Saturday, April 7, 2012

SANDAR KIWO - Marubuci Balarabe Murtala (Baharu)

A yi hakuri da yadda format din ya hargitse amma dai shi wannan shafin an tanade shi ne don karatun labarin kawai ba wai don yin nazari akan Format ba. idan ana son mai format a sanar a group sai a turo da rich text na script din.
ESTABLISHMENT SHOT OF A CITY
EXT. MAKARANTA (BAKIN KOFA) - DAY
Wata mota ta alfarma ta nufo bakin kofar makarantar.
DIREBA
hannunsa na hagu ya fito da shi waje rike da ID Card.
SECURITY I
Rike da littafi ya dakatar da motar, Direban ya mika masa ID Card din. sannan bayan tabbatar da sunan direban a cikin littafin, ya yiwa abokin aikinsa alamar ya bude masa kofa ya wuce.
SECURITY II
Ya bude kofar yana mai daga hannu ga direban. Motar ta nufi cikin makarantar yayin da muke jin hayaniyar daliban na karuwa.
EXT. MAKARANTA (HARABA) - DAY
Kaiwa da kawowar yara maza da mata dalibai cikin kayan makaranta, kowanne ya nufi wajen mai jiransa, ko motar da za'a dauke shi. Motar ta gama tsayawa.
DIREBA
Yana daga ciki a zaune ya bude kofarsa. Hafsat I (5) tare da wasu yara Faisal da Mabaruka, sa'anninta suka fito daga aji dauke da jakunkunan makarantarsu a baya.
FAISAL/MABARUKA
Suka nufi wajen motar su a guje cikin murna.
HAFSAT I
Cikin sanyin jiki ta nufi wani dandamali ta zauna fuskarta kamar za ta yi kuka.
INT. KAMFANI (DAKIN TARO) - DAY
Sauran manyan ma'aikatan kamfanin a gefen dama da hagu a zazzaune kowa da takarda a gabansa, meeting yayi zafi ana ta muhawara. Faruk (43) da kaninsa Garba (28) suna fuskantar juna.
GARBA
Yayi shiru yana satar kallon Faruk.
FARUK
Cikin yanayi na damuwa, hankalinsa ba ya tare dasu, ya sake duba agogo hannunsa, kafin ya dauko wayarsa yana bugawa cikin saurare idanuwansa na kallon Garba.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - DAY
Falon cikin matsakaicin haske cike da sauran kayayyakin kawata gida. Mayafi da jaka a kan kujera a ajiye. Rahma da Kande a cikin kitchen suna aikin abinci tare, wayar Rahma ta hannu na gefe a ajiye.
RAHMA
Ta zuba abincin a cikin flaks.
KANDE
Ta dauka ta nufi kan teburin abinci za ta kai. Rahma ta daga kai ta kalli agogo cikin yanayi na kokwanto, ta cigaba da aikin da ta ke yi, yayin da Kande ke jera abincin a kan tebur.
Wayar ta fara kara.
RAHMA
Ta dauki wayar ta kai kunne ba tare da ta tsaya da aikin ba.
Kun taho ne?
MURYAR FARUK
Ai ban ma tafi dauko ta ba, saboda wani mitin da muke yi a ofis.
RAHMA
Ta sake kallon agogo cikin damuwa
Amma gashi har lokacin tashinsu ya wuce.
MURYAR FARUK
Nima ba haka na soba, amma don Allah yi kokari kije ki dauko ta.
RAHMA
Rahma alamar takaicin abin da ya fada.
To shi kenan.
Ta kashe wayar, cikin sauri ta nufo inda mayafinta yake ta dauka ta yafa, sannan ta bude jakar ta dauki makullin mota, bayan ta sake kallon agogo daidai da lokacin da yake kan karfe daya ta wuce.
KANDE
A dawo lafiya.
RAHMA
Allah yasa.
Kande ta koma kitchen, Rahma ta bude kofa ta fita.
EXT. AKAN TITI - DAY
Zirga zirgar motoci a kan wani babban titi, har ya zuwa wata danja da ke bada hannu, motar Rahma na cikin jerin motocin da aka dakatar.
RAHMA
A cikin mota ta saurara, har ya zuwa lokacin da launin wutar ta chanja zuwa koren launi. Sannan Rahma ta dauki wani titin mai karancin motoci.
EXT. MAKARANTA (HARABA) - DAY
Kusan yaran saura 'yan daddeku yayin da Hafsat I ke zaune ita kadai.
HAFSAT I
Ta sake kallon kofa, cikin karin damuwa, ta tashi ta nufi wani abin za ta zauna.
Motar Rahma ta shigo wajen cikin matsakaiciyar tafiya.
RAHMA
Ta hangi Hafsat I tun kafin ta tsaya, sannan ta fito da sauri ta nufi wajen yarinyar.
Hafsat!
Hafsat I ta kalli wajen kiran, nan da nan cikin murna ta runtuma a guje ta nufi inda Rahma ke tahowa, har ta isa gareta suka rungume juna, sannan suka juya suka nufi mota.
HAFSAT I
Umma, ina Abba na?
RAHMA
Tana rike da hannunta cikin murmushi Abbanki aiki ne ya tare shi, ni kuma na tsaya girkin abinci. Ta budewa Hafsat I kofa ta shiga ta rufe, itama zagaya ta shiga motar ta bar wajen.
INT. KAMFANI (DAKIN TARO) - DAY
Surutai kowa na fadar albarkacin bakinsa, Faruk Ya dakatar da su da hannu, suka saurara.
FARUK
Shikenan ya isa haka, kowa yaje ya koma bakin aikinsa. Ni zan san abin da zan yi akai.
Suka fara fita, har Garba ya mike zai fita.
FARUK (CONT'D)
Zauna, Ina da magana da kai.
GARBA
Ya koma ya zauna jikinsa a sanyaye ya kasa hada ido da Faruk.
FARUK
Ya gara masa takardun da ke gabansa.
GARBA
Fuskarsa cikin karin damuwa ya dauki takardun ya duba kana ya ajiye.
Don Allah Yaya...
FARUK
Ya dakatar dashi da hannu
Babu wani Yaya, ina ka kai kayan mutane mota guda na taki?
GARBA
Ya dago kansa a hankali.
EXT. BAKIN HANYA (KOFAR STORE) - DAY
Wata babbar mota a tsaye lullube da tampoling bayan motar a kofar store, leburori sun zagaye ta suna jiran fara sauke kaya. Garba da Alhaji Barau suna daga gefe rakube da motar.
ALH. BARAU
Cikin yanayi na hilata
Haba Garba kai ma kasan na yi kokari.
GARBA
Amma dai Alhaji ko yau muka fara harkar nan ai ya kamata ka doramin wani abu a kai, farashin nan yayi kasa kwarai.
ALH. BARAU
Ya dan yi jim
To shikenan na kara ma hamsin in yaso ranar Litiinin sai na rubuta check na dubu chasa'in na baka sauran dubu dari sati na sama sai ka zo ka karba.
GARBA
Fuskarsa ta sauya
Ban gane ba Alhaji, dubu dari da chasa'in ka sa yi motar takin guda.
ALH. BARAU
Yanda na ke saya haka na saya. Kudi na da nake binka fa da kuma asarar da ka sa na yi ta wadancan kayan fa?
GARBA
Zamiya ka yi kenan?
ALH. BARAU
Ba tare da ya saurare shi ba ya juya ga la burori
A fara aiki kafin rana ta bude.
SHUGABAN LEBURORI
An gama Alhaji.
Suka fara kwance tampoling.
GARBA
Ya yi shiru cikin rashin sanin abin yi.
FARUK
Karo na farko da na biyu na yarda kuskure ne, amma a yanzu ba zan iya hakura ba. Dan ba zai yiwu ka lalata dukiyarka, ni kuma saboda kana dan uwana ka jefa ni cikin gararin da ban san iyakar sa ba.
GARBA
Ya dan yi shiru yana kallon yayan cikin gazawa
Don Allah Yaya ka yi hakuri, nasan na yi kuskure.
FARUK
Yana kallonsa
In har kana son na hakura, sai ka fadamin inda kaje ka sayar da kayan mutane.
GARBA
Ya sake sunkuyar da kansa.
FARUK
Ya daka masa tsawa
Tambayarka na ke yi!
GARBA
Ya dago cikin razana
Doguwa.
EXT. AKAN HANYA (BABBAN TITI) - EVENING
Motar Faruk ta nufi wajen gari cikin matsakaiciyar tafiya.
GARBA
Na gaba a zaune yayi shiru yana kallon hanya.
FARUK
Yana tukawa fuskarsa cikin damuwa, ya dauko waya ya mikawa Garba.
Kirawo min lambar Rahma.
GARBA
Ya karba ya danna ya sa a kunne. Motar ta fara nisa da gari. Ya kasa kama lambar, sannan ya mikawa Faruk
A kashe ta ke.
FARUK
Kira lambar gida.
GARBA
Ya sake kira kamar ransa bai so ba.
Ita ma tana engage.
Ya sake mikawa Faruk wayar. Faruk ya ajiye ba tare da yace komai ba, motar ta nausa zuwa Doguwa.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - NIGHT
Kayan abincin Faruk an jera a kan tebur, Rahma da Hafsat I na zaune a kan kujera, kande ta fito daga kitchen cikin shirin fita dauke da kwanon abinci a leda, tazo ta durkusa gaban Rahma.
KANDE
Zan wuce. Gashi.
RAHMA
Cikin alamu na nuna rashin jin dadi Haba Kande, Wata da watanni kike tafiya da abincin nan, amma kullum sai kin nuna min, bayan shi yace a zuba miki duk yadda ya dace ki tafi dashi, ni kuma na amince ki rinka diba da kanki.
KANDE
in Allah ya yarda ba za'a sake ba.
RAHMA
Tayi murmushi
Allah yasa, dan haka kike fada kullum.
KANDE
Ta mike tana fara'a ta kalli Hafsat I To, hafsat na tafi sai gobe.
HAFSAT I
Karatu na keyi.
Kande da Rahma suka yi dariya, sannan Kande ta fita.
RAHMA
Ya isa haka, lokacin bacci yayi.
HAFSAT I
Ai Abba bai dawo ba muyi karatu.
RAHMA
Dare yayi, sai gobe.
Ta rufe littafin Hafsat I ta kama hannunta suka nufi dakin baccin Hafsat tare agogo na buga karfe takwas.
INT. GIDAN FARUK ( DAKIN HAFSAT I) - NIGHT
Rahma na lullube hafsat da bargon rufa.
HAFSAT I
Tana cikin bargo a kwance. Umma ba muyi addu'a ba.
RAHMA
Ta shafa kanta
To bari mu fara. Rahma ta fara karanta mata Suratul ikhlas da falaq da Nas, hafsat I na bi, suka gama.
RAHMA (CONT'D)
To rufe idonki kiyi bacci.
HAFSAT I
Ta rufe idanunta.
Rahma taci gaba da shafa ta, har ya zuwa lokacin da ta tabbatar tayi bacci, sannan ta tashi ta kashe fitilar ta bude kofa ta fita.
INT. GIDAN FARUK ( DAKIN RAHMA) - NIGHT
RAHMA
A kwance idanunta biyu ta yi shiru kamar mai sauraren jin wani abu. Zuwa wani lokaci ta tashi za ta fita.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - NIGHT
Rahma ta fito daga daki fuskarta cikin yanayi na damuwa, ta nufi wajen teburin abinci ta kewaya yayin da idanunta ke kan agogon bango da ke nuna sha daya da rabi, sannan ta zo ta harde a kan kujera ta yi shiru tana fuskantar kofa. Karar tarhon da ke falon yasa ta tashi da sauri taje ta dauka.
RAHMA
Hello, hello.
Alamar wayar ta yanke cikin sanyin jiki ta mayar da kan wayar ta sake komawa in da take.
EXT. AKAN HANYA (BABBAN TITI) - NIGHT
Yanayin hasken fitilu daga nesa, motar Faruk ta nufo gari.
FARUK
Yana tukawa fuskarsa cikin damuwa.
GARBA
Yana zaune ya dan sad da kansa kasa. Motar ta gilma zuwa shiyyar da hasken ke karuwa.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - NIGHT
RAHMA
A zaune inda take, ta ji sautin injin mota a waje, nan da nan ta tashi ta nufi kofa da sauri.
Suka hadu a kofa, tana kokarin budewa yana kokarin shigowa.
RAHMA (CONT'D)
Mamaki a fuskarta ta dan ja baya dan ya wuce Sannu da zuwa.
FARUK
Yawwa! Kin ganni sai yanzu. Ya nufi kan kujera tana biye da shi
RAHMA
Ina fatan dai lafiya?
Ta zauna kusa dashi tana kallonsa.
FARUK
Wallahi matsalar dai dana fara fada miki a kan abin da Garba yayi.
RAHMA
Cikin sakin fuska
To ai hakuri za ka yi.
FARUK
Hakuri?
Yana yi mata wani kallo
RAHMA
Ta mike fuskarta cikin nuna rashin jin dadin abin da ya fada ta nufi wajen teburin abinci.
FARUK
Inyi hakuri wato goyon bayan sa ma kike yi?
RAHMA
A tsaye kusa da abincin, ta juyo ta kalleshi fuskarta a sake. Ga abincinka.
Ya dan yi shiru na wani lokaci, sannan ya mike ya je ya zauna a kan dayan kujerun ya fara cin abincin, ita kuma ta juya ta nufi wajen fridge za ta dauko ruwa.
RAHMA (CONT'D)
Kamar yadda ka sanar dani rashin samun damar ka na dauko Hafsat a makaranta, da tafiyar ma ya dace ka yiwo min waya ka fadamin. Ta dauko ta dawo wajen sa ta zauna suna fuskantar juna.
FARUK
Cikin cin abinci
Mun bugo wayar a kashe, ta tebur din ma ba ta shiga ba.
RAHMA
Ai kuwa ban kashe waya ta ba, na dai ji kira (ta fadi lokacin) a land line.
FARUK
Ya dakata da cin abincin Duk lokutan biyu ni nasa Garba ya kira.
RAHMA
Ta dan yi jim sannan ta fara tsiyaya ruwa a kofi Wayoyin ne ba su da tabbas!
FARUK
Yaci gaba da cin abinci Hafsat fa, ta yi bacci ko?
RAHMA
Ta kalle shi ta jinjina kanta cikin nufin abin da ya tambaya. Yayi murmushi ya dauki ruwa ya sha yayin da ta daga kai ta kalli aggon bangon da ke nuna sha biyun dare ta wuce.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - MORNING
Motar Faruk da ta Rahma a ajiye. Hafsat I sanye da hijabi ta turo kofa ta fito, Rahma rike da hannun Hafsat I cikin hijabi itama.
HAFSAT I
Ta ruga da gudu ta nufi wajen motar Faruk.
RAHMA
Ta yi maza ta bi ta ta ruko hannunta.
FARUK
Ya fito yana waya ya nufo wajen motar. Rahma ta budewa Hafsat I gidan baya ta shiga dab da karasowar Faruk, ita da shi suka shiga lokaci guda.
KANDE
Na tsaye a bakin kofa, har motar ta fita daga harbar gidan sannan ta koma ciki.
EXT. AKAN HANYA (CIKIN GARI) - MORNING
FARUK/RAHMA/HAFSAT I
A cikin mota cikin nishadi. Motar ta wuce ta nufi Kofar wani kanti.
INT. SUPER MARKET (CIKI) - MORNING
FARUK/RAHMA/HAFSAT I
A cikin kantin suna sayayya.
RAHMA
Na zabar kayan abinci/aikin gida, hankalinta na kan Hafsat.
FARUK
Yana daukar kayan wasa na koya karatu.
HAFSAT I
Na dibar kayan wasa, ta dauki wata 'yar tsana. Rahma ta kwace ta mayar.
FARUK
yana dariya ya musanya mata da wani abu.
EXT. SUPER MARKET (WAJE) - MORNING
FARUK/RAHMA/HAFSAT I
Sun fito wani na biye da su da kayayyakin da suka saya. Suka sa kayan a baya, Faruk yayi masa alheri, cikin ladabi ya karba ya koma ciki daidai lokacin da motar ke barin wajen.
E/I. MAKARANTAR ISLAMIYYA - EVENING
MALAMI I
Yana koya musu karatu.
Rubutu akan allo, sauran daliban suna bin abin da Malamin yake fada.
HAFSAT I
Cikin kayan makaranta tare da sauran dalibai.
EXT. GIDAN FARUK ( KOFAR GIDA) - EVENING
HAFSAT I
Tare da sauran yara, sun nufo kofar gidan. Suka iso, babbar cikinsu ta tura kofar gidan, Hafsat I ta shiga ciki, sauran yaran suka wuce.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - EVENING
FARUK/HAFSAT I
Suna wasa tare cikin nishadi.
RAHMA
Ta fito ta zo ana yi da ita, ta chanja wasan har ya zuwa da ta ja hannun Hafsat I suka shiga cikin gida.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - NIGHT
FARUK
Na zaune yana koyawa Hafsat I karatu.
HAFSAT I
Ta na bin abin da ya ke karantawa.
RAHMA
Ta fito daga daki sanye da hijabi da kur'ani a hannu ta zo ta zauna itama.
EXT. AKAN HANYA (CIKIN GARI) - MORNING
Motar Rahma ta nufo cikin gari.
RAHMA/HAFSAT I
A cikin motar, Rahma na tukawa, Hafsat I na kusa da ita. Motar ta shigo wata unguwa.
EXT. KOFAR GIDAN SU RAHMA - MORNING
Motar ta tsaya.
HAFSAT I
Ta fito ta nufi cikin gidan a guje.
RAHMA
Ta bude kofar baya ta dauki wata leda ta bi bayan Hafsat I.
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - MORNING
Kwanukan abinci da tukwanen girki a wajen wanke wanke.
MAL. HAMZA
Mahaifin Rahma cikin shirin fita, ya nufo kofa, suka yi kichibis da Hafsat I, da ke shigowa aguje, ta rungume shi.
UWANI
Mahaifiyar Rahma, ta fito daga ban daki cikin fara'a. Kada ki yarmin da miji. ta ajiye buta ta taho wajensu.
MAL. HAMZA
Ke da waye?
RAHMA
Ta shigo rike da kayan a hannunta. Salamu alaikum.
MAL. HAMZA
Wa alaikis salam.
UWANI
Ashe tare da uwar suke, sannu da zuwa.
Ta juya ta nufi inda tabarma take ta dauko za ta shimfida, Rahma ta rigaye ta. Mal. Hamza rike da hannun Hafsat I suna biye dasu.
RAHMA
Cikin ladabi
Baba ina kwana?
MAL. HAMZA
Lafiya, Rahma. Yaya mai gidan naki?
HAFSAT I
Ta fada jikin Uwani.
UWANI
Yimin a hankali, kada ki karyamin kafa.
RAHMA
Yace a gaishe ku.
Tana mai mika masa daya jakar ledar Wannan yace na kawo maka.
MAL. HAMZA
Ya karba cikin fara'a da mamaki Kullum dai, Allah ya saka muku da alheri.
RAHMA
Ta sake ajiye daya ledar a gaban Uwani Gashi.
UWANI
Kullum dai. To an gode. Cikin fara'a tana kokarin cirewa Hafsat I hijabi.
MAL. HAMZA
Ya mikawa Uwani ledar
Ni zan fita.
UWANI
Ta karba
Kada ka manta da kanwar.
MAL. HAMZA
To in Allah ya yarda za'a taho da ita.
Suka yi sallama ya fita. Uwani ta tashi ta shiga daki. Rahma ta mike ta nufi wajen kwanukan wanke wanke. Uwani ta fito da urya ta dawo ta sake dora Hafsat I a kan cinyarta.
UWANI
Ta tube hijabin Hafsat I Yau sai kitso ko?
Ta kalli Rahma Da kin barshi sai anjima. Cikin shirin fara yiwa Hafsat I kitso.
RAHMA
Bari dai a yi yanzun.
Ta dauki wani bokiti tana juye ruwan da ke ciki a kan kayan wanke - wanke.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - MORNING
Sautin karatun kur'ani na tashi.
FARUK
Ya fito daga ban daki yana tsane hannunsa alamar ya yi alwala, ya wuce daki. Jimawa kadan Asabe (45) rataye da jaka ta turo kofa ta shigo.
ASABE
Salamu alaikum, ba kowa a gidan ne?
FARUK (O.C.)
Daga daki.
Walakis salam. Gani nan zuwa.
ASABE
Ince ko su Hafsat din ba sa nan ne? Ta nemi waje ta zauna cikin kallon falon tana girgiza kanta.
FARUK (O.C.)
Sun je gidan su Rahma.
ASABE
Ta yatsine fuska.
Kullum ta ke zuwa gidan nasu ne?
FARUK
Ya fito daga dakin, ya dan tsaya yana karasa daura agogo. Duk karshen mako ta ke zuwa. yanzu kike tafe?
ASABE
Ta gyara zama
Daga gida nake, wani abu ya taso ni na ke ta saurin nazo na same ka akai.
FARUK
Ya nufi wajen fredge
Me zan baki? Abinsha ko abinci dan naga kamar kina bukatar dan wani abu da zai kwantar miki da zuciya. Yana kokarin budewa.
ASABE
Ba na son shakiyancin nan naka, ba ciki na kawo gidan ka ba. Wata matsala ce ta taso min shine na zo wajen ka a kanta.
FARUK
Ya fasa budewa
Me ya faru? Ya kashe karatun sannan ya nufo inda take.
ASABE
Kudin adashin nan ne da muke yi na taba dubu tamanin da uku a ciki, shine nazo ka sama min na cika na basu.
FARUK
Ya zauna a hankali suna fuskantar juna Amma Yaya Asabe, me ya kai ki kashe kudin mutane har dubu tamanin, kuma kudin adashi?
ASABE
Ta tsare shi da ido
Ni nace maka kashewa na yi? Kaya muka saya ni da Hajiya Saude ta tafi da su Lagos.
FARUK
Wane irin kaya?
ASABE
Ina ruwan ka da irin kayan? Ya sake sunkuyar da kansa.
ASABE (CONT'D)
Harkar mu ce ta mata. Mun yi da ita shekaranjiya za ta dawo, to sai jiya da daddare ta yiwo min waya, cewar da sauran kudin da bata gama karba ba, sai karshen makon gobe za ta taho.
FARUK
To me zai hana su jira har ta dawo?
ASABE
Yau fa za'a kwashe, sai kuma su jira har zuwa wani satin? ai sai asirina ya tonu.
FARUK
Na dade da baki shawarar ki daina adashin nan, ki daina adashin nan.
ASABE
Kai Faruk ba fada nazo ka yi min ba. Ka ji ko!
Faruk ya yi shiru kansa a sunkuye
ASABE (CONT'D)
Abubuwan da na ke magantawa kaina da karan adashin kasan iyakarsu, ko dan ban biyo ta kan matar ka ba shi yasa za ka fara kawomin kabli da ba'adi?
FARUK
Ya dago kansa da sauri fuskarsa cike da mamaki Me ya kawo Rahma a cikn wannan maganar?
ASABE
Saboda ta mayar da kai rakumi da akala, sai yanda ta yi da kai. Duk wani abu da ba ita ta ce ka yi ba, ba za ka yi shi ba, sai dai kullum ka tare a gindinta da sauran 'yan uwanta.
FARUK
Cikin damuwa ya dago kai ya kalleta Ban yi zaton kema za ki fadi haka ba.
ASABE
Tana kokarin tashi tsaye Za ka bani kudin nan ko kuwa ba za ka bani ba?
FARUK
Yaya Asabe har yanzu ban gama biyan asarar da Garba ya sani ba.
ASABE
Tana mikewa tsaye
Ba za dai ka bani ba.
FARUK
Cikin sassaukar murya
Wallahi a yanzu idan nace ina da kudin da zan iya baki, na yi karya.
ASABE
Allah ya baka.
Ta nufi kofa fuskarta cikin fushi ta fita, yayin da muke jin shigowar motar Rahma a harabar gida. Faruk ya dan yi jim kafin ya mike ya fita.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - MORNING
Rahma na kokarin fitowa daga mota ita da Hafsat I. Asabe na fitowa daga cikin gidan cikin fusata. Rahma ta riski Asabe daidai fitowar Faruk.
RAHMA
Cikin ladabi da fara'a
Yaya ba dai har za ki koma ba? Sannu da zuwa.
ASABE
Ta kalleta shekeke ba tare da ta amsa mata ba ta wuce.
HAFSAT I
Ta kama jikin Asabe ta rungume Anti sannu da zuwa.
ASABE
Ta shafa kanta ta janye ta da jikinta ta nufi kofa. Rahma cikin mamaki da rashin fahimta, Faruk ya biyo Asabe.
FARUK
Amma dan Allah Yaya kiyi hakuri..
ASABE
Ba tare da ta saurara ba ta bude kofa ta fita cikin fusata. Faruk ya tsaya shiru cikin damuwa. Hafsat I ta same shi, ya kama hannunta suka juya. Rahma na tsaye cikin rashin fahimta, ya wuce ya nufi cikin gida.
RAHMA
Ta bishi a baya
Me ka yi mata kuma?
FARUK
Babu komai.
Ya tura kofa suka shiga shi da Hafsat I. Rahma ta bishi cikin yanayi na fusata.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - MORNING
Faruk ya isa ga kujera ya zauna, yayin da Hafsat I ta dauki remote za ta kunna talabijin, Rahma ta shigo.
RAHMA
Ta kalli Hafsat I
Hafsat tashi ki shiga daki, nima yanzun nan zan shigo muyi salla. Hafsat I ta kashe TV sannan ta tashi nufi daki, sai da ta shiga sannan Rahma ta zauna kusa da Faruk.
RAHMA (CONT'D)
Gaskiya abin da ka yi bai dace ba.
FARUK
Kinsan abin da muka yi da ita ne, har kike neman doramin laifi?
RAHMA
Cikin sassaukar murya ta na kokarin zama Koma me ya faru. Ai ita ke gaba da kai.
FARUK
Ya yi mata wani irin kallo Ke Rahma bana son haka kinji ko! Dan kawai tana 'yar uwa ta shi kenan sai kawai nace zan bata abin da nasan bani da shi?
RAHMA
Ni nasan ba za ta tambaye ka abin da zai gagare ka ba.
FARUK
Saboda nine dan Karuna. Yana hararta.
RAHMA
Ta kara matsawa kusa dashi cikin lallashi Baban Hafsat, dan Allah ka daure ka yi mata wani abu.
FARUK
Ya mike tsaye cikin fusata Wai me yasa kike neman matsamin ne a kan koda yaushe sai na biyawa 'yan uwana bukatarsu? Wato ke da su gaba daya ba kwa ganin abin da na ke yi musu kenan?
RAHMA
Cikin sassaukar murya
Amma ai dan Allah kake yi, dan zumunci.
FARUK
Saboda haka shi kenan, da abin da ya dace da wanda bai dace ba, sai na dauka na dorawa kaina. Maimakon na yi dan Allah sai na yi dan na ce na yiwa dan uwana, wato na kare da yin riya kenan ko?
RAHMA
Ta bishi da kallo cikin yanayi na gazawa Menene abin riya a cki?
FARUK
Na fuskanci ma kamar ke kike sawa suke yimin abin da suke so.
RAHMA
Wato so kake na zama abar zargi kenan?
FARUK
Ke, wallahi a yanzu, ko ina da damar yi, ba zan yi ba! In dai duk abin da nayi a baya, bai zama dan Allah dan zumunci ba, to wanda zan yi yanzu ba zai zama na lada ba. Kawai ya juya ya bude kofar dakin ya shiga ya rufe.
RAHMA
Ta yi shiru tana mai bin kofar da kallo yayin da ta ji kwalla na neman zubo mata.
EXT. KOFAR GIDAN SU MURJA - DAY
MURJA
Tana fara'a
Da a ka tambayeni a gida, kawai ni kuma nace kai na keso.
GARBA
Yayi wata 'yar dariya
yanzu dan Allah haka kika ce musu?
MURJA
Ta na murmushi ta amsa masa da ka Kai ma kasan kai kadai ne a cikin zuciya ta.
GARBA
Kinsan Allah, jiya da daddare sai da na yi mafarkin munyi aure, na shigo gida na tarar da ke a zaune kin gama abinci kina zaman jiran dawowa ta daga aiki. Na shigo na fara lallashinki har kika hakura.
MURJA
Cikin fara'a
Yanzu dai abin da Baba ya ce kenan.
GARBA
Cikin nuna karfafa zuciya Ai a cikin satin nan zan je na sami Yaya Faruk, a yi duk yanda za'a yi a kawo kudin auren nan.
MURJA
Nasan halin Baba. Kada dai a saba lokacin da ya bayar. Duk abin da Allah ya hore kawai a kawo. Suka yi dariya gaba dayan su.
MURJA (CONT'D)
Sai yaushe kenan? Dan nasan mai yiwuwa in ka tafi yanzu sai na sake bin ka da waya tukuna zan sake saka a idona.
GARBA
Cikin nufin abinda zai fada Ai ba zan dawo nan ba, sai da bayanin lokacin da zasu zo. Suka yi sallama, Garba na tsaye yana kallon Murja har ta shiga gida, ya juya ya tafi fuskarsa cike da farin ciki.
INT. OFISHIN FARUK - DAY
Computer (lap top) a kunne a kan tebur mai dauke da wasu takrdu a kai.
FARUK
Na zaune ya yi shiru cikin yanayi na damuwa ko alhini. Zuwa wani lokaci ya dauki makullin motarsa ya fita.
GIDAN BARAKA (KOFAR GIDA)- DAY
Motar Faruk a ajiye, Faruk na gaba Baraka da mijinta Abdul suna biye da shi sun fito da cikin gidan zuwa wajen da motar ta ke.
ABDUL
Cikin fara'a Yaya Faruk sai yaushe kenan?
FARUK
Ya tsaya jikin motar
Ai zan rinka lekowa na duba ku.
BARAKA
Cikin raha
Ni dai Yaya zan so ka fadi gaskiya.
FARUK
Yana murmushi
Au yanzu karya na fada?
BARAKA
Ba karya ka yi ba, amma wannan zuwan ma na laifin da kasan ka yi wa...
FARUK
...To kaza mai kwanci na ji ya isa haka.
Suka kwashe da dariya gaba dayansu.
ABDUL
To Yaya a sauka lafiya.
FARUK
To na gode Abdul.
Abdul ya juya ya shiga gida.
FARUK (CONT'D)
Ya dada gyara tsayuwa
(Ni kaina nauyin na je na tunkari Rahma na ke yi, dan nasan bai dace na yi mata haka ba.)
BARAKA
(Ai kai ne Yaya wani lokaci in ka yi fushi duk sai ka rikice gaba daya.)
FARUK
(To ai yanzu shine na zo wajen ki neman shawarar yanda za'a yi. Kisan yadda Rahma ta ke, ba za ta taba nuna min ranta ya baci ba.)
BARAKA
(Ai shine na ce maka kai ya dace ka same ta ka bata hakuri.)
FARUK
Ai ni yadda zan yi matan ne na ke tunani.
BARAKA
ta sheke da dariya har da durkusawa.
FARUK
Menene abin dariya kuma?
BARAKA
Ta dago kanta tana murmushi
(Ai abin ne wai mutum da matar sa, amma ya yi mata laifi bai san yadda zai yi ya bata hakuri ba.)
FARUK
Ya kawar da kai
(To shi kenan gama yimin shakiyancin, nima ai za'a zo neman tawa shawarar ko taimako ne a matsayi na na babban Yaya nima sai...)
BARAKA
(...Tsaya tsaya Yaya. Kai ma kasan mu mata wani lokaci sai ka dan lallashe mu ka yi mana shagwaba tukuna mu ke gane inda kuka sa gaba.)
FARUK
Shagwaba kuma haba Baraka sai ka ce wani karamin yaro.
BARAKA
Kwarai kuwa Yaya, ita ma na san hakan ta ke yi maka idan ta yi maka kuskure.
Suka hada ido da juna sai suka kwashe da dariya.
FARUK
To na dai gane abin da kike nufi. Suka yi sallama ya shiga mota ya tafi, Baraka ta yi gida.
INT. GIDAN FARUK ( HARABA) - AFTERNOON
RAHMA
Na zaune cikin yanayin damuwa.
HAFSAT I
Ta fito sanye da kayan islamiyya ta zo wajen Rahma. Umma zan tafi.
RAHMA
To Hafsat, ki yi karatu da yawa kinji?
Hafsat I ta fita, Faruk ya fito, ya tsaya yana kallon Rahma a inda take a zaune, sannan cikin sanyin jiki ya karaso wajenta. Rahma ta kalleshi ta dan sunkuyar da kai.
RAHMA (CONT'D)
Cikin kokarin boye damuwarta Fita za ka yi?
FARUK
Ya zauna kusa da ita
Ke na zo na baiwa hakuri, nasan dole abin ya dame ki. Amma kinsan yanda Asabe da Garba suke yimin dole ne na...
RAHMA
...dan Allah ka bar maganar nan, ta wuce.
FARUK
Naji zan bari, amma ke ma sai kin nuna min kin hakura.
RAHMA
To na hakura.
FARUK
Cikin zolaya
Hakan ne kin hakura?
RAHMA
To me kake so na yi wanda zai nuna maka na hakura?
FARUK
Tun da safe ko murmushi ban ga kinyi ba, sannan ki ce kin hakura?
RAHMA
Ta dan yi murmushi
Wallahi ba ka rabo da abin dariya.
FARUK
Cikin murmushi
Haba yanzu na ji zance, amma duk kin wani bata rai. Kinga yadda kika koma kuwa? Suka sake kwashewa da dariya.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - MORNING
Talabijin na kunne, ana labarai.
KANDE
Na sanyawa Hafsat I robar ruwa a jakar makaranta.
HAFSAT I
Cikin kayan makaranta, a zaune kusa da Kande.
FARUK
(Ya fito daga daki cikin shirin fita yana karasa daura agogo, ya nufi kofa.)
RAHMA
(Na biye da shi rike da jakarsa ta zuwa aiki.)
Suka tsaya a bakin kofa. Daga can za ka wuce Kadunan kenan?
FARUK
So nake sha daya tayi min a Kaduna.
RAHMA
A goben za ka dawo?
FARUK
Yana fara'a
In Allah ya yarda. A daidai lokacin Garba ya yi sallama ya shigo, Faruk ya dan daure fuskarsa.
RAHMA
Cikin fara'a
Garba, sannu da zuwa.
GARBA
Yawwa, anti Rahma. Ina kwana? Suka gaisa a takaice, Rahma ta koma wajen su Kande tana karasa shirya yarinyar.
GARBA (CONT'D)
Ya dan risna
Barka da a asuba.
FARUK
Lafiya lau, an tashi lafiya? Ya nufi wajen teburin abinci, Garba na biye dashi suka zauna, Yayin da Rahma da Kande ke ta kokarin hada Hafsat I.
FARUK (CONT'D)
Ina fatan dai lafiya.
GARBA
Cikin matsakaiciyar murya Daman wata magana ce a game da yarinyar da nake nema da aure.
FARUK
Fuskarsa ta sauya
Matar ka da kuka rabu ko dai wata ce dabam?
RAHMA
Ta dan yi jim alamar ta ji abin da Garba ke fada.
GARBA
Ita wannan bamu dade da haduwa da ita ba, to yanzu iyayenta suka ce ta fitar da wanda ta ke so. Ya yi shiru.
Kande ta mikar da Hafsat I tana goya mata jakarta a baya.
FARUK
Kuma tace kai ta ke so.
GARBA
Ya dan sunkuyar da kai
FARUK
Kai nake saurare, saboda a kan hanya nake.
GARBA
To shine nazo dan na samu akai kudin auren, da kuma sauran shirye shirye.
RAHMA
Ta zo ta same su, rike da Hafsat I. Ta shirya.
FARUK
Ya dada gyara zama
Wato na fuskanci Namajuju ne kai, a aure aure za ka dawwama.
GARBA
Ya dago kansa da sauri.
FARUK
In ba haka ba me zai hana ka dawo da matarka?
GARBA
Ai saki uku na yi mata.
FARUK
Fuskarsa cikin karin damuwa Saki uku? Hakika ka cika sakarai shashasha mara hankali.
RAHMA
Yarinyar nan za ta makara. Ku tafi tare mana sai ku tattauna ko kuma kai Garba ka bari gobe in ya dawo daga Kaduna ka zo nan gida da yamma ka same shi.
GARBA
Ya daga kai ya kalleta.
FARUK
Cikin fusata ya mike
Ai ko ya zo babu abin da zan yi masa. Ya wuce ya nufi kofa.
RAHMA
Ta bishi da kallo cikin rashin jin dadin abin da ya fada. Garba ya mike jikinsa a sanyaye, ya nufi kofa shima. Faruk kamar ya tuna wani abu ya juyo ya dawo ya nufi daki. Garba ya fita.
RAHMA (CONT'D)
Ta bi faruk a baya
Yaya ka dawo?
FARUK
Mantuwa na yi.
Ya bude kofa ya shiga daki,
RAHMA
A tsaye cikin jimami rike da yarinyar, sannan ta ja ta suka fita.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - MORNING
Fuskar motar Faruk na kallon kofar fita, motar Rahma daga gefe.
GARBA
Na jikin motar Faruk a tsaye yana fuskantar kofar fita.
RAHMA
Rike da Hafsat I suka fito, ganin Garba a inda yake yasa ta yin sarsarfa.
Garba. Garba ya juyo ya kalleta cikin damuwa
RAHMA (CONT'D)
Nace ka tsaya mana ka yi karin kumallo a nan.
GARBA
Yana girgiza kansa
Na ci abinci kafin na zo. Faruk ya fito yana sanya bandir din kudi a aljihunsa.
RAHMA
Shiga mota Hafsat.
Ta tare Faruk tun kafin ya karaso.
HAFSAT I
Baffa budemin.
GARBA
Ya harare ta.
HAFSAT I
Cikin jin tsoro ta bude ta shiga ta zauna.
RAHMA
Cikin sauke murya
Ban ji dadin abin da ka yi ba. Me yasa za ka fada masa haka?
FARUK
Ya tsaya ya tsare ta da ido Dan me ba zan fada masa haka ba?
RAHMA
Amma dai kasan yin auren sa shi yafi da ya zauna haka ko?
FARUK
Ba abin da zan yi a kai, dukiya ta bata yin aure-aure ba ce. Ina da abin da yafi muhimmanci sama da yin aure - sakin da ya ke yi. Kamar zai wuce.
RAHMA
Ta sake shan gabansa
Dan uwanka ne fa ya dace ka manta da kuskuren da yayi a baya.
FARUK
Nace ba zan yi ba! Ko dole ne? Ya wuce ya nufi motar, Garba ya kauce daga jikin motar ya koma daga dan nesa ya tsaya. Faruk yana hararar Garba ya bude kofar motar ya shiga. Rahma ta biyo shi.
RAHMA
Shi kenan haka za ka kyale shi? Cikin girgiza kai yasa hannu a aljihu ya dauko kudi ya kirga ya bata, ya zuba ragowar a kan dash board yana kokarin tashin motar.
RAHMA (CONT'D)
Ta karba tana kallon ragowar da ya ajiye. Shi kenan abin da za ka bashi?
FARUK
Ya juyo ya kalle ta, kafin yayi magana ta duma hannu ta debi kari.
RAHMA
Gaskiya sai ka kara masa. Faruk ya bude kofa zai fito.
HAFSAT I
Kamar za ta yi kuka
Abba mu tafi zan makara. Faruk ya fasa fitowa ya koma ciki, ya tashi motar. Rahma ta nufi wajen da Garba yake a tsaye. motar ta fita daga harabar.
RAHMA
Ta mikawa Garba kudin
Karbi wannan yace a baka, gobe ka zo ka same shi a gida in ya dawo.
GARBA
Ki bar masa kudinsa kawai.
RAHMA
Cikin daurewar fuska
Me kenan da hausa? Fushi ko kuwa me?
GARBA
Babu komai.
RAHMA
To in dai ba fushi ka yi ba ka karba.
GARBA
Ya dan yi jim sannan ya karba Shi kenan sai goben na dawo.
RAHMA
Ta saki fuskarta
Wajen yamma sai kazo lokacin ya dawo. Suka yi sallama ya juya ya fita, ita kuma ta nufi cikin gida.
EXT. AKAN HANYA (CIKIN MOTA) - MORNING
FARUK/HAFSAT I
Cikin mota a zaune kowanne da seat belt sun nufi makaranta.
EXT. MAKARANTA (BAKIN KOFA) - MORNING
Motar ta tsaya. yayin da Security ke ci gaba da aikin su.
HAFSAT I
Abba in za ka dawo za ka sayomin biskuit?
FARUK
In Allah ya yarda zan sayo miki, Hafsat.
Ya shafa kanta. Maza shiga makaranta.
HAFSAT I
Abba a dawo lafiya.
FARUK
Allah yasa, Hafsat.
Ya bude mata kofa ta fita, ta daga masa hannu shima haka tana tsaye, ya bar wajen cikin matsakaiciyar tafiya har ta daina ganin motar sannan ta yi cikin makarantar da gudu ta nufi aji.
INT. GIDAN ASABE ( FALO) - DAY
GARBA
Na zaune suna fuskantar juna da Asabe.
ASABE
Cikin nuna tsana
Wa! Rahma? Duk wannan abin da ta yi maka munafunci ne.
GARBA
Yayi shiru yana kallon yayarsa cikin mamaki. Rahman?
ASABE
Kai yaro ne, sai dai ka yi hakuri. In kuma kana da wasu 'yan kudi a wajenka sai ka har hada ka kawo a san yanda za'a yi a kai gidan su yarinyar.
GARBA
In ina da shi yaushe zan je wajensa?
ASABE
Cikin takaici tana girgiza kanta Amma Rahma ba ta ji dadin rayuwarta ba.
Ta yi ajiyar zuciya To yanzu yaya kenan za'a yi, Garba? Baraka ce ba mai son a taru a rufawa juna asiri ba da sai a hadu a san yadda za a yi.
GARBA
Ya dakatar da ita da hannu Kada ma ki sake cewa komai a kan Baraka itama 'yar goyon bayansa ce.
ASABE
Na ma tuna ba ta son a fadi laifin sa ko miskala zarratin.
GARBA
Za'a kai kudi. Ni kawai so na ke ki yiwa Malam Usman magana in lokacin yayi shi zai wuce gaba a kai kudin.
ASABE
Ta yi kasa da murya
Faruk din fa?
GARBA
Kawai ki bar maganarsa. Ni dai ki yi min abin da nace.
Ya mike tsaye.
ASABE
Ta bishi da kallo daidai lokacin da Mal. Usman ya dan yi tari daga daki.
Tafiya za ka yi?
GARBA
Wajen yarinyar zan je, nace su dan daga min kafa zuwa nan da mako biyu.
ASABE
Ta mike suka nufi tare. Rahma, ai sai dai Allah yayi mana hisabi tsakanin mu. Shi kenan sai ka dawo.
Garba ya bude kofa ya fita, Asabe na juyowa taga mijinta Mal. Usman (52) a tsaye a bakin kofa rike da jarida a hannunsa.
ASABE (CONT'D)
Cikin fara'a ta nufo wajen zaman ta Malam har ka farka daga baccin?
MAL. USMAN
Idona biyu.
Suka zauna kusan tare.
ASABE
Ashe ka ji sakon da Garba yace na shaida maka.
MAL. USMAN
Ya fara buda jaridar
Ina jin hirar da kuke yi. Kuma abin da zan sake baki shawara a kai shine, koda yaushe ki zama mai gyara tsakanin mutane ba mai kokarin bata wani ko zarginsu a kan abin da baki da yakininsa ba.
ASABE
Cikin kwaikwayon rashin fahimta Me na yi kuma Malam?
MAL. USMAN
Ni dai na gaya miki.
Ya ci gaba da duba jaridarsa.
EXT. KOFAR GIDAN SU MURJA - DAY
Garba da Murja a tsaye suna tadi.
MURJA
Tana yi masa wani irin kallo Wai kuwa Garba da gaske kana so na?
GARBA
Ya kalle ta cikin mamaki Wace irin tambaya ce wannan, Murja?
MURJA
Ai dole na tambaye ka, saboda har yanzu ka kasa yin komai a game da zancen kawo kudin da muka yi da kai. Gashi kuma jibi ne wa'adin da iyayena suka deba min dan na gabatar da wanda nake so garesu, ko kuma su aurar da ni ga duk wanda suka ga dama.
GARBA
Nima yanzun dalilin zuwa na kenan dan ki kara min lokaci in karasa 'yan shirye shiryen da suka rage.
MURJA
Cikin mamaki ta kama baki Yanzu kawo kudin zance ne sai ka wani shirya sai kace gobe daura aure?
GARBA
Amma kinsan na fada miki Yaya na na ke son sanarwa tun da su zasu kawo kudin.
MURJA
Jiya da zamu rabu ai cewa ka yi ba za ka dawo nan ba sai ka je ka same shin.
Ta kawar da kanta Gaskiya Garba in kasan baka shrya yin aure ba kada ka yaudare ni.
GARBA
To ai naje na same shin a yau.
MURJA
Ta dan saki fuskarta ta juyo gareshi
GARBA
Amma tunda kika ji na fada miki haka, kinsan akwai matsala saboda har yanzu yaki bani kudi na a hannu na.
MURJA
Cikin kosawa
Ina ganin kawai muna batawa junan mu lokaci ne. Ta juya za ta koma gida.
GARBA
Cikin damuwa da mamaki, yana kokarin fito da kudi daga aljihunsa.
Murja yaya za ki yimin haka? Ga kudin man da kika ce na sayo miki.
MURJA
Ta sake waigowa
Ka je ka hada ka kawo kudin zancen da su. Ko duk ranar da ka sami kudin da za akawo gidan namu, ka dawo. Ta juya ta nufi gida.
GARBA
Ya bita da kallo har ta shige gida, sannan ya juya ya tafi.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - AFTERNOON
Rahma da Hafsat I suna zaune a kan doguwar kujera sun harde suna tafa-tafa.
KANDE
Ta fito daga cikin kitchen ta zo ta sami Rahma. Kawo kudin maganin na je maza na dawo.
RAHMA
Ta bude jaka ta dauko dari biyar ta baiwa Kande Ki sayo kwali daya.
Kande ta tashi ta fita, Rahma da Hafsat I suka ci gaba da tafa-tafa, har ya zuwa lokacin da wayar da ke kan teburin ta fara kara. Rahma ta tashi ta je ta dauka.
RAHMA (CONT'D)
Ta kai kunnenta cikin sauraro. Hello!.. wa alaikamus salam. Fuskarta ta fara sauyawa cikin yanayin tashin hankali, yayin da wasu hawaye suka fara biyo kuncinta, ta juya ta kalli inda Hafsat I take tana wasa ba tare da sani ba.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - MORNING
Mutane sun yi sahu, gawar Faruk a cikin makara za a sallace ta.
MAL. USMAN
A sahun gaba.
INT. GIDAN ASABE ( FALO) - MORNING
RAHMA
A zaune kan darduma cikin lullubi fuskarta na hawaye.
KANDE
Cikin kuka kusa da Rahma a zaune.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - DAY
Mutane a zaz zaune ana zaman makoki
GARBA
Daga tsakiya yayi shiru kamar mai tunanin wani abu.
MAL. USMAN
Daga gefen Garba suna amsar gaisuwa tare.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - DAY
Rahma rungume da Hafsat I da Kande a kusa da ita, Baraka da Tani da Haj. Laure, a waje daya. Asabe da wasu mata biyu daga bangare guda. Uwani da wata dattijuwa su kuma aje daya. Kowacce cikin yanayin alhini.
RAHMA
Cikin hawaye
Inna lili lahi wa inna ilaihir raji'un.
TANI
Ta yi ajiyar zuciya
Kullu nafsin za ikatul mauti.
HAJ.LAURE
Cikin muryar ban tausayi Kowane mai rai macaci ne. Muma zaman jiranta muke yi.
BARAKA
Cikin tsananin damuwa
Allah ka jikan Yaya da rahma.
KANDE & CO
Amin.
Zuwa wani dan lokaci, Haj.Laure da Tani suka mike.
HAJ.LAURE
To mu za mu koma, sai kuma ranar sadaka. Allah ya kara hakuri.
RAHMA
Fuskarta cikin hawaye
Ku gaida gida. Haj. Laure da Tani suka durkusa a gaban Asabe.
TANI
To yaya za mu koma.
ASABE
Tani, an gode Allah ya bada lada. muje na taka muku.
Suka mike suka fita tare. Baraka ma ta mike ta bisu a baya.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - DAY
Mutane na zazzaune, Asabe da Haj. Laure da Tani suka fito suka raba za su wuce, suka dan tsaya daga gefe, Asabe ta yafito Garba da hannu. Mal. Usman ya fara gani sannan ya nunawa Garba, ya tashi yaje ya same su.
ASABE
Su Haj. Laure ne za su tafi, shi yasa na kira ka dan mu ji yanda za' a yi da Hafsat tun da suma suna da hakki a kanta.
GARBA
Cikin nuna fahimta
Gaskiya dai ya kamata tun yanzu musan wanda zai rike ta.
ASABE
Ta juya tana kallon su Haj. Laure Kusan bai dace a barta a hannun Rahma ba, ko kuwa?
HAJ. LAURE/TANI
Suka kalli juna daidai da isowar Baraka garesu.
BARAKA
Ta cafe zancen
A gaskiya Yaya Asabe a bar yarinyar nan a wajen Rahma, dan ni dai ban ga amfanin raba ta da uwarta ba.
HAJ. LAURE/TANI
(Cikin hadin baki)
Wallahi kin riga mu a fili mun riga ki a zuci.
TANI
Muma abin da muke so muce kenan, a bar ta ta ci gaba da zama da uwarta dai zai fi.
Asabe kamar za ta yi magana sai suka hada ido da Mal. Usman daga inda ya ke a zaune yana kallonta, fuskarsa kamar cikin yanayin da ke nuna zargi gareta.
GARBA
Yana yiwa Baraka wani irin kallo. Dole dai a san yadda za'a yi.
ASABE
Daman ai ba za'a rasa mai rike ta ne, amma tunda sun fadi haka ai shi kenan.
BARAKA
Ko ma dai za a yi a bari mana a gama jimamin abin da ya faru.
GARBA
Ya juya ya koma inda ya taso.
TANI
Ai bai ma kamata a ce za'a yi wannan maganar a yanzu ba.
HAJ. LAURE
Cikin nufin abin da za ta fada Ukn, ukn, Tani. Gwara dai a yi yanzu.
ASABE
Cikin rawar jiki da rudewa Ai wallahi shi kenan a bar maganar.
HAJ. LAURE
Ta yi mata wani kallo
A to. Tani mu tafi. Suka tura kofa suka fita, Baraka da Asabe suka juya suka nufi cikin gidan, Asabe na satar kallon Mal. Usman wanda ke cke da nuna jin haushin abin da ta yi.
INT. GIDAN ASABE ( FALO) - DAY
ASABE
Ta gama kukkulla gyada a leda ta zuba a karamin faranti, ta dangwarawa Hafsat I a ka.
HAFSAT I
Cikin yin kuka rigarta a yage, ta fita dauke da farantin talla.
EXT. CIKIN UNGUWA (KWARARO) - DAY
HAFSAT I
Dauke da farantin talla sanye da wata yagaggiyar riga. Ta nufi wajen wasu mutane da ke cin abinci ta tsaya tana kallon su.
MAZA BIYU
Suka dan rage kadan daga abincin, suka mikawa Hafsat I.
HAFSAT I
Ta ajiye farantin ta zauna ta fara cin abincin.
MAZA BIYU
Suka juya za su tafi, daya cikin tausayawa Hafsat I, dayan kuma ya zira mata ido yana yi mata kallon sha'awa. Abokinsa har ya dan yi gaba ya dawo ya ja shi suka tafi.
INT. GIDAN GARBA ( FALO) - NIGHT
Agogo na nuna Tara da minti goma.
HAFSAT I
A gefen kujera ta takure, sanye da kayan makaranta duk sunyi dukun dukun jakarta ta makaranta na kusa da ita.
MURJA
Ta taho wajen Hafsat I a fusace da wata 'yar robar abinci, ta daka mata tsawa ta jawo ta gaba, sannan ta dangwarar mata da kwanon abinci a gabanta. Bayan ta galla mata uwar harara, ta koma daki ta barta.
HAFSAT I
Ta fara cin 'yar farar shinkafar da ke cikin kwanon, hannu baka - hannu kwarya.
GARBA
Ya shigo kamar bai san tana wajen ba, ya wuce ya shige daki.
EXT. GIDAN GARBA ( KOFAR GIDA) - MORNING
Motar Faruk a ajiye, a bakin kofar gidan.
GARBA/MURJA
Cikin shirin zuwa unguwa suka fito suka shiga motar, suka tafi.
Dan jimawa kadan Hafsat I ta fito ko dan kwali babu gashinta duk yayi dukun - dukun, riga dabam wando dabam.
HAFSAT I
Ganin ba sa nan ta runtuma a guje ta nufi daya bangaren.
EXT. CIKIN UNGUWA (KUSA DA TITI) - DAY
HAFSAT I
Cikin galabaita tana tafiya ta nufo titi.
RAHMA
A motar ta, har ta wuce sai ta hangi Hafsat I. Nan da nan ta ja burki ta fito ta yiwo wajen Hafsat I a guje, suka rungume juna Rahma cikin tashin hankalin ganin halin da ta samu Hafsat I.
ASABE/GARBA
Suka tsaya a kanta cikin fusata.
RAHMA
Ta dago kai a hankali. Ganin su ya dada tayar mata da hankali, ta kwakwume Hafsat I, Asabe da Garba kokarin na kokarin kwace ta.
INT. GIDAN FARUK ( DAKIN RAHMA) - NIGHT
RAHMA
Kwance a kan gado tana kici - kici da bargo, ta farka a gigice.
A uzu bil lahi minash shaitanir rajim. Ta dan yi shiru, sannan ta tashi da sauri ta bude kofa ta fita.
INT. GIDAN FARUK ( DAKIN HAFSAT) - NIGHT
Akan gado, bargo ne a kudundune kamar ba mutum a ciki.
RAHMA
Ta shigo da sauri kamar an jeho ta, ta kalli yanda bargon yake. cikin yanayin karin tashin hankali, ta je ta bankada bargon.
HAFSAT I
A takure tana bacci.
RAHMA
Ta yi ajiyar zuciya, ta zauna kusa da ita, ta dan yi shiru, sannan ta kwanta a gefen Hafsat I.
EXT. KOFAR GIDAN SU MURJA - NIGHT
GARBA
Cikin kaya masu tsada, yana tsaye, Babur din da ya zo a kai na gefe a kafe.
YARO I
Ya fito daga cikin gidan ya same shi Wai tana zuwa.
GARBA
To na gode.
Yasa hannu ya dauko kudi daga a ljihunsa ya baiwa yaron ya tafi. Garba ya dada gyara tsayuwa ya duba agogon hannunsa.
MURJA
Ta fito cikin murmushi ta rufe fuskarta da hannu cikin jin kunya.
Har kasa na ji kunya, dan na yi zaton ba kai bane shi yasa da farko nace na yi bacci.
GARBA
Ya na murmushi
Ni kaina na yi mamaki, shi yasa na sake tura yaron.
MURJA
Ta yi masa wani irin fari da ido. Dan Allah darling ka yi hakuri.
GARBA
Babu damuwa. Yanzun ma sauri na ke yi.
MURJA
Cikin kinaya da shagwaba. Haba dan Allah, kwananka nawa rabonka da zuwa, yanzu kuma mintinanka nawa da har za ka tafi? Ta dada shagwabewa
Wallahi zan maka kuka.
GARBA
Ki kwantar da hankalinki, zan je wani waje ne. Kuma daman na zo na fada miki ne ki sanar da gida za'a zo jibi a kawo kudi da kuma sanya lokacin da za'a daura aure.
MURJA
Murna da jin dadinta da abin da ya fada. Gaba daya?
GARBA
Sannan kuma ni da ke tun daga yanzu mu fara tunanin irin abubuwan da za mu shirya na buki da kuma fatin da za'a yi.
MURJA
Cikin fara'a
Duk abin da kace shi kawai za'a yi.
GARBA
Ya sa hannu a aljihu ya zaro kudi masu dan yawa Shi kenan wajen gobe zan dawo mu san yanda za mu yi. Ga wannan. Ya mika mata kudin.
MURJA
Cikin nuna kunya
Dan Allah ka barshi.
GARBA
Ya dan sauya fuska
Kin raina kenan.
MURJA
Ta sake marairiacewa
Haba darling? To kawo. Ta karba har da dan rusnawa. Suka yi sallama ya hau babur ya tafi. Ba ta koma ciki ba har sai da ta daina ganinsa.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - DAY
RAHMA
Na daga gefe a kasa a zaune cikin lullubi. Mal. Usman da Mal. Hamza na kan doguwar kujera, Asabe na kan mai daya.
ASABE
To daman shine nace in dai tana ganin za ta iya zama dashi shikenan sai ya tare anan din. in kuma gidan za ta koma to.
MAL. USMAN
Ai daman nasan duk kece za ki fito da wannan tsirfar.
MAL. HAMZA
Ai shawara ta kawo ko?
MAL. USMAN
To indai haka ne, a raba gadon nan a yanzu shine mafi sauki. Menene amfanin jinkirin?
MAL. HAMZA
Ya dakatar da shi
Ai Malam Usman wannan mai sauki ne. amma a bari a kammala dukiyar tasa waje guda, sannan a yi bincike a biya masa basussukan da suka rage, in yaso sai a yi abin da za'a yi. Gadon nan fa na sune su da yarinyar da ya bari. Sai kuma ita da ke da tumuni. To ai kaga duk abin ba wani na tayar da hankali ba ne.
RAHMA
Ta ja mayafinta ta kara rufe jikinta sosai.
ASABE
Yawwa Malam, kuma bukin nan saura mako guda, in ba nan ba, a ina zai zauna?
MAL. HAMZA
Nima shawarar da muka yanke da Uwani kenan, tun da bukin shi Garba ya matso sai ita Rahma ta koma gida ta karasa takabar a can. Ko kuwa me ka gani?
Rahma ta yi shiru tana share hawaye, yayin da Asabe ke satar kallonta ta wutsiyar ido.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - EVENING
RAHMA
Tana zaune a kan kujera, cikin yanayin damuwa kamar tana tunani.
INT. GIDAN FARUK ( DAKIN RAHMA) - DAY
RAHMA
A zaune kan sallaya ta idar da Salla. Baban Hafsa, maganar sake pentin gidan nan, kwata kwata kama daina yin ta. Ko sai ka dawo daga Kadunan za mu sa rai?
FARUK
Yana tsaye yana sanya hularsa, ya dan yi dariya. Rahma kenan. Ai ni gaba daya ma na fasa yi. Menene na wani yiwa gida fenti sai kace mutum zai dawwama a cikinsa?
(Ya dauki agogonsa ya nufi kofa zai fita.)
RAHMA
Ta bishi da kallo tana kokarin mikewa tsaye Yanzu shi kenan ba za'a yi fentin ba?
FARUK
Ba zan yi musu fenti su shiga ba. Ya bude kofa ya fita.
RAHMA
Fuskarta ta sauya
Ban gane ba. (Ta dauki jakarsa ta bude kofa ta fita.)
INT. GIDAN FARUK ( DAKIN RAHMA) - MORNING
RAHMA
Zaune kan sallaya rike da jarbi cikin alhini, wasu kayan sawa da sarka da kudi a kai na kusa da ita. Karar rufe kofar yasa ta rintse idanunta, sannan ta bude yayin da wasu hawaye suka biyo kuncinta.
KANDE
Ta yi sallama ta shigo ta durkusa a gaban Rahma. Na gama harhada kayan kicin din.
RAHMA
Na cikin firinjin fa?
KANDE
Shima na wanke ba komai a cikin sa.
RAHMA
Ta fara dauko kayan ta ajiye a gaban Kande. Ga wannan, kya karasa aikin gida da su.
KANDE
Ta sunkuyar da kanta ta fara shashshekar kuka Ni dai ba abin da zan ce sai dai Allah ya jikan Faruku da rahma.
RAHMA
Hawaye itama suka biyo kuncinta. To yaya za'a yi.
KANDE
Cikin shashshekar kuka
Rahma ki gafarce ni in na yi miki kuskure a halin zaman mu.
RAHMA
Wallahi Kande babu komai, Allah ya yafe mana gaba daya.
Suka sake fashewa da kuka. Sannan Kande ta mike za ta fita.
ASABE (O.C.)
Rahma! Rahma!!
KANDE
Ta waigo a dan firgice ta kalli inda Rahma ta ke a zaune suka hada ido ta bude kofa ta fita.
RAHMA
Cikin yanayin razana
Na'am! Yaya. Tana kokarin mikewa.
INT. GIDAN FARUK ( FALO) - MORNING
Asabe na zaune a kan kujera, Garba ma haka cikin karewa falon kallo. Kande ta fito daga dakin za ta wuce.
KANDE
Cikin ladabi
Sannunku da zuwa Yaya. Ina kwana?
ASABE
Lafiya.
Garba yana kallon wani waje, Kande ta bude kofa ta fita.
ASABE (CONT'D)
Ta bita da kallo
Gayyar na ayya.
RAHMA
Ta fito cikin lullubi ta nufo kujera za ta zauna Yaya ke da Garba ne, sannun ku da zuwa.
ASABE
Ta gyara zama
Daman maganar karbar Hafsat ce ta kawo mu, kinsan rannan ba muce komai a kai ba. To shi ne muka zo mu sanar da ke cewar idan gobe za ki tafi sai ki kawo ta waje na, na fara riketa kafin a yi bukin Garba ya karbe ta ta ci gaba da zama a wajensa.
RAHMA
Alamar damuwa a fuskarta ta kasa magana.
GARBA
Me zai hana yanzu mu jira mu tafi da ita?
ASABE
Cikin murmushin mugunta Ka dai bari goben.
Ta juya ga Rahma Ai kin fahimci abin da na ce ko?
RAHMA
Ta yi shiru kanta a sunkuye.
ASABE
Ta shi muje Garba.
Suka mike suka nufi kofa, Garba ya fara fita, ita kuma ta dan saurara a bakin kofar ta juyo ta kalli Rahma. Allah ya jikan Faruku. Sannan ta juya ta fita. Rahma ta yi shiru na wani lokaci hawaye na bin kuncinta, sannan ta tashi ta je inda kan tarho ya ke ta dauka ta dialling lamba ta kai kunnenta cikin yanayin saurare.
MURYAR BARAKA
Hello anti Rahma, salamu alaikum.
RAHMA
Ta kasa magana da farko yayin da wasu hawaye suka sa ke biyo kuncinta.
EXT. ZAUREN SHAWARA (WAJE) - EVENING
Motar Faruk da ta Rahma a bakin wajen.
BARAKA (O.C.)
Wallahi ni dai ban goyi bayan a raba ta da ita ba.
GARBA (O.C.)
Ai kuwa ba zai yiwu taci gaba da zama a hannunta ba tun da komai na dangane da gadonta yana hannunmu.
INT. ZAUREN SHAWARA (CIKI) - EVENING
BARAKA
Ni dai maganar yarinya na yi. Mai unguwa da wasu manyan unguwa biyu suna zaune, Asabe a kusa da Baraka, Rahma kuma cikin lullubi rungume da Hafsat I.
MAI UNGUWA
Ya dakatar da su da hannu Wannan ba wani abu ne na tayar da hankali ba. Ke Rahma me kika gani?
ASABE
Ta tsare ta da ido.
RAHMA
Ranka ya dade duk abin da a kaga ya dace shine daidai a wajena. Yarinyar nan 'yar su ce suke da iko da ita.
Garba cikin sakin rai, Baraka cikin nuna rasihn jin dadi.
MAL. HABU
An san da haka, amma ai a yanzu ke ce uwarta, dan haka abinda ya fi masalaha shi za a yi ko dan kyautatuwar rayuwar ita yarinyar.
ALH. JIBRIN
Wannan haka ya ke.
MAL. HABU
Kuma bisa tsarin gaskiya ke yakamata kici gaba da riketa.
GARBA
Ragamar yarinyar hannunta za ta koma kenan dan mahaifinta ya mutu?
MAI UNGUWA
Wa ya ce maka haka?
Ya juya ya kalli Malam Habu Yarinya dai a ke nufin ta zauna wajen ta, sauran hakkokinta ba gaka ba sai kaci gaba da kula da su. Kai ne magajin mahaifinta ko kuwa?
ALH. JIBRIN
In a ka yi hakan an yi daidai.
MAL. HABU
Sai dai kuma kowannen ku sai yayi kokari ya kula da amanar da ke hannunsa.
Garba kamar zai yi magana, Asabe ta hana shi da ido.
ASABE
Shi kenan, Allah ya taya riko. Baraka kamar ranta bai so ba.
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - EVENING
RAHMA
Cikin lullubi tana zaune tana karatu.
UWANI
Ta fito daga ban daki, ta dan tsaya ta kalli Rahma kafin ta ajiye butar ta zo ta shiga daki.
HAFSAT I
Ta dawo daga islamiyya ta zo ta zauna kusa da Rahma.
EXT. SNACK SHOP - DAY
Motar Faruk a ajiye a kofar wajen.
GARBA/MURJA
Sun fito rike da abubuwan da suka sayo a cikin leda. Suka shiga mota, ya saki sauti, ya juya suka bar wajen.
EXT. AKAN HANYA (BABBAN TITI) - DAY
Motar Faruk na wucewa, kida na tashi daga cikinta.
GARBA
Hannunsa daya na kan sitiyari ya karkace yana tukawa.
MURJA
A gefe a zaune tana wasa da waya tana rausayawa daga zaune. Motar ta nufi rukunin gidajen G. R. A.
INT. GIDAN BUKI - DAY
Mata sun hadu ana ta hayaniyar buki.
RAHMA
Ta shigo gidan cikin lullubi.
TANI
Ta tare ta da fara'a.
Lah! Rahma ai na dauka ma ba zaki zo ba. Ashe kin fita daga takaba?
RAHMA
Cikin yake
Wajen sati biyu.
TANI
Cikin raha.
Ai ba mu ga sadaka ba.
RAHMA
Wace sadaka zan yi banda addu'ar da na ke masa a koda yaushe. Suka yi dariya suka nufi wajen su Baraka.
BARAKA
Ta rungume Rahma
Anti Rahma, o yo yo!
RAHMA
Ni dai kada ki kayar dani.
BARAKA
Cikin murmushi ta dan kalli Rahma An dai fita? To Allah ya bada ladan takaba.
HAJ. LAURE/TANI
Suka amsa kusan lokaci guda.
BARAKA
Allah ya kawo wani bazawarin da gaggawa.
RAHMA
Kinji ta kuma, za ta bata rawar da tsalle.
HAJ. LAURE
Cikin fara'a
Ai addu'a ta yi, sai dai ace ba ta karasa da cewa na gari ba. Suka sake kwashewa da dariya.
HAJ. LAURE (CONT'D)
To Baraka ki ji da ni maganar wadda za ta yiwo mana Cincin da Cake da samosa da meat pie din nan. Ta dan yi shiru tana saurare.
BARAKA
Ni dai a yanzu kam bani da wadda za ta yi mana.
Ta kalli Tani Ke ce mai kawaye da yawa.
TANI
Kema ba ki samu ba, sai ni.
BARAKA
Anti Rahma ki taimaka mana.
RAHMA
Ta dan yi dariya
Akwai wata da nasan tana yi.
Dakkaninsu suka nuna jin dadi.
HAJ. LAURE
Yawwa! Rahama dan Allah ki taimaka mana, mu fita kunya.
RAHMA
Tana murmushi
Nasan in dai na same ta za ta yi, amma ita matasalar daya.
HAJ. LAURE
Cikin nuna matsuwa
Menene mastalar?
RAHMA
In dai kana son aikinta a kan lokaci to sai ka bata rabin kudin aikin.
Alamar sakin rai a fuskar Haj. Laure da Tani.
HAJ. LAURE
In wannan ne ta kwana gidan sauki. Nawa zan baki kije da shi?
EXT. KASUWA - DAY
RAHMA/KANDE
Ta kawo wasu kayan ta tana sayarwa. An saya an bata kudin, ta juya ta tafi.
EXT. KASUWA - DAY
RAHMA/KANDE
Suna sayayyar kayan aiki.
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - EVENING
RAHMA/KANDE
Sun hada gumi suna yin aikin tare sun kusa kamallawa.
UWANI
Ta zo ta dauki wani abin tana yi. Rahma ta bar abin da ta ke yi, ta zo zata karbe ta, Uwani ta hana ta.
INT. GIDAN BUKI - EVENING
Mata na ta hayaniya an ta kaiwa da kawowa, wasu na aikin abinci. Tani ta zo ta sami Haj. Laure.
TANI
Kayan party kada a manta.
HAJ. LAURE
Tayi kamar ta tuna
Allah ya shi miki albarka. Ina Baraka?
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - EVENING
Manyan robobi na aiki wasu a rufe, Kande na karasa rufe wata babbar roba mai dauke da kayan cincin da leda. Rahma a gaban kaskon tuya ta hada gumi kashirban. Hafsat I na daga gefe a kan tabarma da littafi tana karatu.
KANDE
Yaya, wannan ma ya kamalla.
RAHMA
To Kande. Ba ri na karasa sai na je na samo tasi mu yi maza mu kai musu kada lokaci ya kure.
KANDE
Tana kokarin daukar robar Bari na leka kofar gida ko za'a samu.
Rahma ta taso ta kamawa Kande su ka kinkima suka ajiye daga gefe. Rahma ta koma kan kaskon tuya. Kande ta nufi kofa zata fita, suka yi kacibus da Baraka tana shigowa.
BARAKA
Salamu alaikum.
Kande da Rahma suka amsa kusan lokaci guda, Hafsat I ta tashi taje ta rungume Baraka.
HAFSAT I
Anti sannu da zuwa.
BARAKA
Ta kasa amsawa Hafsat I sai dai ta kama hannunta ta rike.
RAHMA
Ta juyo cikin fara'a
Sannu da zuwa.
KANDE
Wannan fitar da zan yi ta neman mota ce.
BARAKA
Cikin matukar mamaki a inda ta ke a tsaye rike da Hafsat I.
RAHMA
Karaso ga kujera.
Ta janyo wata karamar kujera kusa da ita.
BARAKA
Tana rike da Hafsat I ta zo ta zauna kusa da Rahma Bangane da yin tuya a gaban wuta ba.
KANDE
Maganar samo motar.
RAHMA
Tana kallon Baraka
Da ke ta ke.
BARAKA
Ba tare da dauke idonta daga kan Rahma ba Da mota nazo.
RAHMA
Kin ji da mota ta zo Kande. Kande ta koma kan wani aikin.
BARAKA
Haba Anti, gaskiya ban yi zaton za ki yi mana haka ba.
RAHMA
Ta ci gaba da abin da ta ke yi Sana'a sa'a ko kuwa?
BARAKA
Don Allah Anti Rahma daman ke ce za ki fara sana'ar nan, amma ba ki fada ko jari a karba a cikin gadon Hafsat a baki ki rinka juya ba.
RAHMA
Ta tsame wanda ke kan wuta ta yi wata 'yar karamar dariya Baraka kenan kudin makarantar ma kun gagara ku biya, ina kuma ga bani jarin yin kasuwanci...
BARAKA
...dakata Anti. Kina nufin ba a biya kudin makarantar ta ba?
RAHMA
Kwarai kuwa.
Ta tsare Baraka da ido.
EXT. MAKARANTA (HARABA) - DAY
HAFSAT I
A zaune a barandar aji rungume da jakarta da wata takarda a hannunta cikin damuwa. Motar Rahma ta shigo, har ta yi parking Hafsat I ba ta tashi ta je ba.
RAHMA
Ta fito tana duba agogo alamar ta shigo kafin a tashi, ta je ta same ta ta tsuguna a gaban Hafsat I. Fitowa kika yi kafin ku tashi ko?
HAFSAT I
Ta girgiza kanta
Ba a barni na shiga aji ba.
RAHMA
Nan da nan fuskarta ta sauya An hana ki shiga aji?
HAFSAT I
Ta mika mata takardar da ta ke rike da ita. Wannan a ka bani.
RAHMA
Ta karba ta duba, yanayin damuwa a fuskarta, ta mike tsaye. Taso mu tafi.
Ta kama hannun Hafsat I suka nufi gun motar suka shiga Rahma ta rufe kofa.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - DAY
RAHMA
Ta bude kofa ta fito daga motar, ta nufi cikin gidan da sauri. Motar Faruk na ajiye a wajen.
GARBA
Yana fitowa daga cikin gidan.
MURJA
Na biye dashi. Ganin Rahma yasa suka dan dakata ta zo ta riske su.
RAHMA
Salamu alaikum.
MURJA
Tana yi mata wani kallo.
GARBA
Rahma lafiya?
RAHMA
Wurinka na zo. Naje ofis ance baka nan shine na biyo ka gida.
GARBA
Yana murmushi
Kinsan yanzu Allah ya kawo hutu, bana fita da wuri tun da muma yanzu sai dai muyi yanda muke so. mamaki ya bayyana a fuskarta ta yi shiru ba ta ce komai ba.
MURJA
Ta fara wata irin yankwana. Darling ka yi maza ka tafi, yunwa na ke ji.
GARBA
Kinga sauri na ke yi, zan je na sayo wa matata abinci. Me zai hana ki dawo wani lokaci?
RAHMA
Maganar kudin makarantar Hafsat ne ya kawo ni saboda yau ba a barta ta shiga aji ba.
GARBA
Ya yi kwaikwayon tunawa Ai ni na manta. Kuma a gaskiya yanzu ba kudi a kasa, sai dai ki bari farkon watan gobe sai aje a biya. In kuma ke za ki zo ki karba sai kizo ofis ki saman, amma ba gida na ba, dan bana son a rinka zuwa wajena ko da yaushe.
RAHMA
Cikin mamaki
Kudin makarantar da za'a biya ne babu? Amma Garba in ka yi haka ba ka yi adalci ba.
GARBA
Ke Rahma wallahi ki kiyayi halshenki kinji ko!
Yana nuna ta da yatsa
RAHMA
Garba ni ka ke dakawa tsawa?
GARBA
Yimin shiru! Ko kuma na lakada miki dan banzan duka a gidan nan. Ya daga hannu kamar zai dake ta.
RAHMA
Ta dakatar da shi da nunin yatsa Saurara!
Garba ya sauke hannunsa ya yin da Murja ke cike da tsoron ganin yanda fuskar Rahma ta canja. Ta dawo ta rakube a bayan Garba.
RAHMA (CONT'D)
Ka da kuskura hannunka ya taba jiki na, wallahi sai na yi kasa kasa da kai.
MURJA
Dan Allah darling ka rabu da ita ka je ka siyomin snack din.
GARBA
Ya dan saci kallon Murja yayi ajiyar zuciya, ya kalli Rahma. Kin ci arzikin halin da matata ta ke ciki, amma da kinga yanda a ke wulakanci.
Ya nufi wajen motar Faruk.
RAHMA
Kai ma kuwa da ka gane kuskurenka.
GARBA
Ya bude mota ya shiga. Kada ki sake na dawo na same ki a gida na. Ya ja motar ya fita.
RAHMA
Shashasha mara kunyar banza mara kunyar wofi. Maciji wanda baya ramin kansa.
Ta je ta bude motarta ta shiga sannan ta waigo ta kalli Murja. Ke kuma kallon me kike yimin?
MURJA
Cikin jin tsoro.
Allah ya baki hakuri. Ta juya sum sum ta shige gida. Rahma ta tuka ta fita.
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - DAY
UWANI
Ina ke ina tanka masa uhmn?
RAHMA
Ai wallahi ba zan kyale ba tun da dai dukiyarta ce. Mun riga munsa kafar wando daya da shi kenan.
MAL. HAMZA
Ya leko daga daki
Me kike cewa Rahma?
RAHMA
Ta sunkuyar da kanta.
MAL. HAMZA
Ya karasa fitowa
Daman abin da kike so kiyi kenan, shi yasa kika je kika same shi dan kuyi tashin hankali da shi.
RAHMA
Maganar kudin makarantarta...
MAL. HAMZA
Ya tari numfashinta
Kudin makaranto! Nace makaranto!! Ya tsaya a kanta To bari na gaya miki, daga yau kada na sake jin kin yi wata magana a game da hakkin Hafsat, in kuwa ba haka ba, za ki gamu da bacin ran da baki taba gani ba.
UWANI
Ni kaina sai da na gargade ta.
MAL. HAMZA
Kaga sakarai. In kinsan ba za ki iya rike ta ba, ki mayar da ita gare su mana, ai su sai su rike ta tun da 'yar dan uwansu ce.
RAHMA
Idanuwanta suka cika da kwalla.
MAL. HAMZA
Shashasha wadda ta ke nema ta jawowa mutane abin magana a gari. Ya juya ya fita.
UWANI
Cikin takaici.
Daman abin da na jiye miki kenan. Rahma ta sunkuyar da kanta tana hawaye.
BACK TO:
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - EVENING
Rahma na karasa share hawayen fuskarta.
BARAKA
Ckiin karin harzuka ta mike tsaye Ina zuwa.
Ta nufi kofar fita.
RAHMA
Ta mike tsaye itama Kayan patin kuma fa?
BARAKA
Har ta kai kofa ba tare da ta juyo ba Ga Kande nan ki aiketa ta kai musu. Ta fice ta bar Rahma a tsaye cikin fargaba.
INT. GIDAN ASABE ( KOFAR GIDA) - EVENING
Asabe na fitowa cikin shirin zuwa unguwa, motar taxi na tsayawa a kofar gidan, Baraka ta fito.
ASABE
Alamun fargaba a fuskarta ganin Baraka.
BARAKA
Ta sallami mai taxi.
ASABE
Allah ya yi za ki saman, wajen wunin bukin nan na ke shirin tafiya.
BARAKA
Fuskarta cikin damuwa
Yaya ke kika hana Garba ya biya kudin makarantar Hafsat?
ASABE
Cikin tsorata da mammaki ta kama baki Ni! ko kadan.
Tana girgiza kanta Yaushe rabon da na sa Garba a ido na?
BARAKA
Wannan ai cin amana ne.
INT. OFISHIN FARUK (CIKI) - EVENING
GARBA
Ya dora kafarsa daya kan daya yana waya Kada ki damu nawa ne kudin? Alamar saurare.
MURYAR MACE
Gaskiya zai kai Fifty thousand. Baraka ta yi sallama ta shigo ta tsaya.
GARBA
Ya dan daga kai ya kalli Baraka. ya jinjina kansa Shi kenan zan aiko miki da dubu hamsin din.
MURYAR MACE
Thank you darling. Na gode da yawa, please don't keep me waiting.
GARBA
Kada ki damu, zan kira ki in an jima.
Ya kashe wayar ya sake duban Baraka. Baraka lafiya kika tsayamin kerere a gaba haka?
BARAKA
Mai ya hana a biya kudin makarantar Hafsat?
GARBA
Ya gyara zama yana kallonta saboda babu kudin a kasa a lokacin da a ka ce a biya.
BARAKA
Amma ai har yanzu yarinyar tana gida, kuma ma yaya za'a yi ka ce wai babu kudin da za'a biya, bayan yarinyar abin da a ke samu na riba ma daga dukiyarta ya isa a yi duk wata dawainiyarta.
(CONT'D)
GARBA
Ya daki tebur yana mai mikewa tsaye Ke Baraka! Shiga taitayinki. Wato kun hado baki da Rahma kin zo kici mutunci na ko?
BARAKA
Ta kawar da kai
Kawai malam ka saki dukiyar marainiya.
GARBA
Ba za a bayar ba. kuma wallahi ki fita daga ofis din nan ko kuma naci zarafinki yanzun nan.
BARAKA
Wallahi ba ka isa ba! in ita ta kyale, ni ba zan kyale ba.
GARBA
Ki fita ki barmin ofis nace! Yana kokarin zagayowa cikin fusata.
BARAKA
Tana ja da baya zuwa kofa Zan fita na bar maka ofis mai ofis, amma a kan hakkin Hafsat sai inda karfina ya kare.
GARBA
Ya nade hannun riga yana huci Za Ki fice min daga ofis ko kuwa?
BARAKA
Ta bude kofa ta fita.
INT. MAKARANTA (OFISHIN HEAD MASTER) - DAY
RAHMA
Ta gama kirga kudi ta mikawa head master.
HEAD MASTER
Ya karba ya rubuta reciept ya bata, Rahma ta tashi ta fita.
EXT. HARABAR KOTU - MORNING
Kai da kawowar mutane, wasu a cikin kayan lauya, wasu a kayan gida.
BARAKA
Ta biyo wajen tana 'yan dube - dube, ta tsayar da wani cikin kayan lauya tana tambayarsa.
LAUYA I
Bayan ya gama sauraronta ya nuna mata wata kofa an rubuta MULTI DOOR COURT a saman ta da manyan baki.
INT. MULTI DOOR COURT - MORNING
Wani ma'aikaci a zaune kan kujera da teburi a gabansa mai cike da takardu yana shirya su a cikin wasu file - file.
BARAKA
Ta bude kofa gami da yin sallama ta shigo.
MA'AIKACI I
Ya daga kai ya kalleta
Wa alaikis salam.
BARAKA
Ta isa gareshi
Yallabai korafi nake dashi.
EXT. GIDAN FARUK ( HARABA) - DAY
Garba na fitowa zai shiga mota, Masinjan kotu na shigowa.
GARBA
Malam lafiya?
MASINJA
Yana zaro wata doguwar ambulan Daga kotu na ke a ka ce na kawo maka wannan takardar sammaci ce. Ya mikawa Garba.
GARBA
Kotu kuma?
Ya karba ya farka yana dubawa. Ya gama dubawa ya dago kansa cikin yanayin damuwa.
INT. MULTI DOOR COURT - DAY
Alkalin na wajen zamansa, sauran ma'aikatan kotun na gudanar da ayyukan su, yayin da Tani da Rahma ke waje guda, Garba kuma na daya bangaren tare da Asabe, Mai unguwa da Mal. Habu da Alh. Jibrin da kuma Mal. Usman a waje daya.
BARAKA
Tana mikawa Proscutor wasu takardu Ga kwafi din takardun.
PROSCUTOR
Ya karba ya mikawa Alkali.
ALKALI
Ya karba yana dubawa
Sune abubuwan da ta gada daga rabon gadon nata?
BARAKA
Sune ranka ya dade.
ASABE
Suka hada ido da Mal. Usman ta yi maza ta kawar da kai.
MAL. USMAN
Fuskarsa cikin nuna takaici.
PROSCUTOR
Ka ji dukkan bayanan da a ka gabatar a game da maganar dukiyar wannan yarinya da ta ke hannunka. Haka ne ko ba haka ba ne? Garba ya saci kallon Asabe, suka hada ido ta sunkuyar da kanta.
GARBA
Haka ne.
PROSCUTOR
Ya juya wajen Alkali
Ya ce haka ne ya mai Shari'a.
ALKALI
Ya jinjina kansa, ya yi rubutu a kan takardar da ke gabansa To daman abin da kotu ke bukata maslaha, kuma halin da ka nuna ya tabbatar da ba za ka iya kula da wannan marainiyar yarinya ba. Don haka kotu za ta tattara dukkan hakkin yarinyar da ke wajen ka, ta sanya su a muhallin da ya dace domin kula da ita bisa adalci da rikon amana.
RAHMA
Ta yi shiru kanta a sunkuye.
TANI
Ta dan zunguri Rahma da kafada.
BARAKA
Alamar farin ciki a fuskarta.
EXT. KOFAR GIDAN SU RAHMA - DAY
Kafinta na kafa signboard mai dauke da tallan sana'ar Rahma.
RAHMA
Na tsaye tana kallon yanda yake aikin
KAFINTA
Ya gama ya sauko, Rahma ta sallame shi ta shiga gida. Ba dadewa wasu mata a mota suka zo wucewa suka hangi signboard din suka tsaya, daya ta fito ta shiga gidan.
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - DAY
Rahma tare da 'yan aikinta tana bayar da umarni/aiki.
MACE I
Ta shigo tayi tambaya a kan abin da ta ke so.
RAHMA
Suka yi tsada da ita.
MACE I
Ta bude jaka ta dauko kudi ta fara kirga ta mikawa Rahma.
KANDE
Ta shigo gidan ta dawo daga sayayya.
HAFSAT I
Ta tashi da gudu taje daki ta dauko raciept ta kawo.
RAHMA
Ta karba ta rubuta ta baiwa matar. Suka yi sallama ta fita.
INT. GIDAN SU RAHMA (CIKIN DAKI) - DAY
HAFSAT I
Ta yi rub da ciki tana rubutu a kan littafi.
RAHMA
Ta shigo ta cire mayafinta ta dora/rataye ta dauki wata riga ta fita.
HAFSAT II
(18) Ta yi ringingine tana nazarin wani littafi.
RAHMA
Ta sake shigowa ta umarce ta taje ta yiwo alwala bayan ta nuna mata agogo.
INT. MAKARANTA (CIKIN AJI) - MORNING
MALAMI II
Yana rubutu a kan allo ya gama ya juyo yayi tambaya Dalibai su ka yi shiru kafin wani Yaro II da Hafsat II su daga hannu kusan lokaci guda.
MALAMI II (CONT'D)
Ya baiwa yaron dama.
YARO II
Ya mike ya bayar da amsa ba daidai ba, Malami II ya zaunar da shi sannan ya nuna Hafsat II.
HAFSAT II
Ta mike ta yi bayani cikin nutsuwa. Malami II ya fara tafa mata kafin sauran yaran ajin.
INT. BOOK SHOP - DAY
RAHMA
Na sayen littafan karatu na 'yan aji Shidda.
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - MORNING
UWANI
Na yiwa Hafsat II wasan jika da kaka.
Rahma ta shigo sanye da hijabinta da jakar leda ta je ta ajiye.
HAFSAT II
Ta tashi da gudu ta je ta rungume ta, suka dawo tare suka zauna a kan tabarma. Uwani ta tashi ta shiga daki. Hafsat II ta dauko littafinta ta bude.
INT. MAKARANTA (CIKIN AJI) - DAY
Dalibai kowa ya nutsu ana jarrabawa.
HAFSAT II
Ta dukufa tana rubutu.
INT. GIDAN SU RAHMA (CIKIN DAKI) - NIGHT
RAHMA/HAFSAT II
Sun bude kur'ani suna karatu tare. Zuwa wani lokaci.
HAFSAT II
Ta tashi ta na lafila, sannan ta kwanta.
EXT. MAKARANTA (HARABA/NOTICE BOARD) - DAY
Wani malami ya zo ya kafe wata takarda, ya juya ya tafi. A kan takardar sunayen yaran da suka zama na daya da na biyu har zuwa na goma a jarrabawar da a ka yi a gaba dayan jihar. Sunan "HAFSAT FARUK" ne na farko a ka rubuta balo - balo da manyan baki. An tashi, yara sun fito gaba daya. wasu suka nufi notice.
HAFSAT II
Na daga baya a tsaye.
FA'IZA
Ta gani cikin murna ta juya ta kamo hannun Hafsa II. Nan da nan sauran yaran suka rungume Hafsat II.
HAFSAT II
Ta kwace da kyar, ta runtuma a guje ta nufi gida.
INT. GIDAN SU RAHMA (TSAKAR GIDA) - DAY
RAHMA
Na fitowa daga daki za ta fita.
HAFSAT II
Ta shigo a guje.
Umma! Umma.
RAHMA
Lafiya?
HAFSAT II
Ta je ta rungume ta.
Umma jarrabawar da muka yi, na zo ta daya a duk fadin jihar nan.
RAHMA
Ta dan banbare ta daga jikinta tana kallonta Hafsat! Hafsat!! Hafsat!!!
HAFSAT II
Ta kalli Rahma tana murmushi.
RAHMA
Ta sake rungume ta tana hawaye. Allah na gode maka. Allah kai ne abin godiya.
EXT. MAKARANTA (HARABA) - DAY
Iyayen yara Malaman makaranta da suran jama'ar gari. Dalibai maza da mata kowanne cikin kayan makranta.
HEAD MASTER
Na tsaye a wajen da a ka kebe da yin jawabi. Saboda haka mun gode muku. A yanzu kuma zan kira mai girma shugaban karamar hukuma domin ya bayar da kyautar yabo ga wannan yarinya. Head master ya sauka, Chairman ya hau.
MAI GABATARWA
Hafsat Faruk!
Hafsat II a kusa da Fa'iza ta tashi ta kutso cikin dalibai 'yan uwanta, ta nufi kan munbari.
CHAIRMAN
Rike da kyautar yana murmushi, ya mikawa Hafsat II.
HAFSAT II
Ta dan risna ta karba.
Mutane suka rude da tafi.
RAHMA
Cikin murmushi wasu hawaye na bin kuncinta.
BARAKA
Cikin murmushi tasa hannu ta sharewa Rahma fuska.
TANI
Ta dan kwanta a jikin Rahma tana dariya.
ASABE
Na daga gefen Tani, cikin murna da murmushi har da tafawa ta mike tsaye.
Mutane suka dan saurara.
MAI GABATARWA
Ya mikawa Hafsat II Microphone.
HAFSAT II
Ta karba da hannun dama, yayin da ta ke rike da kyautar a hannun hagu.
Na godewa Allah wanda ba shi da abokin tarayya. Kuma ina godiya ga dukkannin jama'ar da suka taru anan. Ta dan saurara ta kalli bangaren da su Rahma ke zaune.
HAFSAT II (CONT'D)
Kafin nace komai, ina rokon da mahaifiya ta ta fito filin nan ta tsaya.
RAHMA
Cikin matukar farin ciki ta kalli Baraka.
BARAKA
Tana murmushi ta cicciba Rahma Maza je ki mana.
RAHMA
Ta tashi ta je ta tsaya a kusa da inda Hafsat II ta ke.
HAFSAT II
Ba tare da ta kalli Rahma ba Sannan ina sake godiya ga Allah da kuma mahaifiya ta Rahma, wadda ba dan jajircewarta da taimakonta ba, da yanzu ina tallan gyada ko goro.
ASABE
Cikin sanyin jiki ta sake komawa ta zauna.
RAHMA
Gaba daya kowa ya koma ga duban Rahma.
RAHMA (CONT'D)
Wasu hawaye suka biyo kuncin ta, ta sa hannu ta share.
HAFSAT II
Cikin ladabi ta mikawa Rahma microphone.
RAHMA
Ta karba ta dan yi shiru Da farko nima godiya zan yi ga Allah Madaukakin Sarki tare da duk wanda ke wannan wajen,sannan da kuma malamanta wadanda suka bada da gagarumar gudummawa ga wannan yarinya.
Mutane suka sake tafawa, ta sake share wasu hawayen.
RAHMA (CONT'D)
Sai dai kuma dalilin zubar hawaye na a yau shine, ga Hafsat ta fara kaiwa ga matakin da uwarta da ubanta suka mutu da burin ganin ta kai ba tare da sun shaida wannnan rana ba.
Alhini a fuskar Baraka da Tani da wasu daga cikin mutane.
RAHMA (CONT'D)
Hakika nin gaskiya ba nice na haifi Hafsat ba.
HAFSAT II
Cikin hawaye da tashin hankali ta juyo da sauri ta kalli Rahma.
RAHMA
Ta kalle ta cikin ban tausayi tana hawaye.
INT. A DAKI - NIGHT
RAHMA
Cikin hawaye durkushe a kusa da Maryam.
MARYAM
A kwance cikin halin tsanantar ciwo taja numfashi da kyar. Jinjinniya a shimfide kusa da ita tana bacci.
RAHMA
Sannu Yaya.
MARYAM
Ta amsa da kyar
Rahma, nasan irin zaman da muka yi da ke. Ta yi wata gyatsa. Dan haka ina son koda Allah yasa ban tashi daga ciwon nan ba, ga Hafsat nan amana a hannunki.
RAHMA
Cikin hawaye ta sa hannu ta dauki jinjiniyar ta rungume. Allah ma zai baki lafiya.
MARYAM
Ki rike ta kamar ke kika haife ta, saboda koda Allah ya raya ta, mai yiwuwa ta zama mai amfani ga dukkan al'umma.
RAHMA
Dan Allah Yaya Maryam ki daina tayarmin da hankali.
Maryam ta sake yin gyatsa gami da fara shakuwa.
RAHMA (CONT'D)
Ta yi maza ta ajiye jinjinniyar. Yaya! Yaya Maryam!
Ta kurawa Maryam ido, wasu hawaye suka sake kwaranyowa daga fuskarta.
EXT. MAKARANTA (HARABA) - DAY
RAHMA
Hannun Rahma na karasa share hawayen da ya biyo kuncinta.
ASABE
Cikin hawaye kashirban, tana mai girgiza kanta cikin nadama.
wajen yayi tsit kowa na kallon Rahma da Hafsat II cikin yanayi na tausayi.
RAHMA
Ta yi ajiyar zuciya a hankali. Duk da ban kasance mahaifiyar Hafsat ba, amma ina mai matukar farin ciki da ubangiji Allah ya bani damar kawo Hafsat izuwa wannnan gaci.
Ta kalli wajen da Baraka ta ke
Sannan ina matukar godiya ga 'yar uwar mahaifinta wadda ta jajirce wajen ganin an sanya gadon Hafsat a matsayin da ya dace, dan Hafsat din ta sami amfana daga dukiyar da mahaifinta ya sha wahalar tarawa, dan ganin 'yar sa ta sami ilimin da zai amfane ta da sauran al'umma gaba daya.
Ta sake yin ajiyar zuciya a hankali
A karshe ina fatan al'umma da hukuma za su taimaka wajen kula da marayun yaran da ba su da iyaye, dan inganta rayuwar su da kuma bada tallafin wajen daukar nauyin iliminsu.
Ta mikawa Mai Gabatarwa microphone, cikin tausayawa ta kalli Hafsat II sannan ta juya a hankali tana mai barin wajen tana sake goge fuskarta.
HAFSAT II
Ta na rike da kyautar ta runtumo a guje ta zo ta rungume Rahma suna kuka tare.
FREEZE
END CREDIT

1 comment:

  1. A gaskiya muna yiwa Mal. Baharu jinjina ta musamman da wannan yunkurin. Allah ya kara basira.

    ReplyDelete